Showing 87001 words to 90000 words out of 152206 words

Chapter 30 - HALYSAAH by Khlst Hydrr

13 May 2026

115

talaka da ni Awdul yasa a daureni wa zai cece ni, sai ma Kinga
kallon da yake min jiya kamar bai yarda da ni ba" Khaleesat ta dago da kyar tana kallon Baaba Gaje
hawaye na sauka idonta, Baaba Gaje dai zai zazzare ido take tace "Ni ban ma yarda bai sa CID unguwar
nan su kula da shige da fice na ba, yanxu hka sai da na zaga kamar zan je Yan kaba sannan na taho gidan
nan" Cikin sanyin murya Khaleesat tace "Don Allah Baaba Gaje ki min alfarman dauko min jakana a can
gidanmu" Baaba Gaje ta gwalo ido tace "Wani jakar?" Khaleesat tace "Karamin jakata, akwai wayata a ciki
zanyi amfani da shi" Baaba Gaje tace "Um um Khaleesat, ta yaya zan dauko jaka ana gani na da rana
tsaka?" Khaleesat ta girgiza mata kai tace "Karamin jaka ne bai da girma, ko a gyalenki zaki iya boyewa
don girman Allah ki rufa min asiri ki taimakeni Baba Gaje ki dauko min, har da kudi cikin jakan, zaki ga
jakar kusa da akwatina a gefen katifar Umman mu" Maman Fu'ad dai sai baza ido take taji Khaleesat zata
bar gidanta amma shiru bata ji ba, can dai tace "To ke ina kika nufa daga gidan nan yanzu?" Khaleesat na
share hawayenta a hankali tace "Idan ta dauko min jakar zan san inda zan je in sha Allah" Maman Fu'ad ta
sauke boyayyen ajiyar zuciya, faridan ma bazata kira ba kar daga karshe a gane ita ta ajiye Khaleesat a
gidanta ta shiga uku, Da kyar Baba Gaje ta yarda zuwa Mariri dauko jakan don duk a tsorace take, shi ma
sai da Maman Fu'ad ta saka baki tunda taji ance in dai aka dauko jaka to za a bar gidanta, shi sa tayi ta
lallaba Gaje taje Mariri dauko jakar, bayan kusan awa daya sai ga Gaje da jakar ta kudundunosa a gyalenta,
Khaleesat ta amsa jakar ta bude ta ciro wayar Jay dake ciki, ta ga dollars din da ya bata suna ciki har
sannan, Call log ta shiga sai kuma ta kalli Maman Fu'ad tace "Don Allah ki ara min wayarki bani da Sim
card a nawa" Maman Fu'ad tace "Ai ko babu kati, tunda ga wayar Gaje bari in bada dari biyu a siyo sai ki
saka a nata wayar ki kira" Nan duk dubara Maman Fu'ad tayi kar a ga Khaleesat tayi kira da wayarta idan
bincike yayi bincike, Gaje ta mika ma Khaleesat wayarta ta fita ta amso mata katin dari biyun da Maman
Fu'ad ta dauko ta bada, Khaleesat na saka katin ta fara dialing number Jay, ta kira yafi sau biyar sai dai
kiran ya dawo mata alamar bai je ba, bata hakura ba still tayi ta kira baya shiga bata san ko katin ne yayi
kadan ba kuma Number sa na Nigeria yake using a can din ma, wasu sabbin hawayen suka fara sauka
idonta ta sake shiga call log din wayar tana scrolling slowly, number AJ ta gani shi ma Nigeria Line dinsa,
ta ɗan yi jim tana kallon number, sai kuma tayi dialing tana share hawayen dake zuba idonta, ringing ya
fara yi har ya katse bai daga ba, ta sake kiransa, sai da ya kusa katsewa sannan yayi picking, muryarta na
rawa tace "Good Afternoon" Shiru yayi, kafin yace "Wacece?" Ta sauke idonta tace "Ni ce" Yace "Ke wa?"
