Showing 39001 words to 42000 words out of 295847 words

Chapter 14 - Ku Dube Mu by Batul Mamman

Malamijo yayi tsamo dashi yana kallonsu
zuciyarsa ta cika da firgici da ya ga cikin matasan harda masu sanduna. Sandarsu ce
ta fulani da ado baya cika sai da ita, amma da yake ba gaskiya gareshi ba sai ya
manta da wannan al'adar ya luluka tunanin ko dai duka zasu yi masa. Fulatanci suke
ziryan baka jin komai sai sunan Mairama. To shima dai yaren gidansa kenan sai dai
suna taba Hausa sosai.


Gaban Radhiya sai da ya fadi da ta hangosu q ta tabota "Ummi sun kara yawa wallahi
harda sanduna."


A kidime tace "dan gidan wa kika tabo kuma?"


Harda dan guntun hawayenta na tsoro tace "ni da bana fita wa zan taba?"


"Mairama kwantar da hankalinki muje wajen don nan bazai daukemu ba. Ni da su duka
dangin Mairo ne mahaifiyarki"


"Me? Da gaske?" Matsawa tayi daga jikin Radhiya hannuwanta suna neman kofa da sauri
zata fita.


Innawuro jiki ya kama rawa ganin da yadda Mairama ta fita. Radhiya ta kalla hawaye
suna wanke fuskarta.


"Bata gani ne?"


Radhiya tabi bayan Mairama don ta karasa da ita gabansu tana cewa "eh"


"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" ta iya fada tana kuka har wajen suna jin
sautinta.


Duka idanunsu sun koma kan Mairama tana kuka take tambayar Radhiya da ta rike mata
hannu su nawa ne?


Baffa Gide kamar yadda 'ya'yan 'yan uwa suke kiransa ji yayi kamar iska zata daga
shi don tashin hankali da yaji me takw cewa kuma tamkar ya ga Mairo haka kamanin
Mairama suke da na 'yar uwarta. Kyaunta ne yasa Malamijo zabarta da biyan bashi duk
da a lokacin Innawuro ta girme mata kuma itama bata yi aure ba.


Tsakar gidan kamar gidan kallo ya koma. Ga dangin mahaifiyar Mairama ga ahalin
gidan Malamijo kacokan.


Shi Baffa Habubakari kuka yake ma saboda rauninsa yafi na dan uwansa. 'Ya'yansu
jiki yayi sanyi. Basu san Mairo ba don manyan ma suna kanana komai ya faru amma sun
san wannan makauniyar da ta nufosu jininsu ce. Ga dai idanu a bude amma basa ganin
komai.


Sai da suka zo tsakiya Radhiya taja hannunta don su gaishesu tunda ta ga akwai
manya "ummi mu gaishesu"
Emzee sai ya baro gefe shima ya dawo ya durkusa tare da Umminsa da Addarsa.


"Ina wuninku, yaya hanya....Allah sarki ashe baku manta dani ba" shine abinda
Mairama take cewa tana ta waige hagu da dama saboda rashin sanin a ina suke.


Su Radhiya ma gaishe su suka yi bakin Mairama kamar gonar auduga duk da bata san
mutum nawa bane. Ganinsu su ukun nan ya ishi bawa tausayi. Ga uwa mai cike da
kuruciya amma makauniya mai marayu biyu a gabanta. Ga kuma 'ya'yanta tamkar zakuna
suna gadin farincikinsu, jigon rayuwarsu.


Sautin kuka Mairama ta fara ji daga yawancin matan da suke wurin ta rinka murmushi
tana jiran taji wani cikinsu ya tabata taji dumin uwa. Kamar Innawuro ta sani ta
durkusa a gabanta ta rungumeta suna sakin kuka a tare.


Ardo Barkindo ya kalli Malamijo ya fito a tsolon rakensa yace "a bamu wuri mu zauna
ko"


Sai kuma ya farga ya dawo daga duniyar tunani "kai, kai ina kuke ne, ga baki a
shimfada musu tabarmi daga jikin bangon can yafi inuwa."


