Showing 150001 words to 152206 words out of 152206 words

Chapter 51 - HALYSAAH by Khlst Hydrr

13 May 2026

118

saɓa maki
wallahi, kuma bari kiji, common University din kasar nan ma baza ki yi ba balle na wata kasar don babu
inda aka ce lallai lallai sai kinyi karatu, at first nayi tunanin kina da kamun kai da nutsuwa ne shi yasa
confidently na kai ki America, amma sai kika tafi kina rayuwa da wani ƙaton ɗan iska a gida daya without
my knowledge, ya kai ya kawo ko kudi na tura maki sai kiyi kamar baki gani ba for days tunda kin samu
ɗan iskan dake siya maki abubuwa, not even one guy, kattin maza har biyu kika je kina mu'amala da su a
can, ko wanne kuma ke kika san abinda kike basa da yake kashe maki kudi, so ko da kuskure kika sake
kawo min maganar karatu wallahi sai na maki abinda har ki koma ga Allah baza ki manta ba" Yana kai wa
nan ya dau wayarsa ya fice daga parlon kamar zai tashi sama, Khaleesat ta bi sa da kallo hawaye masu zafi
na sauka idonta. Har dare Khaleesat na dakinta abun duniya ya taru ya mata yawa, wajen karfe sha biyun
dare har ta fara bacci taji an bude kofar dakinfa, a hankali ta bude idonta, wutan dakin taga ya kunna sai
kuma ya kashe, ita dai tana kwance bata juyo ba, ya karaso inda take kwance ya cire duvet din jikinta ya
cire hulan kanta yana shafa dogon gashinta ya kai fuskarsa kusa da nata murya can kasa yace "You gave me
Neither lunch Nor dinner today, saboda kinfi karfin a gaya maki gaskiya ko?" Ita dai bata ce komai ba duk
da tana jin sa, dagota yayi zaune ya rungumeta yace "Then let me have you since you are not giving me
what u cook" Bai jira abinda zata ce ba ya fara kissing dinta, Sosai Abdul ya bata lokaci wajen romancing
dinta irin yanda yasan zai gigita ta, in ba ita ba ma babu warce ya taɓa romancing har haka, ko lube din bai
dauko ba yau don baya ganin zasu bukace sa ma, a wannan moment din Frustration dinsa yafi na kullum
don sosai ya kai zuciyarsa nesa bai kai mata hannu ba, yana wani irin huci ya fixgota da karfi yace "Why
are you doing this to me Khaleesat? Why are you frustrating me?" Kasa ce masa komai tayi jikinta na rawa
hawaye na zuba idonta, ta gaji da ce masa ita bata san abinda ke faruwa ba, cikin daga murya jikinsa na
rawa yace "Ki bani amsa? Me na maki kike wahal dani kike cutata haka?" Khaleesat dai ta kasa ce masa
komai jikinta na rawa don tsoron magana ma take ya gaggaura mata mari, yana wani irin huci ya turata
yace "Ki jika abun ki ki sha" Yana fadin haka ya sauka daga saman gadon ya saka Pajamas dinsa ya fice
daga dakin kamar zai tashi sama, Khaleesat dai ta jawo duvet ta rufe jikinta har sannan zuciyarta na bugawa
