Showing 69001 words to 72000 words out of 152206 words

Chapter 24 - HALYSAAH by Khlst Hydrr

13 May 2026

75

mata murmushin tace "Hlo" Ita dai Khaleesat ta dauke kai tana biye da Safiyyah suka tafi dakin da
take, Safiyyah ta kulle kofar ta dora hannu a ka tace "Na shiga uku, ke yanzu Khaleesat me yasa baza ki
daina abu kamar warce bata waye ba? Mun ga yarinya ta fito daga daki kika san ko gidansu ne maimakon
kice mata Hi kamar yanda kika ga nayi amma kika wani yi shiru kamar kurma kina bin ta da ido?"
Innocently Khaleesat tace "To ai naga bamu santa bane" A fusace Safiyyah tace "Gaskiya na gaji da halin
ki, ke ko ina sai kin sa an mana kallon en kauye? Ki ga yarinya er gayu wayayyiya abinda kema
wayancewa zaki yi yanda nayi ki ce mata Hi, to meye amfanin ilimin in baka iya zaman duniya da kowa
ba? Ko ɗan uwan nan nasa da kike complain a kai kece baki iya siyasar zama da shi ba, ba gashi ni yana
kulani ba har da tambayata ya exams, gaskiya ki canza hali Khaleesat, ya ci ace kin yi koyi da ni akan
abubuwa da yawa" Khaleesat dai bata tanka ta ba, Safiyyah tace "Duk sai kika sa kunya ya kama ni tsamo
tsamo, yanzu zata su kuma wa ennan en kauyen daga ina" Safiyyah ta dau jakarta tana ciro wayarta taga
miss calls din Mustapha tace "Ahaf ai na sani" Tsaki ta ja ta fara kokarin order din ride din da zai maida ta
gida. AJ ya bude kofar dakinsa jin ana knocking, tana kallonsa daga inda take tsaye ba tare da taje kusa
kusa da kofar ba tana ɗan kame kame tace "Ya Ajay, naga wasu mata ne a gidan, kun yi baki ne?" AJ ya
gyara tsayuwarsa yace "Ohk, su nawa?" Ta ɗan bude manyan idanuwanta tace "Su biyu" Ya gyada kai yace
"Good, you saw the fair Slim one that is like yellow pawpaw?" Yarinyar tace "Sure" Yace "To sabuwar
budurwar saurayinki ce, all of a sudden ya tattaro ta ya dawo da ita gidan nan suke zama tare, when i said i
am reporting him back home he threatened me" The lady look totally speechless and confuse, a hankali tace
"Budurwarsa kuma Ya Ajay?" Ya wani hade rai yace "Ina wasa da ke ne balle in maki karya?" Shiru tayi
bata ce komai ba ta sauke idonta kasa, yace "She's been in this house for 3 weeks now, ya kai ta school ya
dawo da ita" Yarinyar ta sake daga ido ta kallesa, AJ ya daga kafada ya kulle kofarsa, juyawa tayi tana
tafiya a hankali ta bar wajen. Har waje Khaleesat ta raka Safiyyah bayan ta takurata ta rakata, sai ma da
suka jira Lyft din ya karaso sannan Safiyyah ta shiga ta mata sallama, Khaleesat ta daga mata hannu sannan
ta juya ta koma cikin gidan, zaune ta ga yarinyar daxu a parlor, suna hada ido Khaleesat ta sauke kanta sai
ta kasa wuce sai da tace mata "Hi, i am Khaleesat" Ido kawai yarinyar ta zuba mata tana kallonta babu yabo
babu fallasa kuma babu alamar zata amsa mata, hakan yasa Khaleesat ta fara tafiya ta wuce sama, lkci daya
jikinta yayi sanyi ta shiga dakin da take ciki ta kulle. AJ ya fito dakinsa zai sauka downstairs kenan sai ga
Jay ya hauro sama fixgosa yayi a fusace yace "Are you out of ur senses Junaid, what did u just do?" AJ
yace "Ban gane what did i just do ba, Hadeeyah came, she requested to know the lady she saw in this
house, kai kuma baka isa inyi karya saboda kare ka ba tunda ba tsoronka nake ji ba, when i told u to look
for another alternative for the brat ai mayar dani mahaukaci kayi" Bude kofar wani daki aka yi sai ga
Hadeeyar ta fito da Handbag dinta, Jay ya sake AJ, ya bi ta da kallo yace "Hadeeyah" ko juyawa bata yi ba
