Showing 192001 words to 195000 words out of 295847 words

Chapter 65 - Ku Dube Mu by Batul Mamman

da wata kalmar
don naji dadi"


"Zayyan...fitina" yace yana dariya

[11/2, 7:24 AM]🏽
]🏽 : 48..💕

"Kinci albarkacin 'yarki bazan biye miki ba" Maman Danmama tace tana sakin labulen.


Bata bar wurin ba Halifa yayi sallama. Muryarsa kamar a kan Salame akayi recording
tuni ta gano ko waye tace ya shigo. Sai da ta fita ta harari Maman Danmama irin
abin nan na danta yazo sannan tace ya shigo ciki. Kannen nasa ma an sabar musu idan
sun ganshi sun ga kudi ko abincin kirki shiyasa suna ganinsa suka fara murna zasu
rungume shi ya dakatar dasu. Kazamai ne na ajin karshe shi kuma tsaftarsa har taso
tayi yawa. Zama ma kasawa yayi dakin wari da zarnin fitsari kawai yake yi. Rahima
da kanta ke duke tana sharar kwalla ta dan dago da murmushi don tasan sunan ko da
suke dadewa basu hadu ba.


"Yaya Halifa barka da zuwa"


Wata muguwar tsawa Salame ta daka mata "tashi dan ubanki kwadayayiya. Wuce ki tafi
gidanku ai kin dubani mun gaisa ko."


Zabura tayi ta mike a gigice saboda yadda ta razana da tsawar tayi hanyar kofa
Halifa ya fincikota saboda gefen fuskarta kawai ya gani ya gane kanwarsa ce.


"Rahima" ya furta a hankali yana kallon jajayen idanunta. Yarinyar da kadan ta fi
rabinsa. 'Yar karama ce wahalar rayuwa ta tsotseta.


"Cikani" tace wasu hawayen masu zafi na sauko mata ta kwace hannunta ta fita. Ta
sani Ummansu bata kaunarta amma yadda take nuna bambanci kirikiri yana kona mata
rai. Mahaifinta talaka ne futuk amma yana kaunarta tamkar rai. Amaryarsa da ta fara
son azabtar da ita dashi da babarsa suka tashi tsaye akan ko ta rungumeta kamar 'ya
ko ta koma inda ta fito. Kudin sana'arta da Salame take sakawa ido har nawa ne?
Zuwan karshe gabadaya ta tattara mata kudin ta bayar. Wannan karon kuma a kofar
gida taji wani makocinsu yana yiwa babanta tijara akan ya ranta masa kudin da ya
biya mata WAEC da zata rubuta a farkon sabuwar shekara bai biya ba. Tilas da fito
da kudin ta bashi ya bawa mutumin ba don yaso ba. Abin ko kwana uku ba'ayi ba kuma
babu wanda ta yiwa lalle bayan nan bare ta sami na zuwa dubiyar. Yanzu abin takaici
zani daga akwati Salame ta dauko za ta shimfidawa Halifa saboda babansa yana da
kudi.


Ta soma tafiya kenan Halifa ya risketa ashe ya biyota "Rahima tsaya mana"


Cak ta tsaya amma bata ce masa komai ba. Hannunta ya kama ya dora mata bandir din
naira dari bibbiyu sababbi "kiyi hakuri da halin Umma. Ki rike wannan zan zo gidan
naku muyi magana kinji ko"


"Nagode" sai dai kudin mika masa tayi yaki karba sai kawai ta ajiye akan wani bulo
da yake gefen hanyar irin wanda ake zama a kai tayi gaba abinta tana goge hawaye.


Ko kadan Halifa baiji dadi ba. Sai ya tuna da Radhiya tace shine babba ya kamata ya
hade kan kannensa. Idan suka tafi a haka tabbas Salame zata ginasu da kiyayyar juna
ne. Kana ganin Rahima kasan tana bukatar taimako amma zuciya irin tata ta sanya
bazata kwantar da kai tana roko ba bare aji dadin goranta mata. Idan ruwa kadai
babanta zai iya bata tasha in sha Allahu zata yi hakuri dashi bazata gaza ba.


Da yake ana ji dashi ko fadan bin Rahima da yayi bata masa ba sai kudurin ko nawa
ya bata sai tasa ta kawo mata.
"Zauna mana mu gaisa ka tsaya"


"Sauri nake yi Umma. Dama munzo da baki ne gidan Malamijo shine nace ko zaki zo ku
gaisa"


Fuskarta ta nuna bata ji dadi ba "can kuma ka fara zuwa?"


"Ko shiga banyi ba na taho nan"


"Su waye bakin?"


