Showing 33001 words to 36000 words out of 152206 words

Chapter 12 - HALYSAAH by Khlst Hydrr

13 May 2026

74

yasa ta ɗan saki jiki kadan ta fara cin
abincin duk da ba sosai ba, ta ci iya abinda zata iya ci ta dau drink tana sha a hankali, sai a sannan ya daga
kai ya kalleta after almost finishing his food yace "Ko dai a maki packaging abincin ki ci a gida, naga
kamar kina kunyan ki ci abinci cikin mutane, or should i give u privacy?" Tana kallonsa a hankali tace
"Privacy in an open restaurant? Ni nace ina kunyan in ci abincin?" Ya ɗan bude ido yace "Naga u ate just
the Tacos bayan ga abinci da yawa a gabanki" Ta sauke idonta tace "Nafi son sa ne" Yana goge lips dinsa da
tissue alamar ya koshi yace "Ohk, so now can i talk to you?" Shiru tayi na few seconds, sai kuma ta kallesa
a hankali tace "Ohk" Ya karasa shanye drink dinsa yace "A nan America kika hadu da saurayin naki ko a
Nigeria?" Khaleesat was silent, sai kuma ta sauke idonta tace "Nigeria" Yace "Ohk, but me kike tunanin
yake janyo maku matsala tsakaninku?" Ta girgiza kai tace "Nima ban sani ba" Yace "Saboda ke ya taho nan
daga Nigeria or he have a business here?" Ta gyada masa kai tace "Saboda ni ya zo" ya gyara zama yace
"Kinga yana sonki kenan, sosai ma kuwa yake sonki, he left everything he was doing and came over just to
see you, in na fahimta bai son kiyi sharing apartment da namiji a kasar nan ko?" Ita dai Khaleesat bata ce
komai ba tana wasa da gefen mayafinta, yace "Sure... yana da gaskiyarsa, don ko ni bazan bar budurwata
tayi communal living ba" Khaleesat ta daga kai ta kallesa, Yace "Yanzu dai kiyi kokari ki basa hakuri ku dai
daita kanku, ni kuma i will think of another alternative for peace to reign between u and ur boyfriend,
sannan shawaran da zan baki shine try all possible best ki dinga nuna masa abinda baza ki yi tolerating ba
tun kafin kuyi aure, ya kamata ace akwai mutual understanding tsakanin ku, he look cool though kawai
yana da hot temper ne and i notice insecurity na daya daga cikin matsalarku da shi, but you can definitely
change him gradually Halysaah, so last maganar da zan maki ina ga ba abinda ya shafeni bane, kawai dai
zan tunatar da ke Do's and don't din addininki ta bangaren relationship tsakanin mace da namiji" Khaleesat
dai sauraronsa kawai take without looking at him, kuma taki ce masa komai tana kokarin fahimtar abinda
zancensa na karshe ke nufi, shirun da taji yayi yasa ta daga manyan idanuwanta ta kallesa, at the same time
ta kalli wa enda yake kallo a cikin restaurant din, 3 Guys ne suka shigo restaurant din gaba dayansu yan
Africa, amma daya ne ɗan Nigeria a cikin su, guys din da ba yan Nigeria ba suka daga ma Housemate din
nata hannu alamar girmamawa, and he waved back at them with smile on his face, Khaleesat ta dinga
kallon daya mutumin da ya nufo su don ta ma ganesa, su sauran biyun kuma suka tafi yin abinda ya kawo
su restaurant din, Mutumin na isowa kusa da table dinsu yana kallon Housemate dinta yace "Done with the
power point?" Tuni kamshin turarensa ya cika wajen, Housemate dinta ya daga kai ya kallesa yace "Yau
kuma har da kai za a ci abinci a nan kenan...." Yace "Not at all, i am getting some Steak for legend,
meanwhile ashe kana nan" Housemate dinta yace "Yea, i came with my friend for Dinner" Khaleesat dai
danna wayarta kawai take don mutumin yi yayi kamar bai san da Allah yayi ruwanta a wajen ba, ita ma ko
kallon direction dinsa bata yi ba, Housemate dinta ya nuna masa bill dinsu yace "Get the bill cleared"
juyawa mutumin yayi ya bar wajen yana tafiya irin ta ƙasaita, Khaleesat ta bi sa da kallon gefen ido, he was
wearing a Jogger and a white Polo, ta dai ci gaba da danna wayarta, muryar Housemate dinta taji yace
"That's my gee Halysaah, we share the same name with him...." Khaleesat ta daga kai without interest tace
"Ohk" Yace "Sorry about his attitude, he isn't friendly, but i promise you he is good" Khaleesat tace
"Likewise myself" Murmushi housemate dinta yayi sannan yayi excusing kansa ya mike ya nufi gun wanda
ya kira da gee dinsa, daga inda take zaune taji mutumin na cewa "Kai kuma ina ka samo waccan yarinyar
