Showing 111001 words to 114000 words out of 152206 words
Dakin Umma ta nufa tace "To ke Salame kike ko wa?
Ki fito mana ki shigar mata da dukiyar nan dake bakin kofa kar a faki ido a sungume mata wani abun,
kayan abinci ai dukiya ce me zaman kanta a yanxu, Allah kadai yasan dubu dari nawa suka kashe wajen
siyo kayan abincin nan...." Maman Salame ta fito daga dakin Umma ta fara shigar da kayan abincin ciki,
Mama Shatu ta shige dakinta fuska a murtuke, Mama Zubaida ma ta tabe baki ta shige nata dakin ta sako
tsumman labulenta dake rataye da kyauren dakin. Jay na fita waje ya tarar da Ajay cikin mota yana zaune a
kujera me zaman banza ya kwantar da seat din kujeran idonsa a lumshe, Jay ya bude driver seat ya shiga
yana kallon Ajay jin yanda ya kure AC din motar gaba daya, Ajay ya gyara zamansa yana kallonsa, Jay dai
yayi murmushi ya fara driving motar Ajay ya nuna masa hanyar da suka bi suka fita ranan da yayi dropping
Khaleesat, motar dake bayan su ma ya bi su, Ajay sai sake kare ma unguwan kallo yake with distress har
suka isa main road, bayan sun hau saman titi ya kalli Jay yace "In za a samu gida ko na 30M zuwa 50M ne
a siya pls su bar wannan vicinity din" Jay yace "I think that will be okay idan anyi releasing mai gidan but
not now" Ajay yace "Duk daya ne Bruh, plss kayi ma Salisu magana a fara duba gidan daga yau zuwa gobe,
that house isn't healthy for a living thing, ta yaya me rai zai dinga rayuwa a gida irin wannan? This is so
pathetic, or am i exaggerating pls?" Jay yace "But haka kawai baza mu yanke decision without the release
of the head of the House ba, so kake mu kara triggering saurayin nata bayan har yanxu ba mu yi achieving
ko abu daya ba, we are following everything step by step Ajay, we will reach der in sha Allah" Ajay bai
sake cewa komai ba, amma da gaske hankalin sa ya tashi kwarai ganin condition din cikin gidan most
especially the compound, in ba dole ba shi kam babu abinda zai sake kai sa gidan nan, it's not about the
house structure or where it's located but the hygiene of the house, sai kace cikin prison, ji yake kamar har
ya kamu da cholera don har wani zazzabi zazzabi ya fara ji, ya kai hannu ya rage Ac din motar, shi dai Jay
driving dinsa kawai yake. Washegari da yamma haka nan suka sake komawa gidan bayan Lauyan su yayi
requesting su tambayi matan Malam Ali ko da akwai wani written debt forgiveness document kuma
original one din da kotu ta bashi bayan masu karansa sun janye karar, cause in dai babu takardun to sai dai
ayi case din biyan bashin da yake bin Alhaji Musa amma ba dai su yi karan sa ba, Bayan Ajay yayi parking
ya juya yana kallon Jay yace "Zan jira ka" Er dariya Jay yayi yace "Toh ai da baka biyo ni ba kayi zaman
ka a gida kawai" Bai jira cewar Ajay ba ya sauka daga cikin motar ya nufi cikin gidan, yau ma dai kamar
jiya ba su kadai suka zo unguwan ba don securities da suka biyo su har sun fi na jiya tunda basu san ko
Abdul na da Spy a unguwan ba, infact bazai ma rasa ba, definitely za a basa labarin wasu sun zo gidan su
Khaleesat jiya, so they are not loosing guard by any means, and they are never going to let him take them
unaware, A takaice Jay ya gaida Kishiyoyin Umma dake zaune tsakar gidan sun yi rashe rashe da su, yau ko
