Showing 1 words to 3000 words out of 238465 words
htt
ps://chat.whatsapp.com/IcgqoNAQ9V612x1JRXBMVS
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
WATA KISHIYAR 🥰👹
(Alkhairi CE KO SHARRI)
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
Na Maryamah_Mrs AM
Page 1
Lagos Nigeria
Cikin sauri nake har hada takaddun ina qara duba agogon hannuna dukda nasan dakyar
idan bazan makara, qarfe Tara jirginmu ze tashi zuwa Kano dan halartar wani
conference meeting da aka turani daga office din mu. Gaba daya befi saura 45 mins
Taran tayi ba inda na dan samu kwanciyar hankali babu nisan tazara tsakanin unguwar
tamu zuwa Airport din. Buda qofar dakina da akayi da dan qarfi ya sani cewa " not
now please" azatona daya daga cikin yara nane sedai shirun da naji yasani
waiwayawa, megidan ne da kansa wato ENGINEER BASHIR AHMAD da nake Kira da Baban Ali
Yara kuma suna ce masa Abbi, Aliyu sunan babban Dana wanda Sunan Amininsa ne ya
saka masa da ya rasu sati biyu kafin na haifi Aliyun.
Fuskar sa a hade duk da kasancewarsa dama ba mutum bane me fara'a amma dai ai
yanayimun nidai. Kallona yake kamar yanda nima nake kallonsa fuskata dauke da
gajeran murmushi nace "Baban Ali ka ganni har yanzu ko? Wallahi Amna ce tayi mun
shirme tun jiya da dare nace ta zubamun papers din nan a jaka ashe batayi ba (Amna
Qanwata ce kuma Autar mu danake ruqo bayan rasuwar Mahaifin mu da Mahaifiyarmu ta
sake aure).
"Uhm" kawai yace mun yana nufar gaban mirror na, ban damuba na qarasa zuge jakata
tareda ratayata na dauki wayata dake gefe kafin na nufi qofa da niyyar fita
"Idan kin dawo zuwa end of the month ku fara shirya zaku koma Gombe" muryarsa ta
doki kunnena,
"To meya faru kuma? Bari dai in na dawo se muyi maganar a nutse" na sa kai na fice
daga dakin. Already Emmanuel Driver office dinmu na waje yana jirana dan haka da
sauri na fita ina amsa a dawo lafiyan da yara suka biyo ni suna yimun.
Bayan na nutsu a bayan motar zuciyata ta tafi tunanin me zamujeyi a Gombe kodai
wani abune ya faru a bangaren sa? To bangarensa mana dan nidai ko da safiyar nan
nayi waya da yan uwana kuma ba abinda akacemun ya faru to ko Matar tasa ta haihu
ne? Aa in haihuwa tayi ai kaitsaye zece Amira ta haihu bawai kawai zakuje Gombe ba.
Haka dai naita tunane tunane har zuwa Sanda Jirgin mu ya tashi.
A matuqar gajiye na shigo gida kusan qarfe 9 na dare, se yanzu nai dana sanin qin
bari na kwana a Kanon dan jirgin 6 na biyo na dawo saboda ban gayawa yarana zan
kwana ba nasan bazasuji dadi ba musamman da yake Gobe Saturday ne munsaba zama a
gida. Bayan nayi sallar Magriba da Isha naci abincin da Aliyu ya kawo min, ina
zaune tsakiyarsu kowa da hirar da yakeyi mun wani irin farin ciki yana cikamun
zuciya. Tabbas yaya rahma ne, a duk sanda na kalli yara na ina jin tamkar bani da
sauran wani damuwa a rayuwa se fatan Allah ya rayamun su.
Amna qanwata dake matsayin babbar Yata a yanzu nada shekaru 15 tana SS2 se Aliyu
shekaru 13 ya shiga SS1 saboda Jumping da makarantarsu suka masa dan Yaro Masha
Allah yana da qoqari tamkar Mahaifinsa. Jafar ke bi masa se Farida, Abdallah, se
yan biyu na masu shekaru 5 Ahamd da Muhammad su Shidan nan sune rayuwata ban kuma
hadasu da komai ba.
