Showing 1 words to 3000 words out of 295847 words

Chapter 1 - Ku Dube Mu by Batul Mamman

[02/11 7:27 AM] My 2nd Mtn: A
*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*

*5/2/2019*

*Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah SWT da Ya bani damar fara rubuta wannan
labari. Ina addu’a Allah Yasa yadda na fara lafiya na gama lafiya kuma ni daku mu
amfani da abinda ya kunsa. Kuskuren da yake ciki kuma ALLAH Ya yafe min. Amin*

*HAKKIN MALLAKA*
©Batul Mamman

*Wannan labari da duka abinda ya kunsa mallakar BATUL MAMMAN ne. Ban yarda wani ko
wata ya juya min ko da shafi daya ne batare da izini ba. Sannan ban yarda a yada
min wannan labari ta kowace siga ba ta kafofin sa da zumunta, bugawa ko karantawa.
Sabawa hakan zai janyo daukar mataki akan duk wanda aka samu da laifin. Nagode.*




*FARKON FARI*

*1992*



Gidan Mal Ali Gidado babban gida ne a cikin karamar hukumar Sumaila dake Kano.
Attajiri ne wanda Allah Ya azurta da dabbobi masu tarin yawa. Garken shanu, tumaki
da awakinsa bazasu kirgu ba saboda yawansu. Wata katuwar gona ya samu a can bayan
gari ya zubesu yana kula da kayansa da taimakon mutane kalilan saboda bazai juri
biyan da yawa ba. Bafillatani ne na usuli dan siriri ba kiba ko kadan amma kallo
daya zai tabbatar maka an zuba kyau zamanin kuruciya. Mutan gari da iyalinsa suna
kiransa Malamijo. Duk tarin arzikin Malamijo kusan kowa ya sanshi a matsayin
rikakken mai mako da bakar rowa. Kudinsa basa tabuwa indai ba aure ya tashi yi ba.
To a nan fa yarinya da iyayenta zasu ci su tada kai. Idan anyi auren ma amarya ita
ce tauraruwa taci mai kyau tasha mai kyau. Gidan gabadaya hannunta sai dawo har
zuwa lokacin da Malamijo zai gaji da ita ko tayi ciki. Daga nan fa ita da babu duk
daya don gwani ne wurin wulakanta mata da cin zarafinsu saboda shima ya sani
kudinsa suke aure.

Malamijo ko suturar kirki baya sakawa saboda kada ya kashe kudinsa. Sau tari zaka
ganshi cikin kodaddun kaya yana yawo don bai taba yarda yayi dinki daidai jikinsa
ba saboda gudun raini. A halin yanzu ‘ya’yansa goma sha biyar amma shida ne kadai
da iyayensu mata a cikin gidan. Sauran taran basu da gata suna ga Allah suna ga
Yadikko mata ta biyu a jerin aure auren Malamijo wadda har yau ya kasa sakinta
saboda mace ce da ta gagare shi juyawa. Bata taba haihuwa ba kuma nata mahaifin ma
da arzikinsa lokacin da akayi aurensu. Duk da haka dai auren nasu yana da tsahon
rai domin kuwa duka ‘ya’yan Malamijo akan idonta aka haifesu. Idan ya saki uwar
yaran tana kokari matuka wurin kulawa dasu sai dai rashin wadatasu da yake yi yasa
itama abubuwan sai a hankali. Yaran da suka ci sa’a suma sun taso da nasu iyayen a
gidan to duk abinda aka kawo wawaso ake dasawa mai uwa a gindin murhu ya tsira da
abin arziki. Wanda babu tasa kuma ya koma gefe yasha kallo.

