Showing 129001 words to 132000 words out of 152206 words

Chapter 44 - HALYSAAH by Khlst Hydrr

13 May 2026

113

alfarma daya zan nema wajenka" Murya can kasa yace "Say
it Khaleesat" Tayi karfin halin cewa "I don't want you to hurt anyone because of me...." Kasa ci gaba tayi
tana kuka a hankali, ya dinga kallonta don sarai yasan su wa take nufi, Calmly yace "Ohk u mean ur Body
Guards that sue me?" Ita dai kuka kawai take, Ya ɗan yi wani murmushi yace "I don't think i will leave dem
cause they started everything first, they intruded in what wasn't der business, basu baki labarin harbin da
aka yi ma wani dake da alaka da su ba, I mean Salem..." Khaleesat ta daga kai da sauri ta kallesa hawaye na
sauka idonta gabanta na faduwa, lkci daya ta tuna sanda Aunty Farida ke sanar mata Ajay yace mata an
harbi wani abokinsu a kano, yana wani murmushi yace "To su ma ana nan ana targeting din su, amma in
kince in kyalesu i will do that under 2 condition..." Khaleesat dai kallonsa kawai take ta kasa cewa komai
duk jikinta yayi sanyi, yace "The first condition is that.... zaki yi magana ta waya da su ki gaya masu ke za
ki zauna da mijin ki they should back off, sannan ki gaya masu su janye karan da suka kai kotu..." Bata san
sanda ta fashe da matsanancin kuka ba, ya dinga kallonta sai kuma yayi murmushi yace "Baza ki yi ba
kenan?" Muryarta na rawa tace "Ban ce bazan yi ba" Wayarsa ya dauko ya mika mata yana kallonta, da
kyar tace "Bani da number ai" Yace "Amma aunt dinki na da shi ai... Call her and ask her to send you the
number" Ta girgiza masa kai tana jin kamar numfashinta zai dauke sbda rikicewan da tayi bayan ya fadi
conditions dinsa, cikin kuka tace "Bani da numberta offhand" Yace "Ni ina da shi, i will call her now sai ki
gaya mata ta turo maki number daya daga cikinsu, and mind you kada ki kuskura ki ce mata komai, number
kawai zaki yi requesting ta turo maki" Ta fashe masa da kuka sosai tace "Why are you doing this plss Ya
Abdul" Yace "Ohk, i will revenge and nothing is gonna stop me, i promise you this, shi abokinsu da aka
harba ai yayi surviving, i hope they survive too....." Tana kuka sosai tace "No plsss..." Wayar ya dauka yayi
dialing number din Aunty Farida yana fara ringing ya mika mata yana kallonta.
[6/17, 7:43 PM] khaleesat Haiydar ✍️: Har Aunty Farida ta ɗaga kiran Khaleesat bata amshi wayar da
Abdul ke mika mata ba hawaye na zuba idonta, lkci daya ya hade rai yana mata wani irin kallo, babu shiri
ta amshi wayar hannunta na rawa, a sanyaye tace "Aunty" Cikin rikicewa Aunty Farida tace "Khaleesat?"
Khaleesat ta sauke idonta tayi shiru, hankali tashe Aunty Farida tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un,
Khaleesat kina ji na? Don Allah kiyi magana, Hello Khaleesat" Khaleesat ta kasa ce mata komai hawaye
masu zafi na sauka idonta, kiris ya rage ta fashe mata da matsanancin kuka a wannan lokacin, Abdul ya
fixge wayar yayi a hannunta ya katse yana mata wani mugun kallon da ya tsorata ta sosai yace "Are you
daring me?" ta fashe masa da kukan da take dannewa tana girgiza masa kai, a fusace yace "Ohk then, since
abinda kika zabar masu kenan to ina me tabbatar maki zan aikata hakan nan ba da jimawa ba kuwa, sannan
bayan nayi zan sanar maki, don bani da imanin kyale duk wani mahalukin da yace zai shiga hurumina, i
don't mind sending that person to his early grave, and mind you.... i will so deal with them yanda in their
next life baza su kara shisshigi akan abinda bai shafesu ba, if you think i am bragging watch and see, bani
da conscience...." Khaleesat ta girgiza masa kai cikin karfin hali tace "Duk ba sai ka masu komai ba, zan yi
abinda kace" Wayar ta amsa a hannunsa ta cire a Flight mode din da ya saka sannan ta sake dialing number
Aunty Farida, yana fara ringing Aunty Farida ta daga da sauri tace "Khaleesat, kina ji na Khaleesat??