Har qarfe 11 muna zaune duk da irin gajiyar da nayi dan har wani ciwo kaina yakeyi,
sauqin dana samu tun a kano na aika da report din komai Office dan haka Weekend din
nan bacci zan shaqa. Sallamar Baban Ali ce ta katse ni na dago ina kallonsa da
mamaki dan Duk hirar da muke a zatona yana Dakinsa dan shi dama be fiya zama ayi
irin dogon hirar nan dashi ba, gaba daya muka masa sannu da zuwa ya Amsa yana nufar
dakinsa. Se a sannan na tuna ko kirana beyi ba yaji ya na sauka, Se na miqe nima
ganin kamar baya cikin yana yi me dadi dan in lafiya seya dan tsaya damu ko ze
shige dakin ga kuma fita da yayi da daren nan, tashina yasa suma duk suka miqe
mukayi exchanging Hugs kafin Mazan suka nufi dakinsu matan ma haka.
A tsaye na same shi yana cire rigarsa na qara sa taya shi ina cewa "Ashe baka nan,
na tambayi yara sukace kamar Zoom meeting kukeyi kana daki"
"Uhm" ya kuma amsa mun. Nan da nan naji raina ya baci dan gaskiya ina da saurin
Hasala amma fa ina da sauqin kai rainin hankali ne bana so, to rainin hankali mana
ace wani inje kano in dawo a ranar ai ya tambayeni ya hanya koda yake dama duk
satin nan tunda ya dawo Weekend naga yana wani fuzga ban kula shi ba nasan qiris
yake jira ya sauke abinda ita yar Gwal din baze iya mata ba. A raina naja tsaki
tareda cewa "Dan rainin hankali wato ga bolarka can Yarinya ta bato maka rai kazo
ka juyemun to bazan tanka ba". Ganin ya shiga Toilet yasa na fita, dakinan yaran na
shiga can na tarar da Ahmad da Moh suna kwasar Dambe abun haushi wai Jafar na musu
waqa Su Casu bame rabasu, haka suke kamar Kaji kullum fada kamar ko yaushe kuma
akan Gado ne saboda Bunk ne dasu Aliyu da Jafar se nasu Muhammad, Ahmad da Abdallah
Babban gado suke kwana su ukun to wai se ace A gadon Yah Jafar za'a kwanta shine a
sama dan haka yau in wannan ya kwana gobe wannan amma rigima irin ta Ahmad se yace
sedai dan uwan ya bashi kwanansa. fada na musu kafin kwantar dasu dukka a gadonsu
muka karanta Azkar din bacci naja musu qofa tareda kashe fitila.
Amna da Farida tuni sunyi bacci suma Adduar na qarayi musu ma ja musu qofar na
shiga dakina, jikina na qara gyarawa tareda daukar wayata na ja qofar na fita. Har
Baban Ali ya kwanta ganin rigima yake nema yasakani kashe fitilar da ya bari a
kunne nima na nemi wuri nesa dashi na aje muqamiqina wata gajiya na sake saukar
mun.
"Kufa fara Shiryawa Next week zaku koma Gombe" ya sake fada, sena gyara kwanciyata
ina cewa "Allah ya kaimu dan wallahi na gaji bacci nake so inyi kuma na biye masa
surutu zamuyi tayi dan dai yasan abinda yake fada bame yiwuwa bane tunda na fara
aiki ai bama zuwa Gombe se lokacin hutu shima ba kowanne ba se yayi corresponding
hutun Yara da nawa ko kuma da wani babban dalili amma rana tsaka ana tsakiyar Term
yace wani tafiya ko yar Gwal din ce ta haihu wlh bazan bar aikina na tafi ba duk
sanda nai hutu naje mata Barka. Ina wannan mitar bacci yai awon gaba dani da ban
farka ba se Qarfe 7 harda Rabi na safe.
Yau Baban Ali halin fulani ya motsa kenan ko ya tashe ni sallah dan gajiya ce ta
danne ni banajin ko juyi nayi a baccin nan. A gurguje na dauro Alwala nai sallah
bayanna idar da azkar dakyar na miqe dan bawai baccin ya sake ni bane na fito
palour, Amna da Farida na zaune Se Ahmad dake bacci a kan Three sitter. A tare suka
gaida ni na amsa ina tambayan ina Su Jafar Amna ce tace sun fita Jogging da Abbi
"Kunyi karatun Asuba ne" na tambayesu suka amsamin da eh
Mamaki ya qara kamani amma na dake na shiga kitchen Tea nake so nasha kafin na koma
bacci. Kafin na fito sun koma dakin su har Ahmad sun dauke shi daga wurin dan haka
na zauna kan Dining ina shan Tea ina tunanin meya ke damun Eng ne haka. Haka na
qarasa na koma baccina wanda koda na sake farkawa 12 harta gota na rana.