murhu basu kunna ba don dawowar su kenan daga wajen Malamai, tun asuban fari suka bar gida sai yanxu
suke dawowa, duk suka bi Jay da kallo, Jay dai yana tafe yana kallon Islam da Noor dake ma Umma wanke
wanke a tsakar gidan don ko ba a gaya masa ba yasan siblings din Khaleesat ne duba da pheomelanin din
su, a tare suka gaishesa ya sakar masu murmushi yace "How are you?" Murmushin kawai suka yi basu ce
masa komai ba Islam na wanke wanke Noor na mata dauraya, Jay ya isa har kofar dakin Umma yayi
sallama, Umma da ta gama gyara dakinta kenan ta saka turaren wuta na tsinke ta amsa sallaman sa, a
kullum in zaka shigo dakin Umma a haka zaka tarar da shi fes fes, duk da ba komai bane a dakinta don ta
siyar da komai nata amma kullum a gyara zaka same dakin da turaren tsinke, Jay ya shiga dakin Umma na
kallonsa tace "Sannu da zuwa" Tabarma ta dauko ta shimfida masa don bata yi tunanin zai dawo yau kamar
yanda yace mata jiya ba, Jay ya zauna yana murmushi ya gaisheta, Umma ta zauna kan dardumanta ta amsa
gaisuwar sa, har a sannan zaka ga damuwar dake tare da ita alamar karfin hali kawai take, sai kuma ta mike
tace "Bari in kawo maka ruwa" Ruwa ta debo masa a cup din stainless ta karaso ta ajiye masa a gabansa
sannan ta koma ta zauna, yace "Nagode Umma" Ɗan murmushi kawai tayi, Mama Zubaida da Mama Shatu
suka yi tsit a tsakar gida ko wacce ta kasa kunne ko zata ji abinda ake cewa a dakin Umma, Ajay ne ya
shigo gidan duk suka zuba masa na mujiya, sau daya ya kallesu ya dauke kai ya nufi dakin Umma, yau dai
tsakar gidan a bushe yake bai yi gaja gaja da ruwa ba da yake basu yi girkin siyarwa ba, Islam na tsaye
bakin kofar dakin Umma bayan ta shiga da kayan wanke wanken da suka yi da twin sis dinta, Ita kuma
Noor na share inda suka yi wanke wanke, Idan Ajay ya kalli Noor sai ya kalli Islam, ya amsa gaisuwar da
Noor ke masa tana rike da tsintsiya, yana isa bakin kofar dakin Umma ya ja dogon hancin Islam don ita ce
ke mugun kama da Khaleesat har bakinsu iri daya ne, murmushi tayi tana kallonsa yace "How are you?" Ta
sauke idonta bata ce komai ba yanda dai Khaleesat ke yi, da sallama ya shiga dakin Umma, Jay ya daga kai
yana kallonsu don bai yi tunanin zai shigo ba, Umma ta amsa sallamansa, ya zauna daga gefen Jay sannan
ya gaisheta, Umma ta amsa da murmushin karfin hali tana masa sannu da zuwa, after some seconds Jay ya
fara magana a hankali yace "Umma akwai wasu takardu na yarjejeniyar kotu na yafiyan bashin da aka yi
ma Mai gidan nan, Allah yasa kun san in da takardun suke ana bukatarsu ne" Umma tayi shiru, can tace
"To, amma wallahi ban sani ba sai dai ko a duba dakinsa ko suna nan" Jay yace "Eh a duba Umma, Allah
ya sa a gani" Umma tace "Ameen" Mikewa Umma tayi ta fita daga dakin, Mama Zubaida da Mama Shatu
suka bi ta da kallo har ta shiga dakin Malam Ali, after almost 8 mins sai ga Umma ta fito da wasu takardu
wanda bata san ko na menene ba dai zata kai masu su duba ko akwai wanda ake nema a ciki, a haka ta
wuce Kishiyoyinta da idanuwansa duk ke kanta, ta koma dakinta ta mika ma Jay takardun sannan ta koma
kan dardumanta ta zauna, Jay ya dinga duba takardun daya bayan daya, yaga har da takardun makarantar
