Showing 201001 words to 204000 words out of 295847 words
zuwa ayi daku"
Yawu mai daci ne ya tokare masa a wuya da yaji me tace. Dan murmushin nasa ya bace
bat. Hajji har mutum shida kamar tana son talauta shi. Bai bata amsa ba yace Emzee
su zo su tafi gidan Talle a fito masa da shanunsa. Radhiya tace to a bata tinkiyar
mara ciki a yanka.
"Indai nama ne muje gonar sha Allah an dena miya lami a gidan Malamijo amma ki sake
shawara akan batun zuwa hajji. Idan ba kaina zan sayar ba dame zan biya kudin"
***********
Safiyar laraba washegarin tahowarsu daga Abuja jiki a sanyaye Ummi ta ajiye wayarta
tana matsar kwalla a boye. Ashe Daada yana kula da ita. Fita tazo yi daga dakin
saboda kukan da ya taho mata ya yi saurin tare hanyar.
"Haba Fillo me zaki boye min? Waye ya rasu kike kuka kuma baki son na sani?"
Kukan gabadaya ya taho mata yana rarrashinta sannan da kyar ta fada masa cewa matar
Badaru ce ta kirata wai yau sadakar uku na rasuwar Mal. Aminu abokin mahaifinsa mai
matsayin uba a gareshi wanda yake ta dokin zuwa ya gani. Jikinsa ne ya saki ya
zauna ya dafe kai.
"Sojana kayi hakuri" tace wata kwallar na taruwa a idonta.
"Waye ya isa yaja da ikon Allah? Zamu iya tafiya a yau ko kin gaji?"
Da sauri ta tashi "muje yau din."
Ba wasu kaya suka baza ba, abinci ma siya sukayi jiya da yau din shiyasa cikin
abinda bai kai minti shabiyar ba sun gama kimtsawa dreban kawai suke jira yaje
siyan mai. A hanyarsu ta zuwa Sakkwaton babu wata hira. Zayyan yaci burin zaman
hira da Mal. Aminu Allah bai nufa ba. Sun isa da sauran haske Ummi ta rinka
kwatantawa dreban Daddy din da ya kawosu. Zayyan ganin garin yayi kamar ba
Sakkwaton da ya sani ba. Kamar sauran wuraren da ya gani nan ma an sami chanji na
fasalin abubuwa da cigaban rayuwa. Karuwar tituna da gine gine yasa bai gane lungun
gidan nasu ba. Har yanzu dai mota bata shiga amma duk da haka wurin ya sauya. Sun
fara tafiya Ummi ta dan dakatar dashi da suka karya kwanar gidan Mal. Aminu
maimakon su mike hanyar gidan nasa iyayen.
"Ko za ka jira na fara zuwa na sanar dasu kada ganinka ya tsorata mutane da yawa."
Bai musa mata ba don yasan gaskiya ta fada. Ita kadai ta karasa kofar gidan daga
gefe an saka rumfa inda maza suke nasu zaman makokin. Kan ta a kasa taji an kira
sunanta "Maman Radhiya kece da yamman nan?"
Rayyanu ne yayan Zayyan wanda yake bi. Gefe ta dan matsa yazo ya sameta suka gaisa.
"Kinje gidan babu kowa ko? Da yake yau za'a rufe zaman makokin duka muna nan"
Ta'aziyya ta fara yi masa kafin cikin nutsuwa ta sanar dashi dawowar Zayyan a
takaice. Ikon Allah kawai ya rinka ambata kafin yace ta shiga ciki zai taho dashi.
Tana kallonsa ya duka yana yiwa Badaru rada kafin ta karasa shiga gidan. A tare
suka nufi hanyar da ta baro da sauri kamar zai tafi kafin su karasa.