ta fashe da matsanancin kuka, bayan kusan minti goma taji fitar motarsa a gidan gaba daya. Da yammacin
ranan Momy na parlonta da Godiya sai ga Abdul ya shigo kamar an hankado sa, Momy na kallonsa tace
"A'a Babana, sannu da zuwa" Juyawa yayi ya fice daga parlon ganin Godiya, Momy ta ɗan zaro ido tana
kallon Godiya sai kuma ta mike da sauri ta tafi kusa da kofar ta bude tana leka corridor taga bangaren
Abbansa ya tafi, ita ta dade bata gansa cikin irin wannan yanayin ba ma, ta kulle kofar ta dawo tana kallon
godiya tace "Anya Godiya Malamin nan ba maye bane kuwa, kin ga dama yace Abdul zai zo yau gashi
kuma ya zo din kamar an jefosa" Godiya tayi wani dariya tace "Ke ma dai wallahi sai kace yau Danger ya
taɓa maki aiki da zaki yi mamaki? Yanxu dai sai ki tashi kije ki dora masa girkin da ya fi so da maganin"
Momy tace "Ikon Allah, in dai kana da kudin ka zaka ga aiki da cikawa kawai, yanxu ki dubi yanda ya
shigo mana a firgice kamar mara lafiya" Godiya tace "Ina kuwa lafiya dama an hanasa angwancewa da
amarya, sai kace baki san maza in suka kwallafa rai kan wannan lamari ba" Suka kwashe da dariya gaba
daya har da kyakyatawa, Momy tace "Toh yanxu zan tura cikon aikin nan na karshe, yaushe zaki koma
wajensa mu je tare in masa godiya" Godiya tace "Nan da kwana uku in sha Allah, kin ga bari in tashi in tafi
mai gidana na hanyar dawowa yau" Momy tace "Haka fa kika ce, toh shikenan sai mun yi waya dai kawai"
A haka Momy ta raka Godiya har gun motar ta sannan ta dawo cikin gidan ranta fari ƙal, bangaren Alhaji ta
nufa ta tarar da Abdul kwance a parlor idonsa a lumshe, zaunawa tayi gefensa tana kallonsa cikin kwantar
da murya tace "Babana baka da lafiya ne?" A takaice yace "Hutawa nake yi Momy, i need privacy pls"
Momy tace "Toh shikenan, bari in sa a daura maka favorite din ka, ina Mamata fa?" Shiru yayi yaki ba
Momy amsa, Momy ta mike ta nufi kofa ta fita daga dakin ta kullo kofar, sai a sannan tayi wani murmushi
ta koma bangarenta zata dau maganin da Godiya ta kawo mata wanda zata zuba a cikin girkin abinda Abdul
ya fi so, sai da ta kori mai aikinta can compound sannan ta fara girka masa Pounded yam da Vegetable
soup, cikin miyan ta zazzage duk maganin da kyauta ta kawo har kala uku, wajen karfe bakwai ta gama ta
dau abincin ta kai masa dining table ta ajiye, dama iya cin sa kawai ta girka wato malmala daya kuma ba
babba ba, miyar ma ɗan tsut yanda zai cinye gaba daya, sai bayan isha Abdul ya ci abincin da Momy tayi
masa, ya bar ma mai aiki ta kwashe sannan ya wuce sama zuwa dakinsa, Momy ta fito dakin Meemah
kenan ta bi sa da kallo har ya shiga dakinsa sannan ta bi bayansa, tana shiga dakin tace "Wai lafiya Babana?
