Showing 99001 words to 102000 words out of 152206 words

Chapter 34 - HALYSAAH by Khlst Hydrr

13 May 2026

114

ba ta amince da bukatar Abdul na
son aurenta don case din ya mutu gaba daya, gashi tun bayan dawowar Malam Ali yayi ta rashin lafiya ko
kudin kai sa asibiti babu, duba da hakan ne ma yasa muka yi ta karfafa ma Khaleesat gwiwa muna bata
baki, a haka dai muka samu muka lallabata ta fara hakura, nan kishiyoyin Ummanta suka fito da baƙin
cikinsu da hassada a fili tunda su ma ai suna da 'ya ya mata sa'annin Khaleesat da ma wa enda suka girmeta
amma shine Abdul zai ce sai Khaleesat, nan fa duk suka hau gaba sosai da yayata saboda ɗan mai kudi ya
ga Khaleesat yace yana so, ranan farko da Abdul ya fara zuwa unguwan cewa yayi shi bazai shigo da
motarsa layin ba ta fito bakin titi ta samesa, gashi daga gidan zuwa bakin titi akwai tafiya sosai, haka nan
uwar ta lallabata ta shirya ta saka nikab dinta kannenta biyu suka rakata har bakin titin ta samesa, a ranan
kuma ya bata babban waya ya kuma hadata da dubu hamsin, ba ma ita ta amsa ba don nuna masa tayi bata
so shine ya ba kannenta yayi tafiyarsa, da kudin aka samu aka biya mata waec dinta tunda ba mu da yanda
za mu yi, a kaf tarihi ban taɓa jin wanda yake neman yarinya da isa da gadara da walakanci kamar Abdul
ba, for almost 2 months in Abdul zai zo unguwan mu sai dai dole ta fito titi ta samesa shi bazai shiga layin
da motarsa ba, watarana ne ya kira bata da lafiya shine da ya tashi zuwa dubata da yamma ya shigo layin a
karo na farko tunda ya fara zuwa gurin ta, daga nan kuma ya dena cewa ta fito bakin titi in ya zo sai dai ya
karasa ciki da motarsa, ya kai ya kawo har cikin gida yana shigowa, tun a wannan lokacin Abdul baya raga
ma Khaleesat, fadan yau daban na gobe daban, bashi da fahimta bashi da uxuri, ga nuna isa da gadara
abinda yace yake so dole shi zata yi, haka nan yarinyar nan ke hakuri da halinsa duk don saboda
mahaifinta, rana daddaya ne baya sa ta kuka, sai dai ni da uwarta mu yi ta bata hakuri muna ganin duk me
sauki ne tunda har yana sonta kuma yaji zai aureta ya zauna da ita wataran zata canza sa da kanta, ni dai a
sanda na fara sarewa da lamarin Abdul jikina yayi sanyi shine watarana da ya daga hannu ya mareta har sai
da shatin yatsunsa ya kwanta fuskarta, mu dai har yau bata gaya mana me tayi masa da yayi mata haka ba
don a cikin motarsa hakan ya faru, nan jikin uwarta ma ya fara sanyi kan lamarin har ta samu Mai gidanta
ta gaya masa amma Malam Ali yayi ta kakkarewa har da cewa duk wanda ma ya kara tada maganar Allah
ya isa, ana haka har ya biya mata jamb ya kai ta da kansa ta zana don fara jami'a tunda waec dinta ya fito
kuma sakamakonta yayi kyau sosai, kawai rana daya kwatsam ubansa ya kira mahaifinta wai ga abinda
Abdul yace yake so, wato zai tura Khaleesat Amurka tayi karatu a can, duk kawaicin da yayata take
wannan karan sai da ta nuna bata amince da hakan ba, don ana ta bin su a yanda suke so ba hakan ke nufin
bamu da ta cewa akan lamarin Khaleesat ba, ba Yayata ba har kakar Khaleesat Nenne ta nuna rashin
amincewarta a wannan bukatar tasu, babu ta yanda za a dau yarinya karama haka da ko mallakan
hankalinta bata gama yi ba ace za a tura ta har Amurka da sunan karatu, in haka ne kawai a daura auren