"Su Gwaggo Mairama ne..."


So tayi ta kwada masa mari sai dai kuma kada ta toshewa kanta kofar ihsani dan
abinda zai bata ya fasa.


"Mairaman zanje in gaisar saboda ka raina uwarka? Me ya kaika wurinta har kake cewa
tare kuka zo?"


Shi fa irin wadannan abubuwan ke kara nesanta shi da ita.

"Umma tare muka zo daga Abuja kuma ba ita kadai bace"


Tabe baki tayi "wato ka fara shege mata kawai saboda ance tana wani karatun banza a
Kano kuma suna zuwa Abuja ko. To bari kaji in fada maka duka kwarewa ne a maula ita
da 'ya'yan suke zubar da mutumcinsu a gaban masu kudi. Ni nafi tunanin aikatau take
yi"


"Umma ni zan tafi idan bazaki je ba. Na rasa me tayi miki ba kya gajiya da aibata
ta. Ga wannan" ya mika mata kudi a cikin envelop da ya riko dominta.


"To muje bari na dauko mayafi" tace a sanyaye bata kaunar batawa yaron nan rai.
Iyaka idan taje ta yanka mata kashedi ta dena bibiyar danta ba tare suka haifeshi
ba.


Ba wata tafiyar kirki suka yi ba suka iso kofar gidan Salame tana ta hura hanci ita
mai da. Sauran kuwa a gida ta barsu har wadda ta yaye idan ta sami abinci ta tafi
musu dashi.


Emzee da Ibrahim suna bakin mota suna sauko da kaya suka iso.


"Drama ta barka Halifa" Emzee yace yana dariya.


"Ko me akayi a dawo dashi farko gaskiya"
Salame ta kallesu ta watsar Emzee sau biyu yana cewa Gwaggo Salame ina wuni tayi
kamar bata ji ba. Sai yake ya yiwa Ibrahim shima bata amsa shi ba yace wai kila don
tana sauri ne bata ji su ba. Ta kai bakin kofa su kuma suna fitowa. Ummi da Daada
zasu yiwa rakiya da zasu tafi yanzu. Sai kuma dreban gidan su Halifa shima zai tafi
idan sun tashi tafiya Halifa zai kira shi yazo ya tafi dasu.


Gaban Salame wani irin bugu yayi da ta ga Mairama tayi wani irin kyau ta kara
haske. Kayan jikinta a hasashen Salame sai kace wata matar gwamna. Wannan 'yar ta
ta mai kama da aljanu itama ka kalleta sai ka kara ga wasu 'yan matan Zayyana da
Hibba su ma kowacce ta hadu karahe. Bayan wani ta gani kusa da Malamijo suna magana
ta wuce su Mairama a fusace za ta shiga cikin gidan.


"Salame babu gaisuwa? Ko ba ita bace?" Zayyan yace albarkacin Halifa da ya tabo shi
yana cewa ga Ummansa.


Ba ta iya juyowa ba sai tsuma da take yi tun daga tsakar kanta har tafin kafa.
Tasan muryar nan da irin tasirin da ta jima tana yi mata a duk lokacin da taji ta.
Sannu a hankali ta juyo idanunta suka sauka akan Zayyan Muhammad Tureta mutumin da
har yau babu wani namiji da ya kaishi daraja da kima a idanunta.


Takowa take yi jiki a mace zuwa gabansa ta ma manta da kowa da komai sai tashin
tsumin kaunar da take masa. Idanunta suna kwararar da hawaye ta kusa isa gareshi
"Zayyan dama kana raye?"


Malamijo gani yayi tana neman wuce gona da iri yasha gabanta "sai ki ka ga mijin
kanwarki ko? Ashe tsahon shekarun nan yana daure a gidan yari"



"Gidan yari? Allah sai Ya saka mana. Ni dama jikina yana bani baka barmu ba Zayyan"
tace tana kuka sosai.


"Zai saka mana kam ni da iyalina. Mairama matso ku gaisa mu tafi" Zayyan yace
fuskarsa babu digon fara'a ko kadan. Ji wannan zubar da mutumci da take neman yi a
gaba danta, mahaifi da kanwarta kuma matarsa.


Ita Mairama dama tsayawa tayi ta ga iya gudun ruwanta saboda yadda ta kula kamar
bata cikin hayyacinta. Da ace bata san tana son mijin nata ba sai tayi tsammanin
tsabar kaduwa ce kawai.


