Showing 48001 words to 51000 words out of 152206 words
kansa abokan nasa ina tausaya masu biyesa da suke" Khaleesat tace "Shi ne yasa kake Co-living?"
Yace "Yeah, shekaranmu na karshe kenan idan Allah ya yarda so i need much privacy to study very hard to
earn my PhD, in kana tare da Ajay ba wani abun arziki da zaka yi in dai bangaren karatu ne, sannan baya
barina inyi bacci sosai, nuisance ne shi fa, Ya Subhanallah" Khaleesat tayi shiru tana kallonsa, sai kuma ta
sauke idonta, yace "Year nawa kike yanzu?" A hankali tace "Year 3" yace "Kince Pharmacy ko?" Ta gyada
masa kai, yace "Kin kusa gamawa kema ai in sha Allah" ita dai tayi shiru bata ce komai ba suna ci gaba da
tafiya slowly, ita ce tayi breaking silence din after almost 10 mins da ya biyo baya tace "You know him
back home?" Jay ya kalleta yace "Wai Ajay? Yeah he is my favorite, yanzu ma dai kin ga budurwa nake
nema masa bashi da mashinshiniya ko daya wallahi" Khaleesat tace "Ashe bazai taba samu ba, ai he is way
too rude and full of himself, wacece zata yarda ta auresa in dai ba auren dole aka mata da shi ba, ko makala
mata shi aka yi?" Jay dai dariya kawai yake yana kallonta yace "Ya kai Saurayin ki?" Nan da nan mood
dinta ya canza, taki ce masa komai tana ci gaba da tafiyarta, yana kallonta yace "Naga kin yi shiru ko
compare and contrasting kike yi a zuciyarki? Tell me pls ya kai saurayinki?" Without looking at him tace
"Kamar lokacin sallah yayi, and it's getting dark already" Yace "Ke ina ruwanki da sallah tunda ba yi kike
ba?" Khaleesat was dumbfounded jin abinda yace, ta kasa kallonsa kuma taki basa amsa still walking
slowly, Roadside chair ta hango ta tafi ta zauna, ya karasa wajen yace "Ko har kin gaji ne?" Tace "To da
bazan gaji ba, muna ta tafiya for almost an hour now" Yace "Akwai wani Eatry a area din nan, mu je sai mu
yi dinner before going back home, the eatry isn't far away from here" Khaleesat tayi shiru, ta san Eatry din
da yake magana don sun taɓa zuwa da Abdul kuma abincin wajen shegen tsada ne da shi, yace "Let go"
Yana fadin haka ya juya ya fara tafiya, hakan ya sa ta mike ta bi bayansa, ya jira har ta iso inda yake sannan
suka ci gaba da tafiya a tare har suka isa Eatry din, suna shiga ta kalli Jay that was grinning kamar yaga
wanda ya sani a cikin Eatry din, lkci daya ta hango Ajay that was sitted da wata baturiya a cikin eatry din
yana mata magana, ga abinci kala kala a gabanta, shi kuma ruwan gora ne kawai a gabansa, Khaleesat ta
dauke idonta speaking calmly tace "I think zan tafi gida kawai, dama ba wani yunwa nake ji ba, i will order
a Lyft in koma gida" Jay ya riko gyalenta don har ta juya zata fita yace "C'mon Halysaah, so kike ya kara
raina ki, kina fita zai yi zaton tsoronsa ne yasa kika kasa shigowa kika fita and he will be very happy, kawai
kiyi fuska ki tafi ki zauna" Khaleesat ta tsaya bayan ta ɗan yi nazarin abinda Jay yace, kuma fa haka ne zai
yi zaton tsoronsa take, hakan yasa ta karasa Jay na biye da ita a baya ya jawo mata kujeran dake facing inda
su Ajay ke zaune ta zauna, Jay ma ya zauna sannan ya kalli direction din Ajay dake kallonsu babu yabo
babu fallasa, Jay ya daga masa hannu with smile all over his face alamar Hi, Ajay ya dauke kai kamar bai
taɓa saninsa ba a rayuwa, Jay ya daga kafadarsa yana murmushi sannan ya dau menu dake saman table ya