Duk bakin hali na Malamijo yaransa sun tsira da abu daya wato ilimi na zamani da na
arabiya. Wannan ludufi da suka samu ya samo asali ne daga shawarar da abokinsa da
suke kai dabbobi kudu tare ya bashi na cewa idan sunyi karatu shine zai mora domin
zasu sami aikin gwamnati kuma a matsayinsa na mahaifinsu shine zaifi kowa jindadi
da samun yaran. To dayake zuciyar ta nema ce kawai ba musu ya amince. Shi kuwa
abokin nasa Mal Kallamu yayi haka ne domin ya taimakawa yaran da suke walagigi a
cikin gari. Shawara dai irin ta abokai yana kokarin bashi bakin gwargwado akan
tsarin rayuwarsa amma yaki ji. Banda Mal Kallamun ma waye ya isa ya fadawa Malamijo
magana irin wannan kai tsaye batare da ya auna masa rashin mutumci ko da rabin
kwano bane ya kai masa har kofar gida.

Yau yake dawowa daga kudu inda ya kai motoci uku na dabbobi. Duk yadda aka san
Fulani da son dabbobinsu haka yake a wurinsa sai dai kudi ya fiye masa komai. Kuma
gashi da nasibi don yana samun alkhairi sosai kamar yau din da ya dawo.

‘Ya’ya da matansa haka suka yi ta fitowa ana masa barka da dawowa yana faman hura
hanci kada wata tayi gigin neman karbar jakarsa.

‘Yan mata biyu ne a daki daya tana kwance akan yamutsatsiyar katifa dayar kuma mai
alamun ta girmeta tana daga tsaye a kanta.

“Wai bakiji shigowar Malamijo bane?”

Siririn tsaki taja tana juyawa daya bangaren “naji mana”

Yayarta ta da suke daga iyaye mata daban ta zauna a gefen katifar tana rage murya
“Mairama kinsan idan bamu je ba duk abinda yazo dashi su Inno karbewa zasuyi ko?”

Cikin bacin rai Mairama ta juyo “Adda Salame ban fa hanaki zuwa ba.”

Batare da kosawa ba sanin halin kanwarta ta sake murmushi “Mairama ki dena wasa da
iyaye babu kyau”

Tasowa tayi a harzuke sai dai ko kafin ta fara magana ta soma kukan abinda yake ci
mata rai “Adda har kin manta ranar da zai tafi yace mana mun cika masa gida kamar
‘ya’yan Allah bani, wato irin wanda ba’a kaunarsu an dai haifemu bisa lalura. Gara
ma ke kina zuwa wurin Innarki, ni kuwa da kasa ta rufe idon tawa bani da wani gata”

Kuka Mairama take sosai Salame tana bata baki. Yarinya ce mai zuciya shiyasa
abubuwan rashin adalcin gidan nasu suke ci mata tuwo a kwarya. Ada da suke
makarantar kwana idan suka tafi ko marmarin hutu bata yi. Gashi yanzu sun gama
harda watanni. Da yake sune manya Salame mahaifiyarta ce uwargidansa ita kuma
Mairama tata ita ce ta uku. Dukkaninsu babu wadda ta budi ido da mahaifiyarta a
gidan. Yayin da Salame take da mugun sanyin hali ita Mairama saurin fushi gareta
musamman akan yanayin gidan nasu.

Labulen dakin aka bankada Hajjo mai mulkin gidan a yanzu saboda ita ce amarya kuma
yayinta bai kare ba ta sakar musu harara.

“To tabbatattu isassu. Kuna kwance a daki Malamijo ya dawo bazaku je ku gaishe shi
ba”

Da rawar jiki Salame ta mike tana tayar da Mairama “yanzu zamu fito”

Tsaki taja ta koma suka fito babu kowa a tsakar gidan sai kannensu maza da mata
kusan kowa rike da agwaluma daidai a hannu daga su har uwayensu. Hatta Yadikko rike
take da guda tana lailayawa a hannu don taji dadin sha. Kallonsu tayi idanun
Mairama jajir.
“Me ya hanaku fitowa da wuri har ya gama rabon tsaraba?”