A dakin nai wanka na shirya kafin na fito ina jin gajiyar ta sake ni. Palour kamar
Gidan biki saboda hayaniya Farida da Jafar na musu akan wani film da suka kalla. Da
gudu Ahmad da Moh suka nufoni har suna neman kadani na riqe hannayensu muka qarasa
cikin palour.
"Ina Abbi" na tambayesu dan koda na farka ban ganshi a dakin ba kuma dai nasan
Saturday Sunday yana gida seda babban Dalili yake fita kafin su bani amsa ya shigo
da sallama ciki ciki, kallo daya yamun ya dauke kai tareda nufar kan Dining ya aje
abunda ya shigo dashi, jin an fara kiran sallah yace su tashi suyi Alwala suka wuce
masallaci da Mazan mu kuma muka tayar da tamu a Gida.
Abun mamaki bayan sun dawo kuma se gashi ya zauna a palour tareda yaransa suna hira
dan nidai kitchen na shiga na fara qoqarin dora mana abincin rana dan na dare a
waje zamu je muci in yaga dama kenan. Da wuri na gama dan Garnished spaghetti na
mana se na dumama Grill Fish din daya shigo dashi ko a ina ya samo da safen oho.
Farida da Amna na kira suka jera komai akan Dining kafin muka zauna gaba daya banda
Abbi dake amsa waya sena dakata har ya gama sannan na masa maganar Abincin.
"Kifin kawai zaki kawomun da juice" ya fada. Ban kawo komai ba dan nasan spaghetti
bata wani dame shi ba amma dai yana ci musamman irin wadda nayin, na hada abinda ya
buqata na kai masa sannan na koma muka ci gaba da cin abincinmu. Koda muka gama
wurinsa Twins suka koma da Abdallah Jafar da Aliyu suka kwashe kwanuka zuwa kitchen
tareda wanke wa Amna da Farida kuma daki suka shiga Farida zata yiwa Amna tsifa.
Nima palour na koma muka hadu muna yar hira sedai abinda na fahimta Baban Ali
yaransa kadai yake amsawa dana saka baki se naji yayi shiru tsam na miqe Ahmad ya
tashi shima ze bini dan haka yake indai muna gida da na dauke qafa ze aje tasa nace
masa "koma ka zauna aiki zanyi" ban ma shiga dakinsa ba na shige nawa.
Kwanciya nayi kan gadona ina replying whatsapp messages daga nan muka shiga hira da
yayata Alawiyya da muke Uba daya, tamu tazo daya nan na shiga bata labarin abinda
Baban Ali ya tsiro dashi kuma. Dariya tayi tana cewa "kedai da Engineer Miskili
kafi mahaukaci ban haushi" nan muka ci gaba da firar mu ban san lokaci ya tafi ba
seda naji ana kiran La'asar.
A dakin nayi sallata ina idarwa na shiga wanka, daidai na fito naji Knocking nasan
yaran ne basa shigomun daki sena basu izini koda kuwa Ahmad da Muhammmad da suke
qanana. Bayan na amsa Abdallah ya shigo, sak kamanninsa da yanayin Miskilancinsa
irin na Bashir ne sedai duk cikin yarana ya fisu haquri wannan kuma halin
takwaransa wato mahaifina ya gado. Cikin sanyinsa Yace "Mami Wai Abbi yace kiyi
masa text na abinda zamu taho miki dashi".
Se naji wani dus kamar yaya na masa text? Ba tare zamu tafi ba? Har na bude baki da
niyyar tambayarsa se kuma na fasa nace masa " Kacewa Abbi ya leqo ina son magana
dashi". Da toh ya amsamin kafin ya fita ya barni da mamakin wannan sabon rainin
hankalin.
Abbi
Lokacin da yaron ya gaya masa saqon har sun shiga mota ya ma kunnata, ganin idon su
ya sahe cewa yana zuwa ya fito yana qara daure fuskar sa. Tana shafa wa santala
santalan cinyoyinta mai ya sameta, yaso ya shagala da binta da kallo dan a duniya
ASMA'U takai duk inda mace ake so takai, Asma'u mace ce guda harda Rabi wallahi ta
ko ina ta hadu bakuma ze taba manta halaccinta a rayuwarsa ba shikansa ya kasa gane
dalilin da yasa yake mata wasu abubuwan. Waiwayowan da tayi tana qoqarin sakin
towel din jikinta dan sam bata ji motsinsa ba yau saurin juya fuskarsa dan a wannan
bangaren baya taba iya tsallake tarkonta. Jikinta tamkar Magnet yake ga idonsa, a
kullum gani yake kamar qara mata kyau da sura akeyi Ma'u bata tsufa.