mika ma Khaleesat yace "Duba abinda zaki ci" Ta amshi Menu din tana kallo, cikin few minutes Jay ya
saka masu order aka kawo masu abincin, duk da Khaleesat tana facing din Ajay ko da wasa bata yarda ta
kallesa ba, tayi kamar bata san da shi a Eatry din ba, Jay kuwa cin abincinsa kawai yake with full
concentration not minding her in his front, lkci lkci Khaleesat ke kallonsa, ta lura he doesn't joke with food
and sleep for anything, dariya ma ita yake bata, ita kam a hankali take cin abincin gabanta, ya daga kai
ganin bata wani ci Crab patatoe Chips din gabanta ba yace "Should i fetch some of urs?" Ta wani kallesa
tace "Do you have an extra stomach?" Bai san sanda yayi dariya ba yace "I don't understand an extra
stomach?" Tana kallonsa calmly tace "Naga duk kai ka kusa cinye abincin kan table din nan" Jay ya bude
ido sosai yace "Har da sharri? Me da me na ci a table din?" Ta tallabi chin dinta tana murmushi tana
kallonsa wanda har sai da dimples dinta ya lotsa, Mistakenly ta daga ido suka hada ido da Ajay dake
kallonsu babu yabo babu fallasa, nan da nan murmushin dake fuskarta ya bace ta sha kunu, Jay bai ma san
tana yi ba don tuni ya ci gaba da cin abincinsa har ma ya diba na gabanta, Khaleesat ta kalli wayarta dake
vibrate kan table, sosai gabanta ya fadi ganin Abdul ne ke kiranta, Jay ya daga kai ya kalleta yace "Ba kiran
ki ake ba?" A hankali tace "Na sani" Yace "Why are you not picking?" Tayi shiru, sai a sannan ta tuna fa
ashe ya kirata severally bata daga kiransa ba, Jay yace "Ko de saurayinki ne?" Ta daga manyan idanuwanta
ta kallesa, yace "Ki daga mana kar kiyi laifi" Sauke idonta tayi ta daga kiran a hankali ta kai kunne tare da
sallama cikin sanyin murya.....
✍🏻
07087865788
[5/14, 5:45 PM] khaleesat Haiydar ✍️: Read My Book "HALYSAAH" on
ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=681294ff01c6bd900451c8e6
✨✨ HALYSAAH✨✨
✍🏻
By _Khaleesat Haiydar_
17....
Daga daya bangaren Abdul yace "What is wrong with you these days Khaleesat? Me yake damun ki?"
Tunanin abinda zata ce masa ta fara yi, tayi shiru gabanta na faduwa, ita ta ma rasa me yasa take ƙin daga
kiransa kwanan nan, kawai a zuciyarta take jin bata son waya da shi, Jay ya daga kai ya kalleta jin tayi
shiru ga waya ƙare a kunnenta, amsar wayar yayi ta zaro ido tana kallonsa da mamaki with fear, ya sa
wayar handsfree ya rage volume sannan ya ajiye saman table ya ci gaba da cin abincinsa, a fusace Abdul
yace "Wai baki ji na ne, or is something wrong with you?" A hankali Khaleesat tace "Ina jin ka mana, na
mance wayar ne a gidansu Safiyyah, i just got it now" Sounding so provoked yace "Ni zaki raina ma
hankali? Ke ce zaki bar wayarki tun jiya gidansu Safiyyah?" Khaleesat ta wani kyabe baki ta kauda kai tace
"Haka dai kawai bazan ki daga kiranka ba, me yasa baza ka min uxuri ba?" Abdul yace "Wait Khaleesat,
where are you getting ur liver from these days? Who is ur vendor? Yaushe kika fara samun courage din
mayar min da magana?" Khaleesat tace "Toh ni yanzu me nayi? Nace maka wayar baya wajena and u are
trying to create an issue out of nothing, Nan da few weeks fa za mu fara jarabawa, you are only adding
more pressure to the one i am already in, ka dinga considering dina mana pls" Jay ya ɗan daga kai ya
kalleta, sai kuma yayi murmushi ya dau ruwan gora ya bude yana sha, Abdul yace "A kanki aka fara