Ko dai akwai wani matsalan da kake boye min ne" a takaice yace "Ba komai, zan shiga wanka" Yana fadin
haka ya fara cire kayan jikinsa, Momy tace "To ka ci abincin?" Yace "Na ci" Momy na murmushi tace "You
like it?" Yace "Miyan yayi dadi, but it's little" Tana murmushi tace "To maa sha Allah, amma ai ya isheka
dai" Yace "Ya isa" Tace "Toh je kayi wankan ka nima bari inje in ci abinci" Fita tayi daga dakin ya shiga
bandaki, Momy na zaune parlonta tana cin farfesu dake cike cikin bowl din hannunta Abdul ya shigo,
kallonsa tayi ganin yanda ya shirya sai zuba azababben kamshi yake, tace "Har zaka tafi Babana" Yace "Eh,
sai da safe" Tace "To ko in zuba maka farfesun ka kai ma Mamata" A takaice yace "A'a ni ba gida zan
kwana ba" Momy tayi murmushi tace "To Allah ya tsare Babana" Yace "Ameen" Daga haka ya fita daga
gidan. The next 10 days a gidan Abdul was a living hell for Khaleesat, gaba daya Abdul ya sauya mata a
gidan ya dawo kamar wani monster, dukanta da yace ya dena sai dai bai samu slightest opportunity din yin
hakan ba, kawai ya maida ta punching bag dinsa a gidan barin in ya zo gareta bai samu biyan bukata ba,
kuma bai fasa zuwa mata da bukatar tasa ba amma as usual sai dai kawai ya doketa ya fita bai cimma
burinsa ba, kwata kwata ya dena cin abincin gidan, ya dena kwana sai sanda ya ga dama, duk wani
ingredients din girki ya dena siyowa sai dai tayi ta cin indomie, hatta bottle water ma da ya kare yaki
siyowa, kuma ko Satchet water yaki siya ya ajiye, sai dai ta sha ruwan pampo, gaba daya Khaleesat ta fita
hayyacinta a gidan ta dawo kamar ba Khaleesat ba, ga karyewa da gashinta ya dinga yi sosai saboda
tsananin damuwa, kana ganinta kasan tana cikin jarabawan rayuwa, bata da aiki sai kuka sai kuma addu'a
da sallan dare, gaba daya ta maida duk lamarinta ga Allah, kullum haka take kwana ta tashi da zazzabi
amma ina taga fuskar ce masa bata da lafiya, sai dai tayi ta daurewa a haka, in ma ta gaya masa don ya zagi
iyayenta ba komai bane a wajensa, in zazzaɓin ya rufeta sai dai ta kwanta har sai sanda zata ji dama dama
sannan ta daure ta tashi. Ranan Friday tana dakinta a kwance ko breakfast bata yi ba har kusan karfe sha
biyu da rabi, zuwa yanxu ta gaji da cin indomie da ma tana da dakakken yaji sai ta dinga yin ko shinkafa da
mai da yaji ne amma babu, indomie duk ya fita a kanta bata iya ci ko ta dafa, gashi haka take dafasa babu
yaji balle albasa, bude kofar dakin nata yayi ta mike zaune da sauri tana kallonsa gabanta na faduwa, kamar
zai fasa mata dodon kunne taji yace "Ina Cufflinks din da na bari a parlor shekaranjiya?" Sauka tayi daga
kan gado, ita dai ta gyara parlon ta goge ko ina jiya da yau amma bata ga wani Cufflinks dinsa ba, a hankali
tace "Toh bari in duba a parlon" Wani mugun kallo yake mata hakan yasa ta raɓa tabi ta gefensa ta fita daga
dakin zuciyarta na bugawa ta tafi parlor tana dudduba Cufflinks din, da alama masallaci zai je don yin
sallan juma'a, babu ta yanda za ace iya Cufflinks din da yake tambayarta yake da shi a gidan, amma sbda
neman hanyar da zai musguna mata yake shi yasa zai saka ta gaba ta fito da abinda bata gani ba, kuma
rabonsa da gidan tun shekaranjiyan, tana cikin dube dube a parlon shi kuma yana tsaye fuskarsa a murtuke
alamar he is loosing his patient aka bude kofar parlon, Momy ce ta shigo da Cousin sis din Alhaji Musa,
warce suke kira da Ummu, Yau kwanan Ummu uku a Nigeria daga Dubai inda take aure da yaranta duk a
can, kuma a yau zata koma Dubai shi ne ta sa a kawota ta ga matar Abdul kafin a kai ta airport, duk da
Abdul yaje ya gaisheta san da ta zo, Khaleesat da duk a rude take ta kalli Abdul a hankali tace "Wallahi ban
gansa ba da nake gyaran parlorn jiya da yau, kilan ka sha'afa ko a daki ka bar su ne ka manta" Bata rufe
baki ba ya sauke mata wani gigitattcen mari yana huci ya fixgota yace "Ni zaki gaya ma a daki na bar su?"