"Au Abbi ka shigo ashe, Ban gane me Babana yake fada ba yau kuma danwaken zagaye
zakumin kenan" na fada ina cigaba da zura rigata dan nayi sauri na shirya nasan
Bashir baya son jira sam a zatona ma dalilin daya sa zasu fita su barni kenan.
"Nop banyi niyyar fita dake bane, kiyimun text din abinda zaki ci mu taho miki
dashi in kuma beyi miki ba shikenan" kawai yasa kai ya fita.
Se na raka bayan sa da kallo kawai kamar wata doluwa, " tofa Baban Ali kodai gamo
yai da Aljanu ne" na tambayi kaina ina qara cika da tsabar mamaki.
Share
Share
Share
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
Na Maryamah_Mrs AM
Page 2
WATA KISHIYA(ALKAHIRI CE KO SHARRI)
Ni kadai tsuru kamar mayya a gida har qarfe 10pm ga gyangyadi inayi amma na kasa
shiga daki na kwanta saboda tsoro gashi har sannan basu dawo ba. Tsayuwar motarsa
da naji ta sani miqewa daidai lokacin da Ahmad ya kwaso da gudu yana kwallamun kira
"Mami Mami"
"Na'am Ahmad meya faru" na fada ina tare shi, labarin inda sukaje ya fara bani,
gurin wasan da ya kaisu, Favorite restaurant dina sukaje suka ci abinci daga nan
suka tsaya Cinema sukayi kallo abinda ya saka su yin dare kenan.
Saboda gajiya kowa dakinsu suka nufa, dakaina nayiwa Twins wanka na shirya su kafin
11pm gida yayi tsit duk sunyi bacci sannan na shiga dakina raina yana suya,
Tsabar bacin rai ko takan take away din da sukamun ban bi ba nima wankan na shiga
ina sake danne zuciyata na shirya na nufi dakin Baban Ali.
A kan gado na sameshi yayi daidai yana amsa waya fuskarsa dauke da wani shegen
murmushin da bazan iya tuna rabonda yayi mun shi ba ko ba'a fada ba nasan da Amira
yake waya dan Baban Ali bashida kwashe kwashen yammata, Ada ni kadai ce a rayuwarsa
kafin ya kwaso min Alaqaqai.
Wayar dana tarar yana yi ita ta qara bata mun rai saboda wannan ai wulaqanci ne ko?
Nasan matar sa ce amma ya kamata nima ya mutuntani idan zeyi wayarsa se ya nemi
kebantaccen wuri bawai cikin dakina akan Gado na ba, wannan sabuwar ta'asar da ya
samu ta fara kaini bango dan haka ban san sanda na saki wani wawan tsaki ba ina
janye ido na daga kansa bayan mun hada ido.
"Ke dawa kike tsaki?" Ya tambayeni still wayar na kunnensa.
"Ni da waye a dakin" na fada raina na qara quna.
"Anty ce ko" na jiyo muryar Amira na tambayar sa daidai sanda na duqa kusa dashi
dan na dauke Safar daya ajiye akan gadon sena daga sauti yanda nasan zata jiyo nace
"Nice din yar iya ko kina da magana ne"
"A ko yaushe ina gaya miki ki ringa jan girmanki ko? Amma shikenan" ya fada yana
miqewa daga kan gadon ya nufi qofa. Wani baqin ciki ya tokare mun wuya, kawai na
haye gadon na kwanta tareda fashe wa da kuka.
Duk yanda nake daurewa se Bashir ya qure ni tunda ya auri yarinyar nan ban sakeyin
sati ba tare da nayi kukan baqin ciki ba shikenan ni a haka zan qare? Bansan
sandaya dawo dakin ba na dai farka cikin dare naji mutum ya kwaqumeni aiko na
ingizashi da qarfi har seda ya farka na tashi daga gadon na shige toilet. Fitsari
nayi na dauro Alwala, hijabina na zura na fara jero Salloli tare da dogayen Addua.