Tabarmin aka kawo suka zazzauna ya sake dubansu "wace mai girki ne a kawo musu
abinci"


Hajjo sarkin bakar magana ta tabe baki "Binta ce kuma yanzu ka dankara mata saki ko
a kirawo ta ne?"


Kunya tamkar wanda aka watsawa ruwan kankara haka Malamijo yaji ya muzanta a gaban
mutanen da ya taba wulakantawa yau suka taru suka yi masa kwarjini.


Allah Ya taimake shi Yadikko ta dawo yace "Uhmm, uhmmm....Yadikko fito da kwanuka
aje gidan Tsahare ayi musu hadin wake da shinkafa amma da miya za'a siyo da salak.
Idan akwai taliya 'yar gwamnati duka ta bada saboda ya ishesu. Sannan tasa nama a
wadace do Allah"


Yau wace rana Malamijo zaiyi abin kai. Ya zura hannu zai zaro kudi yaji hankalinsa
ya tashi...mutanen nan fa da yawa, anya ba duka rugarsu Gide ya kwaso ba?


Ardo ya dakatar dashi don bai manta bayanan da yaji game da Malamijo ba.


"Kaga Malam Ali ba zama zamuyi ba a kan hanya muke. Ka zauna muyi magana"


A tsorace ya zauna daga gefen Baffa Gide don kallon da yake masa kamar zai wafto
shi ya shiga dukansa ne. Bangaren matan kuwa Mairama sai dai taji wannan ta rike
mata hannu ko an shafa bayanta suna fadin sunayensu.
Da addua ga marigayiya Mairo Ardo ya fara bude zaman nasu sannan ya ari bakin duka
dangin nasu ya baiwa Mairama hakuri akan zumunci da suka yi sakaci dashi. Daga
karshe ya gabatar da bukatarsu da cewa a yau dinnan ba gobe ba suke son daukarta da
'ya'yanta zasu koma da ita wurinsu.


"Don Allah da gaske?" Mairama ta sami kanta da fada cike da farinciki. Bata sansu
ba kuma bata san halayensu ba amma ko don samun nutsuwarta tana so ace gata da
dangin mahaifiyarta.


Matar Baffa Habubakari tace mata "Allah Yasa ki yarda ki bimu"


Ita kuwa me zai hanata yarda idan ba rashin sanin ciwon kai ba. Ardo ya umarci
yaran nasu maza da su je su shigo da kayan da suka zo dasu. Malamijo ya baza ido ya
ga wane shirgin suka kawo sai kukan tumaki ya ratsa kunnensa.


Raguna hudu ne da katoto kuma kosasshen sa guda daya. Kwanduna manya manya guda
biyu cike da kwan zabi, buhun shinkafa daya 'yar gwamnati mai doki sai 'yar hausa
daya da kuma buhun gero shima biyu.


"Tun daga haihuwar Mairama har aurenta, haihuwar jikokinmu da rasuwar mijinta da
muka sami labari babu wani abu daya da muka halarta balle mu bada gudunmawa a
matsayin iyayenta. Mal Ali ga wannan kayan, ba wai sakayya bace sai dai ihsani ne
daga garemu kuma muna godiya a madadin marigayiya Mairo na kula da marainiyar Allah
da kayi" Baffa Gide ya ce sauran suna gyada kai.