Salame taji babu dadi don ranta ya biya. Kayan kwalama irin wannan da wuya yake
musu tsaraba sai anyi matukar sa’a. Harara ta gallawa Mairama don ta tuna ya taba
kawo musu agwalumar kudun akwai zaki. Tare suka shiga rumfar Malamijo. Fankar kasa
ce aka sakar masa a ka yana shan iska kafin a hada ruwan wanka. Tabe baki yayi ya
wani juyar da kai.
“Malamijo yaya hanya?” cewar Salame ya amsa da kyar.

“Barka da dawowa” Mairama tace tana gintse fuska.

“Chege ‘yar kunama wai nan fushi kike yi saboda nashe zan dena ciyar daku kafin
nayi tafiya? Baffanku Kallamu ne ya fada min kuna gamawa zaku fara aikin gwamnati
ku soma daukar albashi kuna yaga min kawai kuma sai naji shiru.”

Da mamaki suke kallonsa. Ashe dalilin tijarar da yayi musu kenan a ranar harda
kiransu kattin banza ‘ya’yan Allah bani. Don kansa ya saki fuska yace yayi bincike
an fada masa ashe sai sunyi wata makarantar ta gaba da sakandire.

“Qur’anin Ubangiji ni kuma bazan sake biya muku komai ba. Ku fiddo mazajen aure na
kawar daku a sami sarari a gidan nan. Ga kannanku nan rida-rida dasu suma kullum
cikin sasake ni suke. Wannan adashin da babu alamun riba na kudin makaranta na
soma gajiya”

Dije mata ta biyu a yanzu tayi burum ta fado dakin

“Yasin Malamijo yarana sai sun gama makaranta. Haka kawai wasu ma suka gama bare
nawa kuma maza”

Hularsa ya turo gaba yana kankance idanu “Ki shiga hankalinki dani Dije. Sai hegen
labe kamar kadangaruwa kullum kina manne da bango. Ina jiye miki kada watarana ki
jiyowa kanki sallama”

Idanu ta zaro cike da tsoro su Salame suka fita suka barsu.

Kwanakin da suka biyo baya gidan bai canja zani ta kowacce fuska ba sai ma tsananin
da Salame da Mairama suka kara shiga na rashin kawo mazajen aure. Malamijo har
ikirarin hadasu da masu yi masa aikin dabbobi yayi. Yaran nasa ne tubarakallah ga
kyau amma fa babu farinjini….da farinjinin dai tsayayye ne babu saboda babu mai
kaunar hada iri da Malamijo saboda halinsa kaf babu na zabe.
[02/11 7:27 AM] My 2nd Mtn: **********
B

ARMY BARRACK SOKOTO
Sojoji ne ta kowane bangare a cikin barikin suna gudanar da al’amuran gabansu.

Yawancinsu sanye suke da farar t-shirt da dogon wandon khakinsu, kadan ne da
cikakkun kayan suna bada umarni a bangarori daban daban.

Cikin jerin wadanda suke gudun da aka fi sani da 4-40 wasu matasa ne guda biyu suke
magana kasakasa don kada a ji me suke tattaunawa.

“zamu din kuwa in fara shiri tun wuri muna gama training”

Wanda yake yiwa maganar yayi gajeren murmushin gefen baki “ta fada min tana da
kanwa kuwa”

Yana kallon yadda farinciki ya bayyana a kan fuskar abokin nasa ya fadada
murmushinsa. Baya bukatar wani abu da zai bata masa ranar ta yau domin burinsa bai
wuce ya sami damar zuwa tadi wurin sabuwar budurwarsa ba. Mantawa suka yi da wurin
da suke suka cigaba da hirarsu sai da suka ji tsawa daga wanda yake jagorantar
training din nasu.

“Tureta and Murtala fall in”
Sun san manufarsa su daidaita kansu da sauran cikin sauri suka ce a tare “Yes sir,
sorry sir”

Daya daga cikin wakokinsu na sojoji da suka saba suka fara yi tare da sauran suna
gudun har lokacin da babban nasu ya dakatar dasu.