mana sai ya kai ta duk inda ma zai kai ta tayi karatu, in ko ba haka ba babu inda er ta zata je da sunan
karatu sai dai duk abinda zai faru ya faru, a nan dai laifin Mahaifin Khaleesat ne da ya dau tsoron duniya ya
dora ma Abdul da mahaifinsa ba kuma tsoron komai ba sai tsoron kar su sake maidasa inda ya baro wato
prison, dama tunda ya baro can ya dawo gashi nan gashin nan dai kamar ya ɗan samu matsala a
kwakwalwarsa, yau lafiya gobe akasin haka, ya dawo kamar ba Malam Ali ba, a lokacin duk ya gigice yayi
ta bala'i wai ina ne ba a tura yaro karatu a zamanin yanxu, yarinya me shekara sha bakwai ce za ace ma
yarinya, inda yake shiga ba nan yake fita ba, hakan ya zame masu bacin rai sosai da mahaifiyar Khaleesat
har sai da ta bar gidan ta koma gidan Mahaifiyarsa warce ita ma yaki sauraronta, haka nan Malam Ali ya
dau Khaleesat ya damka ma Abdul ba tare da amincewar uwarta ba ya kai ta karatu Amurka, Shiru Aunty
Farida tayi tana kallon su Ajay dake kallonta duk suna sauraronta, a hankali tace "Tun daga sannan shi yake
sponsoring komai nata a Amurka, cin ta da shan ta, da suturanta komai dai shi ne, sai san da ya ga dama ne
yake bari ta zo hutu Nigeria, mu tsakaninmu da ita dama sai sanda muka ganta ko kuma muyi magana ta
WhatsApp, gashi yaki a daura auren nasu wai sai ta gama karatun wanda wnn ne ke kara daga mana
hankali, a haka ake ta rayuwar bamu da kwanciyar hankali, a ko da yaushe fatanmu shine ayi ayi auren don
duk wasu iyaye nagari baza a same su da kwanciyar hankali ba ace yau er su budurwa bata gabansu, kusan
kullum sai uwarta ta zubda hawaye kan wannan lamari sanadiyar hakan har sai da hawan jini ya kamata,
ace bata da iko da er ta sai dai abinda Abdul da ubansa suka tsara gashi mai gidanta ya dau tsoron duniya ya
dora masu sai jan sa suke kamar rakumi da akala.... ko wata biyu ba ayi ba ranan yayata ta kirani take sanar
min sun kawo kudin auren Khaleesat, duk muka yi farin ciki sosai da hakan, muka yi fatan Allah ya sa
hakan alkhairi ne a rayuwar Khaleesat tunda mu ma mun fi son ayi auren kowa ma ya huta, kawai ranan
juma'an nan da ta wuce sai ga kiran yayata wai an daura auren Khaleesat da Abdul, nace mata ban gane ba,
Khaleesat din ta dawo ne? Sannan dama ana daura aure haka ba shiri? Nan take gaya min ai mahaifin
Abdul din ne ya kira Baban Khaleesat da yamma likis yace ga bukatarsu gobe juma'a, babu bata lokaci
kuma aka daura auren kamar yanda suka bukata washegarin, nace mata to shikenan Allah sa hakan shine
mafi alkhairi, zuwa satin da za a shiga zan shigo kanon tunda tace Khaleesat din ma na Amurka bata dawo
ba, ban kuma san komai dake faruwa ba sai ranan Lahadi da kirani, mun yi waya da kai babu dadewa sai ga
yayata ma ta kirani tana kuka" Ajay ya sauke idonsa kasa, Calmly yace "Amma dai baki ce mata tana nan
ba har yanxu ko?" Aunty Farida ta girgiza kai tace "Ai tunda muka yi waya kace kar in nuna ma kowa
nasan inda take wallahi ban nuna ma yayata nasan komai ba, ita kanta har yanxu bata san inda Khaleesat
take ba, Nasan Baaba Gaje bazata gaya mata ba ita ma" Ajay ya sauke ajiyar zuciya yace "Shikenan,
yanxun ma kar ki nuna tana wajenki, in sha Allah za mu ga yanda za ayi, in ma kudin baban nasa da abinda
