Showing 12001 words to 15000 words out of 295847 words

Chapter 5 - Ku Dube Mu by Batul Mamman

na saka hauka, kan Salame ya dade da kwancewa
akan mijin kanwarta. Kuka ne ya kwace mata mai cin rai da zuciya. Mairama ta rigata
samun abinda take muradi. Salisu ya tsaya kallon ikon Allah yadda take kuka haikan.

“Yanzu meye abin kuka bayan kema kina da cikin nan” a tunaninsa ko don ta riga ta
haihuwa ne.

“Allah Ya sauwake nayi kuka don ta rigani haihuwa” tace cike da tsiwa.

Tsareta yayi da idanu “to kukan me kike yi?”

Gabanta ne ya fadi ta soma inda-inda “banda abin Mairama da kwarewa a rashin kunya
daga auren sai ta bashi kanta. Wannan ai zubar da mutumci ne. A lissafina sai nan
da kwana hudu ma zamu cika wata tara da aure amma gashi ita ta haihu. Anya ma kuwa
cikin nan….”

“Ke Salame! Shiga taitayinki. Kanwar ta ki kike neman jifa da kazafi saboda wani
shirmenku na banza da hofi. Na dade da kula ko sunanta na ambata ko agidan ku aka
ambaceta sai fuskarki ta sauya. Idan ma wani abin ne ya hadaku ki shirya jibi zamu
wuce Sakkwaton sai ku sasanta”

Kallon wulakanci ta jefa masa duk da taji tsoron tsawar da yayi mata “ba zani ba
idan ka matsu da ganinsu kaje kai kadai”

Ransa ne ya soma baci shima “na fasa a gobe ma zamu tafi, haba yarinya mai nutsuwa
da kunya baki da aiki sai na kusheta da jifanta da bakaken kalamai”

“Da kasan tana da halayen kirki me ya hana ka nemi aurenta ka barni na auri wanda
nake….”

Tasss taji saukar mari a kumatunta sai da ta ga haske, rai a matukar bace Salisu ya
nunata da yatsa “bar ganin ina lallabaki wallahi sai nayi miki shegen duka a gidan
nan. Ke wace irin mutum ce ne? Kina ta abubuwa ina kawar da kai to amma tura ta kai
bango tunda har jininki baki raga musu ba. Ki shirya gobe zamu tafi sannan ki tashi
ki hada ruwan omo da dettol ki bi duka gidan nan ki goge min. Su bayan kofofi da
kujeru duka ki tsaftace min gida ko ina warin yawu ya isheni. Idan na sake kamaki
kina tofa yawu nan ba a wancan abin ba wallahi jikinki ne zai gaya miki. Tashi ki
bani wuri ni”

Ba karamin tsorata tayi ba ta kai mai hakuri bango. Tsoro ne da ita tun da can,
soyayyar Zayyan da ta bari a zuciyarta da kyashin kanwarta su ne suka maidata haka.
Jiki na rawa ta tashi yace ta dawo sai ta gama cin abincinta tukunna.
[02/11 7:28 AM] My 2nd Mtn: 9
*KANA NAKA…*

Shirye shiryen tarbar bakin da zasu zo suna ya kankama. Zayyan ya dage a gidan
mahaifinsa za’ayi taron duk da cewa kawunansa da Mal Aminu sun ce gara ya yi a nasu
saboda gudun bacin rai da ga Jume ko ‘ya’yanta. Ya riga ya gama tsara yadda zai bi
da su domin gujewa hakan. Gidan yaje har daki ya same ta ta hakimce tana taunar
goro.

“Hutawa akeyi ne Jume? Kawarki tana gaisheki”

Tabe baki tayi tana kallonsa ya zauna a kan yagaggiyar ledar dakin “kawarsu dai
wadanda aka haifawa. Ni a su wa kuma?”
Basarwa yayi ya tankwashe kafafu “dama alfarma nazo nema, ina son ayi taron sunan a
gidan nan ne”

“Dama jiranka nake naga iya gudun ruwanka tun da aka fara shigowa da bokatan fenti
dazu. Ita matar taka basu da dangi ne da bazata koma gidansu ba? Naga haihuwar fari
ce, ya dace ace tana gaban iyayenta. Tsabagen rashin ta ido ka barta a gidanka kuna
kwana daki guda.”

“Cikin masu zuwa sunan akwai matar babanta da zata zauna har ayi arba’in tare da
ita. Ni zan koma wani gidan a cikin barikin kafin su gama”

Maikudi ne ya shigo fakam fakam ya sami guri ya tsaya ayi zancen dashi. Zayyan ya
sake fada mata yana son sauke baki da ga Nijar da kuma mutanen Sumaila a gidan nasu
tunda babba ne.

