Showing 21001 words to 24000 words out of 295847 words
soma rigima sai ya dauketa. Duk da haka kukan take masa ya
sabata yana haki "gaskiya kin fiye kuka Alheran dinnan"
Kamar taji me yace kuwa ta kai masa duka a fuska harda yakushi. Zafin da yaji a
gefen idonsa na hagu yasa shi sakinta tim a kasa ta fasa wata gigitacciyar kara.
Zainab da Mami ke rige rigen shiga dakin ya dafe gefen idonsa da yake jini ko ta
kanta bai bi ba a kasan. Zainab tayi saurin daukarta yayin da Mami babu tambayar
ba'asi ta dauke Awwab da mari.
"Me kayi mata take wannan kukan?"
Shima kukan yake sosai Mairama ta taho ta rike shi murya na rawa ya nuna mata wurin
"yakushi na tayi fa"
"Sai kayi mata me?" Mami ta kuma tahowa kamar za ta doke shi.
Da karamar murya ya amsa "Faduwa tayi daga hannuna"
Takaici ne ya kamata kuma wai Mairama tana kare masa. "Bari Daddynku ya dawo sai na
fada masa" ta koma ga Mairama rai a bace "ke kuma kin karbi yarinyar nan kin
rarrasheta ko kuwa"
Mairama tace to yau abin harda ita. Karbarta tayi ba shiri an tabo Mami yau ta
fara shayar da ita amai ya taso mata da gudu tayi bandaki. Abu kamar wasa sai gata
ko tashi da kafafunta ta kasa. Mazajen nasu ba ma sa cikin barrack din an turasu
wani training cikin jeji sai sunyi kwanaki. Dalilin ma da suke tarewa gidan Mamin
kenan.
Abu na taron mata tare su ukun da yaransu suka tafi asibiti. Ciki aka gano a jikin
Mairama har wata uku. Kuka ta saka ganin Radhiya duka duka nawa take. Kuma ga
kunyar ace yarinya bata shekara ba ta sake ciki. Su Zainab kuwa sai murna. Mami
tace mata ya kamata kafin su Zayyan su dawo ta yaye Radhiya saboda cikin yana
wahalar da ita ga tsotso. Da yake akwai kawaici a daren ta tafi ta barwa Mami ita
sai kayanta da ta turo Awwab dasu.
Yadda Mami ke bawa Radhiya kulawa ya kara tabbatar musu da cewa zaman mutumci da
amana ba sai da jini ba. Da ita da yaranta duk sun tare a jikin Radhiya an bar
Mairama da uban laulayi sai Zainab dake sintirin zuwa wurinta.
A kwana na biyar su Zayyan su ka dawo. Sun sha wahala sosai sai dai kuma aiki ne na
sabo. Da murnarsa ya shigo yana kiran 'yar soja Mairama tace masa tana gidan Major
ta tafi yaye.
"Yaye Mairam? Ko shekara bata yi ba"
Hannunsa ta kama suka zauna ta dora kanta a kafadarsa "Sojana bani da lafiya ne"
Ya dago kan ta "na sani kuma asibiti zan kaiki, amma meyasa baki bari na dawo ba
sai yaye?"
Baki ta tura masa "to ba..."
"Me?"
"Ciki" tace tana rufe fuska da tafukan hannayenta
Sungumarta Zayyan yayi yana murna "Mairam kice Tureta ya tureki a karo na biyu"
Salati ta hau yi tana mai jin kunyarsa shi kuwa ko a jikinsa. Dama ta samu sai
sabon amarci don ma laulayin yana hana sakewa. Sai da Radhiya ta cika kwana goma
sannan Mami ta dawo da ita da kaya da tarkacen wasa.
******
Bayan wata guda da yaye Radhiya wata litinin Mairama tana gyaran wake za ta yi
alala da rana Zayyan ya shigo ba lokacin dawowarsa ba. Hannunta ta dauraye ta fito
wurinsa.
