Showing 21001 words to 24000 words out of 152206 words

Chapter 8 - HALYSAAH by Khlst Hydrr

13 May 2026

51

masu Uniform" Umma tace "Ko dai baki da hankali ne Khaleesah? baki ji
shawaran da Farida ta kawo bane halan?" Aunty Farida ta mayar mata da 100k din tace "Aa gaskiya ban ga
alamar da kan nan ba Umma, ina ga hakoranmu za mu je mu jera mata a gida idan bikin ya tashi...."
Khaleesat bata san sanda tayi dariya ba tace "Akwai fa kudade a account dina wanda Abdul ke bani kuma
suna da yawa za su isa ayi duk abinda za ayi sannan Aunty" It took Khaleesat almost an eternity to
convince her Mother and aunt akan su rike kudin da ta basu, nan kuma bata da wani kudin a zo a gani a
account dinta sai miliyan 10 na Abdul da ya ajiye a account din wanda nashi ne ba nata ba, iya kudin
foodstuff kawai yake tura mata duk karshen wata sai kuma kudin Uber na zuwa makaranta, sai house rent
dinta da yake biya at due time, iya abinda kawai yake mata kenan amma naira biyar dinsa baya bata a
matsayin kyauta, instead sai dai ya siya mata kaya masu tsada, monthly kuma yake mata subscription a
waya, apart from this bai bata kudi da sunan kudin kashewa, a haka dai ta samu tayi convincing Umma da
Aunty Farida suka amshi kudin da ta basu, Aunty Farida na kallon Umma tace "To kinga sai kiyi kaffa
kaffa da wayar nan kar su sace maki tunda sun saba maki haka, kin dai ga ba dan karamin kudi aka siyo
wayar da shi ba" Umma na kallon Khaleesat tace "To shi Malam din me kika siya masa?" Aunty Farida ta
wani kalli yayarta, Khaleesat ma dai kallon Ummanta tayi bata ce komai ba, Aunty Farida ta kyabe baki ta
kauda kai, Umma ta kalli Aunty Farida tace "Wai saboda hakki, naga ta siya min waya shima da sai ta nemi
abinda ta siya masa kwatankwacin wayar, kuma bashi da wayar shi ma wallahi" Aunty Farida na kallon
yayarta da kyau tace "Umma in kinsan zuwa za kiyi ki kyautar da wayar nan da ta siya maki to gwara dai ki
bar mata kayanta, ina ce kwanaki can matansa ya siya ma Atamfa yar gadagalle lkcn bikin Salisu ke ya siya
maki?" Umma tace "Aa ba ruwanta da wannan Farida, ai ubanta ne, kuma don ta siyi abu ta basa ai ba
faduwa tayi ba" Aunty Farida bata sake tanka Umma ba ta fara harhada ma Khaleesat kayayyakin abinci da
ta siyo waje daya, Sai kusan la'asar su Umma suka bar gidan kuma har sannan Baaba Gaje bata dawo ba, a
boye Khaleesat ta ba Siblings dinta 50k wanda ta saka a karamin jakar Islam tace masu in sun je gida su ba
Umma kuma ta ja masu kunni sosai kan daukan sabon wayar da ta siya ma Umma kar su lalata mata.
Washegari da safe Khaleesat ta fito wanka wayarta ya fara ring tana dauka taga mutumin nan ne dai, bayan
ta daga suka gaisa sannan yace "Hajiya nan da karfe tara da rabi wani driver zai kiraki sai kiyi masa
kwatancen inda zai zo ya daukeki ya kai ki airport, don flight dinki zuwa Abuja na karfe sha daya ne, in