Dan uwa dan uwane komai lalacewarsa. Lokacin da yake tare dasu a shekarun da suka
gabata kiyayya, kyara, hassada da bakinciki ne kadai abinda yake gani a idanun 'yan
uwan nasa. Yanzu kuwa kafin su karasa gaban juna daga shi har su hawayen farinciki
suke zubdawa. Dayake dreban Daddy yana da labarin yadda akayi zaton Zayyan ya rasu
da dawowarsa baiyi mamaki ba da ya ga magidanta irinsu rungume da juna suna hawaye.
Hakuri ya rinka basu amma sai da kyar suka iya mallakar kawunansu don ma a waje
suke.
"Muje Jume ta ganka Zayyan." Badaru ya ja hannunsa kamar ya kama yaro.
A ciki kuma bayan yin gaisuwa ga Gwaggo Ladi da 'ya'yanta mata dake wurin Ummi ta
matsa kusa da su Mubaraka da matan su Badaru ta fada musu dawowar Zayyan. Matan
mazan na alhini yayunsa mata suna kuka. Jume ta zaga bayi sai Gwaggo Ladi suka
fadawa. Hankula suka tattara suka koma kofar gida sai suka fara tunanin ko dai su
koma nasu gidan ne tunda nan gidan gaisuwa ne ga matan mutane a zazzaune.
"Ku barni na ganshi kafin ku tafi. Allah bai kaddari haduwarsa da babansa ba ku
bari na gane masa Zayyanu" cewar Gwaggo Ladi.
Sallamar babban dan Mal. Aminu da kannensa maza dasu Badaru ita ta sanya matan kuka
da ganin Zayyan da yake tsakiyarsu. Idonsa a kan Gwaggo Ladi tana dago masa hannu
ya taho gareta. Girma ya kamata sosai tafiya tana wahalar da ita. A gabanta ya
durkusa gidan ya koma tamkar yanzu akayi mutuwar. Daga inda Jume take bayan ta fito
daga bandakin take jiyo koke koke. A tsaye suke ita da wata jikarta ta wurin 'yarta
mace ta saka ta kiran Maikudi a waya. Kare masa tanadi tayi rai a bace har anyi uku
bai zo ba. Yana gidan ma aka aiko da rasuwar yaki fita wai ciwon jiki yake yi. Ya
riga ya sakawa ransa cewa Mal. Aminu makiyinsa ne bai ga dalilin zuwa jana'iza ko
gaisuwa ba. Sai da ta gama fadan ta ajiye wayar ta tako itama din kafafun sai a
hankali.
Kamar ance ta kalli gaban Gwaggo Ladi sai ganin mutum tayi a durkushe gabanta 'yan
uwansa sun kusa rufe shi. Gaba na faduwa da rawar murya tace "wa nake gani kar Mal.
Muhammadu?"
Kama yayi mata sosai da mijinta matar Rayyanu ta kamo hannunta a hankali ta zaunar
a gefen Gwaggo Ladi. Zayyan ya matso yana murmushi da 'yar kwallarsa.
"Jume Zayyanu ne ya dawo"
Idanunta ta shafa harda gogewa da zaninta tayi murmushi mai ciwo "ko dai nima na
mutu ne?"
Sai ta sake tsinkewa jama'a zukata aka cigaba da kuka.
"Jume ni din ne dai Zayyanu ba mutuwa nayi ba"
"Nagode Allah da bakina zan rokeka gafara" tace tana wani irin kuka da take tuna
bakar izayar da ta rinka gana masa tun kuruciya. Maikudi da ya gagareta har yanzu
waye silar lalacewarsa idan ba ita ba.
Basu barta ta cigaba da magana ba suka tattara duka iyalin gidan Marigayi Muhammadu
Tureta suka tafi nasu gidan. Murna a wurin 'yan uwansa da 'ya'yansu da suka sanshi
a matsayin baban su Radhiya ba kadan ba.