"Sojana ya dai yau ka dawo da wuri"
Mikewa yayi akan doguwar kujera yana riko hannunta ta zauna a wurin da ya matsa
mata.
"Me kike dafa mana ne?"
"Alala zanyi"
Hanci ya dage "Uhmm kayan bata ciki"
Hancin nasa ta riko tana dariya "nasan ba ka ci, banyi tsammanin dawowarka yanzu ba
ne. Sai na canja abincin, waken...."
Kofar falon da taji ana bugawa da karfi kuma kamar muryar Zainab yasa bata gama
fadin me tayi niyar fada ba. Da sauri ta bude kofar tayi baya a tsorace ganin
Zainab tana rusa kuka kamar ranta zai fita ga Hadir a bayanta dauke da Ibrahim.
Hanya ta basu su ka wuce cikin falon Zayyan ya hada ido da Hadir yayi murmushin
dole jikinsa a sanyaye yace "ka fada mata ne?"
Zainab kuka take har lokacin Mairama ta rude sai tambayarta take me ya faru. Hadir
take kallo tana jiran bayani daga baya tace "ko dai aure za ka kara?"
"Wallahi dama auren ne Ummin Awwab da ya fiye min da wannan tashin hankalin"
Kanta ya sake shiga duhu "ba dai saki bane ko?"
"Liberia zai tafi"
Dif Mairama tayi sakon yana sauka a kwakwalwarta. Liberian da babu wanda yake cikin
barikin da bai san tashin hankalin da suke ciki ba. Nigeria ta shiga cikin lamarin
tana basu gudunmawar sojoji domin a kwantar da tarzoma. Dibansu akeyi lokaci lokaci
ana turawa. Rawa taji jikinta yana yi ta kasa tsayuwa da kyau sai da Zayyan ya
riketa ya zaunar da ita a kusa dashi.
Cikin tsantsar tashin hankali tace "da kai za'ayi tafiyar?"
Abinda ya dawo dashi gida da wuri kenan ya kasa fada mata. Kai ya gyada kawai ta
kalli yadda Zainab ke kuka itama ta soma hawaye. Duk wata kalmar rarrashi da ban
baki abokan sun lalubo domin kwantarwa matansu da hankali. Zainab ta fi gigicewa
itama tana son Hadir fiye da zato da tsammani. Da kyar ya samu ta tashi su ka koma
gidansu aka bar Zayyan da Mairama.
Ranar bata iya yin girkin ba jikinta yayi mugun sanyi. Abincin Radhiya ma sai shi
yake bata. Ita kwanciya tayi a daki kawai tana zubar da hawaye. Bai ce mata komai
ba sai cikin dare ya kwantar da ita a jikinsa yana rarrashi
"Mairam nayi zaton zaki bani goyon baya sosai har naje na dawo mu koma Kano"
"Yaushe zaku dawo?" Ta tambaye shi murya a dashe.
Tsokanarta ya fara yi don ta sake "tafiyar wata uku ce fa, zan dawo kafin ki haihu
in Allah Ya yarda"
Sake shigewa jikinsa tayi yana jin cikinta da ya fara tasawa ya dora hannu a kai
"Ashe haka ki ke so na ban sani ba?"
Shiru tayi ya cigaba da maganarsa shi kadai "a iya zamana dake Mairam bani da wani
abu da zan fada akanki sai alkhairi. Duk abubuwan da na rasa a baya zuwanki ya
wanke min kuncinsu. Shiyasa nake matukar son ki. Wannan tafiya da ina da yadda
zanyi ko dai na tafi daku ko kuma na hakura ne. Ina rokonki da ki karfafa min gwiwa
naji dadin bautawa kasata."
Wani irin abu take ji yana mata yawo a jikinta. Idan a da tana tunanin tana son
mijinta to a yau sonsa yana neman ranta ne. Gani take kamar bazata iya jurar
rashinsa a tare da ita ko da na kwana daya bane. Ashe baka sanin mahimmancin abun
da ka ke dashi sai yayi nisa da kai. Bata san lokacin da bacci ya dauketa ba sai
ajiyar zuciya da take ta saukewa.
