Showing 108001 words to 111000 words out of 152206 words
tunda nima ta kira layina ai ranan, but how did he get Salem's
line?" Ajay yayi murmushi yace "Definitely layinta ya sa a duba masa numbers din wa enda take waya da,
and he is using that to track us" Jay ya mike yace "We need to take down our sim card AJ, decidedly zai
samu information mun shigo kano since we are in his list, sannan i think before anything ya kamata mu fara
fighting for her innocent father's release tunda ita Halysaah yanxu bai san inda take ba and she is safe
where she is, but the Man needs help" Ajay yace "No, i don't think she is safe with her aunt, although aunt
din tace bai san inda ta koma ba amma as far as yana da number wayarta zai iya sakawa ayi tracing din inda
take ita ma" Jay ya juya yana kallonsa yayi shiru, he just realize of course hakan zai iya faruwa cause ya
daina underrating Abdul yanxu, Jay ya sauke wani ajiyar zuciya yace "That guy is something else Ajay, duk
wata salon mugunta ya sani adding it to his career skills, ina jin kawai a duba mana if there is flight zuwa
Niger republic a biya masu kawai su tafi can da aunt dinta har zuwa sanda za mu gama da Case din dad
dinta, in the other hand shi kuma mun yi sue dinsa requesting for divorce for her" Ajay yayi shiru, can yace
"But what if she is needed in court?" Jay yace "For now her lawyer will represent her, in ma an bukace ta a
court we will sort that out" Jay yace "I think that's cool, amma ya kamata mu je gidan su gun mahaifiyarta"
Ajay dai kallonsa kawai yake, can yace "Is that necessary?" Jay yace "Of course, kasan aunt dinta tace
mana the mother is not medically fit, kada wannan damuwar yayi weighing dinta down" Ajay yace "Sai mu
je a matsayin su wa?" jay ya mike yace "Human right" Abdul na tsaye rike da takardan da mahaifiyar sa ta
mika masa daga shigowar sa parlor idonsa na kan takardar yana karanta content din jiki, Meema yayarsa
ma na zaune parlon tana kallonsa fuskarta dauke da bacin rai karara, wani murmushi Abdul yayi ya
cukuikuye takardar ya jefar kan kujera, Mahaifiyar sa dake ta kallonsa ta tabe baki tace "To yanxu menene
amfanin wannan tozarcin da kaskantar da kai da ake yi? Sam kace kai baza ka ji maganata ka dau shawara
ta ba Abdallah?" Meema ta katse ta tana kallonta a fusace tace "Haba Momy ta yaya kike son ya ji
maganarki bayan uban kudin da ya kashe ma tsinanniyar shegiyar yarinyar? Ai jin maganar ki ba nasa bane
wallahi, kuma don an kawo masa sammaci ba shi ke nufin ya hakura zai saketa ba, kotu ce kawai za a shiga
ayi ta gwabzawa, kuma in sha Allahu duk inda kafafuwana za su shiga sai na shigar da su don Abdallah
yayi nasara a wannan case din, bazan taɓa bari a tozarta min kanina ba ga mari ga tsinka jaka bazai taɓa
yiwuwa ba wallahi, alamar koma waye ya zugata ta yarda aka yi karansa zai iya biyan ko nawa aka ce ya
biya a kotu, kai jama'a amma yarinyar nan anyi babbar er iska butulu, dama ni tun asali ban goyi bayan da
yace zai kai yarinyar nan Amurka ba ina jiye masa tsoron kar idonta ya bude, to gashi nan bayan karatun
har da karuwanci ta dinga yi da manyan kasar nan tunda gashi har ta samu wanda zai tsaya mata da lauya
ya biya makudan kudin da aka kashe mata kilan yace har da miliyan 100 da ubanta ya salwantar, abun
