Showing 153001 words to 156000 words out of 295847 words

Chapter 52 - Ku Dube Mu by Batul Mamman

wadanda su ma suke
karatu kuma take ta kokarin gyara zumuncin gidansu shiyasa ta taho dasu.


Baba Hadir kuma watansu uku suka dawo yana motsa hannuwansa da kafa amma tafiyar
bata kankama ba sosai sai yau da Ibrahim ya fadawa Radhiya.


***********


"Dad please kaje dani mana"


"Ke komai kike so sai anyi miki ne kamar wata yarinya?" Inji mamanta


"Kina matsa mata da yawa fa. Meye a ciki don ta raka babanta taron karrama sojoji
masu fita (POP)"


"Naga official taro ne your excellency " maman tace tana murmushi.


"Official baya nufin naki zuwa da 'yata. Arifah ki shirya dake zani Kadunan"


Bayan ta fita daga dakin nasa tana dariya mamanta ta sake sako masa zancen rashin
aurenta da yake damunta.


"Kasanta da jin kai gashi masu yawan zuwa yanzu yawanci duka saboda mukaminka suke
son ace sun zama surukan gwamna"


"Ki dena damuwa mijinta yana tafe in sha Allah. Ni fa tafiyar nan wani dadi nake ji
game da ita na rasa dalili."


Murmushi tayi tana tunanin ko don yana kewar harkokinsu na sojoji ne. Gashi a
matsayinsa na tsohon soja an gayyace shi bako na musamman a taron POP din sababbin
jaruman da kasa zata yaye bana.

💕[11/2, 7:11 AM]: 37. 💕
Sabon salon make murya yayi don ya ga alamun larabawa ne mutanen nan "Assalam
alaikum ya 'yan uwa. Kaifal durus wa ayna kaifal amal"


Allah Yasa akwai hayaniya a wurin kuma ya make murya ba kowa yaji ba sai Ummi da
Radhiya. Kunya kamar Ummi ta nutse Radhiya kuwa juyawa tayi zata bar wurin saboda
kunya ga dariya na cin ta. Malamijo ko a kwalarsa ya rinka mika hannu ana gaisawa.
Ya sha mamaki ashe Zayyan yana da wannan dangi masu arziki haka amma yaron nan
Maikudi ko tsinanne wallahi. Yayi musu tsakani da arziki irin wannan.


Magariba har ta kawo kai suka tashi aka rako su waje. Mammee tana kallon Ummi da
murmushi tace "ni kuwa ina wani yaro nan lokacin taron sunan Alheran wanda baya son
kowa ya tabata. Har yanzu ina da hotonku tare"


Ummi ta kalli Awwab tana dariya lokacin ya gane dashi ake ya zubawa Radhiya ido aka
rinka dariya da Mammee tana fadin irin rigimar da aka rinka yi dashi da masu son
daukar baby.


"Ina fata dashi zamu yi bikin ko?" Alh Sidi yace yana riko hannun Radhiya da ta
dukar da kai.


Malamijo sai dariya "au, au, ashe anata abu bani da labari. Kai abu kyau"


Awwab ya kurawa Radhiya idanu fuskarsa dauke da murmushi ko kunya, yadda kowa sai
da ya fuskanci akwai wani abu a tsakaninsu. Iyaye sai murna don abin yayi musu
dadi. Sun fadawa Ummi zasu shigar da kara akan Maikudi amma sai bayan sunje musu
tukunna. Bayan tafiyarsu Radhiya da wasu suka je suna kwashe kwanuka a can gefe
kuma Ummi ce ta zaunar dashi da plate din abinci.


"Na kula ba ka son cin abinci Awwab. Ko yanayin aikinka ne yasa ka zama haka? Ace
mutum da ance abinci sai yace baya jin yunwa"


Janyo plate din yayi yana kallon inda Radhiya ta duka tana daukar food flask. Ummi
ta kawar da kai tana murmushi har sai da ya gama cin abincin sannan ta nutsu ta
fara magana.