ta ci gaba da sauka downstairs, ita dai tasan AJ ba wasa yake yi da ita ba balle yayi mata karya, yaushe ma
ya sake maka fuska balle ya maka karya, Jay yace "Look Hadeeyah, ko da wasa kika ce zaki ma people
back home wannan magana i won't take it likely with you, and that will be the end between me and you,
cause u never gave me a listening ear" Sai a sannan ta juyo tace "And so effing what? Wannan ne dalilin da
yasa all this days baka da lokacina dama ko Ya Jawwad? I am not surprise" Tana kai wa nan ta sauka ta nufi
hanyar fita gidan, Jay ya kalli AJ da ya daga kafada shima yana kallonsa. Jay wasn't even that bordered
kamar babu abinda ya faru, amma gaba daya ya fita harkan AJ a gidan, ko kallon inda yake baya yi, ya
canza code din kofar dakinsa ta yanda ma bazai shigo masa daki ba, yasan ba lallai ma Hadeeyah ta gaya
ma yan gida komai ba, she won't even dare try that, amma still yaki ko da kiranta a waya, dama ita ce me
kiran nasa, daga Oxford University take kuma bata ma ce masa zata shigo Maryland ba she just came
without notice, ita ko Khaleesat bata ma san abinda ke faruwa a gidan ba amma abinda Hadeeyah ta mata
ya tsaya mata a rai. Ranan friday Khaleesat suka yi second to the last exam dinsu, na karshen kuma za su yi
ranan talata, gaba daya ta kagu su gama ta bar kasar zuwa sannan hankalinta yayi gida, she just want to go
home, duk da tasan Housemate dinta zai ce zai siya mata flight ticket amma gani take she is just a burden to
him, for weeks now hidima kawai yake da ita, ya kai ta schl, at times ya jira ta gama jarabawa ya maidota
gida, wani lkcn dab da sanda yasan zata fito exam zai koma schl din don daukota, he really tried for her
during this period and he is always making sure that she is fine, bata ma san ta inda zata fara appreciating
din shi da Safiyyah ba, they where by her side all through, ba don su ba da bazata iya jarabawan ba ma, yau
kam tunda ta tashi take jin ta wani iri tana dai kwance da tunani iri iri a ranta, ji take kamar ta jawo
monday. AJ na zaune reading nook din dake parlor yana kokarin hada references dinsa a laptop dinsa, ga
textbooks kaca kaca a gabansa, gaba daya Jay ya bi ya goge duk wanda ya tura masa ta WhatsApp, infact
duk wani abu da Jay yasan AJ zai karu da shi na bangaren PhD da suke sai da yabi ya goge tas, shi da AJ
bai nuna masa ma yasan abinda yayi ba, shi yasa ya dukufa tun asuba yake reading nook, ɗaga kai yayi
bayan yayi perceiving din wani turare da ya gauraye ko ina na parlon, he was a bit shock ganin wanda ya
shigo parlon tare da wasu mutane biyu suna biye da shi, ya sauke idonsa, he was surprise and shock, sai
kuma ya mike ya dawo cikin parlon, ya ɗan dukar da kansa yace "Sannu da zuwa Abba" Wanda ya kira da
Abba yace "Ya karatun? Ina Ahmad?" AJ yace "He is upstairs, Abba surprise visit ka mana" Zaunawa
Abban yayi saman kujera yana amsa gaisuwan da ma'aikatan gidan ke masa cike da ladabi sannan ya kalli
AJ yace "I just branched to check on u both, daga England mu ke munje wani taro" AJ dai ya sunkuyar da
kansa, sai kuma ga wata mata da bazata wuce 50 ba cikin shiga ta alfarma ta shigo parlon da wata yarinya
that is 16 years old, AJ dai ya shafa kansa don shi abun ma dariya ya fara basa, ya dai gaisheta ta amsa,
yarinyar ta tafi ta rungumesa tace "Ya AJ naga ka zama kato, are you going to the Gym?" Matar da suka
shigo tare ta nemi waje ta zauna tace "Allah sa karatun yake" Wani kallo ya mata ta gefen ido ya wuce
sama su kuma masu aikin gidan suka tafi dauko bottle water da lemo, direct dakin Jay ya nufa a dai lkcn da