dake zaune kamar gunki bata iya gaisuwa ba, duk wani harkar raini ka iya ja ma mutane, that was how the
other day da ka kawota karfe ukun dare a mota ta dinga kallon mutane kamar statue da aka dasa a gaban
motar" Definitely yayi maganar ne ta yanda zata ji, Housemate dinta dake kallonsa yace "Ban gane bata iya
gaisuwa ba, ba kai ka sameta a wajen ba, kayi mata magana ne kaga bata amsa maka ba?" Maimakon ya ba
Housemate dinta amsar abinda yace sai taji yace "Na kai Legend gun Veterinary daxu" Taji Housemate
dinta yace "Hope he is better now?" Mutumin yace "Let me get the bill cleared mu tafi gidan Mike
yanxu...." Housemate dinta yace "No kayi tafiyarka zan yi dropping frnd dina first" Taji mutumin yace
"Like seriously kai ko wani irresponsible being sae kace friend dinka, why are you stooping your self soo
low Jay" Taji Housemate dinta yace "C'mon Ajay, come off it, this is so harsh..." Mutumin da ya kira da
Ajay ya tafi ya bar sa gun a tsaye, Dawowa Housemate din nata yayi inda take, tuni ta mike tana gyara
gyalenta without looking at him tace "Thanks for the dinner, kawata na kirana zan tafi gida" Housemate
dinta yace "Ke kika kawo kanki da za ki koma ke kadai?" Taki kallonsa tace "Ae naga ur responsible frnds
are here, so let me get going" Yace "Halysaah" ta daga kai ta kallesa, yace "Jira ni inyi clearing bill dinmu
in yi dropping dinki gida" Yana fadin haka daya daga masu aiki a restaurant din ya nufosa da ladabi ya
sanar masa anyi clearing bill din su, ya bi A-jay da ya fita daga Restaurant din da kallo, wa enda suka shigo
tare na biye da shi a baya. Khaleesat bata yarda ta hada ido da Housemate dinta ba har suka fito daga
Restaurant din zuwa inda yayi parking motarsa, sai da ya shiga motar sannan ita ma ta shiga ta zauna tana
danna wayarta, bai tada motar ba ya kalleta, speaking calmly yace "Hope you are not offended Halysaah?"
Without looking at him tace "Offended at what?" Yace "I don't really know" Ta kada baki tace "Ai ni ban yi
kama da someone that isn't responsible ba balle in zama Offended at what a random stranger spew out, out
of his ignorance, shi dai da bashi da manner shi ne babban irresponsible being, ai da ya fada a gabana yaji
abinda zan gaya masa" Housemate dinta ya bude baki yana kallonta da mamaki looking completely
speechless, bai yi tunanin taji abinda Ajay din ya fada ba, bai kuma yi tunanin tana ma da baki haka ba,
after few seconds yayi kasa da murya yace "Pls kiyi hakuri Halysaah, bana son wannan yasa ranki ya bace,
i purposely brought you out to cheer you up and make you lively don naga kamar kina cikin damuwa,
amma ba don a kara bata maki rai ba, plss ignore Ajay's attitude, wani lkcn yana da problem i think today is
one of those days" Khaleesat bata sake cewa komai ba but she is trying hard not to cry, ya ci sa'a ba yana
tsaye gabanta ya fadi haka ba da tsaff zata mayar masa da baƙar magana dai dai da abinda ya gaya mata a
wajen, Housemate dinta ya tada mota suka bar Restaurant din, hakuri ya dinga bata kamar shi ne yayi mata
laifi har suka isa gida, direct dakinta kawai ta wuce, after like 40 mins ta fito wanka tana duba sleeping
dress din da zata sa taji yayi knocking kofar dakinta, hijab din da tayi sallah ta dauka da sauri ta saka, bai
bude kofar dakin ba har sai da taje ta bude tana kallonsa, yace "Sae da safe Halysaah, pls ki kwantar da
hankalinki and get some rest, gobe kuma ki je school" ta sauke idonta bata ce komai ba, taji yace "Take
care" Sai da ya juya ya bar wajen sannan ta daga kai ta bi sa da kallo cikin sanyin murya tace "Thank you
so much, for..." Sai kuma tayi shiru, ya juya yace "For?" Ta langwabar da kai tace "The Dinner" Ya ɗan
buda ido yace "My pleasure Halysaah" A hankali tace "But.... i don't... know, ur name" Yace "Oh really,
amma ranan da na fara zuwa gidan nan ai nayi introducing kaina sai dai in kin manta, I am Ahmad Jawwad
Yusuf, my frnds call me Jayy" Kallonsa Khaleesat ta dinga yi without blinking, yace "Are you okay with
that?" Ta sauke idonta tace "Alright, i really appreciate you" Ya sakar mata murmushi yace "See yah
tomorrow" daga haka ya bar wajen ta bi sa da ido har ya fita daga gidan gaba daya sannan ta juya a hankali
ta koma dakinta ta kulle kofar.