Ta dafe kuncinta hawaye cike idonta tana girgiza masa kai, nan da nan fuskarta yayi ja, ko minding uwar sa
da Cousin sis din Babansa da suka shigo parlon bai yi ba, duk suka yi cirko cirko baki bude suna kallon
ikon Allah, cikin tsawa yace "Baza ki fito min da shi ba sai na maki dukan tsiya a nan?" Tana shesshekan
kuka tace "Nace maka ni ban ga wani links din ka ba wallahi...." Bata rufe baki ba ya sake sauke mata wani
wawan marin, Momy da taji ranta yayi fari tass cikin kwantar da murya tace "Subhanallahi, Babana ka bi a
hankali, hakuri ake Babana" Ummu ta jefar da handbag dinta kan kujera ta nufesa cikin bacin rai tace
"Abdallah?? kana hauka ne kake marin mace haka don uban ka?" Momy ta wani hade rai tana kallon
Ummu, Abdul yaki ko kallon Ummu dake masa magana, ya wani haure Khaleesat a mugun fusace har sai
da ta fadi kasa, Wani Mari Ummu ta sauke masa a fuska, cikin fushi tace "Ashe kai jahili ne shashasha ban
sani ba?" Juyowa yayi yana kallon Ummu da mamaki baya ko kiftawa, Momy ta dinga huci tana kallon
Ummu ita ma, nan da nan idanuwanta suka kankance don bacin dai, tunda ta haifi Abdul bata taɓa marinsa
ba haka ma ubansa sai gashi yau an maresa a gabanta, Abdul dake kallon Ummu kamar me counting din
words dinsa yace "Ummu akan wannan jakar yarinyar kika mareni??" Ummu tace "Na mare ka din, zaka
rama ne? Wawa kawai mahaukaci ka saka yarinya karama haka a gaba kana duka? Tarbiyar da aka maka
kenan? In na san abinda zan zo in tarar a gidan ka kenan uban me zai kawo ni?" Abdul da idanuwansa suka
sauya launi ya kalli Khaleesat yace "Ki je... na sake ki" Yana fadin haka ya dau makullin motarsa ya fice
daga parlon kamar zai tashi sama, Khaleesat ta bi sa da kallo babu ko kiftawa kamar bata fahimci abinda
yace ba, Momy ta sauke wani bayanannen ajiyar zuciya tace "To Alhamdulillah, Alhamdulillah,
Alhamdulillah" Sai kuma ta kalli Ummu tace "Ke kuma Muhusina kin ci darajar Musa banda haka da babu
uban da zai hanani rama ma ɗa na marin da kika masa don tunda na haifesa ban taɓa marinsa ba haka ma
ubansa, kuma Abdul yayi min dai dai hukuncin da ya dauka, dama me ake da auren er gidan talakawa er
gidan matsiyata? Ai ba class din mu bace ita, kuma duk bama goyon bayan wannan tsinannen auren, kawai
irin wannan rana muke ta jira gashi Allah ya kawo mu cikin ruwan sanyi, Alhamdulillah Allah na gode
maka, Allah na gode maka, yau zan yi bacci cikin farin ciki da kwanciyar hankali burina ya cika, effort dina
kuma bai tashi a banza ba" Momy na kai wa nan ta nufi kofa tana tafiya gansan gansan farin ciki fal a ranta
mara misaltuwa tana murmushi ta bude kofar parlon, Khaleesat ta bi Momy da kallo with shock ko
kwakkwaran motsi ta kasa tsabar mamaki, maganganun Momy suka dinga yawo a kanta kamar a mafarki,
Ummu ta zauna gefen kujera ta dafe kanta tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Sai a sannan Khaleesat
taji hawaye masu zafi na silalowa fuskarta, ta mike tana tafiya a hankali ta tafi daki ta dauko hijab dinta har
kasa ta fito.....

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login