Da kyar tace "Plss i want to speak to you" Kawai ta fashe da kuka uncontrollably, shiru yayi for almost 15
seconds, can yace "What happened?" Tana kuka tace "I need to speak to you pls" Ya kara yin wani shirun,
can yace "Where are you?" Tace "Hotoro" He still kept quiet for some seconds kafin yace "Address" Katse
wayar Khaleesat tayi ta tambayi Maman Fu'ad address din unguwan, Maman Fu'ad ta gaya mata sannan ta
tura masa ta message, Gaje dake zaune kan kujera tace "Wanene wannan din da kika kira?" Ita dai
Khaleesat tayi shiru wasu hawayen na taruwa idonta, Baba Gaje tace "Gashi idon naki sai kara ja yake yi,
wallahi makantar da ke kawai yayi niyyar yi matsiyacin nan" Bayan kusan 35 mins wayar Gaje ya fara
ring, Gaje ta mika ma Khaleesat da sauri tace "Ko wanda kika kira ne?" Khaleesat ta amsa tana kallon
wayar taga AJ ne ke kira, dagawa tayi yace "I am outside" Khaleesat ta ajiye wayar sannan ta kalli Maman
Fu'ad tace "Aunty don Allah kina da Nikab?" Maman Fu'ad tace "Yaushe rabona da Nikab, bani da shi
yanzu kam" Khaleesat ta mike tana rike da handbag dinta da wayar Jay ta fita daga gidan, not far away
from the house yayi parking, yana jingine jikin motar ya rungume hannunsa looking at a different direction,
tana tafiya a hankali ta nufesa tana kallonsa, tana isowa kusa da shi ya juya jin Footstep, ya gyara
tsayuwarsa ya dinga kallon idonta babu ko kiftawa, she tried her best na ganin bata fashe da kukan da ya
taho mata ba amma ta kasa daurewa ta hade kanta da jikin motar ta fara kuka har da shessheka.
[5/26, 9:21 PM] khaleesat Haiydar ✍️: Ajay bai ce mata komai ba sai da tayi kukan me isarta don kanta tayi
shiru, tana share idonta ta daga kai ta kallesa taga kallonta yake har sannan, Calmly yace "He did all this to
you?" Kai ta gyada masa wasu hawayen na taruwa idonta, yayi shiru for a while kamar me nazari, sai kuma
yace "Ɗan kano ne?" Nan ma ta gyada masa kai, yace "A ina yake a kano?" Muryarta na rawa tace "I don't
really know" Zai yi magana Baba Gaje ta leko kofar gidan kamar munafuka tana zazzare ido, Ajay ya ɗan
sauke kansa ya gaisheta bayan sun hada ido da ita, fitowa tayi da sauri tana kalle kallen Unguwan tace
"Lafiya lau ɗan nan, wallahi yarinyar nan tana cikin mummunan masifa, bata da kowa sai Allah, ta dawo
daga turai ta tarar an daura mata aure da lafcecen yaron nan ɗan iska, dama kuma duk mun san ɗan iska ne
muke kauda kai tunda bamu da yanda za mu yi, ashe bai ma yi shawara da ita ba kansa tsaye ya taho ya
samu iyayen da ya raina suka daura aure shekaranjiya, to tunda tace bata son auren in dai ba tsinannen
mutumi ba ai sai ya kyaleta ga mata kaca kaca a duniya, wani mugun kuduri ne a ransa haka da yasa aka
daura auren a gaggauce ko shiri babu? dubi fa abinda ya mata a fuska daga ya dannata a mota taki bin sa,
yanxu haka duk ya baza CID a unguwan nan ana nemanta, sai kaga tijaran da yaje ya ma iyayen nata jiya
da daddare, shi sa ka gan mu duk a tsorace" Tun da ta fara magana Ajay ke kallonta ko kiftawa baya yi,
mamaki ne sosai kwance a fuskarsa, can ya kalli Khaleesat dake kuka kamar Baaba Gaje na dada tunzurata,
ya sake kallon Gaje yace "Aure kuma Mama?" Gaje tace "Wallahi da gantalallun igiyoyinsa har uku a kanta
yanxu haka, tun jiya ta gudo nan bayan ta samu ta tsere da kyar daga hannunsa" Gaje ta fashe da kuka tana
matsar kwalla da gyalenta tace "Wallahi bata da kowa sai Allah, iyayen basu da bakin magana, basu da ta
cewa, ni kuma ba kowa bace makociyarsu ce mun yi zaman Mariri tare kuma ni talaka ce, ni ko taimaka
mata ne kayi ka kai ta wajen masu kare hakkin ɗan Adam ta kai masu kukanta su kwato mata hakkinta da
ake neman tauyewa" Har sannan Ajay ya kasa cewa komai, can ya bude gaban motarsa yana kallon
Khaleesat, Baaba Gaje ta fara tura ta ciki tace "Maza shiga ku je ya kai ki ofishinsu, in ma rike ki za su yi