Sai da ya tabbatar tayi bacci ya tashi ya dauro alwala. Yasan yaudarar kansa zaiyi
idan yace zaiyi bacci a wannan daren. Nan da kwana biyar zasu bar kasar, zai bar
iyalinsa wanda basu dogara da kowa ba sai Allah sai kuma shi da nauyinsu yake
wuyansa. Yayi nafila raka'a goma tare da witri sannan ya zauna yana jero addu'o'i.
Motsin Radhiya yaji yayi saurin fita da ita daga dakin don kada ta tashi Mairam
yaje ya hada mata tea a feeder ta shanye. Yana jiran ta koma bacci yarinya ido ya
soye ta fara kiriniya. Bata tafiya sai rarrafe da mikewa. Biye mata yayi suna
wasan. Sai gabanin asuba ta bingire a jikinsa tayi bacci. Kan ta ya rinka shafawa
baiyi zato ba sai hawaye ya ziraro masa ya goge da sauri yana baiwa zuciyarsa
hakurin cewa wata uku a wurin Allah kamar kiftawar ido zasu zo su wuce.
**********
Gidan Hadir ma basuyi bacci ba don Zainab kwana tayi kuka. Mami da sauki tunda ba
zuwan Major na farko wurin rikici ko yaki kenan ba. Sai dai itanma kukan tayi don
ba'a sabo da rabuwa.
Washegari harabar gidajen nasu kaf babu wata hayaniyar kirki. Sojoji ashirin ne
zasu tafi a cikin magidantan da suke wurin. Kowa yana gida tare da iyalinsa.
Bayan la'asar Zayyan ya dauki Mairam su ka je gidansu da gidan kawunansa da Mal
Aminu ya fada musu zaiyi tafiya. Kowa yayi masa addua da fatan alkhairi ban da Jume
da bata dena jin zafin rashin basu kudi ba. Duk da haka ya yi musu kyauta ita da su
Maikudi tunda sunyi aure. Matan ma a ranar sai da ya kai musu ziyara.
Sukuku su Mairam su ka koma babu walwala a tare dasu ita da Zainab. Mami ce tayi
musu fada akan idan sun cigaba da haka a wane yanayi suke so mazajensu su tafi. Sun
ji maganarta don kowacce sai da tayi kokarin gyarawa. Mairam dambun nama ta yiwa
Zayyan gari guda sai da ya dibarwa Hadir da Major. Ta kuma saki jiki tana bashi
kulawa fiye da yadda ta saba.
Sauran kwana biyu su tafi tana goge masa khakinsa Radhiya ta fito daga daki da
kafafunta a hankali saboda rashin kwarin tafiyar. Murna ta kama Zayyan ya sunkuceta
yana sumbatar kumatunta.
" 'Yar soja ta girma, yau yawo zamu je tunda anyi kafa"
Kamar taji me yace ta rinka bangala dariya. Ajiyeta yayi zai chanja kaya su fita
tasa masa kuka "Daaadaa" yaji tace tana dago masa hannuwa.
A nutse ya juyo ya tabbatar shi take kira. Har yanzu hannuwanta take miko masa
"Daaadaa". Ya kalli Mairam ita ma mamakin yarinyar ya kamata. Awwab bashi da aiki
sai koya mata Ummi da Daddy wai dole sai tayi magana. Yau gashi ta kira mahaifinta
dadi yasa yaji idonsa na alamun zafin kwalla. Daukanta yayi ya shiga dakin su ka
bar Mairam tana guga tana diga masa hawaye a kayansa.
Ranar ashirin da daya ga watan Mayu na 1993 ne Giginya Barrack dake cikin garin
Sakkwato ta kwashi sojojinta za'a kaisu Lagos washegari su tashi zuwa Liberia ta
ruwa.