ya kashe mata na makaranta za a mayar masu wannan ba matsala bane in sha Allah" Aunty Farida ta gwalo
ido jin abinda yace, ko dai bai ji amount din da ta kira bane da kyau, a hankali tace "Kudaden ne da yawa ai
Junaid, miliyan dari fa banda abinda zai ce ya kashe mata na makaranta da bamu sani ba" Ajay yace "Bazai
dai ce ya kashe mata sama da miliyan dari a makarantar ba, mu ma duk makarantar muke ai, in ma yace
haka miliyan dari biyu ba abu bane da muke fatan zai gagara a mayar masu, so kawai kar ki ce ma kowa
tana wajenki, we will see how things will go in sha Allah" Ita dai Aunty Farida tsabar yanda jikinta yayi
sanyi ta kasa cewa komai, dama tun da ya sakko daga mota jiya taga kalansa take ta kallonsa tana mamakin
inda Khaleesat ta samo shi, hatta wanda ya kira ɗan uwansa bata ga yayi kalar tsiya ba shima, Shi dai Jay
yayi shiru bai ce komai ba idonsa akan buhun shinkafa biyu da babban jarkan man gyada da carton din
taliya dake parlon Aunty Farida, kana gani kasan food vendor ce, Ajay ya mike yana kallon Jay alamar ya
tashi su tafi, Jay ya sauke boyayyen ajiyar zuciya yana kallon Aunty Farida a hankali yace "Bacci take ne?"
Ajay ya wani kallesa sai kuma yayi ficewarsa daga parlon, Aunty Farida ta mike tace "Bari in duba ta"
Dakinta ta nufa Jay ya bi ta da kallo, after few seconds sai ga ta ta fito tana kallonsa tace "Ehh bacci take"
Yace "Ohk, amma Drip din na raguwa kuwa?" Aunty Farida tace "Eh yana sauka" Mikewa yayi yace "Toh
shikenan, sai anjima Aunty, kilan zuwa gobe da safe in sha Allah za mu shigo" Aunty Farida ta ɗan yi
murmushi tace "Toh Allah ya kai mu Jawwad, mun gode sosai" Murmushin ya mayar mata ya nufi kofa,
har ya fita ya sake juyowa yace "Amma Aunty ki ɗan dinga duba drip din idan ya kare sai kiyi ma
makociyar taki magana ta cire" Aunty Farida tace "Ina sha Allah, mun gode Jawwad" Daga haka ya fita
daga parlon ya nufi kofar gida, cikin mota ya tadda Junaid har ya tada mota, ya karasa ya bude front seat ya
shiga ya zauna ya jinginar da kansa da kujeran motar ya lumshe ido ya bude, saukansa kenan daga America
ko hutawa bai yi ba balle ya ci abinci, yayi wanka kawai suka taho gidan Aunty Farida da Ajay, har suka isa
gidan Cousin sister din parent dinsu dake Banana Island babu wanda yace komai a cikin motar, it's almost
7pm tsabar traffic din Lagos da ya rike su a hanya, bayan Ajay yayi parking Jay ya sauka daga motar ya
nufi entrance din shiga gidan Ajay na biye da shi, a parlor suka tarar da Hajiya Fatima warce suke kira da
Ummi, ta amsa gaisuwar da suka mata ta bi su da kallo, Ajay dai ya nufi sama, Tana kallon Jay tace "Baka
ci abincin da aka ajiye maka ba Jawwad, ina ma ku ka je haka sai yanxu ku ke dawowa?" Jay ya shafa
kansa a hankali yace "Wajen wani abokinmu" Daga haka shi ma ya wuce sama, ta bi sa da kallo. Wajen
karfe tara na dare Ajay ya gama saka pajamas dinsa, Jay ya ajiye mug din tea dake hannunsa yana kallonsa
Calmly yace "So now what is ur suggestion Ajay, gaba daya kai na ya kulle akan issue din nan, that guy
have evil in mind shi yasa ya saka aka daura auren tun bata dawo ba, he have a different plan, abinda kayi
masa a USA na ransa har yanzu.... He married her immediately just to deal with her, I don't think he still