“Ince ko ka ga nayi kama da baiwar gidanku da zan zauna tarbar baki. Kaga Zayyanu
tun wuri ka san me kake ciki da bakinka”

Murmushi ta ga yayi maimakon ya tashi ma sai ya gyara zama “to babu matsala zan
yiwa su Kawu magana. Sai abu na biyu nace idan an kawo kudin rakuman wace sana’a
Maikudi zai fara?”

A tare su ka taso masa kamar zasu zaune sh. Maikudi ya zauna a gefensa yana fara’a
kamar gonar auduga, hakansa zai cimma ruwa. Jume ma sai ta saki fuska kamar ba ita
ba.

“An sayar da rakuman naka ne?” Maikudi ya tambayeshi da zumudi.

“Eh, zasu taho min da kudin, jibi nake sa ran isowarsu” ya bashi amsa.

Sai ga Maikudi ya tashi jiki na rawa “Bari na kira yayyenka malalatan banza su zo a
fara gyara gidan nan, mu gidanmu da yake da wadatar dakuna kamar ramin bera, Jume
yaushe zaki ce sai ya nemi su Kawu don iya tonawa kai asiri”

Matsowa tayi kusa da Zayyan tana dariya “shima yasan wasa nake yi masa. Ka nemi
masu fentin su zo ayi a gama da wuri sai a share dakunan ayi shimfida.”

Mayar da kansa wawa yayi suna ta bidirinsu yana biye musu. Maikudi da son banza
harda cewa an hutar dasu yin fenti tunda su ma baifi wata uku ya rage dukkansu su
ukun zasuyi aure ba.

**********

Cikin ikon Allah baki sun iso an kaisu masauki, washegari za’ayi taron suna. Zayyan
ya wadata iyalinsa da duk abin da ya dace. Wani hadin kai da ga bangaren sojojin su
ma sun hada masa gudunmawa sannan matayensu sun zage dasu ake komai kamar yadda su
ka saba idan dayarsu ta haihu ko wani taro ya tashi. Salame da Nene Marka kanwar
Malamijo a gidan zasu kwana sauran kuma duka suna gidansu Zayyan.
Su Nene sun riga isowa ga yamma jama’ar gidan sun watse sai ita da Mairama da
Zainab. Mami ta wuce gida Fauziyya tana fama da zazzabi. Salisu na tsayar da mota a
harabar gidajen da suke jere a wurin ta fito da sauri gabanta yana faduwa ta barshi
yana yiwa security din da yayi musu rakiya zuwa gidan godiya.

Ciki ta shige tana fatan yin tozali da Zayyan. Sai dai idanunta akan na Mairama su
ka sauka tana shayar da jaririyarta. Wani kululun bakinciki ya taso ya tsaya mata a
wuya. Mairama tayi wani mugun kyau ta ciko ko ta ina. Kallo daya zaka yi mata kasan
cewa hankalinta a kwance yake. Da sauri ta cire yarinyar da ga bakin abincinta ta
tashi ta fada jikin Salame tana murna da tsalle sai da Yadikko tace tayi a hankali
saboda yanayin jikin haihuwa.

“Wayyo Adda Salame nayi kewarki sosai ashe kina hanya. Ina yayan namu?”
Da kyar ta amsa “yana waje, ki tura mijinki ya bashi masauki”

Tsabar murna duk ta rude ma tayi hanyar daki neman mayafi sai ta jiyo muryar Zayyan
din suna magana da Salisu. Salame cikin zakuwa ta juya “bari naje mu gaisa da angon
karni”

Nene ce ta dakatar da ita “wa yake ta angon karni baki ga ‘yar taki ba, dawo kiyi
zamanki nasan zasu shigo”

Ba haka taso ba amma dolente ta zauna. Mairama ta gabatar da Zainab wadda ta tashi
tana tayata hadowa su Salame abinci da sha.

Daga nan Zainab din tayi sallama ta tafi Yadikko kuma ta shiga wanka. Baby tana
kwance akan wani bargon yara mai kyau Mairama ta sake komawa kitchen ta soma kuka.
Har wannan lokacin Salame dama bata yi karar cewa a bata ita ba bare ta dauketa
saboda bata ma son ganinta har ranta. Kukan ya tsananta Mairama tana ji ta kasa
cewa ta dauketa tunda ai ba kurma bace sannan tana jin nauyin ta fito ta dauketa a
ga tayi rashin kunya.

