Showing 138001 words to 141000 words out of 295847 words
ga sanda aka yi harbin ya sa hannu zai janyo shi wani
bullet din ya sami Zayyan a baya. Jikinsa ya saki duk yadda Col. Nasiruddeen yaso
ko da gawarsa ce ya fitar daga wannan tsinannan gida bukata bata biya ba domin
fadawa yayi baya aka cigaba da harbe harbe.
Col. Nasiruddeen ya sauka ta daya barin yasa gudu yayin da aka duba masu rai cikin
'yan tawaye harda Zayyan aka yi awon gaba dasu.
Taimako daya aka yi musu shi da sauran masu ran an cire musu bullets din jikinsu.
Amma an gwada musu izaya da azaba nau'i daban daban domin su fadi inda sauran suke
abu yaci tura. Sauran uban taurin kai ne yake damunsu shi kuwa Zayyan banda rashin
sanin komai ya dage shi dan Nigeria ne. Da suka ga ya dage sai suka yi bincike akan
unit da yace a cikinsu yake. Tashin farko akace wani mai suna Hadir Murtala ne
kadai ya tsira a cikinsu tare da mutum daya daga wani unit din wato Major
Mustapha.
Abu na ceton rai sauran ma kowa ya fara cewa shima wani ne baya cikin wadannan 'yan
tawaye. Zasu fara dogon bincike aka kaiwa wani babban barikin sojojinsu mummunan
hari wanda ya janyo gabadaya mutanen da aka kama harda 'yan wani kauye da tsautsayi
ya ritsa dasu duka aka maka su a kurkuku.
Da fari Zayyan kusan hauka yayi a wurin. Tunanin iyalinsa yake yi. Mairama da
Alheran da cikinta da yake tsammanin ta riga ta haife shi yanzu. A wane hali suke
koma waye yake duba iyalansa? Yakan dauki tsahon lokaci yana zubar da hawaye masu
zafi da kona zuciya. Uzurinsa na cewa shi ba dan tawaye bane bai karbo ba domin
mutanen da ake kamowa sun hada da magidanta da matasa bisa tsautsayi. Kowa cikinsu
kuma ya dage shima ba dan tawaye bane. Sai ake rasa gane waye mai gaskiya da
makaryaci. Dadin matsakar kasar babu zaman lafiyar da zai bada damar a bata lokaci
wurin sauraren korafinsu. A irin haka sojojin kasashe da dama suke riskar kawunansu
a kurkuku daga zuwa kai dauki ga kasashen da suke cikin rikici.
Sannu a hankali ya karbi kaddararsa da hannu bibbiyu ya fawwalawa Allah lamuransa.
Baya shiga harkar kowa a wurin sai ma shi da akan sami masu shiga tasa. Sai ayi
masa duka bai ko daga yatsa. Rayuwarsa ta kuntata komai ya fice masa a rai. Daga
baya ne ya sake rungumar addini fiye da baya har kusan kowa ya sallama masa hadda
wadanda ba musulman ba kuwa. Zaman lafiyarsa da yanayin mu'amala yasa ya shiga
zukatan jama'ar wurin. Zayyan Muhammad Tureta tun asalinsa mutum ne mai shiga rai
shiyasa a nan din ma ya zama na kowa. Babu wanda zai yi yunkurin taka Zayyan wasu
basu saita masa zama ba.
Col. Nasiruddeen yayi nasarar komawa gida ga iyalinsa. Satinsa guda da komawa yasa
aka binciko masa barikin su Zayyan. Daga can ya sami kwatancen gidan iyayensa. Da
kansa yaje Sakkwato ba sako ba har kofar gidansu. Da yake wahala bata yankewa su
Mairamu ba a wannan lokaci da yasa ayi masa sallama da dan uwan Zayyan ba wanda ya
fito sai Maikudi. Ya ga mutum a fige saboda tsabar wahala sai hanci dan firit.
Yanayinsa gabadaya kama yayi masa da mutanen Nijar yayi zaton aiko shi akayi saboda
basu yarda da bayanin da yayi musu ba. Rufe ido yayi ya maimaita masa cewa Mairama
ta haifi da ba rai, ita da 'yarta kuma sunyi hatsari sun mutu. Col. Nasiruddeen
yaji babu dadi jikinsa yayi mugun sanyi ya koma Jos wurin iyalinsa cike da damuwa.
