Showing 216001 words to 219000 words out of 295847 words
masu fruits. A tunaninta wani abu zai saya amma
kowa yazo tambayarsa me za'a kawo sai yace babu komai. Wurin minti shabiyar Zayyana
ta gaji da dukar da kan nata ta dago a hankali tace "washh" saboda kagewar da yayi.
"Da baki dago ba nan zamuyi ta zama" yace yana tayar da motar.
"Me yasa" ta tambaye shi murya kasa tana faman shafa wuyanta.
Maimakon ya amsa sai cewa yayi "Rinka juya shi hagu da dama zaifi saurin sakewa"
A hankali ta dago kai su ka hada ido. Wata irin faduwar gaba taji tamkar yau ta
fara ganin Ibrahim din ba shiri ta kawar da kanta. Bai sake mata magana ba sai da
ya rage tafiyar tasu saura kadan.
"Zayyanatu"
Babu inda bai amsa kiran nan ba a jikinta sai bakinta da ta kasa motsawa.
"Nasan kinji abinda naji yanzu kafin ki koma kallon titi haka ne?" Baiyi tsammanin
jin amsarta ba ya cigaba da kallon gabansa "my feelings are true idan na sami
karbuwa ina fatan kare rayuwata Zayyana Mustapha tana tale min baki idan tana jin
shagwaba. Abu daya ne bana so....dena yi min magana da kike yi"
Cusa kanta tayi kawai a tsakanin cinyoyinta gabanta na tsananta bugu ba ita ta sake
dagowa ba har aka bude gate din gidan suka shiga.
A raunane Ibrahim ya dakatar da ita da zata fita "please Zayyana kice wani abu".
Saboda yadda yake jinta a ransa idan taki amincewa bai san ina zai saka kansa ba.
A guje ta fice batare da tayi magana ba. Tana shiga gidan tayi sama da gudu dakin
Radhiya ta kankameta tana murna. Lokacin ko awa daya basuyi da isowa ba Rahima tana
wanka.
"Kalau kike kuwa?"
Dariya tayi "Ras ras Adda" yau anya ma zata iya bacci kuwa take kissimawa a ranta.
Gani take kamar ba gaske ba. Wai sai da yayi maganar take ji a ranta tamkar ta
shekara da soyayyarsa sai yanzu ta farga. Wayarta ce tayi kara ta kasa dauka da ta
ga shine sai rawa da jikinta yake yi ta saka a silent ta fice daga dakin zuwa wurin
Ummi. A can tayi zamanta daga baya suka sauka kasa tare Ummi na son dora girki
kafin Daada ya dawo tunda bata da mai aiki yanzu dai suke neman ko da mai shara ce
ita zata cigaba da girkinta.
Ibrahim suka tarar a falon ya kunna tv amma hankalinsa baya wurin. Kamar ta koma
Ummi ta gama amsa gaisuwarta ta turata kitchen ta samo masa abin sha. Tana tafiya
Radhiya da Rahima suka sauko daidai fitowarta daga kitchen Radhiya tana dariyar
shakiyanci ta mika mata wayarta.
"Gashi nan kin barta a daki wani Khaleel yana ta kira"
Da sauri ta karbe tayi sama sauran kadan ta fadi Ummi ta bita da kallon tuhuma.
Ibrahim ne ya hade rai ya cika yayi fam wato tana da wani Khaleel shine taki amsa
masa dazu. Ummi ce tace ya hau sama dakinta su gaisa da Innuwuro don tace ita da
saukowa sai da safe saboda ba ta kaunar hawa bene.
Saman ya hau ya sami Zayyana a falo tana ta kai kawo da waya a hannu. Karbe wayar
yayi ran nan a bace ya ga akwai lock ya mika mata.
"Bude min"
Budewar tayi ya sake karba da sauri ya nemo sunan Khaleel din ya kira a fusace yana
jira a dauka ya fara fada sai wayarsa ta soma ringing. Guntun tsaki yayi saboda
Khaleel din yaki dauka ga wayarsa ta dame shi da ruri.
"Ana yi maka waya" Zayyana tace tana kallonsa a kunyace
"Babu ruwanki....shi Khaleel din baya daukar waya ne?"
"Nima ban sani ba"
Kira yayi na uku can ba'a dauka ba tasa wayar kuma anki hakura. Yana zaro ta daga
aljihu Zayyana ta karbe da sauri ta daga tasa a kunne idanunta a kansa.
"Ya Khaleel ya akayi ne?"
Kallonta yayi ya ciro wayarta dake kunnensa ya tabbatar muryarta ce a ciki yaji.