"Adda Salame yaya gida da yara? Da Halifa bai taso ki ba ma zamu tsaya a gidan naki
ai su gaisa da maigidan naki"


Firgigit ta tuna wai tana da aure. Amma Allah Ya isa Alh Indararo. Wallahi tayar
masa da hankali kawai zata yi ya sauwake mata ta huta. Sakin fuska tayi don dole
suka gaisa da Mairama ta rakata har bakin mota. Ta bangaren da Zayyan yake zaune a
baya ta tsaya yayi saurin danna abin rufe window ya dage glass din. Bata bata rai
ba ta dawo bangaren Mairama ta leko da kanta.
"Hmm nace bari nayi miki karambani. Kun dai tambayi malamai game da matsayin auren
naku ko. Kada aje ana haramtaccen zama. Idan babu auren gara a san me ake ciki tun
wuri"


Da Mairama tana zagi da sai ta hado mai kyau ta zubawa Salame. Wannan jaraba har
ina. Daga sake haduwa dashi take kokarin dawo da maitarta a fili.


"Kinsan ba sakina yayi ba kuma ban sake aure ba. Saboda haka auren mu yana nan har
yanzu"


"Mu tafi mana" Zayyan yace da dreban rai a dan bace tun bayan dawowarsa. Ba don ta
gaji da kallonsa ba ta koma gefe aka ja motar tana tsaye tana daga hannu "bye bye,
bye bye" take ta fadi tana murmushi.


Hannun Mairama ya rike yana kallon fuskarta "meye na tsayawa yi mata dogon bayani
bayan kinsan akan hanya muke?"


Murmushi tayi ya karawa fuskarta kyau "gani nayi gara nayi mata bayani tun wuri
kada tayi tunanin akwai wata kofa da za ta iya samu ta shiga gidanka"


Bude baki yayi ya kalleta "kada kice min ta fada miki"


"Bata ji komai ba ta sanar dani kuma shine dalilin mutuwar aurenta kamar yadda Alh
Salisu ya fada min jiya da kana waya da Baban Arifah lokacin da yazo. Cewa yayi
nayi hankali da ita mai hali baya fasa halinsa kuma gashi na gani"


"Mairama ina so ki sani wallahi ban taba cin amanarki ba akan Salame"


Kanta ta dora akan kafadarsa ta rufe ido "kada zancenta ya bata mana farincikinmu"


Alamun saka zip yayi a baki yana dariya suka cigaba da hirarsu cikin shauki har
suka isa Kano. Gidan da ya gina da guminsa da kuma gadon mahaifiyarsa ya shiga yana
tuna baya. Saboda hazo ya fara kura amma da gani an kashe masa kudi wurin gyara da
kayan alatu. Mairama ya janyo ya dora kansa a kafadarta yana tsaye a bayanta yace
"kin tuna zuwanmu gidan nan na farko?"


Sai da taji kunya Allah Yasa baya ganin fuskarta "ban tuna komai ba"


"Da gaske? Ni kuwa kamar a kaina aka ajiye ranakun da Mairama ta rinka nunawa
Zayyan soyayya irin wadda nake sa ran a maimaita. Jikina yana bani a nan kika samo
Zayyan fa"


"Ni dai ka kyaleni gyaran gida zanyi" tace a kunyace
"Muje na tayaki ai muna da lokaci. Sai jibi zamu tafi Sakkwato in je mu hadu da
Maikudi"


Ajiyar zuciya tayi tana hango wannan haduwa bazata yiwa Maikudi kyau ba ko kadan.


**********


Ranar da daddare bayan Yadikko ta dawo ne Radhiya taji komai game da amaryar
Malamijo a wurinta. Taji zafin sakin Hajjo ita ma tayi ta bawa Yadikko baki akan
kada ta tafi wa zasu gani su ji dadi.


Shima Malamijon kuma sai ya fada mata abubuwan da Hajiyayyen tayi masa.


"Malamijo ai kowa maye ne sai dai idan baiso nunawa ba. Ka rubuta mata takardarta
tun dare gobe zaka bata kuma wallahi Hajjo kadai na yarda ka dawo da ita"


"Ba ma sai kin fada ba 'Yar soja ikon Allah. Na ma gama aure yanzu sai dai ku"


"Wai ni su waye ma suke yi maka waliyai ne a aure auren Malamijo?"


"Kaniyarki mai ido a tsakar ka" yace yana laluben takalmi zai biyota dashi ta gudu.

11/2, 7:24 AM] 🏽
🏽 : 47..💕

'Ya'yan nasu sun hadu a falon Ummi kowa na bawa Daada labarin kansa musamman game
da karatu shi kuma yana rike da Daada Karami. Radhiya ta kalli yaron ya kurawa
babanta ido tayi murmushi tana tambayar Mami da suke shigowa tare da Mama suna
neman wucewa dakin Ummi wai yaushe zasu yi taron sunansa ne.