loves her, he married her to take revenge" Ajay yace "Dama ai ba saboda Allah ya sa aka daura auren ba,
akwai abinda yake nufi da hakan, ashe ma karamin ɗan iska ne shi ban sani ba tun da bai yarda da kansa ba,
da ya yarda da kansa bazai dinga kashe waya ba" Jay yace "Kamar ya?" Ajay yace "Na karbi numbersa na
sa a duba min location dinsa, his location was showing Abuja on Sunday, tun sunday din har zuwa yau bai
sake kunna wayarsa ba, kuma baya location din da aka gansa bayan na sa an je can" Jay ya bude baki yana
kallonsa, can yace "Ban gane ka sa an je can ba, what are you trying to do? Plss ni bana son wannan
dabancin naka Ajay, ni na zata fa ka shiryu, is that why u were busy shouting ku hadu a Nigeria on that
very day? No pls ka girmi haka yanxu Prince, why spare ur precious time for a tout like him, don ni wallahi
kallon tout nake ma gayen, sannan kar ka manta barrister ne shi kamar yanda kanwar mamarta ta gaya
mana, definitely yasan plan dinka a kansa da yasa ka dage ku hadu a Naija, kaga bazai bar wayarsa a kunne
ba kuwa" Ajay yace "Ai sai dai bai kunna wayarsa ba amma wallahi duk sai ya janye batancin da yayi min
a parlon nan ranan, ya zata ana zagina a tafi scot free? I will so deal with him" Jay ya tabe baki yace
"Yanxu dai that aside, meye abun yi" a takaice Ajay yace "Abun yi kawai a makasa a kotu ya fadi duk
abinda ya kashe a biyasa ya saketa taje tayi rayuwarta, cause in har ta zauna zaman aure da mutumin nan
zai iya kasheta har lahira, don prisoner zai mayar da ita kawai" Jay yayi shiru at first, can yace "But Ajay
bamu san ko anyi a rubuce kan cewar an basa aurenta a madadin kudin da mahaifinta zai biya mahaifin
Abdul din ba, sannan gayen nan Barrister ne, kana ganin zai bari ayi wannan yarjejeniyar babu sa hannu or
anything of such ta bangaren shari'a?" Ajay yace "Su na ma iyayenta kallon talakawa marasu galihu da basu
da wani say shine za su tsaya wani yarjejeniya? Ai masu arziki ke yarjejeniya, bayan sun san har a tashi
duniya iyayen nata ba samun hanyar biyan miliyoyin kudin nan za su yi ba? Ai hankalinsu da tunani ma
bazai je kan wata yarjejeniya ba cause they just assume sun samu yarinyar sun gama kuma ba wani abu da
zai gifta ya hana hakan, so now we are taking this case to court, da bakinta zata ce ma alkali bata auren a
kotu, iyaka ace ta biyasa abinda ya kashe mata na karatu sannan tayi masa wani auren ba shikenan ba" Jay
yayi murmushi yace "Case din babanta da shi mahaifin Abdul din fa?" Ajay yace "We will reach der also"
Jay yace "I just hope the agreement isn't in written form, but before mu je kotu nawa ne a account din ka
Ajay?" Dariyar da Ajay bai yi niyya ba yayi yana shafa kansa, can ya kallesa yace "Why are you asking me
that silly question Jay?" Jay yayi murmushi yace "Let me know first cause the money in my bank account
isn't more than that amount" Ajay yace "200M?" Jay yace "Ban sani ba" Dariya sosai Ajay yayi yace "Na
raina capacity dinka Bruh, meye kuma 200M a account dinka? Na zata account dinka ya doshi 1 Billion
yanxu, Ohhh i remember baka wasa da investing fa, sannan kai Momy's boy ne har account din Momy
ajiye kudi kake, Allah sa 200M din ma baya account dinta" Jay yaki tanka sa, Ajay yace "Kasan me, yanxu