kun iso Abuja kuma jirgin da zaki bi zuwa Amurka jirgin karfe biyu saura ne" Khaleesat tace "To ba
damuwa Nagode" Aunty Farida kadai ce ta zo gidan Baaba Gaje yi ma Khaleesat sallama, Khaleesat bata ji
dadin da Umma bata biyo ta ba, duk jikinta yayi sanyi sosai, a haka drivern da zai kai ta airport ya iso,
Baaba Gaje ta dinga sa mata albarkan wayar da ta siya mata da abubuwan da ta siyo ma jikokinta, bayan an
kai akwatin kayanta cikin mota su Aunty Farida da Baaba Gaje suka rakata har bakin motar, bayan
Khaleesat ta shiga motar ta daga masu hannu a sanyaye tana murmushin karfin hali, har cikin ranta bata ji
dadin da bata yi sallama da Ummanta ba, a haka suka kama hanyar airport da drivern da ya zo daukarta,
suna sauka Abuja karfe daya da minti 40 jirgin su ya tashi. The flight to the United state was so comfortable
for Khaleesat in her business class seat, don throughout bacci tayi, karfe hudu saura na asuba jirginsu ya
sauka Maryland, It was soo cold in Maryland gashi bata da sweater a kayanta, bayan ta fito da luggages
dinta tana duba Uber da zai kai ta gida tana rike da wayar kamar ance ta daga kai taga motar da yayi
parking, kallo daya tayi masa sai kuma ta sauke kai kasa, ya karaso har inda take yace "Jirgin ya dade da
sauka ne?" Sai a sannan ta kara kallon Sleepy face dinsa, sai kuma ta girgiza kai tace "Aa" Yace "Ohk let
me drop you home" Daga haka ya koma gun motarsa ta bi bayansa with both of her luggages, ya bude
booth ya amshi daya trolley dinta ya sa a booth, ita ma ta sa dayan, ya zaga ya shiga driver seat, tana jan
kafa ta karasa front seat ta bude motar sannan ta shiga tana kallonsa da gefen ido, jinginar da kansa taga
yayi da kujeran motar idonsa a lumshe, ta kulle motar gently, after few seconds ta sake kallonsa ga
mamakinta sai taga kamar fa bacci yake, kallonsa ta dinga yi, and they seated for almost 3 minutes a haka
ita dai bata tashesa ba kuma bata ce komai ba, Vibration din wayarta ne ya sa ya bude ido, ya wara ido ya
fara kokarin tada motar, bude jakarta tayi to stop the alarm din da ya sa wayarta ke vibrate, bayan ya ja
motar sun bar wajen, still not sounding normal yace "Ya jikin Mama?" Ta sauke idonta tace
"Alhamdulillah, You shouldn't have bothered coming tunda akwai Lyft ko Uber" Without looking at her
yace "The house key is with me, shi yasa na taho, cause i estimated when u are arriving" Bata sake ce masa
komai ba shi ma haka, a haka har suka iso gida yayi parking, ya sake jinginar da kansa da kujeran motar, ita
dai ta bude motar gently ta fita, jin fitarta ya sa ya bude ido, shi ma ya sauka daga motar, Entrance din shiga
gidan ya nufa ta bi bayansa, Pajamas ne jikinsa sai Jacket da ya saka saboda sanyi, yana isa kofar ya kai
hannu aljihu alamar zai ciro makulli, still taga yayi a bakin kofar, ita dai kallonsa kawai take, after some