*Make ur payment before the end of free pages, kar a ji shiru*


✍🏻
07087865788
[5/9, 4:49 PM] khaleesat Haiydar ✍️: ✨✨HALYSAAH✨✨




✍🏻
By _Khaleesat Haiydar_




12.....

Washegari da safe Khaleesat ta gama duk abinda zata yi a gida ta shirya ta tafi makaranta, tana zaune
favourite spot dinsu ita da Safiyyah bayan sun fito daga aji, Safiyyah na facing dinta tace "Tsakaninki da
Allah ina kika je jiya da yamma da naje gidan baki nan? Ni dai nasan babu inda kike zuwa a garin nan, ba
kuma frnds gare ki ba, So where did u go?" Khaleesat da idonta ke kan jotting da tayi a aji tace "To ke
meye na zuwa da yamma likis, i was expecting you around 5pm not 7pm" Safiyyah ta amshi takardan
hannunta tace "Ina maki tambaya kina min tambaya, ko akwai abinda kika fara boye min ne Khaleesat?"
Tagumi tayi tana kallon Khaleesat din da tuhuma, sai a sannan Khaleesat ta daga kai ta kalleta, dariya ta
bata amma bata yi ba, kamar dai bazata ce mata komai ba sai kuma ta bude baki tace "Mun fita zuwa
restaurant ne da Housemate dina" Safiyyah ta buda baki tana kallonta with surprise, can tace "Waw, really?
Housemate dinki fa kika ce?" Sai kuma tayi dariya tana gyara zama idanuwanta kamar za su fito tace
"Anya Khalee babu magana a kasa kuwa? Restaurant fa kika ce? How did he convince you har kika bi sa
zuwa restaurant?" Khaleesat ta tabe baki tace "Toh meye kuma a kasa? Daga dai ya kai ni restaurant mu ci
abinci? Kinsan yaushe rabon da inci abincin kirki a gidan?" Khaleesat ta sauke idonta a hankali tace "He
notice i haven't been eating shi ne yasa har ya kai ni restaurant" Safiyyah ta sauke ajiyar zuciya tace "Ai
kece da dora ma kanki abinda Allah bai dora maki ba kawata, akan Abdul din da naga yayi updating status
da jersey jiya alamar har ya koma Nigeria ya ci gaba da harkokin gabansa ke kina nan kina neman kashe
kanki, wallahi in zaki ajiye lamarin gayen nan a gefe da zai fi maki alkhairi a rayuwarki, very very heartless
guy with no conscience, dubi tsabar zuciyarsa ta dutse ne ya gwammace ya kara siyan ticket yayi juyawarsa
ya koma Nigeria, Allah ma yasa yayi maki ya jiki zuwan da yayi" Khaleesat dai tayi shiru tana kallon
Safiyyah, Safiyyah ta daga kafada tace "Ga dai Housemate din nan naki duka duka yaushe har ma ku ka san
juna? Amma ya gane kina cikin damuwa har da kai ki restaurant for dinner, to this is how a caring and
understanding Boyfriend and a Gentleman should be" Khaleesat ta sauke ajiyar zuciya a hankali tace "Ni
babban damuwata kar ya sake dawowa kasar ban sani ba Sophie, ce masa nayi Housemate dina frnd din
Nancy ne fa, kinsan bai san Nancy bata gidan ba ai har yanzu, to kar ya sake dawowa unexpectedly ya
gansa" Safiyyah tace "Abinda zai faru kawai kiransa zaki yi ta yi har sanda ya ga daman daga kiranki, ki
basa hakuri ki samu ku shirya, in har ku ka shirya duk wani movement dinsa zaki dinga sani, yanzun ma ai