arziki dai bai amshe mu ba a family din nan, ban ga laifin ki da baki son talakawa ba Momy, shi yasa nima
bana son su na tsane su" Momy dai girgiza kafa kawai take tsabar takaici da bakin ciki ta kasa cewa komai,
Meema ta kalli Abdul daka safa da marwa a parlon yana ɗan murmushi tace "Ka kwantar da hankalin ka
Abdul, as far as ina numfashi kuma uwar mu na numfashi ko don ka rama duk abinda yarinyar nan tayi
maka za mu shiga mu fita har sai kotu ta baka ita, in sun san wata ai basu san wata ba, koma waye ke taka
mata baya daga karshe kashe kudadensa kawai zai yi a banza don sai ta shigo gidan nan mun ci ubanta da
izinin Allah, banda kaddara me ma zaka yi da er gagurumin barawo kuma makaryaci, daga basa dukiya ya
kai Lagos yace an kwace mota" Sama Abdul ya wuce kamar zai tashi sama, Momy ta bi sa da kallo cikin
bacin rai tace "Kai Allah Ubangiji ya tsine ma mutanen nan albarka, yanda suka sa ɗa na a damuwa Allah
ya saka duk zuri'arsu a damuwa, ita kuma yarinya Allah ya kasheta ma duk mu huta, tun da lamarin nan ya
faru ko abincin kirki Abdallah yaki ya zauna ya ci a gidan nan, in ya fita tun safe sai dare muke ganinsa
gaba daya ba shi da sukuni akan er talakawa, wannan wani irin iftila'i ne ya same mu" Meema tace "Tashi
tsaye kawai za mu yi ayi abinda ya kamata Momy, gidan nan ai kamar ta shigo sa ne in sha Allahu, da
bakinta zata ce ita ta hakura a kai ta gidan mijinta kawai, kuma ta shigo nan ta same mu muna jiranta" Daga
haka Meema ta mike ta bi bayan Abdallah. Jay na zaune tare da Ajay a office din lauyansu suna sauraron
sa, lauyan yace "He is trying to re-litigate a case already resolved in court, don an riga an rufe case din a
kotu tunda yace ya yafe, har lauyoyinsa sun yi filing notice of discontinuance kuma kotu tayi approving
sannan ta kulle case din ta yi releasing debtor dinsu from any further liability, but like seriously ban san
wani irin lauya bane ɗan sa, don har da written confirmation of debt forgiveness da suka yi a kotu duk yana
nan, why let them arrest the man again? Ko dai ɗan nasa bai gaya masa consequences din hakan da yayi
bane cause this is pure abuse of process and malicious prosecution" Jay yace "To yanxu meye abun yi
Barrister?" Lawyern ya ajiye pen din hannunsa yace "Za mu yi Filing motion to dismiss the already
forgiven case, and we will plead abuse of process, sannan muyi Raising estopped from pursuing the debt
again in near future, just that za mu yi presenting documentation of the original debt forgiveness and court
records to the court, wannan ma ai sun yi breaching court order ne kuma hakan laifi ne me zaman kansa"
Ajay yace "That is because suna ganin ba shi da wanda zai tsaya masa ko shekara nawa zai yi a kulle, his
family have no voice to do so, that was why the breached the court order for their selfish interest" Lauyan
yace "Babu matsala in sha Allah za mu shigar da kara kotu, and the man will be bailed out while the case is
going on, they will even have to pay him damages...." Bayan la'asar Ajay yayi parking a kofar gidansu
Khaleesat, dai dai inda yayi parking ranan da suka yi dropping dinta da daddare, a bayansu kuma wata
mota ce ita ma tayi parking, Guard uku ne suka fito daga cikin motar dukkansu suka yi tsaye jikin motar da
suka sauka, shi dai Jay kallon unguwan kawai yake, Ajay ya bude mota ya sauka, ya jingina da motar ya