su rikeki ki zauna har sai sun bi maki hakkin ki, amma kar ki ce nasan komai, kar ma ki saka ni a maganar"
Khaleesat dai kuka kawai take ta shiga motar, Baba Gaje ta amshi wayarta dake hannunta ta kulle motar
gbamm tace "Maza ku je" Ajay dai ya zaga ya bude driver seat ya shiga, Da sauri Baaba Gaje ta koma gate
din Maman Fu'ad kamar ba daga kusa da motar ta taho ba, ta makale tana kallonsu har suka fita daga layin,
driving kawai AJ yake idonsa a kan titi, gaba daya he look speechlesss, tunda ya kalleta sau daya bai sake
kallonta ba, ita dai Khaleesat ta rufe fuskarta da Hijab dinta saboda hasken rana dake damun idonta kuma
tana tsoron kar ace su hadu da Abdul dan motar babu Tint, har sannan bata daina kukan tashin hankalin da
take ba, after driving for 20 mins AJ ya kalli wayarsa dake vibrate, Number Jay ne ke kiransa, hakan ya sa
ya rage tafiyar da yake ya gangara gefen titi yayi parking sannan ya dau wayar yayi picking ya kai kunne a
hankali yace "Jay" Khaleesat ta zame hijab dinta daga fuska jin sunan da ya kira ta juya ta kallesa, Calmly
taji yace "I am cool" tambayarsa Jay yayi ko ya bar Kano, AJ yace "Am still around, when are you leaving
Maryland?" After few seconds AJ yace "Alright, we will talk later" Daga haka ya katse wayar ya ajiye ya
jinginar da kansa jikin kujerar motar ya kafe titi da ido for almost 2 mins, can ya sake daukar wayarsa don
duba available flight to Abuja ranan, yaga jirgin karfe uku kuma saura just few seats, National ID card dinta
da passport dake motarsa tun ranan da suka dawo US da drivern su na Lagos ya amsa a wajenta don mata
booking ticket to kano, ticket ya siya mata immediately na zuwa Abuja sannan ya ajiye wayar, Aunty na
nan gidansu na kano sun zo biki shi sa ma bazai fara kai ta can gidan ba, juyawa Khaleesat tayi da kyar ta
kallesa tana dafe kanta pleadingly tace "Kanwar Ummata tana Lagos, don girman Allah ka taimakeni i want
to go to her plss" Shi dai kallonta kawai yake, Calmly yace "Where in Lagos?" Tace "Zan kira in
tambayeta, amma bani da numberta ne" Ya ga alamar gaba daya she is confuse and in fear, yace "Ta yaya
zaki kirata baki da numberta?" Wayarsa ta dauka da sauri ta shiga call logs dinsa tana duba number Baaba
Gaje, dialing tayi yana fara ring Baaba Gaje ta daga, da sauri Khaleesat tace "Baaba Gaje don Allah number
Aunty Farida za a duba a wayarki sai a turo ta wannan layin" Baba Gaje tace "Har kun je wajen kare hakkin
ɗan Adam din?" Khaleesat tace "Ki dai turo min don Allah yanxu Baaba" Baaba Gaje tace "Toh bari in je
makota kin san ban san kan wayar ba ai" Khaleesat ta gyada kai da sauri tace "To ina jira" Katse wayar tayi
ta jinginar da kanta jikin kujera tana sauke numfashi, wani dishi dishi take gani tsabar kuka, Shi dai Ajay
idonsa na kan titi alamar dai kansa ya gama kullewa, ya kalli agogon wrist dinsa yaga karfe biyu ya gota,
driving motar ya ci gaba da yi da tunani iri iri a ransa ya nufi wani eatry ya sauka ya shiga ciki, Khaleesat
ta dinga bin haraban wajen da kallo sai kuma ta rufe fuskarta da Hijab dinta da sauri zuciyarta na bugawa,
incident din jiya ne kawai ke dawo mata a kai as if she is hallucinating, sai taga kamar yanzu incident din
ke faruwa yanda Abdul yayi parking ya fita daga mota ya shiga eatry, kan kace me ko ina na jikinta ya fara
rawa taji kamar numfashinta zai dauke, ba a dau lokaci ba Ajay ya fito daga gidan cin abincin da leda a
hannunsa, yana shiga motar ya ajiye ledan da sauri yana kallonta yace "Me ya faru??" Ta dago kanta
hawaye caba caba a fuskarta, sai kuma ta kamo hannunsa gam tace "I just want to leave here plss, don
Allah mu bar nan" Gaba daya ta dawo kamar warce ta zauce, ya fara bin area din da kallo tunaninsa ko
Abdul din ta gani, can ya sake kallonta bayan ya zauna cikin motar, cikin nutsuwa yace "Look, stay calm....