Zayyan ya rasu a dalilin ceton ransa kuma iyalansa ma duka babu su. A satin yaje ya
kai takardarsa ta barin aiki. A wurinsa rayuwar soja ba tasa bace. Asibiti ya koma
neman aiki sai dai lokuta da dama idan ya ga yawaitar jini musamman idan hatsari ne
jikinsa ya rinka rawa kenan. Likita da tsoron jini aiki bazai taba yiwuwa ba bisa
dole ya hakura ya tsunduma cikin harkar siyasa ka'in da na'in.
***********
SABON SHAFI
[11/2, 6:51 AM] 🏽
🏽 : 33💕
. Asibitin Nasarawa aka tura su Awwab domin samun kwararren likitan ido. Da za'a
basu daki yace dakin mutum daya yake bukata kada a hadata da kowa. Sunyi sa'a kuwa
an samu. Dakin a gyare yake amma duk da haka ya dage sai an sake karkade shi an
wanke toilet. Da ya ga matar zata yi masa gardama wai sai da safe zata sake zuwa ya
bata dubu biyu. Kafin Mama ta iso da su Emzee da 'yan tarkacen bukata na kwana
irinsu bargo da zanin gado an gyara dakin.
Daure idanun Ummi aka yi da farin bandeji likitan yace bazai bude ba sai gobe a
wurin gwajin ido. Budewar idanun lokaci daya da yawaitar haske ne ya janyo mata
wannan ciwon kan saboda haka tana bukatar hutu. Da an sabunta mata glass din ido
komai zai daidaita in sha Allahu.
Emzee fa rai bai so ba. Abinda aka fi gani wurin Radhiya yau sai gashi yana yi.
Zama yayi kusa da ita a kan gadon yana rokonta wai ko dan yaya ta janye daurin idon
ta kalle shi.
"Kayi hakuri mana Zayyanu gobe fa za'a bude mata."
"Nene shikenan sai ta kwana ni bata ganni ba." Yau abin nasa harda turo baki
musamman da Radhiya take masa gwalo.
Ibrahim ya kalli yadda yake yi ya jinjina kai "yau kuma Zayyana ka koma? Ita ce
bakinta kullum a tabe tsabar shagwaba"
"Kai kuma sarkin sa ido ko" inji Mama ta kalli Emzee tana bashi hakuri.
"Ka fita idona Surbajo" ya yi maganar yana nuna shi da dan yatsa.
"Sunan nan ya fita a bakinka fa"
"Kunga ku tashi mu tafi haka nan kafin ku cika mata kunne. Ummi bari mu gudu dare
na kara yi"
Kwanukan da suka bata na abinci Radhiya ta hada zata kai mota Mama tace tayi musu
sai da safe don tare zasu wuce Nene kadai ce zata kwana.
"Wayyo Mama nidai ki barni"
"Shagwababbun da yawa ashe, ai kuwa sai mun tafi don bazan bari ki zauna ki dameta
ba"
Ibrahim da Emzee suka soma tsokanarta. A bangare daya kuma tasu rigimar su biyu
bata kare ba. Mama dai kada su tayi duka suka fito wurin da ta ajiye motarta. Layin
Awwab ta shiga nema don ya kusa awa daya baya dakin daga zuwa amsa waya.
Ghazalatu ce take kiransa dama shiyasa ya fita daga dakin. Mota ya koma suna waya.
Ta sanar dashi cewa tana tunanin Daddy Haroun yau ya yiwa Alh Baba zancensu don ta
ga ya tambayeta da safe. Hira yake da ita babu wannan irin dokin da yake ji akan
Radhiya da ya hadu da ita kwanaki kadan da suka wuce. Har ga Allah sai yake jin
babu dadi saboda baya son zama maci amana kuma baya son wulakanta kanwarsa. Biye
mata yayi suna hirar kawai don ya faranta mata.
Wayar Mama da take ta shigo masa yace mata yana zuwa ya amsa kiran.
"Awwab ina kayi parking ne? Ka taho mu tafi gida don nasan bazaka gane hanya ba.
Nima ba don Ibrahim ba bata zanyi"
"To Mama gani nan"
Zagayawa yayi inda suke Ibrahim da Emzee suna rige rigen shiga tasa motar saboda
rigimarsu ta dazu tace Radhiya taje ta shiga su bisu a baya. Ibrahim da Emzee su
shiga tata.
"Amma Mama ba mune maza ba sai mu bishi ki tafi da ita" cewar Ibrahim suna hada ido
da Emzee suna dariyar shakiyanci.
"Ita tasan hanyar ne? Ko mu biyu kuke son mu bata?"
"Sai ku biyo mu a baya. Amma a haka kamar kinfi son ta bishi"
Ganin idon Mama kadai ya hana Radhiya kaiwa Emzee duka. Kunya ce ta kama ta sosai.