“Stand at attention ladies”

Captain Mustapha yace yana zagayesu.

Su biyun ne dai masu surutu dazu suka fara dariya. Ba komai ke basu dariyar ba kuwa
sai cewa da suke idan aka kira su ladies wai sai su rinka hango kawunansu da sauran
cikin kayan mata. Captain Mustapha ya gaji da halinsu don basa ji kwata kwata gashi
a karkashin platoon dinsa suke. Sallamar sauran yayi dama duka a gajiye suke. Da
yatsa ya yiwa samarin biyu alama da su cigaba da gudun sai sun sake zagaye uku zasu
tafi.

Wanda ya fi fitinar ya dube shi hankali a tashe sannan ya kame cikin daga murya
yadda suka fi yin magana da na gaba dasu ya roki alfarmar ya daga horon zuwa
washegari.

Dayan Captain Mustapha ya yiwa kallon tambaya baiyi wata wata ba ya fadi uzurin
abokin nasa, wato zance da zaije wurin sabuwar budurwarsa. Murmushi yayi don ya
sami damar horasu yadda yake so.

“Zayyan Tureta”

“Sir” ya sake kamewa.

“Za ka sake yin zagayen nan sau biyar”

Baki ya bude sai kuma yayi saurin rufe shi don kada ya sake yin laifi. Yana kallo
aka sallami abokin nasa don a bata masa rai tunda duka laifukan da suke aikatawa
shine ja gaba. Hadir Murtala ya faki idon Captain Mustapaha ya yi masa gwalo sannan
ya bar wurin.
Ko da zai kare da rarrafe ya sani bin umarni dole ne.

Juyawa yayi a matukar gajiye zai cigaba da gudun Captain yace yaje gidansa ya jira
shi. Idan ya riga shi zuwa yana bukatar ya dawo ya ga a ina yake. Haka yake so yayi
ta yi har sai ya iske shi a gidan.

A guje ya kwasa sai bangaren gidajen sojojin yaje ya dawo Captain yana nan inda ya
barshi kuma yace ya sake tafiya. Sai da yayi haka sau hudu suna haduwa a kan hanya
a wurare mabanbanta a na karshen suka hadu a kofar gidan. Zuwa lokacin Zayyan da
kyar yake motsa gabbansa amma a haka ya kame a bayan Captain Mustapha.

Murmushi Captain din yayi masa. Yana kaunar yaron saboda kwazo da himma amma rashin
jinsa yayi yawa.

“Kana jin yunwa na sani. Mu shiga ciki kaci abinci”

Mamaki ne ya bayyana a fuskarsa don ba haka ya zata ba. Tunaninsa kullum Captain
Mustapha shi yafi tsana duk cikin platoon dinsu. A waje ya jira shi ya fara shiga
ya nemi iyalinsa su shirya zai shigo da bako.
Wani yaro ne da zaiyi kimanin shekaru bakwai ya fito a guje yana dariya yazo
gabansa ya tsaya.

“Kaine Tureta?”

Sakin fuska yayi don akwai shi da son yara “nine”
Sai kawai yaron ya dane jikinsa har suka kusa faduwa yana kyalkyala dariya ya soma
surutu

“kaine kayi karyar rashin lafiya don kada kaje training? Daddy yace rannan ka
sakawa wani kunama a takalmi saboda ya shiga masallaci da takalminsa. Kuma wai ka
iya karatu mai dadi amma baka jin magana”

Baki Zayyan ya rike yana kallon yaron yana ta zuba da bashi labarin abubuwan da
yake na rashin ji tun zuwansa barrack din. Gyaran muryar Captain din suka ji yaron
ya nutsu yana rike da hannun Zayyan.

“Awwab?”