Wani kayataccen murmushi ya saki idonsa yana yawo tsakanin wayar da fuskarta.
"Ni Ibrahim Khaleel din?"
"Bani wayata ni" ta shagwabe masa.
Biye mata yayi batare da ya sani ba shima tasa fuskar yanayin yadda tayi...tale
bakin nan da baya so.
"Kin tayar min da hankali Zayyana. Its not fair sauran kadan zuciyata ta tsaya"
Dariya take a hankali tana sadda kai shi kuwa tamkar ya hadiyeta ya fada tsundum
baya fatan fitowa. Wayar ya mika mata da yaji kamar ana hawowa saman ya motsa
bakinsa kadan "nagode"
Dakin Ummin da yake a bude ya tafi wurin Innawuro ita koma ta koma kasa inda
Radhiya ta hadata da Rahima. Kafin dare su biyun sun dinke tamkar sun jima da sanin
juna.
Sai wurin tara Zayyan ya dawo. Sallamarsa kawai Radhiya taji ta tashi a guje kamar
yarinya taje ta rungume shi suka sa dariya. Rahima ya kalla da ta gaishe shi a
ladabce tare da Zayyana.
Ya saki fuska "Rahima ko? Yaya mutanen gida?"
"Lafiya kalau, mun sameku lafiya?"
"Alhamdulillah" ya amsa mata sannan ya bi bayan Ummi ya hau sama.
***********
A kwanakin da suka gabata Innawuro ta dage wurin wanke jikarta da ruwan lalle mai
kyau wanda babu wani hadi cikinsa sai zallan garin da take jikawa ta hada mata da
ruwan turare wanda matar Baffa Gide ta hada mata da wasu itatuwa. Ranar da zata
nuna mata yadda zata yi sai ga Radhiya ta fito daga toilet a guje fuska sharbe da
hawaye tana cewa ita bazata yi wanka dashi ba.
Innawuro ta rasa yadda zata yi da ita saboda kukan gaske take sai ta Ummi ta shiga
tsakani. Tana faman hawaye da jan hanci daure da tawul tace "Ummi so take kawai
jikina yayi faci faci da jan lalle a ce min dodo ranar bikin. Kinga fa haka ta taba
yi min aski yanzu kuma ruwan lalle...ja take so na koma?"
Zayyan yana jiyo su don ranar asabar ce babu inda yaje hankalinsa yayi dakin kunyar
Innawuro ta hana shi shiga amma da tuni ya fito da 'yarsa. Ummi tun tana fada sai
ta koma lallabata karshe dai ita tayi wanka da ruwan tace ta jira ta gani ko nata
jikin zaiyi ja. Ai kuwa ta jira sai gashi Umminta ta fito jikinta yana wani irin
santsi ga kamshi mai dadi.
Washegari da kanta tace Innawuro ta hada mata tace taki suka gama dramarsu sannan
aka fara gyaran jikin jika. Rigima ta biyu tana wannan baccin nata kamar wadda aka
saukewa buhun siminti Innawuro ta daura mata lalle dungulmi har kusan rabin kafa.
Kafa daya akayi ta farka a gigice zata cire Innawuro tasa Zayyana da Rahima suka
danneta. Babu abinda Radhiya bata ce zata yi musu ba idan ta tashi ko a jikinsu sai
da aka gama Innawuro tayi mata jan ido sosai.
"Wallahi idan kika cire sai na saba miki. Wannan lallen dumama miki jiki zaiyi ana
miki gata kina shirme"
Hawaye ne ya digo mata "to sai ki min tsohuwa ta fada kwata ina laifin ma kice a
siyo salatif ayi na gayu"
Dun jgure mata kai Innawuro tayi "nasan damuwar taki bata wuce kada azo na biki
wannan bai fita ba ko. To kisha kuruminki kina da akalla kwana ashirin dole zai
fita kuma bayi miki zanyi a hannu ba"
Baki ta zumburo "kuma safa zan rinka sakawa kullum"
"Da kuwa kin burgeni domin so nake ki rabu da taka wannan tayil din naku duk ba
gata bane a jikin mace sanyi na ratsa ta"
Ta dai kwana da lalle amma da safe Rahima da Zayyana sai da tasa suka gudu daga
gidan suka koma gidan Mami don cewa tayi balotelli zata yi musu. Tun suna dariya
sai gata da almakashi tuni Zayyana ta tsure saboda ta tuna da.
Akan lallen Awwab kansa yasha mita kamar shi ya kulla mata sai hakuri yake bata.