Allah Ya taimaketa Mama ta kama kunnuwansu shi da Ibrahim ta gwara musu kai sannan
tace su wuce itama tana murmushi.
Kwandon kayan abincin da ta dauko Awwab ya karba ya ajiye a baya sannan ya bude
mata gaban. Ibrahim da Emzee kamar ba fada suke ba suka sake kwashewa da dariya
harda tafawa.
"Shakiyai Allah Ya shirya min ku" Mama tace kawai tana tada mota.
Radhiya a kunyace ta shiga motar duk da cewa dazu tare suka zo a hakan daga Sumaila
amma da Nene da Ummi. Yanzu kuwa su kadai duk bakin ma sai ya mutu. Bangaren
window ta karkata gabadayanta tana kallon waje.
Yatsantsa ya kada mata ta juyo amma taki kallonsa "tunanin me kike yi?"
"Babu komai"
"To in baki abin da zaki je kiyi tunani a kai?"
Da ka ta amsa masa yace "baki da wani course da kike sha'awar karantawa?"
"Duk ban sansu ba, soja kawai na sani"
"Sojan ma ai yana karatu"
"Training din kuma ayi yaushe? Na zata fada kawai ake koya musu da harbin bindiga"
"Sai kace wasu 'yan ta'adda? Kinga kamar Daddy da yayi soja amma computer engineer
ne."
Dena kallon wajen tayi ta gyara zamanta yana mata bayani yadda zata gane.
"Kin dami mutane da son zama soja bayan baki san komai akansu ba"
Baiyi tsammani ba kawai yaji tace "Hamma ka zaba min wanda kake so in karanta"
Kallonta da ya tsaya yi saura kiris motar Mama ta bace masa "kina son mass comm.?"
"Na 'yan jarida?"
"Yes"
Zata bashi amsa wayarsa ta hau ruri. Da yake a kusa da giya ya ajiyeta idonta ya
kai inda hasken yake ta ga ansa My G. Wani irin abu taji ya soki zuciyarta ta dauke
kai da sauri ta koma kallon waje. Awwab sai yaji gabadaya hankalinsa ya tashi. Wai
haka ake yi da mata biyu dama? Shi tun kafin yayi auren kowacce yana kokarin ya ga
ya kawar da abinda zai tuna mata da 'yar uwarta saboda alamun kishi da yake ganin
suna dashi su duka. Wannan shine dauko ruwan dafa kai. Bai taba tunanin hada
girlfriends biyu ba ma a lokaci daya balle mata. Shi irin mutanen nan ne da rigima
ta taho ta hagu sai yabi dama babu karkace hanya. Duk abinda zai tada masa da
hankali gudunsa yake. Shi kadai yake kwankwasar kansa da cewa sai ya jajirce ne fa
komai zai tafi daidai. Yadda Alheran tasan ba ita kadai bace yana komawa Katsina
gobe Ghazalatu ma zata sani. Kai iyayensa ma zasu sani don ya fara ji a ransa
wannan shekarar da ya diba ko kadan bazai iya jira ba. Zamanta yanzu cikin motar ba
karamin jinsa yake a ransa ba. Kiran ya katse wani ya sake shigowa ya dauka yace
mata tuki yake zai kira idan ya tsaya.
Radhiya kuwa sai juya sunan take a ranta wai My G. Lokacin da ya gabatar mata da
ita tun farko da haka ya ambaceta amma yanzu tafi jin abin a ranta. Har ya gama
wayar bata kalle shi ba. Tunawa tayi da wayar da ya bata wadda bata samu nutsuwar
dubawa ba ta dauko a hankali harda karewa da hijab don kada ya ga me take yi ta
budo wurin sunaye. Suna daya tal ta gani a cikin contacts din. Hamma. To saura
fatan akwai kudin kira. Satar kallonsa tayi idanunsa akan titi yana tunanin yadda
zata kaya masa gobe a Katsina yaji waya ta sake kara. Ko kalla baiyi ba tunda yace
zai kira yafi so ta kyale shi ya kira din.
Kamar ba wadda ranta yake a bace ba Radhiya tace cikin karamar murya "Hamma ana
maka waya"
"Bari kawai zan kira idan na tsaya"
So take ta ga da wane suna yayi saving number dinta. Ko bai ma saka sunan ba. Gashi
ya tura wayar a aljihu.
Da ta katse sai ta sake kira "Hamma ka dauka mana"
"Yadda kika bata rai dazu idan na dauka kila kuka zaki yi min" yace daidai lokacin
da Emzee yake bude gate Mama tana shigar da motarta Ibrahim kuma ya shige ciki ya
fadawa kawunsa kanin Baba da ya zauna dashi sun dawo.