Daren ranar ya kasance dare na soyayya, jaddada alkawura da kuma sabunta matsayi a
zukatan su Zayyan da iyalansu. Daga shi har Mairam babu wanda ya runtsa kuma hakan
take a wurin Hadir da Zainab da Major kansa da Mami.
Komai Mairam ce ta yiwa Zayyan hatta abinci a baki take bashi. Tayi ta daurewa kada
tayi kuka zuciyarta ta kasa daukan wannan lamari. Ko kadan baya son nuna mata
damuwar da yake ciki shiyasa ya fake da yiwa Radhiya wasa.
Jiniya mai sanar da su fito ce tayi kara sai da cikin Mairama ya murda kawai ta
fashe da kuka iya karfinta.
"Zayyan"
Tashi yayi ya rungumeta tsam a jikinsa "ashe kin iya fadin suna na"
"Ka ajiye aikin nan mu koma Nijar ko kiwo ka rinka yi"
Fuskarta ya zagaye a tsakiyar tafukan hannunsa.
"I love you Maryam Ali Gidado. Ki rike wannan a zuciyarki har na dawo. Nayi miki
ajiya a kan mudubi idan na tafi ki duba"
Hade bakinsu yayi tamkar ranar su ka fara haduwa yana jin karar jiniyar a karo na
biyu ya saketa ya dauki Radhiya.
"Ki tayani kula da Umminki da baby kinji mamana."
"Daaadaa" tace tana washe hakoranta biyu dimple dinta ya lotsa ciki sosai.
Ita ma ya sumbaci kuncinta hagu da dama kafin Mairam ta farga ya fice daga gidan.
[02/11 7:29 AM] My 2nd Mtn: 12. Daga tashar jirgin ruwa ta Apapa da ke dake Lagos
su Zayyan zasu tashi a jirgin ruwa zuwa babban birnin Liberia wato Monrovia. Akan
tekun Atlantika jirgin nasu ya dau hanya sai da suka wuce Benin republic wadda mu
ka fi sani da Cotounou, sai Togo, Ghana, Cote d'voire sannan Allah Ya saukesu a
kasar da rikici na cikin gida ya kaurewa tun shekarar 1989.
Motocin yaki aka turo domin daukarsu. Zayyan da Hadir zuwansu sansanin yaki irin
wannan na farko kenan. Major Mustapha yazo ne a matsayin babban soja don ba wuri
daya zasu zauna ba. Shi Computer Engineer ne saboda haka aikinsa yafi karfi ne daga
bayan fage musamman da a wannan lokacin babu masu karatu irin nasa da yawa saboda
karancin kayan aiki.
Cikin garuruwa ko kauyuka da rikicin yafi shafa ake watsa sojojin. Sune suke
kwantar da tarzoma da fitina idan ta taso a tsakanin mazauna garin da kuma 'yan
tawaye.
Ranar farko su Zayyan da sauran da su ka zo tare da yawansu basu iya rintsawa ba.
Daki ne kato kowa da yalolowar katifarsa akan gadon karfe mai hawa biyu. Wasu kuma
a kasa katifunsu suke saboda rashin wadatar gadajen. Zayyan da Hadir a kusa da juna
suka shimfida katifun da aka basu. Shi dai tunanin Mairama da Radhiya yake yi. Ko
me sukeyi a wannan lokaci? Tafiyar Radhiya ta kara kwari a kwanakin da suka shafe a
kan ruwa? Idan ya koma zata yi masa kyuya? Gajeren tsaki yayi da wannan tunanin.
Burinsa ace kowane mataki na rayuwar 'yarsa ya faru a kan idanunsa.
Hadir yace "kaima ka kasa bacci ko?"
"Yadda ka san nayi tsuntsuwa naje na gansu na dawo" yayi maganar cike da kewa.