You are safe" Ya gyara mata kujeran motar a hankali ta yanda zata ɗan kwanta yana kallonta, sai da ya jira
for almost 10 mins yaga ta ɗan nutsu tana sauke numfashi a hankali, lkci lkci yake kallon agogonsa saboda
flight din da yayi booking, after a while ya ɗan duba fuskarta yaga kamar ta fara bacci, tada motar yayi ya
bar wajen, still sai da ya kara tsayawa a pharmacy ya siya mata magunguna, ko kashe motar bai yi ba don
kar ta ma san yayi parking, har yaje ya dawo kuma bacci take, ya ja motar ya dau hanyar airport hoping
jirgin bazai tashi kafin su isa ba, suna isa airport din bayan yayi parking yaga saura minti sha biyar kawai
jirgin ya tashi kamar yanda suka sa a ticket, tapping din kujeran motar yayi gently don har lkcn bacci
Khaleesat take, a tsorace ta farka kamar yanda tayi daxu a eatry tana ganinsa kuma tayi shiru tana sauke
ajiyar zuciya, ya bude ledan abincin da ya siya ya ciro mata takeaway din ya bata yace "Take a little before
ur flight..." Ba musu ta amshi abincin tana kallonsa a hankali tace "Lagos din zan je?" Yace "In kin je zaki
gani" Sai da ya hade mata rai sannan ta ci abincin cokali uku da kyar tana hadiyewa kamar magani, ya bude
drugs dinta ya bata ta amsa ta sha da ruwan goran hannunta, without looking at her ya mika mata wayarsa
yace "Saka min number mutumin nan" Zaro ido tayi tana kallonsa, yace "Ko bakya ji na ne?" Kamar zata yi
kuka tace "Kiransa zaka yi?" Yace "Amsa ki sa min number sa nace" Hannunta na rawa ta amshi wayar ta
saka masa lambar Abdul don tana da shi a kanta, ya amshi wayar yana kallon number sannan ya ajiye
wayar yace "Dama an mashi alkawarin aurenki ne?" Ta sunkuyar da kanta cikin sanyin murya tace "Um,
tun shekara hudu da suka wuce" Shiru Ajay yayi yana kallonta, but because of how cautious he is with time
kar tayi missing flight dinta kawai ya ciro Eye drop din da ya siya mata ya mika mata ta diga a idonta, tsoro
ya sa ta kasa digawa don bata san wani kalan azaba zata ji ba, daga karshe ya fixge eye drop din babu yabo
babu fallasa ya diga mata a cikin idon, tuni ya sauka daga motar yana jiran in ta gama kururuwan da take ta
sauko, daga karshe ta sauko daga cikin motar tana rufe idon da Hijab dinta, dayan wayarsa ya mika mata
wanda ticket dinta ke ciki, daga ita sai handbag din ta da wayarsa ta nufi cikin airport din tana waige waige
kamar iska zai kadeta ta fadi, kana ganinta kasan ba dai dai ta ke ba, she is traumatized and stressed, tsoron
Abdul kuma ya gama shigarta sosai, shi dai yana tsaye jikin motarsa yana kallonta har ya ga shigarta cikin
airport din, komawa cikin motarsa yayi yana duba full name din Abdul ta true caller, wani number yayi
dialing yana fara ring aka daga yace "Zan turo maka wata number yanxu, ina son kasa a bincika min
location dinsa a cikin garin kano, i will be waiting for feedback" Bayan ya katse wayar ya ajiye ya jinginar
da kansa da kujeran motar, yana nan zaune har bayan 20 mins just to be sure bata yi missing flight dinta ba
kafin ya bar airport din, Khaleesat ta dinga bin cikin jirgin da kallo kamar idanuwanta za su fito jin anyi
announcing za su tashi zuwa garin Abuja, Abuja kuma? Ita wa ta sani a Abuja? Hawaye ne ya cika idonta ta
dinga waige waigen cikin jirgin, me yasa ya mata booking ticket din Abuja.