"Me zan dafa maka Zayyanu? Ban yarda ka ci abincin kowa ba sai girkina. Kai ku hura
min wutar icce ni ba son girkin risho nake ba"
Zaunar da ita Zayyan yayi yana dariyar yadda ta tashi hankalinta "ki zauna nayi ta
kallonki Jume"
"Har me zaka kalla a jikin matar da taci zalinka ta kasa rike amanar maraya"
Mairamu da kowa ma hawaye suke yi na tausayinsu. Ga su Badaru da suka san yadda
rayuwar gidan nasu ta kasance tun da su ma sai rokonsa gafara suke yi.
"Bana jindadin yadda kuke yi min. Jume ke uwa ce a gareni mai cikakken iko akan
danta. Da dadi da babu dadi kinci kashina kinci fitsarina. Wahalar da nasha ta
kuruciya ita ta samar da Zayyan din da yake gabanki mai hakuri da juriya" ya juya
ga 'yan uwansa "idan kuna biye mata za ku tabbatar min da cewa ni din dan uba ne
kawai baku daukeni kaninku ba"
Kalamansa sunyiwa Jume dadi haka ma yayunsa. Tashi tayi da sauri tayi hanyar
bangaren Maikudi. Yadda baije gidan gaisuwa ba haka ya hana matarsa da 'ya'ya suna
zaune kowa rai a bace amma basu da yadda zasuyi dashi. Matarsa har tafi jindadin
lokacin da aka tsareshi su ka sakata suka wataya son rai a gidan. Yana daga uwar
dakinsa a kwance ya bararraje matarsa tana yi masa tausa. Daga bakin kofa take ta
kwala masa kira ya taso a fusace.
"Jume ya haka zaki zo min har kofar daki. Wannan ai rashin tunani ne, waye yake
zuwa kofar dakin mai aure. Gaisuwa ce dai nace bazanje ba ko ana dole ne inji"
"Ba wanan ya kawoni ba Maikudi kazo ga dan uwanka ya dawo"
Da yana da kudi bai ga dalilin da zaisa shi zaman gidan nan ba. Ya tsani ya farka
ya ga kowa cikinsu saboda babu mai kaunarsa. Haka ya karaci zamansa da shan wahala
a rufe sai sun bushi iska suke lekawa.
Zayyan da sauran suna jiyo yadda yake daga mata murya shiyasa ya tashi yabi
bayanta.
"Ko ma waye dan uwan bai san inda nake bane da bazai karaso ya gaisheni ba sai kin
taso da kanki? Wato gani matsiyaci nine zan fito gaida irin mutanen da kuke yiwa
maula ke da su Badaru....."
Numfashinsa ne ya nemi daukewa a lokacin da Zayyan ya bullo tsakar gidansa inda ya
tsare kofa ya hana Jume wucewa sai ma kukan bakinciki da take yi.
Zayyan yana shigowa bai tsaya ko ina ba sai a gabansa ya cire hannu ya kwada masa
mari. Bude baki yayi yana neman hada kalma ko daya ce ya fada Zayyan ya kara masa
wani. Marinsa ya rinka yi hagu da dama kumatunsa ya dauki radadi kamar garwashin
wuta a take. Idanunsa a rufe suke da takaicin halin Maikudi. Banda bakincikin da
yake ji na muguntar da ya yiwa iyalinsa kuma shine ya kara masa da rashin da'ar da
yake yiwa Jume. Mahaifiyar da duk abinda tayi a baya mai kyau ko akasinsa tayi ne
domin farincikin 'ya'yanta. Shi fa babu abinda zai dorar game da uwa sai labari.
Wane irin farinciki zaiyi da za'a bashi damar kasancewa da tasa uwar ko da na rana
daya ne. Shi wanda ya sami damar yana takewa ta hanyar cusa mata bacin rai.
Marin karshe da ya kai masa sai da bakinsa ya fashe. Mairama na ganin haka ta kama
hannunsa "ya isa haka Sojana ban sanka da fushi ba, kamata mu koma dakinta"
Rungumo Jume yayi a jikinsa suka bar wurin bayan wani mugun kallo da ya yiwa
Maikudin.