Sunkuyar da kai yaron yayi yana kara matse masa hannu suka yi murmushi tare. Bayan
Captain ya bi har cikin falon. Matarsa Hassana da ake kira Mami ta fito fuska a
sake ta nuna masa wurin zama da dan tebur a gaban kujerar wanda ta dora tray din
abinci da abin sha. Wuri suka bashi yana cin abinci Awwab na masa hira tamkar sun
dade da sanin juna. Sai bayan rabin awa Captain ya sake fitowa sanye da jallabiya
irin mai gajeren hannu da fadin nan. Zayyan ya dan gyara zama ya fusakance shi.

“Awwab ya dame ka da surutu ko? Halinku daya na fitina amma shi matsoraci ne”

Dariya Zayyan yayi yana kallon yaron da ya shiga ransa cikin kankanin lokaci. Basu
dade suna hira ba Captain ya sallame shi bayan dogon gargadi akan halayyarsa idan
ba yana da burin a kore shi tun kafin ya zama wani a cikin sojojin ba.

Har Hadir ya dawo Zayyan yana mamakin Captain Mustapha. Mutumin baya magana sosai
idan ta wuce karbar umarni da badawa. Kuma baya nuna damuwarsa akan kowa amma ace
wai banda sanin halinsa har labarinsa yake bawa iyalinsa. Hannun Hadir yaji akan
kafadarsa yana jijjigawa.

“Zayyan lafiyarka kuwa? Inata magana kamar baka ji. Nace naje wurin Zainab mun
daidaita kanmu”

“Na tayaku murna”

Cikin yanayin ko in kula yayi maganar hakan yasa Hadir taba wuyansa “zazzabi kake
ko ciwon kai? Zainab fa nace mun hada kanmu. Da naje babanta ya fito yana yi min
tambayoyi karshe yace in turo. Ina ta kokarin fahimtar dashi ba kai bane sai da ya
tafi tace ta amince min itama. Nima kuma na gani ina so….”

“Wai kasan yau a gidan Captain naci abinci har muka yi hira? Ashe haka yake da
kirki mune bamu fahimce shi ba. Kuma yana da da dan shekara bakwai abin mamaki yayi
auren wuri inajin.”

Hadir ya kalli Zayyan ya tabbatar kalau yake sai ya rabu dashi. Washegari ne suka
sake hirar bayan kowa ya dawo hayyacinsa. Hadir da gaske ya nuna yana son Zainab
kamar yadda ta amince masa shi kuma Zayyan jin kansa yake ya kara girma saboda ya
fahimci Captain baya kinsa. Kowa da nasa farincikin a haka abokan suka cigaba da
zaman barikin suna horowa akan matakan kariya da tsaro. A gefe daya maganar su
Hadir tayi nisa yana shirye shiryen idan sun sami hutu zaije Kano ya sanar da
iyayensa su zo su nema masa aurenta. Zayyan kuma wata nutsuwa ce take sauko masa
don ya burge Captain sannan ga shakuwa mai karfi tsakaninsa da Awwab da kannensa
mata biyu.
Kimanin watanni biyar sun shude kafin aka basu hutun sallah wanda ba wasu kwanaki
bane na azo a gani.
Duk da haka sun karba da godiya kowa yayi nasa wuri. Hadir mutumin Kano ne dan
cikin gari unguwar Madungurun. Shi kuma Zayyan dan wata karamar hukuma ne a cikin
Sakkwato, wato Tureta wadda ta zama inkiyarsa a barikin amma gidansu yana cikin
garin Sakkwaton. Sun tafi gida da murna da abinda suka samu a matsayin albashi
kasancewarsu a mukami mafi karanta a cikin sojojin Nigeria, Second Lieutenant. Su
biyun da mafiya yawa daga cikinsu sun zabi shiga aikin soja ne domin zama ababen
alfahari ga kasar da basu da kamarta. Nigeria kasar da manya manyan dattawa daga
bangarori daban daban suka hadu suka hada karfi da karfe wurin kwato mata ‘yanci.
Wadannan matasan sojoji zukatansu sun tafi ga ganin sun zama kariya ga al’ummar
kasarsu batare da duba da bambancin yare, addini ko al’ada ba. Da wannan kyakkyawar
manufa su Zayyan suka baro jindadi da kwanciyar hankalin da suke samu a gaban
iyayensu suka sadaukar da kuruciyarsu don samarwa na baya kasar da zasuyi alfahari
da ita.