Sake kiransa tayi na ukun ta turo baki "ni dai ka duba mana"
Bai taba kawowa ita ke kiran ba ya dauko wayar da saurinta kuwa ta leka. Shi yana
mamakin kiran me take yi masa ita kuma tsabagen bakinciki tana mamakin wannan wane
irin suna ne ya lakaba mata.
"Meye wannan Hamma? Nawa sunan kenan, meye sha...sha me ma?" Ta daga kai tana kara
kallon rubutun wayar kuma ta katse bata gama hada harufan ta karanta ba.
Idanunta taf da kwalla ta dagosu ta zuba masa "sake nuna min nawa sunan" tace kamar
me bashi umarni. Ya kuwa danno sunan nata ya bata wayar.
Kallon sunan ta sake yi ta ma kasa karantawa. Wata uwar harara ta doka masa ta kama
kofar zata fita ya danna lock kafin ta bude.
Dukan kofar ta shiga yi "ka bude min in fita, kuma na fasa soja zanyi, kuma likita
zan aura"
"Allah baki isa ba Awwab ne mijinki"
"Ni na fasa ka bude min" sunan kawai take tunani ranta yana kara baci. Anya ma ba
shashasha yake nufi ba. Kwafa tayi tana jinjina kai.
"Calm down Schatzi, me ya faru?"
Sai ga digon hawaye ya ziraro "nice shazi din? Ni ko? Ni ko?"
Dariya ta bashi yadda ta kwabe fuska da gaske wai ranta ne ya baci. Gyara motar
yayi a cikin gidan suna kallo kowa ya shige ciki ya sake tambayarta ta fada masa
laifinsa.
"To ba kaine..."
"Me nayi ni Hamman Alheran sarkin laifi"
Sai kuma taji nauyi amma dai dole ta fada ayita ta kare. Bazata yarda kawai don ita
tana da hakuri ba a cewarta kuma yayi mata haka tun yanzu ba.
"Ita da ta kiraka ba my G ka saka mata ba...."
Ido ya lumshe yana dariyar kuruciyarta "shine kika kira ki ga me na saka miki?"
"Eh, kuma kiran yayi min amfani gashi ni nawa sunan ko ma'ana babu. Mu sake gani ma
don na kasa karantawa"
"Schatzi" yace da wata irin siga da ta sauke mata tarkacen rigimar da ta debo ba
shiri. Idanunta yake nema su hada da nasa taki dagawa "Schatzi yana nufin sweetie
in german." Cusa kanta kawai tayi a tsakanin cinyoyinta saboda tsabar kunyar da ta
dirar mata. Tana ji yana tambayarta "Idan kuma ba kya so sai na koma kiranki my A.
Bari na chanja miki" ya fara danna wayar.
"Don Allah ka bari"
"Kina so?"
Ta wani rufe fuska tana dariya ya kada kai ya bude motar suka fito tare. A daidai
bakin kofa zasu shiga ciki yace "rigimammiyar Awwab". Da dan gudu ta shige ciki ta
barshi a nan yana jin kamar an bashi dukkan farincikin duniya.
**********
Washegari Awwab bai bar Kano ba sai da ya tabbatar an gama komai na gwajin da za'a
yiwa Ummi. Ko kwandala basu biya ba shi yayi komai. Ummi da Nene sai addu'a kawai
suke masa yayin da Radhiya take jin sonsa yana kara shigarta. Duk wanda zai mutunta
maka iyaye hakika masoyi ne na kwarai.
Ya fito daga dakin zasu raka shi bakin mota Emzee ya kawo mata wayar Ummi "Kawu
Zakari ne yake son magana dake"
Murmushi ta saki ta mika hannu zata karbi wayar "Allah Sarki Kawu Zakari kwana
biyu"
Yadda Awwab ya juyo da sauri Emzee sai da yaja baya ya fasa bata wayar.
"Ba ka gaisa dashi ba?"
"Eh mun gaisa"
"To kace tana gaishe shi, ke kuma muje ki rakani"
Sumsum ta wuce Emzee ya yi murmushi. Hamma yana burge shi kuma ya tabbatar da gaske
yake son 'yar uwarsa shiyasa yake kara ganin girmansa. Mutum biyu ne damuwarsa a
duniya, daga Ummi sai Adda Radhiya. Farincikinsa shine ya gansu cikin farinciki da
kwanciyar hankali. A dole yayi masa karyar bata kusa. Yace to babu matsala gobe
suna tafe duba Ummi dasu Innawuro.