Muskutawa Hadir yayi ya gyara kwanciyarsa. Shi kuma Zayyan yayi rub da ciki ya rike
fuskarsa a tafukan hannunsa da ya tokare kansa dasu.
"Bansan yaya Zainab take yi da Ibrahim ba yanzu. Kusan wata guda yaron nan ba ya
iya bacci sai akan kirjina"
Dariya Zayyan yayi "kace akwai daru, don ma bai kai Alheran rigima ba abin zai zo
da sauki."
Wani cikin wadanda suka tarar a sansanin yana daga gefe yana jin hirarsu ya soma
dariya "kusan kowa ranar farko sai yayi hirar gida"
Gwangwani ya dauka a kusa da shi ya bubbuga da hancin katuwar bindigarsa. Sai ga
sojoji suna tashi zaune wasu akan gado wasu a katifa. Kalilan ne masu bacci.
Mutumin yace "kunga yau anyi baki ku tashi mu san juna." Ya kalli bangaren da
yawancin bakin nasu suke "babu wani abin debe kewa a wurin nan sai hira da muke
samun yi da juna cikin dare"
Na kan gado na dirowa na kasa na matsawa sai gasu sunyi da'ira sun zagaye katifar
wanda yayi maganar. Da gani zai girmi da yawansu. Kallonsa ya ga suna yi ya kada
kafada.
"Ok, ok ni zan fara"
Ihu wasu suka fara su Zayyan dai abin duka sabo ya zame musu. Duk wata hayaniya sun
saba da ita a irin training da suke zuwa. Amma wannan karon fa a filin yaki suke
tare da sojojin wasu barracks din da basu taba haduwa ba. Muryar mutumin yaji ya
soma magana.
"Nine shugabanku a harkar abinci" sai sowa da tafi yayi murmushi "Chief cook kuke
gani. Suna na Captain Ogbonna Odili. Ina da mata Mabel da yara hudu a Enugu.
Ogechi, Uloma, Nneka da Kachiku muna kiransa Kachi. Kamar kowa a nan ina matukar
son family dina. Musamman ma Uloma saboda tana da kokari sosai a school. Yanzu zaka
rubuta mata abu indai ta karance shi daga farko zuwa karshe to ya gama zama. Da
kuke ganina kudi nake nema domin na kaita wata babbar makaranta a garinmu ta gifted
children. Uloma is born to be a great doctor"
"So shall it beeeee" wasu suka amsa da ihunsu na sojoji. Capt. Ogbonna yana ta
dariya ya cigaba da hirar iyalinsa ana tayashi murna.
Bayan shi sai aka ce mutum daya cikin newcomers ya gabatar da kansa. Papa Dolapo ne
ya fara shima yana bayani ana dariya da kuma nuna tausayi musamman da yace ya baro
matarsa da tsohon ciki suna jinjina masa.
Zayyan sai ya tuna cikin jikin tasa matar ya daga hannu "I am next please, please"
Dariya suka sa ana tsokanarsa ya dake yana basu labarin Mairama da Radhiya "babban
farincikina kafin na taho Alheran ta iya kiran suna na"
"Fada mana ya take cewa" wani yace sauran na goya masa baya.
"Daaadaa"
Ihunsu ya karade dakin masu baccin ma sun tashi anayi dasu.
"Kuma nima matata tana da ciki amma sai mun koma zata haihu In sha Allah. Sorry
Papa Dolapo kaine za'ayi ba kai"
Hadir yayi dariya yana cewa Zayyan yayi masa wayo "muna komawa da wata tara zaka ji
Zainab ta haihu"
Tafawa suka yi wani mutumin Adamawa Austin Bakari dan kabilar Chamba ya fara bada
labarin iyayensa tsofaffi wanda sun dora duk wani buri nasu akan cigabansa. Labarin
iyayen nasa akwai ban tausayi domin dukkansu guragu ne da basu da mataimaki sai shi
kadai. Dan albashin nasa shine cinsu shine shansu. Ya sanya sauran cikin yanayi na
jimami kowa na fadin albarkacin bakinsa sai su ka ji wata muguwar kara mai
razanarwa.