seconds ya juya yana kallonta, zuwa sannan his eyes are very clear gaba daya baccin ya gudu jin babu
makulli jikinsa, ko bai gaya mata ba ta fahimci baya tare da makullin gidan, ya ɗan sosa kai yace "I think....
I think, i left the key at where i am coming from, i am sorry about that Halysaah" Sauke idonta tayi without
saying anything, ya juya ya nufi motarsa ta bi sa da kallo, sai da ya isa gun motar ya juyo, da sauri ta dauke
kanta daga kallonsa, yace "Mu je in dauko makullin, ba wani nisa zuwa can, kinga it's cold out here baza ki
iya tsayawa cikin sanyi ki jirani in dawo ba" Bata yi musu ba ta koma gun motar don yanzun ma sanyin
take ji sosai, sai da ya shiga sannan ita ma ta shiga, his car was so warm, ya tada motar suka bar garage din,
inda yace mata babu wani nisa taga sunyi tafiyar kusan 15 mins basu kai ba, nan taji gabanta ya fara
faduwa, lkci lkci take ɗan satan kallonsa ta gefen ido, wani unguwa suka shigo wanda ko wani gida da gate
dinsa unlike some houses in US, daga karshe taga yayi parking ba tare da ya kashe motar ba yace "Let me
get the keys" Bude motar yayi ya sauka ta bi sa da kallo taga gate din kusa da su ya bude ya shiga, tsaf take
iya kallon hadadden gidan dake ta cikin gate din don ba irin gate dinmu na gida bane, ita dai sai bin
unguwan take da kallo wanda ko ba a fada maka ba kasan na masu hannu da shuni ne a Amurka din, ba a
wani dau lokaci ba sai gashi ya fito da wani Huge Dog dake biye da shi yana shisshige masa, wani faduwa
gabanta yayi don a duniya tana mugun tsoron kare, ya duka yana patting Dog din yana masa magana at the
same time, wani matashi ne dogo just like him ya fito daga cikin gate din gidan sanye da Pajamas shi ma,
Khaleesat ta dinga kallonsa as if ta taɓa saninsa amma kuma bata san sa from anywhere ba, tana kallonsa
tana gyara mayafin kanta kar ma ya kalli direction dinta su hada ido da shi, gabanta kuwa sai faduwa yake
kamar mara gaskiya, matashin ya jingina da gate crossing his both legs yana kallon Housemate dinta taji
yace "Daga ina kake?" Ƙin basa amsa Housemate din nata yayi instead ya mike yana tura masa ƙaton karen
don karen tsaf zai ce zai bi sa, Calmly matashin yace "Ina za ka?" Housemate dinta ya kallesa yace "You
have any issue with that?" Matashin ya ɗan kalli motarsa calmly yace "Is that a lady in ur Car?" Housemate
dinta yayi kamar bai ji sa ba still pushing the Dog to him, Matashin ya sake kallon motar, Khaleesat tayi
saurin kauda kanta, tabe baki yayi yace "Enjoy" Daga haka ya ja karen suka koma cikin gidan, Khaleesat da
duk taji conversation din nasu taji ranta ya baci, House mate dinta ya dawo cikin motarsa ya kulle without
looking at her yace "Sorry for keeping u waiting Halysaah" Yana fara driving ta hade rai tace "Mene yasa
bazaka gaya masa i am just ur housemate ba da kuma dalilin da yasa ka kawo ni nan din?" Housemate dinta
yace "Never mind, ba wai yana da hankali bane"