''Awwab akwai abinda yake faruwa ne a Katsina?"


Da sauri ya dago don da fari wata 'yar kunyarta yake ji.


"Me kika ji?"


"Ka fada min dai idan akwai abinda ke faruwa wanda ya kamata na sani. Gobe in sha
Allah zamu bika mu tafi tare don yadda naji kukan Fauziyya hankalina ya tashi"


Wayarsa ta ga yana lalube a aljihu hankalinsa duk a tashe ta mika masa saboda ya
manta ya bata dazu da aka kira. Ita kuma bata son boye masa saboda iyaye ba abin
wasa bane. Ta yiwu zai iya magance matsalar a matsayinsa na babba. Yana karba ya
shiga kiran Fauziyya wayarta tana chaji bata ji ba.


"Ummi akwai bayanin da nake son yi miki"


A raunane yayi maganar shiyasa kafin ya fara hankalinta ya sake tashi. Bai boye
mata komai ba dangane da Ghazalatu da Radhiya da yake son hadasu.



"Ita wannan din ce take tayar maka da hankali akan bazata zauna da Ghazalatu din ba
ko yaya?"


Dukar da kansa yayi nauyin maganar yasa bai iya bude bakinsa yayi mata gaskiyar
bayani ba.

"A'a Ummi ta amice"


Hakura tayi bata matsa masa ba saboda tana ganin akwai abinda bai dace ta matsa sai
ta sani ba musamman idan danginsu ya shafa. Fatanta bai wuce kada ya kasance
matsala aka samu game da neman Radhiya da yayi ba tunda Fauziyya tace Mummy din
taje sunyi fada da Mami. Wannan damuwar ita ce ta karfafa mata gwiwar son zuwa
Katsinan a washegari. Daren ranar suka yi waya da Zainab suna airport zasu tashi.
Ummi tayi ta jero addu'o'i suna fatan Allah Yasa ayi komai cikin nasara Baba Hadir
ya dawo musu da kafafunsa.


Washegari kuwa bayan daurin aure Ummi suka shirya tafiya Katsina ba zata sami kai
amaren ba. Babu irin tunanin da bata yi ba a matsayin dalilin da zaisa 'yan uwan
Mami su zo gidanta suyi fada da ita da ya wuce kin amincewa ace ko auren Ghazalatu
ba'ayi ba Daddy ya newa Awwab wani auren shi kuma ya karba.


Emzee ne a gaba Radhiya da Ummi a baya. Ba wata hira suke yi sosai ba. Ummi da
Awwab tunanin me zasu tarar a can ke damunsu. Radhiya kuma shirun da ta ga yayi tun
jiya bai sake nemanta ba shine yasa itama ta kama nata bakin.

**********


Sallah Ummi ta idar ta kasa taba komai cikin kayan abincin da aka ajiye mata. Tunda
idanunta suka bude sai yau suka hadu. A waya Mami ta nuna tsananin farinciki ta
tayata murna amma yau da suka hadu abu na farko da ta fara gani a fuskarta shine
damuwa. A haka ma Mami tana ta kokarin boyewa ne. Taji dadin dai ganin Mamin tayi
kyau haka ma su Zahra. Sai dai kaifin tunaninta yasa tasha jinin jikinta da wuri.
Yaran da iyayensu duka suna tattare da wani abu na rashin jindadi a zukatansu.


"Ummin Awwab har yanzu baki tashi kinci abincin ba? Ko na zuba miki da kaina ne?"
Mami ta fada lokacin da take shigowa dakin rike da katunan daurin aurensu Zahra da
aka aiko daga gidan Alh Baba.