Innawuro ta riko hannun Emzee ya zauna a gefenta "ba rabaka zamuyi da ita ba.
Mairama har abada 'yarka ce. Muna so ne dai ta bimu ta sanmu muma mu santa"


Yake Malamijo yake ya rasa dalilin da yasa suka yi masa kwarjini "bama zan hanaku
tafiya da ita ba"


Kasa magana Malamijo yayi sai tarin kunya kamar ya tona rami ya binne kansa. Ba
Mairama ba kadai kaf 'yayansa me zai bugi kirji yace yayi musu. Hajjo sai da ta
magantu taji dadi ta fake da yi musu godiya "Allah Ya saka da alkhairi mungode. Ohh
Malamijo baki sun zo gari -e- gari ko ruwa ba'a basu ba sai karbar kyauta daga
hannunsu. Ke Radhiya tashi muje na tayaku hada kaya yau kakarku ta yanke saka"


Cike da zumudi Radhiya ta mike tana kallon yadda Mairama take ta fara'a a tsakanin
mutane. Idan ma kuruciya tasa bata gane mahimmancin zumunci ba a iya hankalinta ta
sani cewa Umminta tana cikin farinciki. Wannan kuma ya isheta komai.


Yadikko bata hakura ba sai da ta dafa musu dafadukan shinkafa da wake. Babu bama
dai bare kifi amma tayi nata kokarin. Abin kunya ne ace wannan bakin sun zo sun
tafi basu ci komai ba ga nisan hanya. Tasan tsiyar da suka tarar a gidan ita ta
kara tunzura komawarsu a ranar.
Batare da bata lokaci ba suka fito an gama shiri. Wani dan akwati da take ajiyar
mahimman abubuwa kamar khakin Zayyan, wasikarsa da kuma hotuna tace Radhiya ta
tabbata ta dauko. Dariya tayi don ta gama haddace komai na ciki. Hotunan yawanci na
bikin iyayenta ne da na sunanta.


Karfe biyar da kwata sun gama shiga mota. Baffa Gide yana tsaye a gefen mota kusa
da Malamijo suka sake yin musabaha "yanzu da muka dena yawo idan kana nemanmu mun
koma Giade can asalin garinmu amma rugarmu tana daga ciki da dan tafiya daga garin.
Wannan da kake gani mijin Innawuro shine Ardo na biyu bayan kafuwar rugar"


Sallama Mairama tayi da kowa daga ita har su Radhiya ko digon hawaye irin na kewa
dinnan. Rabuwa da Yadikko da Hajjo da kuma sauran 'yan uwa ya dan sa sunji wani iri
to amma fa ko kadan bikin Magaji bazai hana na Magajiya ba.


**********

WAIWAYE....
[02/11 7:29 AM] My 2nd Mtn: 17. "Ahayye nanaye, wallahi mutum ya yi min ba kyalewa
zanyi ba don kaji in gaya maka yaro" tafa hannuwa tayi sannan ta rike kugu tana
girgiza jiki a dole ranta ne a bace.


Abokin fadan nata wani sangamemen yaro ne don shima akwai kuruciya sai girman jiki.

"An fada din" yace sannan ya cigaba da wakar da ta hadasu fada "Malamijo Malamijo
tsolon rake. Ga kwadayi ga rowa yaki yin gaba"


Wani kukan kura Radhiya tayi ta dire a gabansa ta nuna kasa "in ba tsoro ba
dangwali" ta nuna masa kasar wurin. Dabi'arsu kenan 'yan makarantar wadda ta
kasance firamare ta gwamnati idan ka yarda zaku dambace to kowa ya dangwali kasa.
Daga nan sai a kaure karfinka ya kwace ka.


Dukawa yayi zai dangwala ga tsirarun abokansu da basu bar makarantar da wuri ba sun
tsaya kallo. Sai da ta daidaici yayi kasa da fuskar nan kawai ta dauke shi da mari
ta ranta a na kare. Kai tsaye staffroom ta wuce inda malamai suke wurin Umminta.


Tana shiga ta cukwikuye jikin Mairama tana kuka wai su Danmama ne suka dake ta.
Tahowa suka yi Danmama ne a gaba kayansa duk kura saboda faduwar da yayi garin bin
Radhiya. Kofar staffroom din taje ta saka su kneeldown har Radhiya sannan ta nemi
jin ba'asi. Sai aka rasa me fada mata. Duk fitsarar Danmama yasan da kunya dai ya
maimaita wakar a gabanta. Radhiya dama ko me zata yi mata bazata fada ba don kada
ranta ya baci.