Jay ya bude kofar dakinsa ya fito, AJ yayi wata dariyar bosawa yace "Wallahi ga Abba da Aunty a parlor"
Jay ya dinga kallonsa babu ko kiftawa, can yace "Abba da Aunty kuma?" AJ couldn't stop laughing, Jay ya
ɗan leka downstairs yaga da gaske ne, buda baki yayi yana kallon AJ da ya kasa daina dariya, Jay ya sauke
ajiyar zuciya ya jawosa yace "Look, let's talk pls Ajay...." Ajay yace "Talk about what? Ba dai baka jin
maganata ba, zaka san yanda zaka yi da yarinyar nan yau, kaga ban ma kai report ba sun zo da kansu za su
gane ma idonsu rayuwar da ka jefa kanka a Maryland" Jay dai kallonsa kawai yake, AJ ya daga kafada irin
ko a jikinsa din nan ya sauka downstairs yana murmushi, Jay ya fi minti biyu tsaye thinking of what yo do,
daga karshe dai ya nufi bangaren AJ, yana tura kofar dakinsa yaji dakin a bude, juyawa yayi ya tafi dakin
da Khaleesat take yayi knocking, duk da ba bacci take ba amma idonta a kulle, ta bude idonta ta mike
zaune sai gashi ya shigo dakin, Calmly yace "Bacci kike ne Halysaah?" Ta girgiza masa kai tace "A'a" yana
kallonta yace "Ya na ganki haka ko baki da lafiya ne?" Nan ma ta girgiza masa kai tayi shiru, ya kwantar da
murya yace "Gaya min gaskiya, ko dai tunani kike Housemate?" Calmly yake mata maganar kamar ba
komai, ta ɗan yi murmushi cikin sanyin murya tace "A'a" Yace "Good, i think we have visitors a gidan nan
yau, i will change you to another room wanda babu wanda yake shiga zuwa har sanda za su tafi, nasan baza
su wuce kwana biyu ba bakin za su tafi in sha Allah" Ita dai tayi shiru tana kallonsa, ya sakar mata
murmushi, ta sunkuyar da kanta, yace "Alright, ta so mu je ko?" Sauka tayi daga kan gadon ta dau gyalenta,
yace "I will bring you all u need to the room afterward" daga haka ya nufi kofa tana biye da shi, direct ya
nufi bangaren AJ da ita, ya bude kofar dakin yana kallonta yace "Here" ta sauke idonta tana kallon cikin
dakin dake wani kamshi na musamman sannan ta shiga, ko da wasa bata san dakin AJ bane, Jay yace "I will
be back soon Halysaah" Ta gyada masa kai, ya jawo kofar sai dai bai kulle ba tunda bai san code dinsa ba
yanzu, sai bayan da ya bar wajen yaji dariya ya taho masa, to yanzu ta ina ma zai fara lallaba AJ, kawai
yasan ya ma gama kashe AJ, to in ba haka ba bai san way out ba don bangaren AJ ne kadai Halysaah zata
tsaya da babu wanda zai san tana gidan tunda babu me zuwa ko kusa da bangaren nasa sanin halinsa, amma
kaf din gidan yasan Aunty sai ta bude ta shiga banda part din AJ, downstairs ya sauka da sauri don zuwa
gaida su Abba, Khaleesat dai ta kasa daina bin dakin da kallo, komai na cikin dakin fari ne kal har wani
kyalli yake tsabar neatness, ita abun yana mata kamar dakin wani important person ne a gidan Jay ya
kawota, ta karasa ta zauna gefen gadon a hankali, she just don't know why she is not comfortable with the
room. Jay dai na zaune parlor ne amma gaba daya hankalinsa na kan AJ dake ta shan fruit din da aka kawo
ma Abba hankali kwance kamar shi aka kawo ma, Aunty kuwa tana dakin Abba dake nan downstairs tana
gyara masa, AJ ya mike zai tafi sama, Jay na ganin haka ya mike ya bi bayansa da sauri, bayan sun haura
sama Jay yace "Hey let's talk AJ" AJ ya wani kallesa, sai kuma yayi wani dariyar shakiyanci yace "Talk
about what? Pls sort ur self out, ka daina ma involving dina a crime din nan da ka aikata, kar a zata tare
muka aikata" Jay dai ya fara kokarin danne dariyar da ya taho masa don bai ma san ta inda zai fara masa
bayani ba.