Malam Ali, ashe har Degree garesa a Agriculture, kafin nan kuma sai da yayi diploma, yana ta dai duba
tulin takardun har daga karshe yaga wasu takardun da yake saka rai na yarjejeniyar yafiyar da aka yi ma
Malam Ali a kotu na biyan bashin Mahaifin Abdul ne, ya mika ma Ajay shi ma ya amsa yana duba
takardun, Jay ya kalli Umma yace "Ina jin wannan ne takardun da muke nema" Umma tace "To
Alhamdulillah" Jay yace "To za mu koma, duk yanda ake ciki za mu dawo in sha Allah" A hankali Umma
tace "To Allah ya saka da alkhairi, amma sai dai akwai wata uwar dakina da bata ji ba bata gani ba yan
sanda suka tafi da ita shekaranjiya har yanxu ba a ma san wani caji ofis din aka kai ta ba" Ajay dake
kallonta yace "Ko Baabar nan ta Hotoro?" Cike da karfin hali Umma tace "Ita, wallahi bata ji ba bata gani
ba aka je aka tafi da ita" Ajay yayi shiru yana kara mamakin stupidity din Abdul, he don't think that guy is
okay in anyway, after some seconds ya kalli Umma a hankali yace "Za mu bincika inda aka kai ta mu yi
bailing dinta in sha Allah" Umma ta share hawayen da ya kawo idonta ta kasa cewa komai, Jay yace "Ki
kwantar da hankalin ki Umma, in sha Allah komai zai wuce da izinin Allah" Cikin rawan murya Umma
tace "Allah ya sa" Jay ya kalli Ajay, tsabar tausayin Umma kawai yaga gwara su gaya mata gaskiyar inda
Khaleesat take ko zata ɗan samu sukuni a ranta, Jay ya sauke idonsa a hankali yace "Sannan Umma akwai
maganar da zan gaya maki yanxu, amma don Allah kar ki gaya ma kowa har zuwa sanda za mu gama
abinda muke" Ajay ya juya ya wani kallesa don har ya gano maganar da Jay zai gaya ma Umma, Umma na
share idonta tace "To in sha Allah" a hankali Jay yace "Halysaah na Lagos, amma don Allah ba ma son
kowa yasan hakan Umma, ko makusantan ki kar ki gaya ma tukun....." Umma da zuciyarta ke bugawa tace
"Lagos kuma? Wajen wa a Lagos?" Jay yace "Tana wajen sister din ki ne, amma mun ce mata kar ta nuna
maki tana wajenta har sai sanda komai ya dai daita, shi yasa ma har yanxu bata gaya maki ba" Umma tayi
shiru, amma fa ji tayi wani nutsuwa ya zo mata, lkci daya kuma taji hankalinta ya kwanta kamar an yaye
mata kashi saba'in na damuwar da take ciki, Umma tace "In sha Allahu babu wanda zai ji hakan daga gare
ni, yanda ku ka tsaya mana ku ma Allah Ubangiji ya tsaya maku haka, Allah ya saka maku da alkhairi..."
Umma ta kasa ci gaba hawaye masu zafi na sauka idonta, A haka Ajay da Jay suka fita daga dakin Umma
za su koma Office din lauya din su da takardun hoping shi ne kotu zata bukata, yau ma dai Ajay ji yayi
kamar zafi zai kashesa a dakin Umma amma haka ya dinga daurewa har suka fita daga dakin sannan ya ciro
handkerchief dinsa yana goge zufan da yayi, ya kalli Islam dake zaune bakin kofar dakin Umma da
takardan makaranta a hannunta alamar karatu take, Noor kuma na hura gawayi a can gefe, ya saka hannu a
aljihu ya ciro kudaden da bai san ko nawa bane ya mika ma Islam yana kallonta yace "Ku raba ke da er
uwarki" Islam taki amsan kudin, ya hade rai yace "C'mon collect it" Jay dake kallonta shi ma ya sakar mata
murmushi yace "Karba mana cutie" Islam ta kalli Noor amma still taki amsan kudin, Ajay ya zare mata ido
yace "Kee, amsa nace" A hankali ta kai hannu ta amshi kudin, Ajay da Jay suka fita daga compound din,