Daga bayanta taji wani malami yace "Anti barni dasu kiyi tafiyarki gida. Idan na
gama zanesu zan taho da wannan mai kunnen kashin"


Mairama ta gyara zaman farin gilashinta tayi dan murmushinta da ta saba yanzu da
wuya kake ganin bacin ranta ta koma ta dauko 'yan tarkacenta tayi hanyar fita daga
makarantar don dama an riga an tashi. Daga karkashin wata katuwar bishiyar marke
take hango yara suna 'yan wasanninsu. Idanunta suka sauka akan Emzee yana zaune
yayi shiru yadda ya saba yana jiranta.
"Karami zo mu tafi" tace da dan karfi don ta kula bai ganta ba sai gashi ya taso da
saurinsa.


Kayan hannunta zai karba tace ya barsu su tafi "Ummi ina Adda?"


"Kyale wannan yau ma fada tayi"


Sunyi gaba wasu 'yan ajinsu suka rinka kwalo masa kira suna Emzee sai an dawo hutu.
Wannan suna da Mairama ta hakura da yakar sa dole shine sunan da yabi Muhammad
Zayyan har gida. Mutane kalilan ke kiransa Zayyan ko Karami kamar yadda take fada.
Yace wani malami da suka yi a firamare two ne yake kiransa MZ Tureta. Shikenan abu
na yara ya koma Emzee.


A makaranta kuma gurfane gaban Uncle Idris su Radhiya ne da Danmama. Sai da Mairama
ta tafi Radhiya ta fada masa sunan da suke kiran kakanta dashi. Uncle Idris ya
tabbatar zasu aikata yayi musu bulala biyar biyar mai zafi da dorinarsa ita kuma
biyu ladan biye musu. A waje ta jira shi shima ya dauko kayansa tunda yau take
ranar hutu suka tafi yana mata nasihar fada da maza.


A cikin shekarun da suka gabata rayuwar Mairama sai dai godiyar Allah. Zamanta a
gidan Malamijo tamkar zaman gidan haya ne. Iyakar gaskiyarsa shi nauyi ya masa yawa
fitar da kudi kamar ana mintsininsa ne. Ya kara kudin cefane da kyar da sudin goshi
amma daga nan fa ko me mutum ke bukata mace ko namiji cikin iyalinsa sai dai su
nemawa kansu.


Abu na farko da Mairama ta fara yi shine adana kudaden gadonsu a ranta tana
tanadinsu ne domin karatun yaran a gaba. Sai da ta fuskanci sabulun wanka wannan
idan bazata saya ba sai dai su watsa ruwa kawai ta fara taba kudin. A hankali kudi
suka fara samun gibi dole ta fara neman sana'a. Tashin farko ta saro zobo tunda ta
tsira da firig dinta ta soma yin zobo da lamurje na saidawa. TV da bidiyo da duka
kayan gadonta banda katifar da ta ajiye kusu suke kwana da yaran duka suma saidawa
tayi don ta kara jari. Allah Ya dubi halin da suke ciki ya buda mata kasuwa tana
ciniki sosai.


Salame tana gefe kullum tana yawo tsakanin nan gidan nasu da wurin Ta Madina wadda
da fari ta dauki fushi mai tsanani da ita sakamakon mutuwar aurenta. Har gida suka
tura aka nemo Salisu ko zai maidata yace idan ta sami miji tayi aure shima auren
zaiyi.


Zaman gaba, bakinciki da hassada ta dauka tana yi da Mairama. Kayan dakinta Ta
Madina ta sayar ne ana bin malamai domin karkato hankalin Salisu. Shiya janyo ita
bata da komai gashi jiki ya saba da jindadi an manta wanki, shara da wanke-wanke.