"Gajiya ce take tambayata Mami"


"Ga kuma wata da zata tarar miki ke kadai tunda Zainab bata nan"


Ummi ta mike tsaye tana ninke sallayar "dadin abin Maman Ghazalatu da Anti Hussaina
suna nan sai muyi tare"


A take yanayin fuskar Mamin ya sauya wanda shi Ummin ke nema don ta tabbatar da
cewa lallai akwai wata a kasa. Mami sai ta chanja akalar zancen ta dauko hirar
mutanen Nijar.
A bangaren 'yan matan ma Radhiya ce kadai a daki. Zayyana tana falo tare da Emzee
yana cin abinci tana zuba surutu da labarin shirin biki da take yi. Fauziyya kuma
tana can wurin Awwab tana yi masa bayanin abinda taji kuma ta gani a jiya suka
rutsa Zahra akan sai ta fadi waye take so tana ta kuka.


A hasale yace "shirunki bashi da wani amfani da zai mana"


"Kamar yadda fadar ma bata da amfani. Hamma na riga na hakura ba shikenan ba"


"Zahra please ki fada mana" Fauziyya tace idanunta suna taruwar kwalla.


"Let us help you Zahra" Awwab ya sassauta muryarsa yana kallon kanwar tasa.


"Raji ne" tace da muryar da kuka ya sauya ta.


"Raji Abdulwahab?" Awwab yace mamaki na bayyana a fuskarsa. Abokinsa ne duk da cewa
Raji din ya dan girme masa. A zuwa masallaci sallar juma'a da suka mayar al'adar
gidansu a zaman Germany suka hadu da iyalin Ayodeji Abdulwahab mahaifin Raji. Wani
abin dadi shine limami a community din da suka hada nasu na musulmai a wurin 'yan
kasashe daban daban. Tasu tazo daya da Raji babban dan Limamin wanda yake aiki a
kamfanin Benz. Yana yawan zuwa gidansu ashe Zahra yake so babu wanda ya sani.


Kai ta gyade ta kuma fashe musu da kuka "nasan babu mai yarda na aure shi saboda
bayerabe ne shiyasa na kasa fada da wuri. Daga baya Mami ta sani kuma lokacin tayi
alkawarin fadawa Daddy su yiwa Alh Baba magana sai kawai muka ji zancen Fawaz.
Wallahi Hamma Raji har kwanciya yayi a asibiti"


Kukanta yana taba masa zuciya fiye da zato da tsammani. Shi kam Allah bai dora masa
kabilanci ba musamman ga dan uwansa musulmi a duk inda yake. Sai dai a yadda ya
fuskanci akidar su Alh Baba son kansu da yasa suka dagewa auren zumunci kadai
babbar matsala ce balle kuma ace wani yaren daban.


"Daddy yayi miki magana ne jiya bayan Mami ta fada?"


"Yayi min da daddare. Baiji dadi ba da bamu fada masa da wuri ba gashi lokaci ya
kure. Hamma yaya zanyi? Shekaranjiya da Munirat ta kirani kuka take yi wai bashi da
lafiya har yanzu"


Tana kuka ne Fauziyya ma na tayata aka bar Awwab da aikin rarrashi. Kamar ance Mami
ta leka su ta gansu a wannan yanayi ta kuma ji karshen maganganun nasu. Kwalla ce
ta cika mata idanu ta koma batare da ta bari sun ganta ba. Rayuwar 'ya'yanta duka
ta shiga wani yanayi. Fauziyya ce kadai take tunanin kila sun hada kai ita da Bilal
ta kula ya ma fi Fawaz zuwa dama. Abin dai duka kadaran kadahan babu wani karsashi
ko doki a bangaren amaren da angwaye.


Wurin Ummi ta koma suna dan taba hirar Zainab taji sallamar babar Fawaz matar
cousin dinta saboda ta bangaren namiji suka hadu. A harzuke ta shigo gidan ranta
yayi masifar baci ita da Mummy Gambo. Zayyana da take falo da Emzee aka dakawa
tsawar ina mahaifiyarta ta ruga daki ta kirawota.