don baku communicating ne all this while shi yasa kawai ya taho kamar an jefosa, banda haka ai duk sanda
zai zo yana gaya maki" Khaleesat tace "Haka ne, amma kin san irin zuciyarsa wallahi zan iya kiransa sau
goma ma bazai daga ba, ko na masa magana ta WhatsApp bazai yi reply ba" a sanyaye ta kare maganar,
Safiyya tace "Bari in kirasa ta wayana yana picking zan ce ya kirani, daga nan in ya kira sai in baki wayar
ku yi settling dispute din karyan ku" Khaleesat tayi shiru bata ce komai ba, amma tasan hakan kadai shi ne
way out, Safiyyah ta ciro wayarta ta fara kiran Abdul, har ya katse bai daga ba, ta sake kiransa sai gashi ya
daga, sallama tayi masa ta gaishesa tace "Pls in ba damuwa ka kirani" Katse kiran yayi sai gashi ya kira tayi
picking sannan ta mika ma Khaleesat wayar, Khaleesat ta amshi wayar gabanta na faduwa ta kai kunne,
Safiyyah ta tashi ta bar ta a wajen ta koma wani waje ta zauna, a hankali Khaleesat tace "Don Allah kayi
hakuri ka saurareni..." Shiru yayi da yaji muryarta, nan da nan hawaye ya cika idonta muryarta na rawa tace
"Pls kayi hakuri da abinda ya faru, i promise you hakan bazai sake faruwa ba" Yace "Dama akwai abinda ya
faru ne?" Tayi shiru bata ce komai ba, yace "I am asking you, akwai abinda ya faru ne dama?" Ta sunkuyar
da kanta tace "Don Allah kayi hakuri, i am truly sorry plss" Yace "Look i am super busy now, idan kin
shirya gaya min abinda ya faru kike ban hakuri sai ki kirani ta layin ki anjima" Cikin sanyin murya tace
"Toh Nagode" Katse wayar yayi, ta juya tana kallon Safiyyah, Safiyyah ta kyabe baki ta dawo kusa da ita ta
zauna tace "Ya ku ka yi da shi?" Khaleesat ta ja tsaki tana tattara reading material dinta tace "An gaya masa
banda ina tsoron kar ya dawo without notice ni zan sake magana da shi ta waya ne" Safiyyah ta bude baki
tana kallon Khaleesat tana tunanin yaushe bakinta ya fara budewa haka akan Abdul ne wai, Dariya Safiyya
tayi tace "Shi Abdul din naki Khalee?" Khaleesat ta ki bata amsa, har ranta ita fa yanzu tana jin bazata iya
ci gaba da tolerating abubuwan Abdul ba, ita kanta bata san daga inda wannan liver din yake zuwa mata ba,
sai dai duk abinda zai faru ya faru but she is not tolerating anymore. Wajen karfe biyu ta koma gida, bayan
tayi wanka tayi sallah ta sauya kayanta ta kwanta, sai bayan da tayi la'asar ta shiga kitchen ta jingina da
cabinet tana tunanin abinda zata girka, tuwo taji take son ci, kawai daga karshe tayi deciding tayi tuwon
since tana da duk ingredients din girka tuwon, kan kace me ta gama girka tuwo da miyar kuka with enough
obstacles a ciki, ta gama goge gogen kitchen din sannan ta fito parlor wajen karfe biyar, dai dai shigowar
Housemate dinta gidan, ita dai tana tsaye kusa da kitchen, ya juya ya kalleta bayan ya kulle kofar parlon
yace "Good evening Halysaah" Tace "Good evening" Yace "What are you cooking with such a nice Aroma"