[5/28, 8:42 PM] khaleesat Haiydar ✍️: Khaleesat na zaune hall din da jama'a ke jiran Luggages dinsu a
Arrival, duk da bata da kayan da zata jira amma rashin sanin inda ta nufa yasa ta zauna wajen tana bin
kowa da kallo, tun 15 mins ago jirginsu ya sauka Abuja, daurewa kawai take don wani bacci take ji tare da
gajiya, vibration taji a jakarta dake cinyarta alamar ana kiran waya, a hankali ta bude jakar ta ciro wayar da
AJ ya bata tana kallon screen din, har ya katse bata daga ba don number kawai ta gani ba ayi saving ba bata
san ko ta daga ba ko kar ta daga, kiran wayar da ake ta yi continuously ne yasa tayi picking tayi shiru tana
sauraron me magana taji namiji ne, ta amsa sallaman da yayi mata, sannan yayi introducing kansa ya sanar
mata shi ne ya zo daukanta Airport, a hankali Khaleesat tace "Ohk" Mikewa tayi ta fita daga Arrival din
tana kalle kallen inda yace mata yake a Airport din, sai ga shi ya nufota bayan ya gane ita ya zo dauka,
gaisheta yayi da ladabi yace "Babu kaya ko Hajiya?" Khaleesat ta gyada masa kai kawai, yace "Bismillah,
Motar na can nayi parking" Tana biye da shi suka isa inda motar yake, ya bude mata back seat ta shiga ya
kulle sannan ya zaga ya shiga driver seat, Ita dai Khaleesat ji tayi kawai yana sanar mata sun iso, bata san
for how long suka yi tafiyar ba don bacci ne ya dauketa throughout the journey, gyara zama tayi tana kalle
kallen compound din gidan da suke ciki, ta kalli Drivern da ya bude mata back seat, ta sauko a hankali tace
"Nagode" Gida ne babba irin na zamani, tana biye da shi ya kai ta har zuwa Entrance din shiga babban
parlon gidan ya danna bell, ba a dau lokaci ba aka bude kofar wata budurwa ce warce bazata wuce ta ba ta
gani tsaye, da ladabi Drivern yace "Bakuwar da na dauko Airport ce Hajiya" Yarinyar ta ɗan yi murmushi ta
koma gefe tana kallon Khaleesat tace "Sannu da zuwa sister, come in" Khaleesat ta shiga parlon yarinyar ta
kullo kofar tana nuna mata kujera ta zauna, bayan Khaleesat ta zauna yarinyar na kallonta tace "I am
Inteesar" Khaleesat ta daga idanuwanta ta kalleta tace "Sunana Khaleesat" Yarinyar tace "Welcome
Khaleesat, bari in ma Ammin mu magana" Daga haka ta juya ta bar parlon, after a while sai ga ta sun shigo
parlon da wata dattijuwa that is in her middle 50, zamowa kasa Khaleesat tayi a hankali tana gaisheta, da
fara'a matar da ake kira da Ammi ta dagota tace "A'a, koma kiyi zamanki kan kujera diyata" Khaleesat ta
koma ta zauna kan kujeran, Matar ta zauna kusa da ita tace "Sannu da zuwa, ya hanya?" Khaleesat tace
"Alhmdlh, ina yini" Ammi tace "Lafiya lau, ya kika baro mutan gidan?" Khaleesat tace "Suna lafiya lau"
Ammi tace "Ai na zata tare da Yariman ku ke, ashe ke kadai ce" Ita dai Khaleesat ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login