Mami na ganinsu tasan ba lafiya ba ta dai daure tana cewa su zauna mana.


"Ba zama nazo yi ba Hassana" Haj Azumi tace cikin kaushin murya "ni zaki wulakanta
har kike ikirarin 'yarki bata son Fawaz? To wallahi ki jika abarki ki sha indai ni
na haife shi ko ana muzuru ana shaho a dangin nan naku Fawaz bazai auri Zahra ba.
Ke wallahi bari kiji in fada miki ko aurena ne zai mutu sai dai ayita ta kare"


Mami ta daga kai ta kalli Gambo tana mamakin wai kanwarta da suka fito ciki daya ce
take ingiza wannan rigima. Ummi bata fito daga daki ba amma tana jin komai. Haka ma
su Awwab dake daki ya hana kannensa fitowa saboda a ganinsa hakan bai kamata ba.
Radhiya kuwa tsurewa tayi ita kadai a daki tana jin ana wannan daga murya. Ita
fadan ba shine ya dameta ba kamar cewa da matar take yi danta bazai auri Adda Zahra
ba. Me yayi zafi haka za'a raba masoya?


"Haj Azumi ki zauna muyi magana don Allah. Gidan nan da baki ga yara"


"Baki? Ke suka dama bakin. Idan 'yan biki ne suka fara zuwa gara su ji su tattara
su koma inda suka fito. Aure ne nace a bawa Zahra da ta tashi a kasar waje tafi
karfin dana wanda take so. Shi kuwa zan baku mamaki muna nan tare daku mata biyu
zan aura masa a rana daya wanda suka fi taki komai da komai"


"Gambo kinga abinda kika jawo ko?" Mami tace muryarta na fallasa yadda abin yake
mata ciwo.


"Sai kiji idan da dadi, ni ba tawa 'yar kike neman hanawa nata farincikin ba. Ko
bikinsu ba'ayi ba kunje kun nema masa auren wata saboda tsabar son burgewa ace kuna
da zumunci. To amma banda abinki zumunci ya wuce ka fara yi da jininka. Mutanen nan
'yan kauye n....."


Wani lafiyayyen mari Mami ta saukewa Mummy Gambo idanunta jajir kamar garwashi.
Gidan gabadaya shiru yayi Ummi ta kasa daurewa duk da ta soma hawaye ta fito. Awwab
ma fitowar yayi bayan ya gama waya da Daddy ya sanar dashi rigimar da ake yi.


"Gambo ki kiyayeni wallahi. Ba tsoronki nake ji ba sannan baki fi karfina ba. Ki
fice min daga gida kafin mu kaiga abinda rayuka zasu fi haka baci"


"Ni kika mara Hassana saboda wasu can bare da kika hadu dasu rana tsaka?" Mummy
tace hawaye na neman zubo mata.


Ummi lokacin ta fito zuciyarta ta gama karaya ace saboda ita ko 'ya'yanta ake
wannan rigima "Mami don Allah kuyi hakuri"


"Au dama kina ciki? Kun lallabo a cigaba da cusa masa 'ya don ya aura"
Awwab zaiyi magana aka kira shi. Zuciyarsa har suya take saboda bacin rai amma ya
tabbatar idan yayi wani abu na rashin da'a ga matan da suke da matsayin iyaye a
gareshi ba karamin fushi Mami zata yi ba ko da kuwa yayi haka ne domin rama mata.
Sunan Alh Baba ya gani sai da yasha jinin jikinsa.


"Muhammad da kai da kannenka da iyayenka dake cikin gidan nan kuzo gabadaya yanzu
ina jiranku"


Sai da ya dan rissina ya amsa masa sannan ya fada musu sakonsa. Haj Azumi da Mummy
suka fita suna ta masifa. Mami ta kalli Ummi kunyar baiwar Allahn nan ta sa ko
idonta ta kasa kallo. Murmushi Ummi tayi ta saki fuska.