rungume hannunsa, Jay ma ya sauko sannan ya zagayo inda Ajay yake tsaye yace "Where is the house?" Ba
tare da Ajay ya kallesa ba yace "Gashi nan kana kallo" Jay ya kalli gidan dake opposite dinsu, wani almajiri
ne ya zo wucewa Ajay ya kirasa, yaron ya taho da sauri Ajay yace "Shiga cikin gidan can kace ana sallama
da Maman...." Sai kuma ya kalli Jay alamar ya fadi sunan, Jay na kallon almajirin yace "Kace ana sallama
da Maman Halysaah" Almajirin yace "Toh" Da sauri ya nufi gidan, Ajay yace "Meye kuma Halysaah? How
is that even a name? In zaka kira sunanta na asali kawai ka kira" Jay na kallonsa yace "Meye sunan nata na
asali?" Ajay bai kallesa ba har sannan yace "Ka fi ni sani ai, tunda ka fi kusa da ita" Jay ya ɗan yi
murmushi bai sake ce masa komai ba, Nenne ce ta leko kofar gidan tana zazzare ido kuma bata yarda ta fito
waje ba, tana yin ido hudu da su Jay sannan ga wasu samudawa da ta gani har uku tsaye jikin wata motar ta
juya ta koma cikin gidan da sauri har tana tuntube, sai ga Mama Zubaida tana gyara gyalenta da ta yafa
akan daurin kirjin da tayi, Mama Shatu na bayanta tana kokarin saka hijabinta ta bai bai, tsaye duk suka yi
daga cikin gidan suna leko su Ajay da samudawan dake jikin mota a tsaye, Mama Shatu tayi karfin halin
cewa "Ina wuninku?" Jay ne ya karasa har inda suke tsaye, shi dai Ajay na rungume da hannunsa yana
kallon ikon Allah, Jay ya gaishesu duk suka amsa kamar munafukai suna gwale ido, Jay yayi kasa da kai
yace "Mahaifiyar Halysaah mu ke son gani" Da sauri Mama Zubaida tace "A'a to ku shigo mana, Bismillan
ku ai tana ciki, fakewa kawai suka yi da cewar bazata iya fitowa ba bata da lafiya, lafiyarta lauz ku shiga
har dakin ku sameta" Duk tunaninsu an zo tafiya da Umma ne kamar yanda aka zo aka tafi da Malam Ali,
Jay ya juya ya kalli Ajay dake jin duk conversation din su daga inda yake tsaye, ko ba a gaya masa ba yasan
stepmom din Khaleesat ne matan, ya kulle motarsa yana kallon wa enda ke tsaye jikin mota yayi masu
alamar da cewar za su fito in 5 mins sannan ya karasa har inda Jay ke tsaye yana jiransa su shiga gidan, su
Mama Zubaida kuwa har sun koma tsakar gidan sun tsaya cirko cirko suna jiran su ga yanda za a shigo a
fitar da Umma, da hannu suka nuna ma Jay da Ajay hanyar dakin Umma, Jay ne yayi sallama bakin kofar
dakin, shi dai Ajay na tsaye a gefe yana kallon white t-shirt dinsa to be sure ruwan taɓon da yayi gaja gaja a
compound din bai fallatsar masa a jiki ba, Mama Shatu da Mama Zubaida a tsakar compound din suke
zubar da duk wani ruwan da suka yi aiki haka ma yaransu, sun maida compound din kamar na mahaukata,
gashi simintin da aka masa duk ya dagargaje ya kusa komawa kasa, shi yasa in suka zubar da ruwa sai ya
cabe, kudaje sai safa da marwa suke ta ko ina, ga kwanuka gaja gaja, igiyoyin gidan kuwa duk an rataye
kaya, Ajay na ganin Jay ya shiga dakin Umma shi ma ya shiga ciki da sallama, dukawa Jay yayi daga bakin
kofar ya gaida Umma da Maman Salame dake dakin, Ajay ma yayi hakan ya gaishe su, ganin haka Maman
Salame ta tashi da sauri ta shimfida masu darduma a kan ledan dakin tana masu sannu da zuwa, duk
tunaninta ita ma zuwa aka yi za a tafi da Umma amma sai bata ga alamar hakan a tattare da su ba duba da
yanda suka yi gaisuwa cikin girmamawa, Jay ne kawai ya zauna kan darduman Ajay kuwa ya kasa zama ga