**********

Tamkar ba soja ba tun da ya nufo gidansu yake jin faduwar gaba. Don ta shi a datse
hutunsu saboda babu abinda yake tsinta a gidan nasu da ya wuce bacin rai da
bakincikin matar uba da ya’yanta. Zayyan maraya ne ba uwa ba uba. Mahaifiyarsa
mutuniyar Nijar ce ‘yar kabilar Tamasheq a cikin Agadas, mahaifinsa ne Basakkwace.
Sun hadu a yawon fataucinsa na dabino da cukwi da yake zuwa sarowa. Soyayyar lokaci
guda ce ta kamasu shi da Alheran bai kuma sha wahala ba babanta Alh Ghousman Agali
ya amince masa kasancewarsa kwastomansa da aminci ya dade da wanzuwa a tsakaninsu.
Mal Muhammadu Tureta a lokacin yana da matar aure guda daya Jume da yara shida,
maza uku mata uku kuma shima kasuwanci yana damawa dashi kafin daga baya karayar
arziki ta same shi. Wani mummunan zama akayi tsakanin Jume da Alheran. Da fari
Alheran ta kwantar da kai sosai tana bin Jume sau da kafa duk da irin wulakanci da
cin kashin da take yi mata ita da yaranta. Allah ma Ya taimaketa tana jin Hausa
saboda cudanya da suke yi da Hausawan kasar tasu.

Bayan wani lokaci tana hadiyar bacin rai ita kadai ga gorin haihuwa ta ajiye
kawaicin a gefe suke bugawa. Idan Jume ta shirya makircinta Alheran zata fidda
kanta da kissar da wahala ta sanya ta koya karfi da yaji. A shekara ta uku da
aurensu Allah Ya bata ciki. Sunyi murna ba kadan ba ita da maigidanta. Yadda yake
matukar sonta haka yake son abinda yake cikin nata. Wata tara da kwanaki kadan
Allah Ya sauketa lafiya aka sami Zayyan. Kafin suyi arba’in Alh Ghousman ya rasu.
Alheran tasha kuka Mal Muhammadu ya dauketa suka tafi Nijar. A can ya barota bayan
yayi kwana goma sai da ta shefe watanni biyu domin bayan anyi ar’bain aka zo rabon
gado kanin Alh Ghousman yayi tsallan badake yace dukiyarsa ce kaf yayansa yake
juyawa. Aka buga aka raya ya dauko shaidun karya harda barazanar kai iyalan dan
uwan nasa kara. Rigima gagaruma akayi karshe suka hakura ya basu abinda yayi niyya
cikin dukiyar mahaifinsu ya handame sauran. Da wannan bakincikin ta dawo Sakkwato
sai mijinta ne yake ta kokarin kwantar mata da hankali.

Zayyan na da shekara uku ta sake samun ciki. Wannan karon tana laulayi mai
wahalarwa wasu lokutan ko yatsa bata iya dagawa, amma duk da haka bata tsira daga
kaidin Jume. A haka ta shiga wata tara.

Wata asabar ta tashi da nakuda gashi Mal Muhammadu yayi sammakon fita ranar yaran
duka su ma basa nan. Tana cikin wannan yanayi ta rinka kiran Jume tana jinta tayi
biris abinta. Cikin tsananin azaba Alheran ta soma yunkurin haihuwa abinda ke
cikinta kansa ne kawai ya leko Allah Ya karbi ranta. Shima kuma wahala bata barshi
ba bai jima ba ya koma. Jume ta ma manta da cewa ta ji Alheran tana kiranta wanda
tasan haihuwa ce tayi kwanciyarta tana bacci. A yashe a kasa Mal

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login