Kishiyoyin Umma suka dinga kallon uban kudin da aka ba Islam kamar idanuwansu za su fito ko kiftawan
kirki basa yi, Islam ta tashi ta shiga dakin Umma da kudin a hannunta, Mama Zubaida ta mike ta ma Mama
Shatu alamar su shiga daki, duk suka shiga dakin Mama Shatu sannan suka sake labule, Mama Zubaida ta
rike haba tace "Anya kuwa Shatu baza mu san yanda za mu yi Abdul ya samu labarin abinda ke faruwa a
gidan nan ba? Ni wallahi ban yarda wa ennan samarin basu san inda Khaleesat take ba, kina fa ganinsu kin
ga 'ya yan masu kudi, dubi suturan da suka sa wa, ji motocinsu, sannan kalli fatarsu kalan ta yan hutu, in fa
muka yi sake Shatu bakin ciki ne zai kashe mu a gidan nan muna ji muna gani" Mama Shatu tace "Ke ma
dai wallahi kin fiye gaggawa, sai kace kin manta me Malamin yace mana, duka duka ba yau muka kai masa
kudin ba, to mu zuba ido ya fara aiki mana tukun" Mama Zubaida tace "Duk da haka dai gwara mu ma mu
dinga yin namu ta bayan fage Shatu, kada mu sakankance mu bar malami da aiki shi kadai, ya kamata tun
wuri mu san yanda za mu yi mu ankarar da Abdul abinda ke faruwa a gidan nan, don gaskiya na sha jinin
jikina da wa ennan zaratan samarin, ke ki ga tulin kudin da suka ba Islam, sannan kalli uban kayan abincin
da suka jibge jiya daga karshe don walakanci aka biyo mu da kwano uku uku da taliya bibbiyu da man
gyada da manja, sai maggi leda bibbiyu ga mayunwata, ke kiji wai yau Zahra'u ce da tsam mana kayan
abincin da aka jibge mata, bayan haka Allah kadai yasan nawa suka bata a daki tunda ba gaya mana zata yi
ba, ga Nenne ma a gaban mu aka bata rafar kudi yan dubu dubu, anya bamu shiga uku ba Shatu? Ni fa
jikina yayi sanyi hankalina ya tashi, meye hadin su da Khaleesat din da har suke wannan hidima haka a
kanta, mu ga 'ya yanmu a zube har yau babu mataya sai talla suke, ni fa wallahi ko tsirara zan yi yawo
gwara inyi da dai Zahra'u da zuri'arta su ji dadi a duniya" Mama Shatu tace "Yanxu dai Gwaska za mu
samu ya raka mu gidan su Abdul din tunda yace yasan gidan uban sa, nasan Abdul din zai taka ma yan
iskan burki har ma ya bamu makudan kudi fallasa asirin abinda ke faruwa da mu ka yi" Mama Zubaida tace
"Atoh dai tun wuri my gaya masa abinda ke faruwa, zuba ido ba namu bane wallahi, amma sai dai jibi
kenan za mu je gidansu Abdul din don Gwaska ya tafi dambatta daxu uwarsa ke gaya min yaje kai kaya
can" Mama Shatu tace "Ai jibin kamar gobe ne, kin ga gobe dama mu gama girkin mu da wuri mu tafi inda
wannan matar ta mana kwatance daxu a gidan Malam" The next day wajen karfe biyar da rabi na yamma
Sha'awa tayi sallama bakin kofar dakin Umma dake yi ma yan biyun ta gyaran gashi, babu kowa gidan don
duk yan matan gidan basu dawo talla ba, kananun yaran kuma sun tafi gantali, tun Sha'awa bata shigo dakin
Umma ba take cewa "Umma yanxu Ladingo ke sanar min an sako Gaje, wai daxu taje unguwan taga ana ta
shiga gidan yi mata jaje" Umma ta sake gashin Noor ta mike da sauri tace "Da gaske Sha'awa?" Sha'awa
tace "Wallahi kuwa Ladingo bazata min karya ba Umma, tace Gaje dai ta dawo gida ga yan unguwa na ta
tururuwan shiga yi mata jaje tun daxu" Umma ta jawo Hijab dinta tace "To bari in je gidan Allah ya sa da