*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment
07087865788 👈🏻, it's better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don
littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*
[5/22, 6:50 PM] khaleesat Haiydar ✍️: Parlon dake sama Jay ya ja AJ zuwa can yace "Ohk now, let me
explain Bruh" AJ na girgiza kai yace "I am not interested pls Jay, ni fa bana son ma kana min magana a
gidan nan kar ayi zaton tare mu ka kawota" Jay yace "Naji.... bayan yanzu bazan sake maka magana ba,
kawai dai na duba naga duk gidan nan dakin ka ne kadai yake da wahalan shiga..." Nan da nan AJ ya hade
girar sama da ta kasa yana kallonsa yace "I don't understand, me yasa kake using dakina kake misali? What
are you insinuating? What is ur point??" Jay ya shafa sumar kansa a hankali yace "My point is, na kai
Housemate dita dakin ka for the meantime before i find a way out, nasan can ne kadai su Aunty baza su
ganta ba, tunda dakin ka out of bound ne" Haka AJ yayi dropping jaw yana kallon Jay baya ko kiftawa with
shock written all over his face, Jay ya sosa kansa zai yi magana suka ji muryar Hajiya Rukayya warce suke
kira da Aunty, ta karaso parlon tace "Jay ka je Abbanku na magana a parlor" Jay yace "To gani nan zuwa
Aunty" Ta ɗan kalli AJ sannan ta juya ta bar parlon, Jay ya sauke ajiyar zuciya yana kallon AJ that was still
looking at him ko kwakkwaran motsi baya yi, da alama ya ma kasa cewa komai, Jay yayi patting ɗin
shoulder dinsa yace "I know u gat my back Bruh, you won't love seeing Abba Mad at me" Yana fadin haka
ya juya ya bi bayan Aunty yana sauke wani ajiyar zuciya, after almost 15 mins Jay ya dawo sama, zaune ya
tarda AJ a parlon dake sama ya tallabi chin dinsa da duk hannunsa biyu yana girgiza kafa, he looks restless,
Jay dai ya danne dariyar da ya taho masa da kamar zai juya ya koma downstairs, AJ na ganinsa ya mike ya
nufesa a fusace ya fixgosa yace "What offense have i done to you Jawwad? Why my room? Why will u
take her to my privacy, my own comfort zone, what sort of nonsense is this plss? Dakina fa? Meye hadina
da ita zaka kai ta har Bedroom dina?" AJ was so mad at him, nan da nan idonsa suka sauya launi, Jay yace
"To Abba dai na kiran ka, je ka dawo sai ka ci gaba" AJ dai sai kallonsa yake yana huci, can ya turasa ya
bar parlon kamar zai tashi sama, Jay ya wara ido yana shafa kansa yana ɗan murmushi, karkari dai iya
abinda zai yi kenan bazai wuce haka ba, kuma ba wani kiransa da Abba yake yi kawai wahala ne bai so
yasa yace masa ana kiransa downstairs, dakin Khaleesat ya koma ya dauko mata box dinta da abubuwan da
yasan zata yi needing ya kai dakin AJ, Khaleesat ta mike da sauri ganinsa, a hankali tace "But Housemate i
am not comfortable in this room" ya ɗan bude ido yace "Why? Meye da dakin Halysaah?" Tayi shiru bata
ce komai ba, Calmly yace "C'mon Halysaah wannan ma ai yafi wancan da kike ciki" Yana murmushi ya