Shima suna ta nasu shirin da Yousuf saboda ba wasu abokan kirki garesu ba. Awwab
idan ka cire mazajen kannensa da Yousuf din a yanzu da suka yi muguwar shakuwa
bashi da abokai a Nigeria sai na wurin aiki. Shiyasa kayan da zai yi amfani dasu na
daurin aure iyayensa ya barwa ragama. Baba Hadir kaninsa ya turawa kudi da wasu
kayan Awwab din domin ayi masa daidai jikinsa.
A bangaren mata kuwa Mama tuni ta warke don bata zama. Duk abinda za'ayi ita ce
gaba Mami da Ummi 'yan kallo. Siyayya suke yi sosai zuwan Mama Kano sau biyu.
Zayyan dai ya saki bakin aljihu ne hankali kwance wannan arziki da Allah Yayi masa
na ganin auren 'yarsa ba karamin abu bane. Duk wani abu da ake bukata na auren 'yar
gata ya yiwa Alheran. Ana haka sai ga dankareren gado da setin kujeru 'yan Italy
masu dan karen kyau da tsada Alh Mousa mahaifin Yousuf wato mijin Tante Nasara ya
aiko dasu banda kudi masu yawa da ya tura ta account dinta yace kada ta tambayi
Zayyan komai idan tana bukatar kari ta neme shi.
💕[11/2, 7:24 AM] : 53. 💕
Ita da Arifah suma nasu shirin suka fara inda da sahalewar angwayen nasu suka
amince a hada dinner a Abuja bayan kowacce anyi mata nata bikin na gida. Arifah a
Jos za'ayi wasu events din bikin 'yar gwamna guda daya tilo ita kuma Radhiya sai da
aka yi ta tunanin inda yafi dacewa karshe Mama tace ayi a Abuja amma yini a
Sakkwato za'ayi kamar yadda za'ayiwa Arifah a Jos. Ranar kai amarya kowacce a
daukota daga garin mahaifinta washegari suyi dinner dinsu. Daga nan kuma tsugunne
bata kare ba domin Tante tana can Nijar da sauran 'yan uwa ana shirin bikin
'ya'yanta Yousuf da Radhiya saboda haka ana wannan dinner din can zasu wuce ayi
sabon biki sannan amaren su tare. Dama kuma Tante din ta riga ta sanar dasu Ummi
kada a dauko wata mai gyaran jiki zata taho da kawarta tun suna 'yan mata idan sun
zo taron Zayyan zata barta a nan. Arifah daga Nijar zasu wuce France shi kuma Awwab
ya riga yasa an fara nemawa Radhiya visar Germany can zai tafi da ita suyi sati
biyu su dawo Nigeria.
Tun yanzu kowa jiki ya fara fada masa saboda shirye shirye. Ana ta kai dinkunan
biki na amarya , 'yan uwanta da iyaye. Zahra da Raji sun dawo daga Katsina sai hutu
ya kara daga wurin aiki amma fa idan ya koma shekarar kaf bashi da hutu. Fauziyya
itama sauki ya samu sun koma Katsina sai daurin auren Bilal zai taho da ita.
SANNU SANNU BATA HANA ZUWA
Saura kwana uku daurin auren Arifah hakan na nufi kwanaki hudu ya rage na Radhiya
amma har yanzu Awwab bai dawo ba sai bata hakuri yake yi al'amura sun zo ba yadda
yayi zato ba. Radhiya tun tana daurewa sai da tayi masa kuka da daddare akan bata
fatan a daura auren baya nan. Hakuri ya bata domin wani training aka saka yake
jagoranta. Ainihi bashi bane da tuni ma ya dawo gida sai matar wanda zaiyi ta haihu
sati biyar kafin ainihin lokacin haihuwarta. Abu yazo da tangarda dole ya dauki
hutu. Gashi daga shi sai Awwab ne suka yi wannan course din a Ukraine. Tunda sunsan
aure zaiyi shine aka daga masa kafa zai taho ana gobe daurin auren Yousuf.
Ga abu ya dame shi ga fushin Alheran dinsa sannan Mami da Daddy sun kira shi a
lokuta mabambanta kowanne baisan dayan ya kira ba suna jaddada masa idan ya bari
aka daura aure babu shi zai ga fushinsu.