wani zafi da yake ji a duk jikinsa, ya ciro handkerchief dinsa yana goge zufan goshinsa, Mama Salame ta
dau mafici ta mika masa, ya ɗan yi murmushi ya amsa yace "Nagode" Mama Salame ta dage labulen dakin
tana cewa "Yau mun fi sati biyu basu kawo wutan ba, ance tiranspoma tayi bindiga" Nenne dake makale
kofar bandaki rike da buta ta dinga leka dakin Umma bayan Maman Salame ta daga labulen, haka su Mama
Zubaida da suka ji shiru ba a taso keyar Umma an fito da ita ba, Jay na kallon Umma dake zaune don ko ba
a gaya masa ba yasan ita ce mahaifiyar Khaleesat duba da kalan fatarta sannan babu ta inda Khaleesat ta
bar ta, ba karamin kama Khaleesat ke yi da mahaifiyarta ba a nan ta samo asalin kyanta, Yayi kasa da
murya yace "Ya jikin Umma?" Cikin sanyin murya Umma tace "Alhamdulillah da sauki" Ajay ma yayi
mata ya jiki ta amsa tana kallonsu gaba daya don jira kawai take taji me ke tafe da su, in ma cewa za su yi
tafiya suka zo yi da ita dama a shirye take tunda hijab dinta na jikinta, shiru ne ya biyo baya a dakin, don
Jay bai san ta inda zai fara introducing kansa ba ma, haka ma Ajay da yayi shiru zafi na neman hallaka sa,
after few seconds Ajay yayi karfin halin breaking silence din a hankali yace "Makaranta daya mu ke tare da
Jidderh a can America, so kawarta ta sanar mana abinda ke faruwa shi ne muka nemi ta bamu address mu
zo nan duba ki" Sosai hankalin Mama Salame ya kwanta jin abinda Ajay yace, Mama Salame tace "Allah
yayi maku albarka, kuma mun ji dadi mun kuma gode da zuwan da ku ka yi" Jay ya kwantar da murya yace
"Kiyi hakuri Umma kuma ki kwantar da hankalinki, muna tabbatar maki in sha Allah komai zai wuce nan
ba da dadewa ba, don za ayi duk abinda ya kamata, mahaifinta ma in sha Allahu za mu yi abinda ya dace a
sakesa a yan kwanakin nan, ita kanta Halysaah zata dawo gida in sha Allah" Maman Salame ta daga hannu
sama cike da farin ciki tace "Alhamdulillah ya Allah, gaskiya mun ji dadin jin hakan daga gare ku, don
bamu da wanda zai tsaya mana sai Allah, Alhamdulillah" Ita dai Umma kanta na kasa hawaye na zuba
idonta, Ajay yace "Zuwa gobe da safe in sha Allah za mu shigo" Mama Salame tace "To Allah Ubangiji ya
kai mu goben lafiya, mun gode, mun gode" Mikewa Ajay yayi ya kara yi ma Umma sallama sannan ya fita
daga dakin kar yayi suffocate, heat wan finish prince, don in akwai abinda baya shiri da shine zafi, baya son
zafi ko yaya yake, Nenne na ganin Ajay ya fito daga dakin Umma ta sake komawa cikin bandaki da sauri,
su Mama Zubaida da Mama Shatu suka bi sa da kallo har ya fita daga compound din, to su waye wannan
kuma su da suka baza ido da kunne su ga an fito da Umma tana kuka, bayan fitar Ajay da few minutes sai
ga almajirai suna shigowa gidan da buhun shinkafa biyu, carton din taliya biyu, carton din indomie biyu,
manyan gallon na manja da mangyada, da carton din maggi duk kuma aka dinga dire su a kofar dakin
Umma, daga Nenne har su Mama Zubaida haka suka saki baki suna kallon ikon Allah, Maman Salame ta
taso zuwa bakin kofa tana kallon kayan abincin da mamaki tace "Ikon Allah, har da uban hidima haka??"
Jay ya ajiye ma Umma 100k yace "Gashi Umma ayi cefane da wannan, in sha Allah gobe za mu shigo da
izinin Allah" Bai jira cewar Umma that was speechless and shock ba ga hawayen dake sauka idonta kawai
ya fita daga dakin.....