Sawu na daukewa Maikudi ya kwalla kara yana riko matarsa ta zaro idanu a tsorace
kada ya huce a kanta "kin ga abinda na gani yanzu? Kema kin ga fatalwar Zayyan?"
"Ni banga kowa ba" tace cikin halin ko in kula sai ma murnar marin da ya sha da
take ganin rama mata akayi.
Kansa yaji yayi nauyi yasa hannu ya shafi jinin bakinsa ya tabbatar fa gaske an
mare shi din ya fito zuwa dakin Jume. A zaune ya ga Zayyan din yana bata baki akan
tayi hakuri da abinda Maikudi yayi mata.
Buguzum buguzum haka ya shiga dakin babu sallama ya sa hannu a kafadar Zayyan don
ya tabbatar cewa mutum ne da gaske. Yadda idanun Zayyan din suka yi lokacin da ya
dago kansa ya sa Maikudi yin baya da sauri jikinsa na bari.
"Baka mutu ba?"
"Ba haka kaso ba ko? Yadda ka tsara shine na mutu matata ta haifi da ba rai ita da
'yata suyi hatsari su mutu su ma kaci dukiyar da zata zame maka wuta ranar lahira"
Da borin kunyarsa ya kalli Mairama "sannu munaf...."
"MAIKUDI!!!" Zayyan ya daka masa tsawar da hatta Mairama sai da ta razana. Da dan
allinsa ya nuna shi yana kada masa shi a gaban fuska "ko da wasa kada ka sake
yunkurin yiwa matata magana balle kuma ka hadata da kalamai na batanci. Kai ba ita
da Jume ba wani ma a gidan idan ya sake kuka da kai wallahi sai kayi mamakina. Abu
na karshe daga yau har na bar gidannan kada ka bari ko inuwarka ce na sake ganin
gilmawarta a gabana. Get out"
"Ni da gidan ubana kai ka isa kayi min turanci. Ba tsoronka nake ji ba" yace daga
bakin kofa yana sauri kada Zayyan din ya biyo shi. Babu wanda ya sake saka shi a
lissafi. Jume duk yadda yaso hanata da kanta tayi masa tuwon alkama da miyar
karkashi akan wutar murhu. Zaman hira kuwa an raba dare ne ana bashi labarin
abubuwan da suka faru bayan tafiyarsa shima kuma ya fada musu nasa.
**********
Numfarfashi kawai Malamijo yake saki yana daga kwance a dakinsa ko zama baya iyawa
sai an tada shi. Ga mutane cikin 'ya'yansa da jikoki ana ta yi masa sannu. Sallamar
Nene Marka tare da Radhiya su ka shigo dakin. Ba arziki ya tashi yana nuna Radhiya.
Ba don kada a raina shi ba kuka zaiyi ko yaji sassauci a ransa "Wai da gaske so
kike ki karasa ni ne? Dame kike so naji? Shanuna, shanuna shegen yaron nan Talle ya
gudu dasu sannan kin kawo Marka wato tazo in biya musu kudin Hajji da yawun bakina
ko"
Murmushi Radhiya tayi har ranta tana tausayinsa tace "duba ka tazo yi...ku taso mu
basu wuri ko" Tace da su Emzee. Murmushi yayi yayar tasa ta fara daukan haske ta
gane inda ya kamata ta rinka tashi musamman idan manya ne zasuyi magana. Nene Marka
ma ta kalli bayanta har ta saki labulen da suka gama fita tayi dan murmushi.
Radhiya fa tana da hankali idan aka tabota ne kawai bata da dadi. Daure fuska tayi
lokaci guda tana kallon yayanta.
"Ali" tace da kaushin murya.