✍🏻
07087865788
[5/5, 6:00 PM] khaleesat Haiydar ✍️: ✨✨HALYSAAH✨✨




✍🏻
By _Khaleesat Haiydar_




8.......


Har suka isa gida babu wanda ya sake cewa komai a cikinsu, yana parking a garage ya bude motar ya
sauka, ita ma ta sauka tana satan kallonsa, kofar entrance din parlor taga ya nufa without looking at her,
hakan yasa tana tafiya a hankali ta bi bayansa, ya bude kofar parlon ya juya ya kalleta, ita ta fara shiga
parlorn sannan shi ma ya shiga ya kulle kofar, dakinta ta tafi bayan ta bude kofa ta juya ta kallesa,
kwanciya taga yayi a kan 3 seater ya lumshe ido, ta shiga dakinta kawai ta kulle. Washegari da safe karfe
takwas da 'yan mintuna Khaleesat ta fito daga dakinta, zaune ta gansa da text books a gabansa alamar he is
studying, yana daga kai tayi saurin dauke idonta daga kallonsa, har ta karaso cikin parlon ta tsaya jikin
kujera tana wasa da edge din mayafin jikinta, a hankali tace "Ina kwana" Ya ajiye pen din hannunsa yace
"Good morning Halysaah" Still bata dago kanta ba kuma bata fasa wasa da gefen gyalenta ba, yace "How
was ur trip?" Ta ɗan kyafta ido tace "Alhamdulillah" Yace "Sorry jiya ban tambayeki jikin Mama ba, i was
sleepy hope she is better now?" Sai a sannan ta daga kai ta kallesa, tace "She is fine Alhamdulillah" Yace
"Hope ur mind is now at rest?" Sunkuyar da kanta tayi bata ce komai ba, sai kuma ta ɗan gyada masa kai,
wayarsa ne ya fara ring ya dauka sannan yayi picking ya kai kunne, ta ɗaga kanta tana kallonsa, taga shiru
yayi alamar yana sauraron abinda ake gaya masa a wayar, after few seconds yace "It should be upstairs
then" Daga haka ya katse wayar ya ajiye ya daga kai, da sauri Khaleesat ta dauke kanta daga kallonsa, Yace
"Hope nothing Halysaah?" A hankali tace "Kawai, i want to appreciate you, thank you so much, Allah ya
saka da alkhairi...." Cikin calm voice yace "No, You need not to Halysaah, iya abinda zan yi ma kanwata na
maki ai" Cikin sanyin murya tace "To Nagode Allah ya saka da alkhairi" Ya ɗan yi murmushi yace "To
Ameen, so u can be this calm?" Ta wani kallesa, yace "Makarantar zaki tafi baza ki bari ki huta from ur
long journey ba?" Ta sauke idonta tace "I am having presentation today" Yace "Ohk then, Allah ya bada
sa'a" A hankali tace "Ameen" Ya nuna mata Trolley dinta da ya shigo mata da shi parlon yace "Ga boxes
dinki can" Ta kallesu tace "Thank you" Yace "You are welcome" Daga haka ya ci gaba da abinda yake, Sai
da ta kai su dakinta sannan ta dawo ta nufi kitchen, Tea kawai Khaleesat ta sha da Cookies sannan ta dauko
jakarta zata wuce makarantar, makullin gidan ya mika mata yace "The house key...." Ta tsaya tana kallonsa,
sai kuma tace "Ain't u using it?" Ya daga kafada yace "Will sort my self out" Shiru tayi at first, can kuma ta
nufesa ta amshi makullin tace "Thank you" Yace "You are welcome" Daga haka ta fita daga gidan ta kullo
masa kofar. Khaleesat na tafe tare da Safiyyah dake mata mitar Ya Mustapha yace bata daga kiransa, ita dai
Khaleesat tafiyarta kawai take bata ce komai ba, Safiyyah ta tsaya tace "Ohh ga gantalalliya na maki
magana ko?" Khaleesat ta tsaya tana kallonta tace "To me zan ce Sophie? Ke kanki kinsan ina da wanda
zan aura to menene amfanin in daga wayar Yaya Mustapha? Beside wallahi ko da bani da wanda zan aura
ni bazan kulasa ba, ai ana barin halaq ko don kunya" Da wani expression Safiyyah tace "Ban gane ba, as
per cewar Surayya cousin sis dinki ce ko kuma kawarki ce? Where did u know her from? Meye hadinki da
ita da har za a bar halal don kunya? Can you hear ur self pls? If you are not interested in my cousin brother
ba sai kin ta corner corner ba kina kawo zancen da hankali ma bazai dauka ba, meye hadinki da wata
Surayya da zaki bar halal don kunya?" Khaleesat tace "Ni dai don girman Allah ki ma bar wannan zancen,
Ya Mustapha kuma kiyi ma Allah ki gaya masa i am engage, ni bazan daga kiransa ba" Safiyyah tace
"Wallahi bazan fada ba ai kina da baki ki gaya masa da kanki, ke da wa aka yi engaging da zance masa u
are engage? Ai as far as i am concern ni ban san wannan batun ba, kawai nasan kina da wanda baki da wani