Saboda tsokana Emzee sai ya daga murya yadda zasu ji "Adda yace zaku hadu gobe zasu
so duba Ummi"
Tsayuwa Awwab yayi ya juya zai yanka masa magana tuni Emzee ya bace yana ta dariya.
Hararar sai ta koma kan Radhiya ta dan ja da baya.
"Ni kuma me nayi?"
" 'Yar karamarki dake yarinyar nan kina da crush. Allah Yasa yazo kije kina masa
murmushi zan sani ne"
"Shi kuma meye crush din?"
"Ko mutum baiyi niyya ba sai kin sashi dariya" yace yana murmushi.
"Crush din wani ne?"
"Yana nufin wani ya rinka burgeki kiji inama zai zama masoyinki"
Sai da tayi dariya tace ko kishi yake yi ya amsa mata da cewa "sosai ma kuwa, Allah
Schatzi kada na tafi ki fara kula likitocin asibitin nan. Gabana ya soma faduwa
kada suyi min kwace"
Wata dariyar take yana kallon fuskarta yana jindadi. Komai na Radhiya abin so ne a
gareshi. Da kyar ya iya jan motar ya tafi tana ta daga masa hannu har ya fita daga
harabar asibitin.
Tunda ya hau hanya bai tsaya ko ina ba sai cikin gidansu. Wata irin gajiya yaji ta
dirar masa ya samu yayi bacci bayan yayi wanka.
**********
[11/2, 7:06 AM] 🏽
🏽 : 34💕
. Gagarumin taro aka hada na 'ya'yan marigariyi Alh Ghousman da jikokinsa manya.
Hankulansu duka a tashe sai maganganu ake yi cikin harshen tamasheq.
Alh Ghoumar da Alh Sidi sune manya a iyaye maza. Hamshakan 'yan kasuwa ne wadanda
noma da kiwon da suka gada a wurin mahaifinsu ya zama tushen arzikinsu. Har ila yau
a cikin taron akwai Ministan yada labarai Alh Issa Bouba miji ga Gwaggon Zayyan
Aghaisha. Tana zaune a kusa da 'yan uwanta tana ta zubar da hawaye.
"Abinda ban gane ba shine a wane dalili wannan yaro Maikudi zai ce mana sun rasu
gabadaya?" Alh Sidi yayi maganar cikin kunar rai. Duk tsayin shekarun nan iyalin
Zayyan suna raye babu wanda ya sani cikinsu. A tunaninsu tsatson Alheran 'yar
uwarsu ya riga ya kare basu da wani ko wata da zasu kalla su dangantata dasu.
"Ba wannan ba ma, ina suka zauna? Me yasa matarsa bata neme mu ba?"
Cikin kuka Gwaggo Aghaisha wadda suke kira Mamme tace da Alh Ghoumar "ka manta
yanzu fa mutumin nan da yace tare suke da Zayyan a filin yaki yace har makancewa
tayi. Kuma yaushe zaka ga laifinta ma. Mune muka san inda take ita bata taba zuwa
Agadez ba."
"Haka ne kuma" yace jiki a sanyaye.
"Duk shekarun nan kila ta yisu ne cikin jin haushinmu. Tana ganin kamar mun rabu da
ita saboda babu idon mijinta a duniya" Mamme ta sake fashewa da kuka.
Ko cikakken rabin awa basuyi ba da yin waya da Major Mustapha wanda yayi musu
bayanin da zai yiwu ta waya. Bayan ya tura a binciko masa inda suke da takaitaccen
bayanin cewa Mairama da 'ya'yanta suna da rai shine suka hadu cikin tashin hankali
da mamakin wannan labari suka kira nambar da ya bayar. Sun dade suna waya inda ya
fada musu abubuwan da suka sami wannan iyali. Basu da dalilin karyata shi tunda
harda hoto ya tura musu domin shaida a lokacin da yace a nemo su.
Sai da hankula suka dan natsa sannan Alh Sidi yace "ina ganin ya kamata mu shirya
muje mu gansu. Yaran mu kawosu su ga 'yan uwa don kada irin haka ta sake faruwa"
Kowa yayi na'am da wannan shawara. To sai kuma batun su waye zasu je. Babu wanda
yake so a barshi a baya. Jirgi suka fara tunanin bi daga baya aka soke saboda zasu
bukaci motocin hawa idan sun je.
"Babu wani abin damuwa tunda zamu daukosu. A sanar da sauran dangi idan yayi muku
nan da kwanaki kadan sai mu shirya duk abinda ya kamata mu tafi"
Sati