Mama ce ta bata amsa "babu wani taro fa Radhiya tunda babansa ya dawo me kuma zai
bukata? Masu tahowa dai zasu zo amma barka kawai"


"Yaya zaki yi mana haka babu shawara Zainab?" Cewar Mami tana nuna mata rashin
jindadi.


"Ni da dana zata yi min karfa karfa to wallahi ban yarda ba" inji Ummi tana goyon
bayan Mami.


Zayyan ya daga hannu kamar dan makaranta "idan kun bani dama in raba gardama?"


"Mun baka" Mama tace da sauri tana neman tsira. Da Baba Hadir suka yi shawarar soke
taron kawai kwanaki sun kara ja kuma ma dai dawowar Zayyan ita ce abu mafin dadi
garesu.
Kallon iyalan nasu yayi yana jin tamkar Allah Ya bashi fiye da abinda yake nema a
duniya. Major da Hadir harda Baban Arifah da ya sadaukar da rayuwarsa dominsu
batare da tunanin ko kadan zasu saka masa ba gashi sun rike masa iyali da gaskiya.
Idan ya biyewa zuciyarsa kuka zai yi musu daga su har matan kwarai da suke aure
wadanda suka karfafa musu gwiwa wajen dabbaka zumunci a bayan idonsa. Shi ba butulu
bane da zai manta Mami Hassana wadda mijinta Major da Ummi suka bashi labarin cewa
aikatau tayi a Germany domin ciyar da iyalinta amma a cikin abinda take samu Major
ya rinka cire wani abu kafin ya fara aiki yana aikowa matarsa Mairama. Babu wanda
baiyi masa ba amma Allah Ya sani yana jin girman Mami sosai a zuciyarsa. Daga ita
har Mama Zainab sun wuce matan abokai a gareshi sai dai ya kira su 'yan uwa. Sun
burge shi matuka yadda suka tsayawa juna a matsayinsu na matan sojoji suke kokarin
rufawa juna asiri. Ba don a gidan iyayensa an bar kari tun ran tubani ba ai da
kamata yayi ace ya dawo ya sami matarsa a tsakiyar matan su Badaru. Abin takaici
shine sun tashi babu wannan shakuwar tsakaninsa da 'yan uwansa maza da mata. Jume
tun kuruciya ta koya musu tsanarsa a matsayin dan kishiya. Sai dai yaji dadi da
Mairama ta fada masa yanzu kam idan ka cire Maikudi tsakaninsu da sauran musamman
'ya'ya da jikokin Mal Aminu abokin babansa sai dai hamdala. Ita ma a nata bangaren
rashin shakuwa da 'yan uwanta da kuma rashin tsayuwar uba akan 'ya'yansa ya sake
bata lamura. Da ace zumuncin nasu mai karfi ne ya tabbatar ko a daji iyalinsa suke
bazasu wahala ba. Duka rayuwar Mairama bayan tafiyarsa ai a cikin gidan mahaifinta
tayi kafin ta koma Rugar Barkindo amma rashin wannan zumuncin ya sa ita da wadda
bata tare da ahalinta kusan daya.


"Daada" Radhiya ta dan taba shi saboda nisa da ya soma yi a tunani.


Murmushi yayi a lokacin Awwab, Daddy da Baba Hadir suka shigo su ma yace "indai na
isa to na soke taron sunan"


"Kai da danka Daada waye zai hanaka abinda kake so" Mama tace tana murmushi.


Sauran kuwa da gaske sunyi mamaki harda Ummi kuwa. Sai dai abinda yace ya sanya su
wani irin farinciki a take.


"A iya sanina Zayyan kaima ba'ayi taron sunanka ba ko" ya kalli Emzee da suke zaune
kusa da juna shi da Ibrahim tamkar tagwaye. Dariya yayi yana zaro idanu "Daada ba
dai cewa zaka yi a nade ni a shawl a koma baya ba"


Ai kuwa falon ya kaure da dariyar yadda yayi har ya tashi zai bar musu falon da
Ibrahim yace "irin jaririn samudawan nan kawai zaka koma".


"Dawo ka zauna in karasa...Zayyanatun Daada kema ba'ayi miki suna ba"


Zayyana sai ta rasa inda zata saka kanta don dadi Zayyan ya fasa mata kai yace ita
tashi ce. Ibrahim ya dan kalleta yadda take dariya ta tashi ta koma kusa da Zayyan
ta zauna tana narkewa "Daada ba'ayi min ba, ko kayan barka fa bana jin an kawo"


"Kiji tsoron Allah" Mami tace tana dariya.