gaske ne dai" Sha'awa tace "Da ina da kudin mota ai da mun je tare Umma, kusan kwanan ta biyar fa a
kulle, don ma akwai kanwarta da zata kula da jikokinta tunda uwarsu na can Libiya ta tafi aikatau, ubansu
kuma yayi watsi da su, banda haka da yaya makomar jikokin nan nata fisabilillahi?" Umma bata tanka ta ba
ta gama saka hijab dinta ta daura nikab ta dau purse zata fita, Noor da Islam suka marairaice wai za su bi ta,
ganin in ta tafi su kadai zata bari a gida yasa tace su saka hijab gaba daya, haka nan duk suka saka Hijab
suka fita daga dakin Umma na biye da su, kusan kullum sai Umma taje gidan Gaje sau biyu ta duba ko ta
dawo amma sai taga akasin haka sai dai ta samu kanwarta Iya a gidan, jiki a sanyaye take juyawa ta koma
gida don Iya na ganinta take fara masifar ita ta saka er uwarta a uku, Umma zata fita gidan tare da yan
biyunta sai ga su Mama Shatu da Mama Zubaida sun shigo wujiga wujiga da su, kana ganin fuskokinsu
kasan a gajiye suke likis, ga wuyan hijabinsu duk yayi jagab da zufa, kafafuwarsu kuwa kamar wa enda
suka dawo daga gona, Umma dai tayi masu sannu da zuwa kawai ta fita daga gidan su Islam na biye da ita,
ai ko tana isa gidan Gaje taga da gaske an sako Gaje, Gaje na ganin Umma tayi kamar bata taɓa saninta ba
a duniya, yanda take amsa gaisuwa da jajen masu shigo mata haka ta amsa ma Umma kamar ranan ta fara
ganinta, ita dai Umma na zaune tayi shiru ta ma rasa me zata ce, su Islam na zaune gefenta, Gaje bata sake
kallon direction dinta da yaranta ba, duk wanda ya shigo haka take sanar masa yanda Maman Fu'ad ta ci
amanarta tace ma yan sanda ita bata taɓa ganinta ba ma balle wata Khaleesat, In tayi bayanin sai ta rushe da
kuka tace "Ban taɓa tunanin Sadiyah zata min butulci haka ba duk alakar da ke tsakanin mu wai bata taɓa
gani ba, kaji tsoron Allah kaji tsoron mutumin yau kawai, duk kyautata ma yarinyar nan da nake amma ta
barni ni kadai raina a cikin matsalar da na tsoma kaina" Ita dai Umma tayi tagumi tana sauraron duk abinda
Gaje ke cewa.
[6/9, 7:26 PM] khaleesat Haiydar ✍️: Sai bayan da aka yi sallan Magrib Umma ta bar gidan Baaba Gaje da
yan biyun ta, kuma har ta bar gidan Gaje bata nuna ta taɓa saninta ba don casually ma take amsa mata
kamar yanda take ma kowa da ya shigo mata jaje, Umma dai a sanyaye ta baro gidan, tana isa gida taga
mutane tsattsaye a kofar gida kowa da abinda ke fitowa bakinsa, sosai taji gabanta ya fadi gashi ta kasa
fahimtar akan me ake ta surutu haka, can dai ta dubi wata makociyarsu dake tsaye wajen tace "Munnira me
ke faruwa?" Munnira tace "Wallahi Umman su Khaleesah nima fitowa ta kenan da naji hayaniyar tayi
yawa, amma wai kamar wasu mutane ne da ba a san ko su waye ba suka shiga gidan naku suka yi aika aika,
ance a katuwar mota suka zo...." Umma ta kasa cewa komai tana kallonta, da kyar take jan kafa tana rike da
su Islam ta shiga gidan har sannan gabanta bai daina faduwa ba, Su Mama Shatu da Mama Zubaida ta gani
tsaye da 'ya yan su duk sun yi cirko cirko a tsakar gidan da makota ana ta maida magana, tsakar gidan dai
cike yake da jama'a kowa na fadin albarkacin bakinsa, Umma ta dake tace "Wai me ke faruwa ne a gidan?"
Mama Zubaida ta wani kalleta a walakance tace "Ina kuwa za mu san me ke faruwa tunda mu dai muna
zazzaune sai