jarabawa? What is the big deal ah jarabawan da zaki yi? Ko dai Safiyyah ce ke dora ki akan abinda bazai
fisshe ki ba? Safiyyah ce take zuga ki har kika fara samun courage din mayar min da magana ko? Switch to
video call now" Khaleesat taji gabanta ya fadi sosai, Jay dai murmushi kawai yake, a hankali Khaleesat
tace "Ohk i will, amma kayi hakuri let me dress up first..." A mugun fusace yace "Ki bar shi" Yana fadin
haka ya katse wayar, Khaleesat dai tayi shiru tana kallon wayar nata, Jay yace "Ki gama cin abinda zaki ci
mu tafi Halysaah, it's pass magrib now zan je inyi sallah" Khaleesat ta daga idanuwanta tana kallonsa, yace
"Ko ayi maki takeaway din abincin?" Ta sauke idonta bayan sun hada ido da Ajay da ya mike daga inda
yake zaune, Jay ya juya ya ɗan kalli Ajay yace "Hey man, ka hada har nawa bills din" Ajay yaki kallon
direction dinsa kai kace bai san sa ba ma, Jay ya kira daya daga ma'aikatan wajen ta karaso, ya sa tayi masu
packaging abincin da Khaleesat bata ci ba, ita dai Khaleesat har sannan taki cewa komai kana ganinta kasan
she is a bit disturb, Jay ya bi Ajay da kallo har ya fita daga Eatry din da baturiyar da suke tare, shi bai ma
taɓa ganinta ba sai ranan duk kwashe kwashen Ajay ne, bayan ma'aikaciyar wajen ta gama packaging
abincin, yana kallonta ya tambayeta bill dinsa, nan ta sanar masa Ajay ya hada har nasu ya biya, Khaleesat
ta daga kai ta kalli waitress din jin abinda tace, Jay yace "Ok then" Mikewa yayi ya dau ledan abincin
Halysaah yana kallonta, ta tashi ta dau wayarta, yana gaba tana biye da shi suka fita daga wajen cin abincin,
Lyft din da Jay yayi masu order har ya iso, ya bude mata back seat yana jiran ta shiga, Khaleesat felt
somehow hakan da yayi, don duk fitar da suke yi da Abdul bai taɓa mata haka ba, yawanci ma shi yake fara
shiga sannan ta shiga, bayan ta shiga motar Housemate dinta ma ya shiga, sai da suka kusa gida wayarta ya
fara vibrate, ta kasa duba me kiranta sanin kila bazai wuce Abdul ba, Jay dake danna wayarsa ya kalleta
yace "Kiran ki ake ai" Bata ce masa komai ba ta kalli screen din wayar sai taga Safiyyah ce ke kiranta, ta
daga da sauri ta kai kunne tace "Hello Sophie" Safiyyah tace "Am at the door, nayi knocking shiru"
Khaleesat ta ɗan saci kallon Jay, sai kuma a hankali tace "Ohk na ɗan fita ne amma ina hanya yanzu" Da
mamaki Safiyyah tace "Kin fita? Ban gane kin fita ba, Ina kika je?" Khaleesat tayi shiru, Safiyyah tace "Ko
da Housemate din ki?" Khaleesat tace "Um" Safiyyah tace "Hmmm i see, to in dai baku kusa dawowa ba
bari inyi tafiyata kawai" Da sauri Khaleesat tace "Aa ki jirani am on my way" Tana fadin haka ta katse
wayar, ajiyar zuciya ta sauke don tayi tunanin Abdul ne ya kira Safiyyah shine ta kirata, after some minutes
suka isa gida, ta bude side dinta ta sauka daga Uber din, Jay ma ya sauka, Apartment dinsu ta nufa, ta ɗan
rage pace dinta ganin kamar motar Mustapha a vicinity din, shi dai Housemate dinta na biye da ita a baya,
sai ga Safiyyah ta fito daga motar Mustapha, da murmushi fuskarta ta nufesu ta gaida Jay, ya tsaya ya amsa
mata sannan ya wuce cikin gida, Safiyyah ta kalli Khaleesat tace "Toh ki gaida ya Mustapha, dama girki na
tsaya maki na zata har yanzu bakya iya tashi" Khaleesat ta kirkiro murmushi tace "Ohk bari in gaishesa"