"Ai kuwa duk wanda bai kawo ba muna binsa bashi. Su Ummi da Mama kowa ta kwance
bakin jaka"


Anata dariya ta hada ido da Ibrahim wanda ya kasa gane mata tun ranar da yayi
maganar tale baki. Abin ya dame shi sosai ya kasa fadawa Emzee. Yanzu suna hada ido
yayi murmushi ita kuwa ta murguda masa baki ta kawar da kai, babu wanda ya kula sai
shi.


Zayyan ya dago Daada Karami "kaima bakon duniya nazo na tare hanya ba'ayi maka taro
an kawo kayan barka ba. Saboda haka in sha Allahu za'ayi taro na musamman idan
komai ya natsa na Zayyan, Zayyan, Zayyanatu da Zayyan."


Hayaniyar murnar da suka cika falon da ita ba arziki Mami tace su tashi su fita.
Zayyan ya yafito Awwab da hannu. Tun shigowarsa dama baiyi magana ba sai ma dukufa
da yayi yiwa abokin aikinsa text akan abinda zasu yi idan ya koma.


"Idan an gama suna sai mu fara shirin bikin dana. Kunyi min komai daidai amma an
bar min yaro ba aure. To mu dai yarinya ko 'yar waye tunda yana so idan ta kama na
sato ta ne zanyi na kawo maka kaji ko"


Idanu suka koma kansu shi da Radhiya lokacin suna rige rigen arcewa daga falon. Shi
hanyar waje yayi ita kuma tayi kitchen. Su Major ma sai da suka yi dariya.


"Kunga kama kai, yanzu don Allah waye yaji na ambaci suna?"


Da dariya suka fita harda ta kitchen ita ce karshen tafiya. Major yace masa ya fara
tara jikoki ya kamata ya rage chalikanci.


"Idan na dena so kake su rinka guduna? Kuma dai shekarata nawa ina danne Zayyan
Tureta ta karfin tsiya. Yanzu kuwa lokaci yayi da zai fito yayi kara'i"


"Aiki ya sameki kanwata kiyi a hankali kada mu fara ganinsa da kitso da dankunne
irin na matasan zamani" Baba Hadir ya rubuta ya mikawa Mama ta bata.


Zayyan yana ganin tana dariya yace sai ya gani. Daga nan dai hirarsu ce da bata
karewa suka dasa. Sai sakon text Alh Salisu ya yiwa Baba Hadir zai zo suyi sallama
gobe zasu koma Kano da yaran. Ya kara da dan korafin wai ko basu hakura bane yana
ta sa ran zuwansu gidansa ko su ko yaransu amma shiru. Baba Hadir sai yaji babu
dadi ya mikawa Daddy wayar. Kiransa Daddy yayi bayan sun gaisa yace

"Hadir yana mai baka hakurin rashin zuwan nasa. Wani abu ne ya taso amma idan babu
takura kuma kana da lokaci kafin ka tafi goben me zai hana ka shigo ka ga uzurin
nasa?"


"To Allah Ya nuna mana Yasa lafiya. A gaida yaran don Allah"


Da haka suka yi sallama. Matan na daki suna tsokanar Ummi amarya babu lalle babu
gyaran gashi ta ce laifinsu ne. Mama tace ba don jego ba da idan ta fara gyarata
sai sun biya mata Hajji da Umra.


"Ni dai naga ranar da zaki girma Zainabu. Ina jin halinku ne Sakkwatawan nan. Daga
ke har Zayyan sai ku sa cikin mutum ciwo da ban dariya."


"Cewa zakiyi suyi abu su daure fuska ki rantse ba daga bakinsu magana ta fito ba"
Ummi ta fada da dariya.


"Baki ji ba wai zai satowa Awwab Radhiya ya kai masa ita. Uban amarya zai saki
layi."


Kowacce ka gani tana cikin walwala da annashuwa suna jindadin zama da juna sai
fatan Allah Ya kade shaidanu Ya kara hada kawunansu.


**********


Tun dawowar Zayyan yau ce rana ta farko da su ka kebe su kwadai da 'ya'yansu a
bangaren Ummi. Ba kowa ne da wannan tunanin ba kuwa sai Mama Zainab. Bayan sun fita
ta tura musu Radhiya da Emzee da sunan su je ko babansu yana son hira dasu. Babu
wani boye boye tace ya kamata su bashi lokaci yaji matsaloli da cigaban rayuwarsu
kamar yadda kowane uba yake yi. Radhiya taji kunya sosai ganin da su Zahra a wurin.
Amma sai ta kula babu wadda abin ya dama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login