Nene tana da ga bandaki kukan ya isheta tana tunanin me ya sami yarinyar. Harara
Salame ta jefa mata sannan tasa hannu tana dan taba gefen jikinta wai rarrashi.
Daga sama ta bayan kujerar ta ga an zuro hannuwa an dauketa.

Waigawa tayi da sauri idanunta su ka gane mata Zayyan Tureta. Sanye yake da
khakinsa ya zura hularsa cikin wani abu da aka yiwa maballi daga kafadar rigar.
Yayi matukar kyau da haske aure ya sake gyara shi. A kafada ya dora ‘yarsa yana
shafa mata baya.

“Waye ya taba min mamana? Sojoji basa kuka fa ‘Yar soja”

“Zayyan ina wuni?” Salame tace cikin sanyin jiki. Bata san zai shigo ba da ko don
ta burge shi ta dauki ‘yar.
Tamkar bai ga mutum ba ya shareta ya shiga kwalawa Mairama kira. Tana tsaye dama
daga kofar kitchen din duk abinda Salame tayi ta gani tunda kujerar ta bata baya
ne. Mamakin wannan mummunan canjin daga ‘yar uwarta take yi. Ashe ko me ya hadasu
tun kafin suyi aure bai kare ba har yana son shafar ‘ya’ya. Hawaye taji ya soma
sauko mata tana kallon bayan Salame a inda take zaune kamar gunki saboda yadda taji
kunyar abinda ta yiwa jaririyar a gaban babanta.

Hawayen nata Zayyan ya gani ya matsa gareta da dayan hannun da yake shafa babyn ya
janyota jikinsa da karfi ya rungume da hannu daya.

“Kada na sake ganin kin bar min yarinya ita kadai a falo. Idan babu kowa ki goyata
ki shiga kitchen din…kinji”

“Kayi hakuri baza’a kuma ba, na ga Adda tana wurin ne” tace tana karbarta daga
hannunsa. Salame ta juyo kamar mai ciwon wuya tana neman kalaman wanke kanta.

Kamar bai ji ba sai cewa yayi “Taimaka ki hada min abinci da zan tafi dashi inda
zamu kwana da Salisu. Zan kaishi yayi sallah da wanka na dawo na dauka. Amma ki
fara cikawa wannan sojar ciki”

Hannunta daya ta dora a gefen ido tayi masa salute “Yes Sir”

Matsowa yayi yana neman sumbatarta ta goce tana dariya. Mutuwar zaune Salame tayi.
Shi kuwa Zayyan da biyu yake yi don ji yayi ya kara tsanarta. Ba don ta hada jini
da Mairamansa ba da sai ya saka ta a guardroom ko na sa’a daya ne ya huce kukan
‘yarsa.

Da ya fita Mairama ta kawo mata sauran kayan abincin batare da ta sake yi mata
magana ba ta zauna bawa ‘yar nono.

“Ki kwashe ba ci zanyi ba don yanzu ba komai ke zauna min a ciki ba”

Wai nan so take ta sanar da ita itama tana da cikin. Sai Mairama ta gwada mata
halin matar soja da ta fara koyon yadda yake juya zance musamman idan ya fuskanci
abu kake son sanar dashi da dabara don ka bashi haushi.
"Adda yaya hanya? Ya zaman Kano?"

Sai da Salame ta kara kallonta irin baki ji me nace dinnan ba sannan ta chanja
zancen tace lafiya. Zaman kurame su ka koma har Nene ta fito tana tambayar me ya
sami baby dazu take kuka. Babu wadda ta amsa mata a cikinsu duk sun daure fuska sai
ta kyale su ta sa tv a gaba tana kallon tashar NTA.

Zaman ne ya ishi Salame ta tashi ta shiga daki wai zata yi wanka. Mairama ta bi
bayanta taji ko akwai abin da zata bukata. A tsaye ta sameta tana karewa dakin
kallo tana tabe baki.

"Af...ke fa gadon da Malamijo yayi mana dashi aka kawoki ko? Amma naga labulayen
kamar sababbi ga TV ma a falon da firij. Kin fara sana'a ne ko Zayyan din kike
tatikewa?"

"Yo Allah na tuba Adda mace da mijinta har sai kinji yaya ake kudi ke fita har a
gyara mata gida? Dadin zama ne kawai da iya tafiyar da miji"

Ta fadi haka ne saboda gorin da Salamen ke shirin yi mata. Ita kuma Salame sai ta
dauka cin fuska ne ko ta gane ta son sa.