Hello" Khaleesat ta dake ta hadiye sauran kukanta cike da karfin hali tace "Na'am Aunty" Cikin tashin
hankali Aunty Farida tace "Kina ina Khaleesat?" A hankali Khaleesat ta daga kai ta kalli Abdul taga ya
wani murtuke fuska yana kallonta kamar bai taɓa fara'a ba a rayuwarsa, ta sunkuyar da kanta wasu sabbin
hawayen na zubo mata cikin sanyin murya tace "Aunty Number Ahmad za ki turo min yanxu plss" Aunty
Farida da duk ta rude tace "Ahmad kuma Khaleesat? Wanene Ahmad? Kina ina ne yanxu?" Shi dai Abdul
wani devilish look kawai yake mata, tayi kasa da murya tace "Aunty Number Junaid zaki turo min" Da
sauri Aunty Farida tace "To bari in turo maki yanxun nan" Katse kiran Aunty Farida tayi cikin rawan jiki ta
tura ma Khaleesat number Ajay, number na shigowa Abdul ya amshe wayar a hannunta yana kallon number
for almost 5 seconds, can yayi wani murmushi ya mayar mata da wayar, cike da isa yace "Kirasa ki gaya
masa abinda nayi instructing din ki" It took Khaleesat almost 30 seconds kafin ta iya dialing number Ajay,
shi ma saboda irin kallon da Abdul ke mata ne, exactly irin kallon da yake mata in zai gaura mata mari,
cikin muryarsa dake tsoratata taji yace "Kika kuskura kika yi magana da wata muryar da ba normal voice
dinki ba zaki sha mamaki wallahi, and immediately he picks just go straight to ur point, do not give him a
breathing space to say anything to you, go straight and tell him kin hakura zaki zauna da mijinki, kin ji me
nace maki?" Ita dai bata ce masa komai ba hawayen takaici na zuba idonta, sai da kiran ya kusa katsewa
Ajay ya daga, ta ɗan kalli Abdul da bai fasa mata wani irin kallo ba, da kyar ta daure tace "Hello, good
evening....." Mikewa Ajay yayi jin muryarta, bata jira ya gama processing ba ta ci gaba a hankali tace
"Dama ina son in ce maka ni na hakura zan zauna da mijina, and i appreciate all what you've done for me
kai da Yaya Jawwad, thank you so much" Ajay ya juya ya kalli Jay da shigowar sa dakin kenan, as if
counting his words yace "Come again!" Yana fadin haka ya saka wayar a handsfree sannan ya nufi Jawwad
yana kallonsa, Khaleesat ta kalli Abdul, sai kuma ta sunkuyar da kanta tace "Cewa nayi ni na hakura yanxu,
zan zauna da mijina, and thank you for all what you've done for me...." Wasu sabbin hawaye suka hau zarya
a fuskarta tana ji kamar ta fashe da kukan dake cin ta, Abdul ya fixge wayar a hannunta ya katse sannan ya
kashe wayar gaba daya, Ajay ya kalli Jay that looks speechless and shock at the same time, lkci daya ya
jefar da wayarsa saman gado, cikin nutsuwa yace "Nayi da na sanin bata lokacina akan yarinyar nan, i
regret wasting my very precious time...." Jay ya ma rasa me zai ce, walking slowly ya karasa gaban
window din dakin yana kallon Ajay that was boiling from inside, a hankali yace "Look Ajay, i think those
words are not coming from her heart, sakata yayi ta fadi hakan pls mu yi mata uzuri, she is forced to say all
what she said, ba mu san situation din da take ciki ba let consider that plss" Ajay ya masa wani kallo yace
"Billah na cire hannuna a lamarinta kaji na rantse Jay, i have nothing to do with her case again, after all i
was just doing it just for the sake of humanity not because of her, ko kasheta yake ya kamata ta gaya mana