Wahalar gidansu a yanzu har tafi ta da tsanani ko don zawarci suke oho. Hankalin
Mairama yana kan inganta rayuwar 'ya'yanta, na Salame yana kan me zata yi ta kere
Mairama ko ta hanata cigaba. 'Ya'yanta musamman Radhiya sun tsole mata ido. Abu
kadan ne zata yi ta kai mata hannu da duka amma Mairama bata taba tankawa ba.
Lokuta da dama wurin Yadikko suke zama ko Hajjo idan 'yan mutumcin suna kusa.
Wata rana ta gama zobonta da lamurje ta kukkulle a leda santana suna cikin wani
katon baho a nan bakin famfon tsakar gidan inda take aikinta ta tashi ta tafi jawo
ruwa a rijiya zata wanke wurin. Salame tana ta fakonta don dama ta gane yanayin
aikin nata. Idan ta gama kullewa sai ta janyo ruwa ta wanke wurin sannan ta dauka
ta kai firig dinta ta jera. Su kan wuni da wuta amma da wuya ta kwana.


Tafasasshen ruwan zafi Salame ta taho dashi a bokiti tayi daurin kirji kamar mai
niyar shiga wanka sai da tazo daidai bakin bahon da kayan Mairama suke ta sheka
musu ruwan nan. Ledojin dole suka yi laushi sunyi tsamo tsamo babu dadin tabawa.
Salati ta soma yi wai wucewa zata yi ta sirka ruwan wankanta don ta ga kamar famfon
wurin yana diga an kawo ruwa. Mairama ci gaba tayi da diban ruwanta sai da ta ciko
bokiti tana zuwa ta ajiye shi sannan ta cira hannu ta kwashe Salame da mari mai
gigitarwa don tana kallon yadda komai ya faru.


Ihu ta kurma gidan da suke neman abin gani kuwa aka fara fitowa bawa ido abinci.


"Ni kika mara Mairama?"


Rai a bace Mairama tace "ko zaki rama ne?"


"Kan bala'i, billahillazi baki mari banza ba sai na rama"


"Gaki ga kumatun Adda Salame. Na gaji da wannan abubuwan da kika tsira tun kafin
muyi aure har yanzu ana abu daya. Kece dukan min yara, yada min habaici da bakaken
maganganu duk akan me? Me na tsare miki?"


"Dole kice haka mana tunda kin rabani da wanda nake so"


Yadikko na jin haka ta kora yaran gabadaya tace su shiga dakinta. Hajjo ba kunya ta
bisu don jin ba'asi. Salame kasa karasa bayanin tayi don tasan ita ce da jin kunya.
Tabarmar kunya ta nade da hauka wai Mairama tana yi mata gani gani saboda ta fara
rike kudi.


Da daddare da Malamijo ya dawo Yadikko ta bashi shawarar ya raba musu daki mana.


"Babu wadda ta bani ko asi domin ginin gidan saboda haka idan zasu cinye kawunansu
ne ma su cinye bai dameni ba. Wadda taji haushi ta kawo miji tayi aure"


"Idan bazaka rabasu ba ka taimaka ka zame musu uba na kwarai ka kawo karshen wannan
rashin jituwa da yake tsakaninsu. Kafi kowa sanin cewa da ba haka suke ba"


Shu'umar dariya yayi kafin ya turo hularsa gaba ya bata amsa "ki kan bani mamaki
wani lokacin kamar baki san zafin zawarci ba. Kodayake baki taba danawa bane amma
cuta ce mai zaman kanta. Shiyasa kika ga suna harin junansu. Babu mai tayar min
hankali ni dai"
Babu yadda ta iya haka ta tashi ta bar dakin nasa tana kara godewa Allah da bai
bata haihuwa da Malamijo ba.