"Ki dai bi a hankali maza basu da tabbas. Canja mace a wurinsu ba wata tsiya bace"

Zaro idanu Mairama tayi da mamaki. Har fatan aurenta ya mutu kuma Salame take yi?
Indai haka ne dole ta kama kanta don bata ga me ta tsare mata ba da take nuna mata
hassada irin haka. Kowa ya shaida mijinta yana da kudi ta rasa gane bakincikin na
meye.

Karfe goma na safe a gidansu Zayyan tayi musu. Anyi taron suna na kayatarwa don
Zayyan ya sakar musu yadda zasu fita kunya. 'Yan uwansa mutan Agadas sunyi masa
halacci duk da rashin mahaifiyarsa sun zo da yawansu tare da gudunmawa mai yawa. A
cewarsu basu sami bikinsa ba dole a fanshe yanzu. Gashi jaririya ta gaji sunan 'yar
uwarsu.

Mutan Sumaila ma sun sha kallo ganin irin suturar da Zayyan ya wadata Mairama da su
na fitar suna. Abin nasu ya burge sosai musamman da wata kanwar innar Zayyan ta
kawo kayansu na gargajiya na kabilarsu ta Tamasheq ta bawa Mairama.

" 'Yata ga wannan ku saka ke da maigidanki da jikarmu ayi hoto. Dashi nake son
tafiya saboda wadanda basu zo ba su ganku."

Mairama sai godiya take su Zainab suna tayata. Riga ce fara kamar buba ta zarta
gwiwa da kadan gaban ta sha aiki da shudin zare sai zani shudi. Ga kuma sarkoki da
yari duka irin nasu da abubuwan sakawa a ka. Mami ce ta karbi Radhiya yayin da wasu
'yan mata biyu kusan sa'annin Mairama su ka ja ta dakin da su ka kwana. Da
taimakonsu ta shirya komai su suka yi mata. Abin hannu da na wuya da kunne harda
hanci kowanne yayi mata cif. Na gashin kuwa sai da daya ta yi mata kalba kananu
guda uku-uku a gefe da gefen kunnenta ta zubo mata dogon gashin irin nasu sannan
aka dora mata shi ya zauna daga gaba kai kace wata sarauniya ce. Hatta fuskarta
kwalliyarsu aka yi mata leben nan ya sha fenti yayi baki. Da yake fara ce ba
karamin kyau tayi ba ta saje dasu. Wata guda ta soma ji daga tsakar gidan aka dora
mata shudin yadi irin na zanin wani irin yafawa yadda suke yi sannan su ka rike
mata hannuwa aka fito da ita.

Turus tayi ga wata irin kunya kamar sabon aure da su ka hada idanu da Zayyan. Yayi
kyau har bata san yadda za ta kwatanta ba. Shima kayan gargajiyar ne a jikinsa na
ciki farare babbar rigar da kuma rawani duka shudi.

Kanta a kasa shi kuwa ya zuba mata idanu, manya cikin 'yan uwan nasu suna ta guda.
Da shirinsu suka zo da sunan yi masa nasu bikin. Taro ya kayatar da jama'a ba kadan
ba duk da iyakarsu cikin gidan. Salame tamkar ta bude ido ta ganta a matsayin
Mairama. Ganinsa cikin wannan kaya ba karamin sake fama mata ciwon son sa da yake
nukurkusarta yayi ba.

Mai hoto aka kira yazo akayi ta dauka. Gwaggon Zayyan tace suyi su uku zata kai
hoton gida. Days suka dauka a tsakar gidan a tsaye tana rike da Radhiya shi kuma a
gefenta. Dayan kuwa dakin Innarsa yace su shiga a kan tsohon gadonta ya zauna da
'yarsa a hannu ita kuma a kusa dashi. Daga nan ta kira danta Awwab ta dora masa
kanwarsa tana tallabe da kanta daga bayansa ta dan duka aka yi musu sannan Zayyan
ma ya shiga.

Ranar idan ka gansu dole su baka sha'awa. Mutan Agadas har irin abincinsu sun dafa
duk na bikin dansu Zayyan da murnar haihuwar Alheran Radhiya.

A gidan maijego ta kwana ranar tare da danginsa ana ta bata labarin 'yan uwansu da
irin yawan danginsu. Gwaggon Zayyan tace mata cikin gurbatacciyar hausarta da ace
Zayyan ba soja bane gida Nijar suka so komawa dashi bayan rasuwar Mal Muhammadu.

"Idan ya sami saukin aiki ku kawo mana ziyara kinji Mairama. Zayyan dan gata ne
saboda yana zagaye da dangi masu kaunarsa saboda maraicin uwa. Da mahaifinsa ya
amince min naso tun rasuwar Alheran na dauke shi."