option sai na aurensa, but as time goes on ke kanki zaki san kina da option, za kuma ki ji baza ki iya auren
ba sai dai duk abinda zai faru ya faru" Khaleesat ta taɓe baki tace "Kin ga ni yunwa nake ji zan tafi gida, sai
gobe in mun hadu" Safiyyah bata tanka ta ba ta ci gaba da tafiya ta bar ta tsaye a wajen, Khaleesat ta bi ta
da kallo, to wai ma ta yaya zata daga kiran Ya Mustapha, ita a rayuwarta abinda tasan in an mata bazata ji
dadi ba ko by mistake ne bata yi ma wani, ita Safiyyah in ita ce a shoe din Surayya ya zata ji, wannan ai
son zuciya ne ma kawai, bin bayanta Khaleesat tayi tace "Ni dai tunda ba mu da aji mu je gida pls ki mana
girki i am very hungry and at the same time tired from yesterday's journey" A haka ta samu ta lallaba
Safiyyah dake jin haushinta suka kama hanyar gidanta, suna sauka daga Uber ta nufi apartment dinta tana
kallon Garage taga babu motar Housemate dinta, does this mean a bude ya bar kofar tunda makullin na
hannunta, tana murda kofar taji sa a kulle, to ina ya samu key? ko dai magana yayi aka basa wani makullin,
bude jakarta tayi ta ciro key ta bude kofar suka shiga cikin living room din tare da Safiyyah dake biye da
ita, Safiyyah ta dinga bin parlon da kallo ta lumshe ido tace "Kai amma wannan turaren Housemate din
naki ba dai dadin kamshi ba, the perf is so cool" Khaleesat dai bata ce mata komai ba, ta ajiye jakarta da
mayafi ta zauna saman kujera tana ciro wayarta a jaka, Safiyyah ta zauna ita ma kan kujera tace "To kun
hadu da Abdul din a Nigeria?" Khaleesat tayi shiru cause kawai taji ita ko maganar Abdul ma bata son ana
mata yanzu, ganin yanda Safiyyah ta tsareta da ido, a takaice tace "Eh... me zaki dafa mana pls, wllhi
yunwa nake ji" Safiyyah ta mike tace "Toh bari in je in ga what is available in the kitchen" Daga haka ta
mike ta nufi kitchen, tana shiga bayan few minutes sai ga ta ta fito, tana kallon Khaleesat da mamaki tace
"Kee wai Housemate din naki ne ke maku restocking abubuwa a kitchen haka? Look how ur kitchen is
stocked up with costly food items, where is he getting the money to buy all this from?" Khaleesat tace
"Baza dai kiyi girkin ba kenan in zo inyi?" Safiyyah tayi dariya tace "No wallahi mamaki nake naga
abubuwa masu tsada yake siya, don ni dai nasan kudin da Abdul ke turo maki bazai taɓa siya maki wnn
uban abubuwa dake kitchen din nan ba, anya bazan dawo gidan nan ba kuwa Khaleesat? Kinga wasu
tsadaddun cookies da drinks da na gani, even the table water in this kitchen ba na yara bane wallahi, the
fridge is full to the brim" Khaleesat taki tanka ta tana danna waya, hakan yasa Safiyyah ta juya ta koma
kitchen tana kara jaddada anya bazata dawo gidan ba kuwa, Lafiyayyen girki Safiyyah ke yi a kitchen din
komai baja baja malam, Sallah kawai Khaleesat tayi a daki ta dawo ta kwanta kan 3 seater tana danna
wayarta waiting for the food to be ready, kiran Abdul ne ya shigo wayar hannunta, sosai gabanta ya fadi
lkci daya mood dinta ya canza ta hade rai, ta dinga kallon screen din wayar fuskarta babu fara'a tana jiran
sai ya kusa katsewa kafin tayi picking call din, dai dai nan taji alamar ana bude kofar parlon, ta mike zaune
tana gyara scarf dinta sai ga Housemate dinta ya shigo parlon, sallama yayi ganinta zaune living room din,
ta ajiye wayar hannunta ta fasa picking call din Abdul din ta amsa sallamar House mate din nata, yana cire
takalman kafarsa yace "Good evening" Ta sauke idonta tace "Ina yini" Yace "Alhamdulillah, bakuwa kika
yi?" Double foot wear da ya gani bakin kofar yasa yayi tambayar, tace "Um she is my course mate" Yace
"Good" Daki ya nufa, sai a sannan ta kalli wayarta taga kiran Abdul har ya katse tuntuni, she wasn't
bothered at all kuma bata yi attempting bin kiran nasa ba ta ajiye wayar kawai, mikewa tayi ta wuce
kitchen, tare suka fito kitchen da Safiyyah bayan Safiyyar tayi dishing masu abincin a plate daya, Safiyyah
na bin parlon da kallo tace "Ko dai Housemate din naki ya dawo ne kamshin turaren nake kara ji

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login