Ya gama shirinsa tsaf ranar da zai taho ana gobe daurin auren su Arifah yayi ta
kiran Radhiya taki dauka tana ta kunkuni. Text yayi mata mai dauke da dadadan
kalamai ya sanar da ita yana hanya zai sauka shadayan dare. Bata yi masa reply ba
sai sai kowa ya ga sauyi da walwalarta da ta karu. Tante ta fadawa ya taho tace to
maza ta tanadar masa abinci a kai gidan Mami. Yousuf da suka zo da sauran mutanen
Nijar shi acan yayi masauki dakin Awwab tare da Raji. Gidan Major General Zayyan
kuwa babu masaka tsinke saboda 'yan uwansa na Nijar iyaye su Alh Sidi da Alh
Ghoumar. Alh Mousa dai da mijin Mammee da sauran tawagarsu hotel aka kama musu.
'Yan uwa ne aka taru ko ta ina. Emzee ma ya da safe ya iso sai dai gidan Mama ya
wuce kai tsaye ga mamakinsa Halifa ma ya riga shi zuwa suna tare da Ibrahim. Sakin
fuska yayi kamar babu komai a ransa ya rungumi dan uwansa sai dai har ransa yana
jin babu dadi da kuma hangen me zai faru idan gaskiya tayi halinta.
Sai bayan magariba Radhiya ta dora girkin da Tante tace tayiwa Awwab Emzee da
Ibrahim suka zo dauka. Farar shinkafa ta dafa masa tayi shar da ita sai dai baifi
minti biyu ya rage ta kwashe ba ta juye mata alayyahu madaidaici a ciki. Gyareshi
tayi amma bata yayyanka ba a haka tayi amfani dashi bayan ta cire shi. Ba kuma
tsigar nan ta ganye kawai ba, ta hada ne harda itacen inda yayi karfi da yawa kadai
take yankewa. Yau dai tayi kamar na mutum biyar ne tunda tasan su Yousuf na gidan.
Miyar kuwa farfesun kaza ne da ta barshi ya danyi kauri an yanka dankali amma da
girmansa a ciki da caras shima da dan girma sai koren wake. Rahima, Zayyana da
Hibbah suna makale wurin koyon girki tayi ta gama. Sai da ta dibar musu suka sama
mata lafiya. Ibrahim ne ya fara zuwa kitchen din yace Zayyana tazo ta bashi labarin
Khaleel.
Radhiya da bata gano komai ba tace "ashe dai zatona ya zama gaske da nake tunanin
ko saurayinta ne kusan kullum sai ya kirata sai ta gudu don kada muji me ake cewa"
Kashewa Zayyana ido yayi da take ta jin kunya Hibbah da Rahima sun san komai shiru
kawai suke yi "zan binciko mana shi Adda Amarya muna zuwa"
Bai yarda ya fita ba sai da ya sakata a gaba. Rahima ce take ta yiwa Radhiya
tambayoyi suna tsaye ita da Hibbah ita kuma tana wanke kwanukan da ta bata Emzee ya
shigo. Bata ganshi ba sai alama ya yiwa Rahima da suyi shiru. Ido ya rufe mata ta
baya sai dai jini baya buya tuni ta gano rabin jikinta ne Zayyan dan Zayyan.
Rungume juna suka yi tana ihun murna don har ta fitar da ran zai zo saboda tasan
tsananin makarantarsu.
Ya wani kara budewa ya kereta tsaho sosai yana mata dariya ya dan duku kansa "ashe
nayi missing dinki Addata yau gaskiya kwanan hira zamuyi kafin Hamma ya daukeki, na
fasa bin Ibrahim ma"
"Ka manta ko an daura ina gida har sati biyu?"
"Eh to idan ya bani damar hirar kenan. Muje dakina kiga wani abu"
Suna juyawa Hibba tace "Ya Emzee ina wuni"
"Lafiya kalau mai tale baki number two"
Dariya tayi za ta fita taji Rahima tayi mata wani irin riko tabi bayanta da sauri.
Radhiya tayi saurin cewa Emzee ga Rahima tana dakatar da ita su gaisa.
Haba Rahima idanu tuni sun raina fata ashe tunda ya shigo ta tabbatar shine sojan
taji cikinta ya kulle saboda girmansa da ta gani. Sai yanzu ya kula da ita a
zatonsa 'yar uwar Hibbah ce ko wata dai cikin bakin biki ya saki fuska zai amsa
gaisuwar da tayi masa a tsorace suka hada ido. Wani irin yanayi ne da bai taba zato
ko tsammani ba ya fizge shi a take a lokacin ya fadada murmushinsa gareta yanayin
idanunta tamkar wani maganadisu ya zame masa.
"Kinyi kama da matsorata, yaya sunanki?" Ya tambayeta a kasalance.