"Alin ma kai tsaye Marka, wato tunda na soma talaucewa an sace min shanu ga kaji
ance suna murar tsuntsaye shine dan girman da kike bani ya kau. Kada ki manta dai
sunan Malam ne kakanmu ehe. Idan kin kirani Ali kamar kin kira sunan Malam ne babu
kara"
"Kaga dakata min ba wannan ya kawoni ba. Zumunci nazo yi zan duba ka nayi maka
nasiha ta karshe don babu lallai na cigaba da hakurin zuwa gidanka"
Jikinsa ne yayi sanyi kuma. Gidansu ita kadai ce mai hakurin zumunci dashi sauran
har wadanda ya hada uwa dasu sai abu ya kure suke zuwa. Ita kuwa 'yan dakinsu har
gori suke yi mata wai tasa kwadayin abin hannunsa a rai shiyasa take like masa.
Gashi dai shine babba amma sai aci a cinye a gidajen sauran babu shi babu 'ya'yansa
saboda kawai kada ace yayi gudunmawa.
"Yanzu kuma me nayi?"
"Meye ma baka yi ba? Dubi yadda ka koma sai mokadewa kake yi kamar ragowar yunwa.
Ni dinnan da bana takama da komai sai dan rufin asirin da Allah Ya yiwa mijina, ba
da ba jika na fika kyaun gani da cika ido"
"Ku mata dama banda ci me kuka iya?"
Gyara zama tayi bata sake magana ba har yarinyar da ta kawo mata ruwa ta fita
sannan ta cigaba "Malamijo wallahi ka guji haduwarka da Allah akan yadda kake
rayuwa"
"To, tohhh zaki fara ko. Idan kina abu sai kace kin saki nono ne Hajjo ta kama.
Kuyi ta zakulowa mutane laifuka kawai don a rubuta min zunubi to dai kowa mugun
fatanta a kanta zai kare"
Girgiza kai tayi cike da takaici "kaga irin halin naka...ni ka saurareni don banzo
da shirin kwana ba." Sassauta murya tayi ta kafe shi da ido don yasan zancen nata
babu wasa a ciki.
"Malamijo ina tsammanin ko rantsuwa zanyi babu kaffara a kaina cewa duk garin nan
babu mai arzikinka. Tunda Baffanmu ya raba mana shanu tun yana raye ba'a shekara
biyu ba naka suka ninka abinda ya bamu. Ni ko wuka aka saka min a wuya bana ce ga
abinda na tsinana da nawa ba. Amma kai kam ka sami albarkar kiwo. Nafi shekara
arba'in a gidan miji ban taba batan wata ba sai gashi kai da kayi naka bayan ni
yanzu a lissafina mutum talatin da daya ne naka masu rai banda biyar da suka rasu
da masu bari"
"Hakkun" ya gyada kai maganar ta soma samun shigarsa.
"Wadannan 'ya'ya amanar Allah ne kuma kai dai kaci wannan amana. Ko kadan baka
rikesu yadda musulunci ya tanada ba. Rashin wadatasu da abincin kirki ba shi yafi
damuna ba kamar sakaci da zumuncinsu. Yawansu na banza ne saboda babu wanda ya damu
da dan uwansa. Ka ga duk iskancin Salame....."
"Kyale wannan mara mutumcin ko ni kaza ta fini mutumci a idanunta"
"Kaga matsalar ai kayi ta aibatasu. Salame ko tana da mugun hali da sa hannunka a
kara lalacewarta. Duk yadda duniya take wasan gare gare da ita a gidan miji bai sa
tayi hankali ba har yau. Yadda ka banzatar dasu haka ta fita harkar Halifa da
Rahima. Albarkacin kudin uban Halifa yanzu take jansa. Amma Rahima fa?"
Langabe kai yayi "ko a waje muka hadu bazan shaidata ba wannan"
"Shikenan so kake idan kasa ta rufe idanunka sun gama zumunci kenan sai a lahira
idan an hadu a filin hisabi?"