Mairama ta gama yiwa Karami shirin bacci ta goya shi tana jiran kanwarta ta kawo
Radhiya da take wasa a wurinsu Salame ta shigo ta dawo daga zance da dan gayun
saurayinta. Matashi ne ko auren fari baiyi ba. Baje ledar da ya bata ta tsire tayi
a gefen katifarta da burin cusawa Mairama haushi. Abin dariya yadda take ci tana
shuu da baki.


Tana ganin Radhiya ta sake bude ledar da kyau. Yarinya tace "Ummi nama"


Mairama ta dauko wata leda babba ta mikawa Na'ima kanwarta tace suje su raba sannan
ta dauko wata 'yar madaidaiciya ta bude ta janyo hannun Radhiya ta bata cinyar
gasasshiyar kaza. Sai yanzu take gode Allah da haka nan ta bawa Bature kudi ya siyo
kajin nan guda uku. Ta dauki daya ta basu biyu su raba.


Ai kuwa Salame ta shaka har wuya ta shiga fadin maganganu wai gara su suna kwance
ake basu. Wahalallu kuwa sai sunyi da karfin jikinsu kafin su dandani zakin nama.


Shiru ma magana ce. Mairama bata ce mata komai ba haushi ya kamata tsiren ya fice
mata a rai.


"Dazu nace kin rabani da masoyina baki tambayi ko waye ba bare ki bani hakuri"


"Indai Salisu ne nayi imanin bazai sakeki saboda ni ba. Allah kadai Yasan dalilin
mutuwar aurenki sai kuma ku kanku"


Kallon cikin ido ta yiwa kanwar tata "Mairama, na rigaki ganin Zayyan kuma na
rigaki fara...."


A harzuke Mairama ta tashi duk wani kulli na kanta yana kwancewa. Yanzun ta gama
gano duk abubuwan da Salame tayi mata sunfi kama da kishi. Duk da mijin nata baya
raye amma tana tsananin kishinsa itama.


"Ya isheni ba sai kin karasa ba, na fahimci da aurenki kike son nawa mijin. Idan
abinda Salisu ya gano ya sakeki kenan sai ince Allah Ya dada karawa."


Daga haka bata koma cewa komai ba sai da ta tabbatar Salame tayi bacci ta sha kuka
ta godewa Allah. Ta tabbatar Zayyan ya sani shiyasa shima baya son Salame saboda
kada yaci amanarta. Sabuwar kewarsa ke ratsa duk wani sassa na jikinta tana inama
yana nan tare da ita.


***********
Shekararsu biyu a gida Salame tayi aure. Kafin auren Mairama ta tuna cewa Salisu
abokin Hadir ne a lokacin ta kwantar da kai wurin sau uku tana tambayar Salame
kwatancen gidansu Salisu. Ita kuma ganin ta matsu tasan ko meye yana da mahimmanci
shiyasa taki fada. Gashi baya zuwa garin don idan za'a kawo mata Halifa aiko
drebansa yake likkafa ta kara ci gaba.


Bayan auren Salame ne Idris dan gidan Mal Kallamu abokin Malamijo ya sami aikin
koyarwa a makarantar firamare ta gwamnati ta cikin Sumaila. Da yake suna shiri da
Mairama kamar wasa ya gabatarwa Headmaster da ita akan ko 'yan aji daya ne ta samu
ta rinka koyarwa. Shine ya amince aka yi mata cuku cuku sai gashi ta sami aikin a
karkashin L.E.A. Kwalin karatun nata iyakarsa sakandire shiyasa bata wuce aji daya
ba a koyarwar. Ita dai ko yaya ne hakan yayi mata don albashinta yana mata rana ga
cinikin zobo da lamurje.


Haihuwar Salame daya aurenta ya sake mutuwa. Wannan karon lalaci da rainawa miji ya
janyo mijin ya saketa. Duk abinda zai kawo mata sai ta karba a wulakance tace ba
haka baban Halifa yake yi ba. Sai da ta kaishi makurar da yayi mata duka ya sakota.


To yanzu ma an sake dawowa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login