Zagawa tayi zuwa side din Mustapha taga yanda ya bi Jay da kallo har Jay ya shiga cikin gida, gaishesa tayi
kanta a kasa, ya kalleta yace "Who is he Khaleesat?" A hankali Khaleesat tace "Housemate dina ne"
Mustapha ya kalli Safiyyah yace "There was a time da kika ce min mace ce Housemate dinta?" Safiyyah
tace "Eh wallahi the lady packed out shine shi ya shigo, ai bai wani dade sosai da dawowa apartment din
ba" Mustapha ya kalli Khaleesat yace "Me yasa zaki dinga zama gida daya da namiji da sunan Co-living
Khaleesat, why not come stay together with ur frnd Safiyyah in my house?" Safiyyah ta wani kallesa, sai
kuma ta kyabe baki, sai kace ya gama kwatar mata 'yan ci gun shegiyar matarsa balle ya kwatar ma ita da
kawarta, ita dai Khaleesat tayi shiru bata ce komai ba tana wasa da veil dinta, Mustapha yace "Wani yare ne
Housemate din naki?" Caraf Safiyyah tayi tace "He is from Tanzania, yaren can kasar yake yi, beside shi
baya ma wani zama a gidan once a while yake zuwa yayi karatu kawai" Mustapha ya wani kalleta yace "Ke
na tambaya?" Gefe ta koma bata sake cewa komai ba, Mustapha yace "Daga ina ku ke da daddaren nan
Khaleesat?" Khaleesat tace "I was sick tun da safe shine muka je ya siya min abinci yanzu" Mustapha dai
sai kallonta yake, after some seconds yace "I will talk to my wife, sai ki dawo nan gidana kiyi zamanki tare
da Safiyyah har ku gama Exams, i think the exam is by the corner...." Khaleesat tayi murmushi kawai bata
basa amsa ba, Safiyyah tace "Mu je in kai maki abincin da na kawo maki ciki" Bude bayan motar tayi ta
ciro abincin, Khaleesat tayi ma Mustapha sai da safe sannan suka wuce apartment dinta tare da Safiyyah,
nan parlor Safiyyah ta ajiye abincin tayi kasa da murya tana washe baki tace "Ban gane wannan fitar da ku
ke yi da Housemate dinki ba Khaleesat? Ina ku ka je?" Khaleesat tace "Abinci fa muka je ya siya min,
kuma ba wai lapiyata lau muka je ya siya min abincin ba" Khaleesat ta ajiye ledan abincin hannunta ta
zauna gefen kujera tare da sauke boyayyen ajiyar zuciya, Safiyyah dake washe baki tana ma Khaleesat
wani kallo tace "To ya aka yi yasan baki da lafiya, kuma how did he know what was wrong with you?"
Khaleesat tace "Kinga Sophie wnn ba shine damuwata ba yanzu, muna gidan cin abinci Abdul ya kirani"
Safiyyah ta wani yatsine fuska tace "So? Da ya kiraki sai aka yi yaya?" Cike da damuwa Khaleesat ta bata
labarin yanda aka yi da kuma call dinsa da ta ki picking tun jiya, Safiyyah tace "Haba, to ko ke fa da kika
fara kokarin kwatar ma kanki 'yan ci, ni sai nake ga kamar Housemate din nan naki ne ke baki Liver kike
wasu abubuwa yanzu, banda haka yaushe har kika yi bakin gaya ma Abdul magana haka" Tana dariya ta
kare maganar, Khaleesat ta dinga hararanta ganin ta ma maida abun joke, Safiyyah tace "In ni ce ke ma
bazan kirasa ba wallahi, gwara kawai komai ya ruguje kowa ya huta" Khaleesat tace "Kin manta abinda
yayi kwanaki kawai muka gansa kamar an jefosa Sophie? Kinsan yanzun ma ba karamin aikinsa bane sai
ya iya kamo hanya ya zo" Khaleesat ta dafe kanta tsabar she is confuse, Safiyyah tayi shiru, can kuma ta
kyabe baki tace "Kuma haka ne ba kai ne da shi ba sai ya iya kamo hanya tunda ba su dau kudi bakin
komai ba, kawai anjima ki kirasa sai ki kisa abinda zaki ce masa da zai gamsar da shi, kuma kina iya cewa