600M or more ya kamata ace mun ajiye aside for this case cause I don't trust that stupid guy zai iya tripling
kudin a kotu, i will get some more money from dad, Billah i am doing all this for the sake of humanity not
because of that little brat, in don ta ita ne bazan yi ba, infact in don ta ita ne ba ruwana a case din ma" Jay
dai danna wayarsa kawai yake bai ce komai ba don hankalinsa gaba daya yayi kan drip din da aka sa ma
Khaleesat, yasan zuwa yanxu dai ya ci ya kare. Abdul na zaune gidan wani cin abinci tare da abokansa biyu
da ke sauraronsa, Abdul yayi sipping energy drink din gabansa ya ajiye ya ci gaba da magana yace "I am
still trying to gather more informations about the guy, kuma duk inda take yanxu da taimakon guy din taje
can don bata da kowa a cikin garin kano or anywhere da zata je sai wajen sa, all of a sudden fa kawai naga
yarinya ta canza attitude tana min wani sabon kalan raini, at first na zata naughty frnd din nan nata
Safiyyah ce ke zugata duk da ita ma sai nayi maganinta don nasan da hadin bakinta a abubuwan nan da ke
faruwa, i will fish her out too, ashe wai er ficiciyar yarinyar nan maza take kulawa a kasar suke bata liver
take min raini, Billah sai na kauda gayen nan a doron kasa this is a promise i am making, sai dai uwarsa ta
haifi wani, zai san gonata ya shiga sannan zai san bai daki banza ba, ba a dukana a ci gaba da rayuwa
lafiya, he said we should meet in Nigeria ko? nasan yanxu shi ma yana bibiyan inda zai sameni, i don't
want to be taken unaware shi yasa nake kashe wayata don nasan definitely zata basa lambata, idan na gama
shirya masa tuggu zan bude wayar yayi tracking dina ya zo ya sameni inda nake, wallahil Azeem sai na
kawar da shi kuma babu abinda zai faru, ita kuma duk inda take zata shigo hannuna nan ba da jimawa ba
kuwa, sai dai in ban cika Abdallah Musa ba" Abokinsa Aminu yace "Toh kai baka ga fuskar guy din bane?"
Abdul yayi wani murmushi yace "Ai ni yanxu ban damu da naga fuskarsa ko ban gani ba, burina in ga na
aika sa barzahu, kun yankar mana ticket din da nace?" Aminu yace "But ta yaya zaka samu informations
din wanda baka taba sani ba, baka da lambarsa ba, baka san komai kansa ba, baka san wanene shi ba, baka
ma san inda yake a Nigeria ba ko kuma wanda ya san sa, How will that be possible Abdul?" Abdul yayi
wani irin murmushi yana bubbuga kafarsa da kasa a hankali, sai kuma ya karyar da kai yace "Na zata you
will be among people that will never underate my capacity and intelligence Aminu, ai ina da lambar
wayarta ko? Kuma ni nayi mata registering sim card din, toh abokina dake aiki a kamfanin network din sim
da take amfani na ba phone number dinta ya duba min duk calls dinta ya kuma turo min numbers din da
take waya da su frequently a America, he just sent them to me few minutes ago" Yana kai wa nan ya mike
yana wani murmushi yace "Let go" Dariya kawai abokan nasa ke yi, suka tashi duk suka fita daga eatry din.
[6/2, 1:05 PM] khaleesat Haiydar ✍️: Wajen karfe goma na dare Khaleesat na zaune dakin Aunty Farida da
fruits a gabanta ta kasa sha, ita dai Aunty Farida na zaune opposite dinta ta zuba mata ido don har ta gaji da
ce mata ta sha fruit din, ga abinci ma taki ci, tun tuni makociyar Aunty Farida

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login