Basu gama da wannan firgicin da ya sanyasu daukan bindigoginsu cikin sauri ba kuma
sai ga daya daga cikin masu patrol na wannan daren ya shigo bindigarsa tana kan
saiti ya fada musu 'yan tawayen da su ka addabi wannan sansanin nasu sun kawo musu
hari.
Idan da suna jin wai-wai, yau ga su zahiri a filin daga. Harbi ne yake tashi ko ta
ina suka firfito kan kace meye wannan wurin ya kaure. Anyi musayar harsashi sosai
duk da duhun dare sun sami damar fatattakar mutanen har da nasarar cafke mutum
daya.
Wani bacci dama babu shi a lissafi maza suna filin daga. Kwana ukun farko sunyi su
ne cikin rudani da tashin hankali. Da gasken gaske 'yan tawayen suke son korar
sojojin Nigeria daga wurin. Akwai wuraren da suke tsammanin samun nasara su janyo
mutanen garin domin a hadu a ture gwamnatin shugaba mai ci a lokacin. Rigima ta
cikin gida a ganinsu mai zai kawo wasu baki da abin bai shafa ba a matsayin
peacekeepers.
Kafin wani lokaci su Zayyan sun kara gogewa da halin da suka tsinci kansu yanzu.
Shine ya koma yi musu limanci bayan tafiyar Abdulwahid Gbenga wanda ya kasance da
shine limamin. Duk daren da babu gajiya sosai a tare dasu suna zaman hira a daki ko
a waje. Su kunna wuta su zagaye wurin suna jin dumi saboda shigowar sanyi gadan
gadan. Da safe kuma masu manyan mukami su ke jagorantar training dinsu don ba zama.
Watansu daya da kwanaki annobar cholera ta shigo kauyen da yafi kusa da inda suke.
Garin kai taimako wurin fitar da marasa lafiyan zuwa asibiti a cikin gari wasunsu
suka dauko ciwon suka kawo musu.
Cikin kwanaki bakwai mutum tara sun kamu. Amai suke yi sosai da gudawa. Suna ta
kokarin neman agajin babban sansanin domin a kawo musu magunguna sannan a dauke
marasa lafiyan cikinsu zuwa asibiti amma abu yaci tura. Ba wai sakon bai isa garesu
bane, yaje amma su ma suna jiran command daga babbar headquarter saboda komai na
soja bisa doka da oda ake yi.
Major Mustapha da ya ankara cewa sansanin su Zayyan ne ya matsa lamba sosai ranar
da za'a kai musu maganin bayan kwanaki shadaya da fara cutar yabi bayan ma'aikatan
lafiyan cikinsu. Su ma din sojoji ne amma hannuwan rigarsu daga dantse akwai wani
farin abu da yake nuni da alamun cewa su likitoci ne.
Major Mustapha har yanzu bashi da magana sosai amma ya damu kwarai da kannen nasa
Zayyan da Hadir. Motarsu ta iso sansanin a daidai lokacin da Zayyan yake limancin
sallatar gawar Papa Dolapo wanda yayi ta fama da cutar ta amai da gudawa na kwana
uku kafin rai yayi halinsa. Jikin Major yayi sanyi haka na likiticin da suke tare
dasu. Zagaye sansanin nasu akayi da wasu irin wayoyi masu kaifi aka rubuta musu
QUARANTINE da manyan harufa. Ma'ana an kebesu daga shiga ko fita har sai an sami
kyakkyawan tabbacin cutar babu sauranta a tare dasu. Ana gudun su sanyawa wasu
sojijin ko kuma su sakawa mutanen wani kauyen garin kai taimako.
Likitocin kadai aka bari suka shiga suma sun rufe jiki sosai da wasu kaya hatta
fuskokinsu ba'a gani. Sunyiwa