"Kai Markajo ni dai fadi me kike so nayi duk kinbi kin tsorata ni. Kina kallo ba
lafiya gareni ba."
"Ka hada kan zuri'arka. Kafin ka bar duniya ka dinke barakar dake tsakaninsu. Banda
Mairama da Ayuba babu wanda yake nuna damuwarsa a kanka. Abu na biyu yau ka gani da
kaki sharar masallaci ai kayi ta kasuwa. Wata can da bata da gadonka ta kwaso
iyalinta suka tagayyara ka sai jikoki suka kwaceka. Da gidan nan a hade yake
wadancan zaratan samain yaran naka ba ubanta zasu ci ba ta koma inda ta fito daren
da ta tare. Wai ma shin auren bai isheka ba. Kayi lukuta, siririya, fara da baka,
mai kyau da mummuna. Babu kalar da baka taba ajiyewa ba amma kaine har yau aure
kake"
Jikin Malamijo yayi mugun sanyi domin kuwa ya soma ganin ishara. Marka ce kadai ya
tabbatar zata fada masa gaskiya batare da sanya son zuciya ba. Ko Radhiya sai da ta
hado da cewa a kai wasu hajji sai kace zuwa Zaria ne abin.
"Nagode Marka kuma sha Allahu kafin ki tafi zaki ga sauyi. Taron hadin kai zanyi a
gidan nan Mairama tana dawowa daga Nijar"
Sai yanzu tayi murmushi "ya dai kamata, ai Radhiya ta fada min dawowar baban nasu
da alkawarin zasu zo min."
Hirar zumunci suka yi sosai tana ta bashi shawarwari. Rokonta yayi ta taimaka taje
masa bikon Hajjo kafin ya shawo kan Yadikko.
"Wani hanzari ba gudu ba Malamijo" Nene Marka tace kafin ta tashi "ka kira Salame
kayi mata jan ido irin na uba mahaifi wanda ya isa da gidansa . Ita ce fa babba a
gidan nan"
"Ina jin fa kanta ya kwance wannan. Jiya ta bani mamaki wai sai gata. Nayi zaton
dubiya tazo yarinyar nan sai cewa tayi wai tayi magana da wani Malami suna tantamar
ingancin auren Mairama da Zayyan. Wai yace mata shekara hudun farko da basa tare
matsayin saki daya ne, ta biyi kuma saki biyu ta uku saki uku. A takaice dai wai na
rabasu a barshi ya nemi wata itama ta sami daidai ita. Ni dai kaina daurewa yayi
sosai nace Salame ko ta fara hauka ne"
Nene Marka bata taba niyar fallasa maganar son da Salame take yiwa Zayyan ba amma
jin wannan magana ranta in yayi dubu to ya baci. Da za ta ga Salame yanzu wallahi
sai ta mareta. Nan take ta warwarewa Malamijo wannan batu da kuma kakkarfan zargin
da take na cewa ita ta makanta kanwarta Mairama tsahon shekaru goma saboda ta auri
Alh Indararo.
A kidime ya tashi zaune sosai "Kin gane min 'yar jakar uba"
"Shiyasa nace ka hade min kan yaran nan"
Kan Emzee wata irin sarawa yayi da jin wannan mummunan labari. Kawunsa Ayuba ne
yazo da abokansa malamai shine ya turo shi yi musu iso wurin Malamijo kafin ya gama
yiwa tagwayen kannensa addu'a.
Kai tsaye Emzee ya shiga dakin cikin bacin ran da bai taba yin makamancinsa ba.
Jijiyoyin kansa sun tashi idanu sunyi ja.
"Nene" yace da wani irin yanayi mai ciwo.
Hankalinta da na Malamijo a tashe ta dafa shi "Zayyan don Allah ka bar maganar nan
inda ka ji ta. Zancen makarantar kuma