Hawaye ta ga dattijuwar tana gogewa shiyasa taji zuciyarta ta karye "In sha Allahu
zamu zo"

"Allah Ya nuna mana"

Mairamu a ranar tayi kwanan farinciki da bakinciki duka lokaci guda. Soyayyar da
ta samu daga wurin dangin mijinta ta tsaya mata a rai tayi matukar farinciki. Sai
kuma tunanin dangin Innarta da babu wanda zata iya nunawa tace nata ne ta wannan
bangaren. Sun manta da ita da shafin rayuwarta saboda rashin uwa da tsanar da suka
yiwa Malamijo akan rikon sakainar kashin da ya yiwa 'yar uwarsu a gidansa.

Asubar fari aka fara tashi saboda masu shirin komawa. 'Yan Sumaila ne farkon tafiya
aka bar Nene zata zauna wanka idan sunyi arba'in su tafi Sumailan tare. Mutan
Agadas ma kaf sun gama shiri wai basa son dorawa Zayyan nauyi idan suka cigaba da
kwanaki. Kawunnansa biyu ne a cikin tawagar Ghoumar da Sidi. Shatara ta arziki suka
yi masa kyautar kudi da irin abin amfani nasu na can. Kamar kada su tafi haka
Mairama taji har kofar gidan inda bus guda biyu zasu daukesu tayi musu rakiya.

Daga nan gidanta ta koma tare da Yadikko da Salame su ma a ranar zasu wuce.

Manya akwai kaifin tunani da hangen nesa. Cikin kankanin lokaci Nene ta gane
manufar Salame akan Zayyan. Tasha mamaki ba kadan ba saboda a da tana yi mata
kallon wadda zata iya sadaukar da komai domin farantawa kanwarta. Ashe abin ba haka
yake ba. Ta ciki na ciki ne. Jan bakinta tayi ta tsuke bata tona ba sai dai ta jasu
su biyun tayi musu fada akan sabon yanayin alakarsu.
"Nene gara da ki ka kula, ki tambayeta idan na mata laifi ne na bata hakuri"

Kallon Salame Nene tayi ta dauke fuska tare da janyo jakar kayanta tana shan kunu.

Nene tace "Salame idan ma da sabani na kula kece kike jansa. Tun zuwanki ina lura
dake ko da wasa wallahi baki dauki Radhiya ba."

Saurin kallon Mairama tayi don kuwa hakan ne. Mairama tuni ta gane shiru kawai
tayi.

"Nene bana jindadi tunda nazo garin nan shiyasa. Mairama Allah Ya baki
hakuri...shikenan ko" tace a kagauce tana son fita daga dakin.

"Juna biyun shine zai sa ki kasa daukar 'yarki? Ki dai yiwa kanki fada don rayuwa
bata da tabbas"

Mairama bata ma tanka ba ganin za ta rana musu wayo. Da zasu tafi Salisu ya kawo
kudi ya bayar a sayawa Radhiya kaya harda cewa inji mamanta Salame. Godiya suka yi
masa sun san kuma kara ce kawai yayi amma babu wani inji Salame.

Sun shiga gidan Nene ta goya Radhiya ta shige daki wai garin akwai sanyi. Ga gida
mai daki daya tana rufo kofar Zayyan ya rungume Mairama harda ajiyar zuciya.

"Na wahala Mairam, na wahala sosai"

"Taron jama'a ko?" Tace tana kokarin kwace jikinta kada Yadikko ta fito.

"Wane jama'a, a kaina suke? Rashinki ne ya addabeni."

Murmushi tayi ta sunkuyar da kai ya dago habarta "dadina da mutum kunya. Yaci ace
mun wuce wannan matakin fa, ga 'yar soja can kina gani"

"Ni dai kazo ka tafi kada ta fito ta sameka"

"Kin yarda zaki yi min irin kwalliyar jiya idan ta tafi?"

"Na yarda"

Rungumeta ya sake yi sosai "Ina sonki Mairam, shigowarki rayuwata ya sanyani
farinciki mara misaltuwa. Karo na farko naga da dangin Innata su ka zo da yawa haka
saboda ni. Kuma duk a dalilinki ne da kyautar Alheran da kika yi min. Nagode"

"Ina fatan Allah Ya bani ikon cigaba da kyatata maka Sojana. Kayi min komai a
rayuwata. Ka rabani da kunci da bacin rai. Ka zame min miji, aboki kuma dan uwa"

Kashe mata ido yayi "ina ma daga ni sai ke a gidan nan kike wannan kalaman"

Ta gano manufarsa ta shiga dariya a hankali. Kofar dakin aka taba ya tashi a guje
ya fice ita kuma ta dake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login