baki da lafiya gantalallen ya kamo hanya, ni dama ya tafka wani tsiya America su kwace visan sa kowa ya
huta" Duk da damuwar da Khaleesat ke ciki sai da tayi dariya, Safiyyah tace "Allah kuwa, ban ki ba ya zo
ya maki hauka da kaina zan kira masa 911 wallahi" Khaleesat dai tayi murmushin karfin hali kawai, wayar
Safiyyah ne ya fara ring ta duba taga Mustapha ke kiranta, turo baki tayi tace wannan mutumi yana takura
rayuwata a kasar nan, wai daga cewa zan kawo maki abinci ya zata yawo zani shine fa ya biyoni, kema
baki ji ba wai ki dawo gidansa da zama, salon wataran matar ta saka mana guba a abinci mu ci mu mutu
gaba daya, yanzu haka fa ko ga maciji bama yi da ita, ɗan fitar nan da yayi da ni muna nan dake sai ya
zamar masa matsala, tana can ta cika tayi fam tana jiransa, ko a jikina kuwa, sai na ma lallabasa ya kai ni ya
siya min ice-cream ta yanda zata ga na dawo rike da leda" Khaleesat ta sauke ajiyar zuciya bata ce komai
ba, Safiyyah ta mike tace "Bari in je, sai mun hadu Monday in sha Allah" Khaleesat ta rakata bakin kofa a
hankali tace "Thank you Safiyyah" Safiyyah tace "No thanks kawata, ki ce ma Housemate dinki na tafi"
Khaleesat ta gyada mata kai, a haka Safiyyah ta fita daga gidan, Khaleesat ta kullo kofar a hankali, abincin
da Safiyyah ta kawo mata ta dauka ta kai fridge da wanda Housemate dinta ya sa ayi mata takeaway.
Khaleesat ta fito wanka kenan taji Housemate dinta na knocking kofarta, ta dau Hijab dinta ta saka sannan
ta nufi kofar ta bude tana kallonsa, yana rike da laptop dinsa yace "Good night Halysaah, i am sleepy"
Khaleesat tace "To sai da safe, thank you for the dinner" Yace "No thanks.... kin kira BF din naki?"
Khaleesat taki basa amsa, yace "Amma bari in tambayeki, a ina kika hadu da gayen nan ne? Don't know ko
na taɓa tambayarki kwanaki...." Khaleesat ta jingina da kofa without looking at him tace "Back home" Yana
gyada kai yace "I see, ni at first na zata you are not Nigerian, was thinking you are from Niger or Chad,
probably Shuwa Arab" Khaleesat ta dinga kallonsa, bata san sanda tace "Why?" Yace "Na ganki kamar
Buzuwa" Khaleesat ta sauke idonta bata basa amsa ba, yace "Ok, i will be on my way, good night" Daga
haka ya juya ya bar wajen, a hankali ta sauke idonta sannan ta kulle dakinta ta jingina jikin kofar, she stood
there for almost 5 mins kafin ta karasa cikin dakin ta cire hijab din jikinta ta ciro sleeping dress dinta ta
saka, sanitary pad dinta dake gaban dressing mirror ta dinga kallo, sai kuma ta dauke daga wajen, sai da ta
kwanta sannan tayi dialing number Abdul gabanta na faduwa, har ya katse bai daga ba dama tasan ba lallai
ya daga ba, ta sake kiransa nan ma bai daga ba, ta bude WhatsApp tayi masa magana ta nan, reply yayi
mata yace "I don't have ur time so do not border me" tabe baki tayi ta ajiye wayar ta kashe wutan dakin
sannan tayi kwanciyar ta lumshe ido, nan da nan bacci ya dauketa. Washegari bayan Khaleesat ta gama
azkar din da take yi, ta jawo wayarta a hankali, tunda ta tashi jikinta yake a sanyaye don mafarki tayi Abdul
ya zo kamar yanda ya zo wancan lkcn still kuma ya sake haduwa da Housemate dinta a gidan, ba karamin
daga mata hankali mafarkin nan yayi ba, WhatsApp dinta ta bude bayan tayi deciding zata masa message
din ban hakuri duk da bata saka ran reply dinsa ba, cause it won't