[6/6, 5:08 PM] khaleesat Haiydar ✍️: Jay na fitowa dakin Umma, Nenne dake tsaye tsakar gida bayan ta
fahimci ba yan sanda bane ta rushe da matsanancin kuka ta nemi er kujera ta zauna tana kallonsa tace "Da
wannan uban kudaden da ku ka kashe na siyo kayayyakin abincin nan ai da belin ɗa na ku ka yi, wallahi
maraya ne ba shi da kowa, in ba wani ikon Allah ba sai dai ya rube a can, wancan karan ni kadai nasan
wahalan da na sha na ganin an sako sa, babu inda kafata bata shiga ba wallahi, na dinga bi gida gida ina
neman taimakon kudi" Jay ya kwantar da murya yace "In sha Allah za mu yi bakin kokarin mu na ganin an
sako sa kaka, ki kwantar da hankalin ki" Nenne na matsar kwalla da gefen haɓar zaninta tace "Ɗan nan ina
hankalina zai kwanta ɗa na na can furson? In dai daga gidan radio da talabijin ku ke ni dai na amince ku zo
ku dau muryata da fuskata in nemi taimakon al'ummar musulmai ku watsa ni duniya ta gan ni ina jawabi,
kilan gwamna ma in ya gani yaji tausayina ya saka baki a sakar min ɗa na" Jay yace "Ba sai anyi haka ba
Kaka, ina tabbatar maki nan ba da dadewa ba zai dawo gida in sha Allah" Nenne tace "To daga ina ku ke?
Ko dai kungiyar kare haƙƙin en Adam ne" Jay ya ɗan yi shiru, Mama Zubaida da Mama Shatu dai sun yi
cirko cirko a tsakar gida suna gwale ido suna kallon Jay, Jay yace "Makarantar mu daya da Halysaah a can
Amurka, shi ne muka samu labarin abinda ya faru mu ka zo" Nenne ta mike da sauri tace "To ai yau kusan
sati daya kenan ana neman ta ko sama ko kasa, wallahi bamu san inda take ba, ita uwar ta na daki tana
jimamin ta, ni kuma ina nan ina jimamin ɗa na, haka muka raba abun, amma tun da yarinyar nan ta samu
labarin daurin aurenta da annoban nan Awdul ta shiga duniya, wallahi bakina da nata tace min bata son sa
bazata iya auren sa ba, tun da uwata ta haifeni ban taɓa ganin inda ake auren dole ba" Nenne na kai wa nan
ta fasa sabon kuka, Jay dai ya ma rasa abinda zai ce mata, beside baya ma son yayi magana gaban su Mama
Zubaida da suka wangale kunnuwa suna saurare, kawai ya saka hannu a aljihunsa ya ciro dubu ashirin din
da yayi saura, yaje har gaban Nenne ya mika mata da ladabi yace "Ga wannan Kaka, in sha Allah za mu
shigo gobe" Nenne ta daga hannu da sauri tace "A'a, gwara ku hada kawai ku kai furson a sako min ɗa na,
don yafi min ko wani kudi a duniya" Jay yayi murmushi yace "Ki amsa kaka, na maki alkawarin za a sako
sa nan ba da dadewa ba in sha Allah" Nenne ta amshi kudin da hannu bibbiyu tana sa masa albarka cikin
rawan murya tace "In ma Allah ya sa kun zo gobe ba ku sameni a nan ba ku sa a raka ku gidana babu nisa
daga nan" Yana murmushi yace "In sha Allah Kaka" Daga haka yayi mata sallama sannan ya fita daga
gidan su Mama Zubaida suka bi sa da kallo babu fara'a ko wacce da abinda ke yawo a ranta, Nenne ta kulle
kudin a habar zaninta ta soke tace "Dama gobe da asuban fari zan je gun Malam Na ta'ala, Allah ya sa in
samu kwale kwalen da zai tsallakar da ni da sassafe"