"In sha Allahu komai zai daidaita"


"Kiyi hakuri Mairama ban so kika tarar da wannan rigimar ba"


"Haba Mami waye bai san ire iren wadannan matsalolin na dangi ba? Kuje ku dawo
Allah Ya kawo mana mafita"


Daki Mami ta wuce ta sako hijabi ta fito. Fauziyya da Zahra harda Zayyana su ma
kowacce da lullubinta. Ta kalli Zayyana tace mata ta zauna kiran bai shafeta ba.
Dama a firgice take saboda haka bata ji komai ba sai murna da aka hanata zuwa. Suna
fita Mairama ta dubi Emzee.


"Ina yayarka?"


"Tana dakinmu Ummi" Zayyana ta bata amsa.


"Turo min ita dakin Mami ku zauna a nan ke da Karami."


Hawaye ne sharbe a fuskar Radhiya lokacin da ta shiga dakin ta fada jikin Umminta
tana kuka sosai. Taji komai kuma ta fahimta. Duk da bata ga fuskokinsu ba amma ta
gane akwai maman Ghazalatu kuma bata so ta auri Awwab. Ita kuwa wani irin mugun
sonsa ma take ji yanzu bata fatan giftawar abinda zai iya raba su. Bata ki ba ko
mata uku za'a aura masa a danginsu indai itama zata sami gurbi a zuciyarsa da
gidansa.


"Alheran"


Faduwar gaba taji saboda bazata iya tuna yaushe ne taji sunanta ya fito daga bakin
mahaifiyarta ba.


"Na'am"
"Kina son Awwab ne?"


Da ka ta amsa sababbin hawaye na gudu akan kumatunta.


"Meye matsayina a gareki?" Mairama tace babu alamun wasa da ta bari a fuskarta duk
kuwa da cewa abinda take niyar yi tamkar ana yankar zuciyarta ne. Iyalin Major
Mustapha wani bangare ne na rayuwarsu da bazata taba mantawa da alkhairinsu ba.
Daga dawowarsu sai fadi tashi yake a kansu musamman na hadasu da danginsu da yayi.


"Babata ce" cewar Radhiya gabanta na sake faduwa.


"Daga yau babu ke babu Awwab kina jina?" A gigice Radhiya ta dago kai Ummi ta
cigaba da magana nata hawayen na zuba "bani ba ko mahaifinki bana jin akwai mutumin
da zaiso bawa aurenki sama da Awwab amma daga ke har shi farincikinku yayi kadan ya
haddasa husuma a tsakanin iyaye. Saboda soyayyarku Mami yau ta daga hannu ta mari
kanwarta. Zaman da nayi dasu na kwanaki da kuna Kano babu ranar da Mami bazata ce
Gambo ba saboda yadda take sonta ta amma yau akanki ta mareta"


Jiki na rawa Radhiya tace "Ummi kada ki rabani da Hamma don Allah. Ummi tunda na
fada da bakina wallahi kinsan ina son shi....Ummi don Allah"


"Kina sha'awar aure a dangin da basa sonki? Ko an fada miki idan kika aure shi daga
ke sai shi sai iyayensa? Bazaki yi mu'amala da sauran 'yan uwansa bane?"


Shiru tayi babu amsa sai kukan da take yi mai sauti tana gurfane a gaban
mahaifiyarta.


"Gata nake son yi muku ke dashi. Aurenku a yanzu babu abinda zai kawo sai tashin
hankali da rabuwar zumunci. Mu da muka tashi da karancin dangi ai kinga yadda
abubuwa suka kasance mana kafin zuwansu Innawuro ko? Kina sha'awar ki mutu a rasa
mai kula da 'ya'yanki saboda kiyayyar da ake yi miki ne?"