kare maganar, ita dai tayi shiru bata ce komai ba, ya ajiye mata kayanta da wayarsa yace "If you need
anything just call my line" Ta gyada masa kai, ya nuna mata hanyar bandakin dake babban dakin yace "In
zaki yi sallah ga bandaki can" Nan ma dai ta gyada masa kai kawai, ya juya ya fita daga dakin ta koma ta
zauna, gajiya tayi da zama tana son kwanciya amma ta kasa kwantawa saman gadon, ita kanta ta rasa dalili,
can dai ta zamo kasa a hankali ta kwanta saman lallausan carpet dake dakin ai ko nan da nan bacci ya
dauketa, throughout ranan haka Khaleesat ta yini a dakin ita kadai, tun da Housemate dinta ya kawo mata
lunch har lokacin magrib yayi bai dawo dakin ba, sai Cook din gidan ne ya kawo mata dinner, tana zaune
saman darduma bayan ta idar da sallahn isha taji an bude kofar dakin ta daga kai, sosai gabanta ya fadi
ganin AJ, ta sauke idonta daga kallonsa, shi kam ko kallon inda take bai yi ba fuskarsa a murtuke ya tafi ya
dau second phone dinsa da laptop, ya bude press dinsa ya dau pajamas dinsa sannan ya fice daga dakin, sai
a sannan ta daga kai ta bi sa da kallo tana mamakin abinda ya shigo yi, don bata san me ma ya dauka a
dakin ba, har sannan bata kawo cewar dakinsa bane, har ta fara bacci Jay ya shigo dakin da sallama, ta mike
zaune daga kwancen da take a kasa, da mamaki yake kallonta yace "Me yasa kika kwanta a kasa
Halysaah?" Ta girgiza masa kai kawai, yace "C'mon don't do that pls, ga gado zaki wani kwanta a kasa" Ta
kalli gadon tace "Zan kwanta" Yace "Good, hope u need nothing?" Tace "Bana bukatar komai" Yace
"Alright then, good night" A hankali tace "Thank you" ya mata murmushi yace "In kashe maki wutan dakin
ko a maida maki dim light?" Tace "Dim light" Ya mayar mata wutan mara haske sosai sannan ya juya ya
fita daga dakin, bayan fitarsa ta koma tayi kwanciyarta a kasa, ita gani take kamar master bedroom din
gidan ne, may be that's why she is not comfortable, wajen karfe dayan dare dakin yayi sanyi sosai amma
taki daukan duvet din saman gadon ta rufa, kawai ta lullube da Hijab dinta, she was so cold gashi Safiyyah
bata hado mata kayanta da Sweater ba, tana ta kwance ta kasa bacci saboda sanyin da ya dameta sai juye
juye take taji an bude kofar dakin, a hankali ta sauke Hijab dinta kasa kadan tana son ganin wanda ya shigo
don har kanta ta rufe, taga AJ ne ya shigo, kallo daya yayi mata ya tafi daukar abinda zai dauka, zaro ido
tayi bayan ta zargi anya ba dakinsa bane nan kuwa, sai bayan da ya fita taji ya kullo kofar ta mike zaune
tana sake bin dakin da kallo with shock, dumin da taji dakin ya fara dauka gradually ne yasa ta gane ya
kunna mata heatern dakin, ta koma a hankali ta kwanta sai da dakin yayi dumi sannan bacci ya dauketa.....
Washegari da safe Jay na zaune main

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login