Tace "Tuwo ne" Ya karaso cikin parlon yace "Really, it's been long na ci tuwo fa" Tana kallonsa tace "In
kawo maka?" Ya dan buda ido yace "Ok thank you" Juyawa tayi ta koma kitchen din, ya zauna saman
kujera hoping ba da yawa zata saka masa ba, ba a dau lokaci ba sai ga ta ta dawo parlon da plate dauke da
tuwo with a diff bowl of soup, tun da ta duka ta ajiye abincin yake kallon bowl din miyan babu ko kiftawa,
can dai ya daga kai ya kalleta yace "Wani miya ne wannan Halysaah?" Ta koma gefe tace "Miyar kuka ce"
Lkci daya yayi yaƙe yana shafa kansa yace "Wow, but bana cin irin miyan, i thought vegetable soup ne,
baki yi stew ba?" Ta wani kallesa, a takaice tace "Babu, kuma kayi tasting miyan ne kafin kace baka cin irin
sa?" Ya jingina da kujera ya sauke ajiyar zuciya yace "Na ma ci abinci few minutes ago fa" Dukawa tayi ta
dau bowl din ta mika masa miyan tace "Taste it first before concluding" Ya dan kalleta yana murmushin
dole yace "Ok, where is the spoon?" Tace "Shi ba a cin sa da cokali ai, da hannu zaka sha" Yayi shiru sai
kuma yace "Then bari in wanke hannu" Yana fadin haka ya mike, ta koma gefe don basa hanya sannan ta bi
sa da kallo har ya tafi bandakin dake parlorn ya wanke hannu sai gashi ya dawo, bayan ya zauna ta mika
masa miyan tana kallonsa, shi dai bai yarda ya hada ido da ita ba, tun da ya kai finger ya lasa miyan ya kai
baki ya kasa dago kai, ita dai kallonsa kawai take bata ko kiftawa, can dai yana murmushi da kyar ya dago
yace "It's sooo nice amma na ci abinci wallahi Halysaah" Duk da dariyar da ya bata ta dake tace "To ai
tunda ka sa na zuba sai ka ci ko kadan ne cause i am not throwing it away" Bata jira cewarsa ba ta juye
masa miyan a kan tuwon dake plate ta dau plate din ta mika masa tana kallonsa, he was totally speechless
and confuse at the same time, tana kallonsa da kyau tace "Karba" Ya kai hannu a hankali ya amsa plate din
tuwon, in ya debi tuwon sai ya dangwala miyar kamar yana tsoronsa sannan ya kai baki, sosai ya bata
dariya amma fa bata yi ba, instead sai murmushi take, sau uku yana diban tuwon yana ci kuma har sannan
yaki yarda su hada ido da ita, kana ganinsa kasan da kyar yake cin abincin, his facial expression says it all,
wayarsa ne ya fara vibrate, ya ajiye tuwon da sauri ya fiddo wayar yana kallon screen, sai kuma ya kalleta
yace "This is an urgent call Halysaah bari in shiga daki in daga" Kasa basa amsa tayi don kar ma tayi
dariyar da take dannewa, ya mike ya nufi dakinsa da sauri don ko jiran jin abinda zata ce bai yi ba, tana ji
ya sa ma kofar dakin makulli bayan ya shiga, sai a sannan ta zauna gefen kujera ta rike kanta tana dariya,
after some minutes ta mike ta dau plate din tuwon still smiling ta wuce dakinta. Khaleesat na Voice call ta
WhatsApp da Ummanta wajen karfe tara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login