"A'a"


"Alheran Daddynku Major da Mami da 'ya'yansu duka suna son mu suna mutuntamu.
Sakayyar da zamu yi musu kenan mu rabasu da da nasu 'yan uwan? Kina ganin zaki taba
yafewa wata mace ta gida ko bare da zata yi kokarin rabaki da Karami misali? Ki
tayani sakawa su Mami da alkhairi na tabbatar miki wallahi Allah bazai bari ki
wulakanta ba. Ki taimaka kada ki zama sanadin datse igiyar zumunci ki gani idan
Allah bai saka miki da alkhairi ba. Ana barin halal ko don kunya kinji. Kin girma
ke ba wannan karamar yarinyar bace da take fita ayi dambe da ita. Kece kike da
burin yin abin alkhairi domin a nuna ki ace 'yar Zayyan Tureta ce ga dama ta samu
gareki."


Babu abinda Ummi ta fada mata wanda ba gaskiya ba. Baza ta taba yarda ta batawa
Umminta ba bayan wahalar da tasha akansu kuma ta sani cewa rabuwarsu zata taimaka
kwarai wurin daidaita lamura. Tana share hawaye saboda yadda take jin zafin zuciya
har dafe kirjinta tayi tace "Ummi to yaya zanyi da son shi?" muryarta can kasa
kamar ba Radhiya ba.


Tsantsar tausayi da soyayyar 'ya da uwa suka sa Mairama kuka itama. Rabuwa da
masoyi akwai ciwo mai radadi. Bata taba mantawa da Zayyan ba haka nan har yanzu
zuciyarta bata rabo da tasowar kunci lokaci zuwa lokaci idan ta tuna sun rabu kenan
har abada. Soyayya ciwo ce da bata warkewa sai dai hakuri babu abinda ya bari.


"Kiyi hakuri a hankali zaki rinka jin sauki a zuciyarki. Da kaina zan fada musu
cewa ba kya son auren. Ina ganin ma idan munje Nijar din in barki a can har komai
ya lafa"


Duka zantukan da suka yi tun shigar Radhiya dakin zuwa yanzu a kunnuwan Umman su
Mami ne. Ta taho gidan cikin fushi ne saboda a ganinta Mami ita ke neman raba
zumunci tsakanin kannenta. Ko gaisuwar Emzee da Zayyana da suke falon bata amsa ba
tace ta nuna mata dakin Mamin batare da ta saurari bayanin da take mata na cewa
basa gidan ba. Juyawa tayi ta tafi batare da ta yiwa kowa magana ba.

[11/2, 7:11 AM] 🏽
🏽 : 39. 💕

Mami sai da ta waiga baya ta tabbatar su kadai ne sannan ta girgiza kai "kinyi sa'a
da yara a gidan nan da na miki dan biki. Zan zo har gida na sameki"


Da dariya Mama ta bi bayan Ummi saboda yadda ta tsani gidan nata. Komai warinsa
take ji ta rinka amai kenan. Ibrahim abu duk ya dame shi Allah bai sa ya fahimci
kani ko kanwarsa ke tafe ba.


**********


Kwana biyar da dawowarsu Mami Major ya sami waya daga His Excellency yana shaida
masa ya shigo Abuja ko zasu zo shi da Hadir su gaisa.

Mami ya fadawa ta rike baki "yanzu Daddy gwamna da kansa yake kiranka?"


"Mutumin kirkinsa yayi yawa har ina jin tsoro. Ni bana son shigewa 'yan siyasa"


"In sha Allahu alkhairi ya kawo shi garemu. Allah Ya sani bamu cuci kowa ba bazai
hadamu da macuci ba"


"Shiyasa nake son Hassanata."


Dariya tayi tana jindadin yadda mijinta yake yaba mata komai kankantar abu.


"Ki sanar da danki ya shirya muje tare"


"Yau kuma? Awwab ya ga ta kansa. Umminsa ta saka shi a gaba akan zuwa gidan Gambo
sai cewa yake zaije amma har yau shiru. Ni dama abin nasu da Hussaina ya dena bani
mamaki.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login