haka? Mu zata dauka for granted? Beside she spoke confidently meaning she is okay with what he asked
her to say, i am leaving this state first thing tomorrow morning, so unfortunate i waste my time on the brat,
don taga mun yi stooping kan mu so low shi yasa ta dauke mu for granted" Yana kai wa nan ya fice daga
dakin kamar zai tashi sama, Jay ya lumshe ido ya bude don bai san me zai sake ce masa ba da zai sa ya
sauraresa, kuma tunda har ya rantse magana ta kare, ya zare hannunsa kenan babu abinda zai sa ya sake
involving kansa, zaunawa yayi gefen gado ya dafe kansa da yaji ya masa nauyi, at the same time letting out
a sigh, kalmomin Khaleesat ne suka dinga dawo masa kai, he felt really disappointed in her too, but can
kasan zuciyarsa tausayinta ne ya mamayesa ya kuma yi mata uxuri, ya rasa menene yasa shi shiga yanayin
da ya shiga a wnn lkcin, da kyar dai daga karshe ya mike ya fita daga dakin yana tafiya a hankali. Daren
ranan nan Khaleesat bata yi baccin awa biyu ba cikakke, da bacci barawo ya saceta zata farka a firgice, bata
taɓa jin abu ya tsaya mata a rai irin abinda Abdul ya sa tayi ma su Housemate dinta ya tsaya mata ba, gashi
ko digon hawaye yaki fita idonta, her heart is just heavy, but did she have a choice? In bata yi hakan ba
yayi ma su Housemate dinta wani mugun abu ai bazata taɓa yafe ma kanta ba, tunda har yake ikirarin ba shi
da imani babu abinda bazai iya aikatawa ba, tasan kuma sarai zai iya aikatawa din, tunanin sabuwar
rayuwar da take kokarin fadawa take, is she going to survive this at all? Is this not going to be her end? A
ranta taji kilan lokacin mutuwarta ne ke tinkarota, sai a sannan taji hawaye masu zafi for the first time a
idonta, ta kai hannu a hankali tana sharewa ta juya tana kallon Abdul dake baccinsa hankali kwance, dai dai
nan alarm din wayarsa ya kada, ta juya da sauri tayi backing dinsa tana goge hawayen da ya fara zubo mata
sosai, after some seconds taji alamar ya tashi yana karanto addu'an tashi bacci, ita dai hawaye kawai take,
sai da taji yayi sallah ya fita daga dakin sannan ta mike zaune tana kuka a hankali. Nenne ta bude hannu
tana kallon su Aunty Farida cikin nutsuwa tace "To kun ga ai baza mu shiga hurumin Allah ba, ko akwai me
tsaurin idon da zai shiga a cikin ku? Allah Ubangiji ne kadai yasan daliliin da ya maidata hannun mijinta
cikin ruwan sanyi babu tashin hankali, to don me za mu shiga hurumin da ba namu ba? A'a gaskiya banda
ni tunda ni dai nasan wanene Allah, kuma shi kadai yasan hikimarsa ta yin hakan, da yasan Khaleesah zata
cutu hannun Awdul da bazai fara basa sa'ar sungumeta ba don bamu fi sa sani ba, ko ba komai ɗa na zai
samu kwanciyar hankali ya ci gaba da sabgogin rayuwarsa kamar ko wani ɗan adam, mu mun yarda da
kaddara mummuna ko kyakkyawa tunda mu musulmai ne, kuma duk abinda Allah yayi mu din banza za
mu ce don me, domin haka nake cewa Allah ya bata zaman lafiya da mijinta, ɗan halayyarsa da yake yi
mara kyau Allah ya gyara sa ya dena, ai babu wanda bai da taɓon wani mugun abu a rayuwar nan, in sun
dawo kano mu kuma sai mu je ganin daki mu sa albarka, duk sanda ya bar ta ta zo ta gaida mu a Mariri sai