Yawu ta hadiya tace "Rahima"
"Rahima zaki zama kawar soja?" ya sami kansa da cewa babu wani tunani.
Duka Radhiya ta kai masa a baya ganin idanun Rahiman sun kara girma duk ta firgice
"kada ka tsorata min kanwa dama har yanzu bata sakewa idan Daada ya shigo."
Tana ganin Radhiya ta dauke masa hankali ta fita da sauri ta riga Hibbah zuwa daki.
Sai da ta rufe kofa ta soma sauke numfashi da sauri da sauri. Tunda take bata taba
ji ko ganin wani abu da ya kwashe mata nutsuwa kamar wannan bawan Allah ba.
Danganta abin tayi da tsoron sojoji da take yi ta kai hannunta kirji tana jin yadda
zuciyarta ke bugawa.
A kasa kuwa kafin su bar kitchen din Ibrahim ya shigo yana kiran Emzee dreban da
zai dauko Awwab motar ta lalace a hanya Raji kuma da yake gida bai san gari ba
shine Ummi tace suje su dauko shi. Shi dai Emzee so yayi ya zauna a kira masa
yarinyar nan mai idanu bai gaji da kallonta ba.
Da abincin da Radhiya tayi a motar suka je dauko shi. Ibrahim kasa hakuri yayi sai
da yace masa yayi jiki saboda aikin nasa yafi yawa a zaune gashi babu inda yake
zuwa daga gidan da ake basu kamar hostel idan baka da ra'ayin kama wani ko kana da
naka sai office din nasu. Murmushi kawai yake yi yana jin kewar Radhiya amma dare
yayi ana neman shabiyu gashi jirgin safe zasu bi zuwa Jos saboda karfe biyu ne
auren kuma suna tare da ango. Wanka kawai yayi da sallah yaci abincin nan sosai
tare dasu Raji suka kwanta a gajiye bayan ya tura mata text din godiya tunda taki
daukar wayar tasa. Ya dena damuwa don ya ma fi son haduwarsu ta gaba da amsa sunan
matar Awwab.
Da safe kuwa ba a nutse suke ba anata shiri. Duka kayan da zasu saka na daurin
auren a jaka suka saka su. Suka wuce airport mota mota sai Jos. Karfe biyu da 'yan
mintuna bayan sallar azahar Major General Zayyan Tureta ya karbi sadakin Arifah
daga hannun kanin Alh Mousa naira dubu dari da dalleliyar mota. Nan da nan jama'a
suka shaida auren Yousuf da Arifa abinda wata uku da suka wuce ko sanin juna basuyi
ba bare suyi tunanin wannan rana. His Excellency the Executive Governor of Plateau
state Rtd Col. Nasiruddeen Aliyu ya tara jama'a sosai 'yan siyasa manya a wannan
taro mai dumbin tarihi. Ansha hotuna a ranar biyar na yamma suka sake dagewa sai
Birnin Shehu. Ga gajiya an dauko ga wata za'a sake dauka gobe.
Hotel da wani guest inn Zayyan yasa yayunsa kama dakuna da dama saboda yayi mamakin
jama'ar da suka zo wannan aure. Da wuri ya biya kudin masaukin saboda haka basu
sami wata matsala ba. Mutanen Katsina gayya guda sai kayi mamaki kamar ba su bane
masu cewa dole Awwab ya auri 'yar uwarsa don duka kakanin Awwab sunzo su ukun.
Malamijo da 'ya'yansa maza kananun ne kadai babu amma ya dauko kowa ga kannensa
suma motoci suka ciko da mijin Nene. Ga jama'a guda daga Nijar wadanda suka halarci
auren Yousuf jiya. Daga Rugar Barkindo Ardo, Baffa Gide, Baffa Habubakari da su
Zakari kusan kowa yazo shaida auren 'yar soja. Mutanen Tureta da su Alh Salisu da
duk wanda ya kamata sun zo. Chibuzor dashi aka daura na Arifah kuma yau ma yana
tare da babansa Zayyan shima zai shaida. Karfe goma na safe aka saka saboda masu
komawa a ranar su iya tafiya. Kusan ma dai kowa juyawa zaiyi suna sa ran da an
daura anci abinci a fara tafiya.
Zuwa lokacin Zayyan ya ciko sosai don Mairamansa ba da wasa ta tasarma fito da
mijin nata ba. A babban masallacin juma'ar unguwarsu da yake bakin titi za'a daura
auren. Wata hadaddiyar mota ce ta tsaya a harabar masallacin sojoji suka