Kamar kullum a duk sanda muka samu sabani na fara sallar dare nan haka ze zabga
tagumi yana kallona in ya gaji shima ya to Alwalar ya tada Sallah (bawai dan banayi
ba Aa nafi tsawaita Idan mun yi fada dan karna kwanta kusa dashi dan duk bala'i
bama raba gado 😂😂) nasan me yake tunani qila qarar sa nake kaiwa gurin Allah ko 😂😂
wallahi ko daya duk abinda Bashir yake mun ban taba yi masa Allah ya isa ba sedai
ma in roqi Allah daya yafe masa ya kuma bashi ikon Yin Adalci a tsakanin mu ya ci
gaba da bashi yanda zeyi ya kula damu. Ko ba komai nasan Bashir yana sona nima kuma
ina sonsa to ban rabu dashi a lokacin Matsi ba se yanzu da dadi ya samu se in tafi
in barwa yar taka haye?? ina ba wannan magana.
Ban sallame ba har seda aka kira sallar Asuba, ina kallonsa ya fita masallaci kafin
nima na tashi nayi Raka'atanul fajir sannan na bada Farillah. Rashin samun bacci
cikin dare yasa ina idarwa ko Azkar ban samu yi ba na koma bacci, sanda na farka
goma harta gota dan haka anan dakin nayi wanka na shirya kafin na fito palour.
Ko ina qalqal sun gyara dan ko kadan banyi wasa wurin koyawa yarana aikin gida ba
komai nidasu mukeyi bani da me aiki tunda har kuma yanzu dana ke fita aiki da safe
kafin mu fita mukeyin komai tunda kuma ba wuni muke a gidanba baya yin datti. Babu
kowa a palor se Baban Ali yana aiki a system dinsa ya dago yai mun kallo daya
tareda mai da kai ya cigaba se na qarasa kusa dashi ciki ciki nace masa ina kwana
dan har yanzu haushin sa nake ji, se ya amsa ba tareda ya kalleni ba.
A dakin Boys najiyo hayaniya da alama PS sukeyi tunda suna da Tv a dakin nan suke
yin Game dukda lokaci da yawa yana dauketa saboda karsu shagala da wasa a qi karatu
amma Weekend dama aikin kenan wani sa'in hardashi zasu hada anan palour suyi.
Kitchen na nufa dan naga sun kwashe kayan kan dining, a roba na tarar da dankali
ciki ruwa an yanka su, nasan Amnace ta ajiyemun tunda tasan nafison dankali da an
kwashe daga wuta nan da nan na maida man da sukayi suya na zuba kafin na debo kwai
guda uku na fasa tareda zuba abubuwan da nake da buqata a ciki, ina kwashe dankalin
na maida wani pan din na soya kwai, scramble nayi dan ban fiya son me fefe ba na
juye akan plate din chips na zuba Ketchup a gefe na fito. Ta gabansa na wuya ina
juya jiki tareda baza masa qanshin turarukan dana fesa aikuwa naji yanda yaja
numfashi da ajiyar zuciya ina kuma jin idanunsa akaina har na zauna a dining amma
kafin na juyo ya dauke idonsa, girgiza kai nayi ina sake cika da mamakin Bashir a
raina haka naja kayan tea na hada ina ci ina dan kallon drama da akeyi a Tv.
Har na gama ci babu wanda ya leqo a yaran Gogan ma anata latsa laptop kamar besan
Anyi digona a palour ba sena taso na dawo cikin palour na nemi 1 sitter dake facing
nashi na karkace ina latsa wayata nima. Whatsapp na shiga group dinmu na Secondary
na bude aikuwa na tarar da chats bila adadin, ban samu damar bi ba saboda wasu ne
suke qara shigowa se kawai na fara bi daga nan. Ban karanta message din mutum hudu
ba na fuskanci dalilin ubannin messages din dana gani ashe Labor zaayiwa kishiya
(Labor prefect dinmu da muna school kuma abin dadin qanwar daya daga cikin yan ajin
namu qawarta ta hannun dama zaa auro mata, tasan mijin zeyi aure amma bata san
yarinyar ba se yau da taje karban lefen Qanwar Qawarta taga dangin Mijinta ne yan
kawo lefen 🤣🤣😂😂🤣🤣😂)
Wata muguwar dariya na sheqe da ita har ina kwarewa da ta saka Baban Ali dagowa ya
zubamun ido, yasan Ma'u sarai tabbas