ta zo bakinta alekum, shi kuma Ali Allah ya sa karshen wahalarsa kenan a duniya" Wani irin kallo Aunty
Farida ke ma Nenne zuciyarta na tafarfasa, Umma dai kanta na sunkuye bata ce komai ba amma ita kadai
tasan abinda take ji a zuciyarta, Mama Zubaida tace "Amma dai Nenne ai ya kamata a bibiyi halin da take
ciki, an taɓa tarewa haka kawai a zo a sungumi yarinya a mota da asuba ba a san ko shi din ne ba ko ba shi
ba amma duk a rasa me bibiyar hakan, wannan ai abun dubawa ne, tun da mu dai har yanzu bai ce mana shi
ya dauketa ba" Nenne tace "To er bakin ciki, shi din ne ya sungumeta ba kowa ba aniyarki ta bi ki, kuma ai
halaliyarsa ya sunguma ba wata ba, duk wanda ya sake cewa zai bada shawara a wannan lamari idan ban sa
Ali ya sallamesa ba shegiya uwata da ubana suka haifeni, kwata kwata bakwa neman ma ɗa na sauki a
rayuwar nan, burin ku kawai tashin hankali ya kashe Ali ku huta ni kuma in shiga uku, ita uwar da ta
tsugunna ta haifi yarinyar bata da bakin magana sai ke me baki kamar ta dorinar ruwa?" Mikewa Mama
Zubaida tayi ta shige dakinta, Mama Shatu ta kyabe baki tace "To Allah ya kyauta, in ya dawo mana da
gawar ta ai sai mu zauna mu yi zaman makoki ba shikenan ba" Nenne tace "Sai dai ki ga gawar er ki
Labeebah amma ba Khaleesah ba, kuma bakin cikin da ku ka kasa boyewa ne zai kashe ku ke da Zubaida"
Mikewa Umma tayi hawaye cike idonta ta shiga dakinta, Nenne ta kyabe baki ta mike tana kallon Aunty
Farida tace "In Ali ya dawo ki ce masa nace ya zo ya amshi tuwo da miyar taushe zan ajiye masa, wallahi
wata guda zan yi ina masa girki ya marmaro" Daga haka ta fice daga gidan, Aunty Farida tayi tagumi
hawaye cike idonta.
Meemah ta shigo parlon Momy ta zauna tana ɗan murmushi, ta jira har Momy ta gama wayar da take yi da
aminiyarta godiya sannan tace "Momy na samesa a waya" Da sauri Momy tace "Ya daga kuma?" Meemah
tace "Eh ya daga bayan yaga text din da na tura masa kenan" Momy na gyara zama tace "Toh
Alhamdulillahi nagode ma Allah, sai yace maki me?" Meemah tace "Kema kinsan dole zai taho ai, amma
tsorona daya kada ya kira Daddy kuma ya daga waya yace masa ba haka ba" Momy tayi wani murmushi
tace "Bazai daga ba, tunda na riga na gaya masa abinda ke faruwa ai" Meemah ta sauke ajiyar zuciya tace
"Alhamdulillah, in ya samu flight yau za mu iya ganinsu a gidan nan" Momy tace "Me zai hana ya samu
jirgi, ai da sauran lokaci dole zai samu" Mai aikin Momy ce tayi sallama tana makale jikin kofar parlon duk
da a bude yake amma bata shiga ba, hannunta rike da tray me dauke da plate din gasasshen kaza da lemon
kwali biyu, Meemah ce ta amsa sallaman tana mata wani kallo tace "Tun da kika ga kofa a bude ba sai ki
shigo ba, kin wani raɓe jikin kofa kamar munafuka, don Allah ki dena wannan kauyancin yana damun mu a
gidan nan" Momy ta hade rai tana kallonta har ta karaso ta ajiye plate din, cikin ladabi tace "Ga kazar ta
kammala Hajiya" Momy tace "Kalan Hijabin nan naki na daga min hankali a gidan nan, kar ki sake saka
min shi, in yar wa zaki yi to ki yar bana son shi kwata kwata yayi kalar talauci" Mai aikin ta dukar da kai
tace "Toh Hajiya in sha Allah bazan sake sa shi ba, kiyi hakuri" Fita tayi daga parlon da sauri, Momy ta dau
plate din tulin kazar da aka ajiye mata ta fara ci tana cewa "Ai dama tunda aka ce min zai taho da ita
hankali na ya kwanta, don dama taho da ita shi ne me wuyan...." Meemah tayi murmushi ita ma ta dau
yankan kaza daya tana ci tace "I trust you Momy" Khaleesat ta saka Hijab dinta har kasa tana harhada wasu
daga kananun kayan dake cikin closet din dakin kamar yanda Abdul ya umarceta tayi, absentmindedly take
aikin don tayi nisa a tunanin da take, bude kofar dakin yayi ya shigo, ita dai bata juya ba tana ci gaba da
abinda ya sakata, ya karasa har bayanta ya tsaya, taki juyowa gabanta na faduwa, juyo da ita yayi yana
kallonta ta sunkuyar da kanta, yace "Me ya sa baki son ki saki ranki har yanxu? Always looking worried" A
hankali ta daga kanta ta kallesa amma bata ce komai ba, yace "Kin gama hada kayan ne?" Girgiza masa kai
tayi, yace "To gama" ta juya ta ci gaba da abinda take, shi dai yana tsaye yana kallonta, pad ta dauko a
karshe zata saka cikin karamin trolley din yace "What are you using that for? Ba yau zaki gama ba?" Taki
kallonsa zuciyarta na bugawa tace "Amma ban gama ba ai" Bata jira me zai ce ba ta saka a akwatin sannan
ta kulle ta mike tsaye, kamo hannunta biyu yayi yana kallon cikin idonta, speaking slowly yace "Promise
me you won't act silly har mu isa kano Khaleesat" Ta rasa dalilin da hawaye ya cika idonta, shi dai kallonta
kawai yake, after some seconds yace "If you try anything silly, zaki yi matukar mamakin abinda zan yi, i
promise you" Da kyar tace "Toh, amma plss ina son inyi waya da Safiyyah, i am missing her" Yace "Baza
ki yi waya da Safiyyah ba, amma idan muka isa kano zan fara kai ki gidanku ki gaishesu sannan mu tafi
gidanmu" Ita dai bata ce komai ba hawaye na zuba idonta, a haka suka bar gidan zuwa airport tunda yana
da hoton National ID dinta a wayarsa. Da yamma suka sauka garin kano, driver din gidansu har ya iso
airport din yana jiransa, Drivern ya bude ma Khaleesat back seat bayan ya gaisheta, kanta a kasa ta shiga
motar, kana ganinta kasan tana cikin damuwa sosai gashi ta kara zagbewa gaba daya, Abdul ya shiga ta
daya side din, sannan drivern ya shiga motar ya tada suka bar airport din, sai bayan da suka fita daga cikin
airport Abdul ya gaya ma drivern inda zai fara kai su, sun yi nisa sosai da tafiyar Abdul ya juya ya kalli
Khaleesat da tayi nisa cikin tunanin da take, hannunta ya saka cikin nasa wanda hakan ya dawo da ita
reality, ta ɗan kallesa, yayi kasa da murya yace "Are you hungry?" Girgiza masa kai tayi, ya jawota zuwa
jikinsa yana kallonta, ita dai bata ce masa komai ba zuciyarta na bugawa, a haka suka isa Mariri wajen
karfe biyar da rabi na yamma, Drivern na parking daga opposite din gidansu Khaleesat Abdul ya bude
motar ya sauka, jiki a sanyaye Khaleesat ta sauka daga motar, ta ma rasa ko farin ciki zata yi ko akasin haka
ganinta a kofar gidansu, Abdul ya bi ta da kallo har ta shiga cikin gidan sai a sannan hawaye suka cicciko
mata ido, Noor ce ta fara hangota tana hura gawayi ta taso da gudu ta rungumeta, sai a sannan sauran en
gidan duk suka juya suna kallon Khaleesat, Umma dake zaune bakin kofar dakinta ita ma ta dinga kallonta,
Mama Zubaida da Mama Shatu suka taɓe baki suna kallon juna, Aunty Farida dake gyara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login