Showing 90001 words to 93000 words out of 152206 words
sunkuyar da kanta tayi
shiru tana wasa da gefen hijab dinta, Ammi ta kalli Inteesar tace "Inteesar ki kai ta daki ta huta" Inteesar
tace "Ohk" Tare suka tafi dakin Khaleesat na biye da ita, Ammi ta bi su da kallo. Wajen karfe takwas na
dare Khaleesat na zaune daki tare da Inteesar da ta mayar da ita Television, ita dai a hankali take cin fruit
salad din gabanta, tun zuwanta gidan in dai ta kalli Inteesar by mistake zata ga kallonta kawai take, da sun
hada ido kuma sai Inteesar ta mata murmushi, Khaleesat wasn't bothered da kallon don farkon haduwarsu
da Sophie haka ita ma take mata, tayi ta kallonta a makaranta ko gajiya bata yi kuma da sun hada ido sai ta
mata murmushi, bayan sun zama best of friends ne Sophie ke gaya mata she is soo beautiful shi yasa bata
gajiya da kallonta, sai bayan sun zama kawaye Sophie ta dena mata maganar kyanta, kuma dama da wuya
taje waje bata ga mutane na kallonta ba, ba maza ba hatta yan uwanta mata haka suke kallonta, muryar
Inteesar taji a hankali tace "You are Beautiful Khaleesat" Khaleesat ta ɗan kalleta sai kuma ta mayar mata
da murmushin da take mata kawai, Inteesar tace "Sosai fa" Cikin sanyin murya Khaleesat tace "And you
too Inteesar" Inteesar tayi dariya tace "A'a gaskiya ba kamarki ba, ni dai ina son mu zama frnds in baza ki
damu ba, Ya Prince yace gobe zaki tafi Lagos da safe, don Allah ki bani numberki mu dinga zumunci ta
waya, probably baza ki sake dawowa gidanmu ba" Sosai Khaleesat taji wani relieve ya zo mata bayan taji
Inteesar tace zata tafi Lagos da safe, dama gaba daya hankalinta yayi gun kanwar Ummanta, Allah ya gani
daurewa kawai take amma ita kadai tasan me take ji both mentally and physically, tana cikin tashin hankali
sosai but she is trying her best to act normal, Khaleesat tace "Ohk amma nayi misplacing wayana ban yi
welcome back, idan nayi zan amshi lambarki gun sa" Inteesar tace "Ohk to ba damuwa, amma zaki dade a
lagos ne in kin je?" Khaleesat tace "Zan ɗan yi kwana biyu a can in sha Allah" Inteesar tace "Akwai
sisterna dake aure can, idan baza su dawo gida for New year ba in sha Allah zan je Lagos din so that i will
meet with you there" Murmushi Khaleesat tayi tace "Toh shikenan Allah ya kai mu lafiya" Inteesar ta tashi
ta bude press ta dauko mata kayan baccinta don dakinta ta kawo Khaleesat, bayan ta ajiye kayan gefen gado
tace "You can change to this idan kinyi wanka, i will be back later" Khaleesat tace "Alright, thank you so
much" Bayan few minutes da fitan Inteesar Khaleesat ta tashi a hankali ta tafi bandaki, da ta tuna auren
Abdul dake kanta tashin hankalinta ninkuwa yake, sai da ta ci kukanta me isarta sannan tayi wanka ta fito
daga bandakin, ta gama saka kayan da Inteesar ta bata kenan tana kokarin daure gashinta sai ga ta ta shigo
dakin, Inteesar ta wara ido tace "Waow is all that ur hair Khaleesat?" Khaleesat dai ta mata murmushin
karfin hali tana ci gaba da daure gashinta, Inteesar that was looking at the hair with fascination tace "Bari in
baki Hair net" Hair net dinta ta dauko ta ba Khaleesat, Khaleesat ta amsa tace "Nagode sosai" Washegari
karfe tara da rabi na safe Khaleesat ta gama shiryawa tana jiran Drivern gidan, kayan Inteesar ne jikinta da
yake yanayin jikinsu daya babu me cewa ba kayanta bane, tana zaune gefen gadon Inteesar duk da Hijab ne
har kasa jikinta amma sanyi take ji sosai, ga AC dake dakin a kashe amma she is shivering, tun da ta tashi
da asuba tasan she is not feeling okay, breakfast din ma da kyar ta sha shayi kawai, ko irish din bata ci ba
balle bread, she is trying all possible best to look alright don kar ayi cancelling tafiyarta zuwa lagos yau,
Mai aikin gidan ce ta Kwankwasa kofa ta sanar mata driver yana jiran ta, Khaleesat ta tashi da kyar ta dau
handbag dinta ta fita daga dakin zuwa parlor, nan ta tarar da Ammi zaune, Khaleesat ta karasa ta duka kusa
da ita tana mata godiya don sosai suka sake mata kamar da can sun taba saninta, daga karshe dai Inteesar ta
bi su har Airport don rakiya, haka kawai jininta ya hadu da Khaleesat, ita kanta Khaleesat don bata cikin
nutsuwarta ne amma she so much appreciate Inteesar's care toward her, a haka dai suka rabu kamar sun
jima da sanin juna, Khaleesat ta shiga cikin airport din ta amshi boarding pass dinta don Ajay ya tura mata
ticket ta Email din wayar da ya bata hade da hoton National ID dinta da yayi snapping tun karfe bakwai na
safe, bayan ta amshi boarding pass dinta ta nufi Departure Lounge. Karfe sha biyu saura suka sauka garin
Lagos, Khaleesat ta sauka a jirgi da taimakon wata mata don zazzabi ne sosai ya rufeta but she is still
pretending to be fine, a haka suka fito Airport din daga Arrival matar na tambayarta za a zo daukanta ne ko
Taxi xata hau, Kafin Khaleesat tace komai ta hango wani kamar AJ tsaye jikin wata mota yana danna
wayarsa, sai da ta kifta ido ta bude to be sure he is the one she is seeing, ta kalli matar kusa da ita da kyar ta
sanar mata yayanta ya zo daukanta, a haka suka rabu da matar, Khaleesat ta nufi inda ta hango Ajay, sae da
ta iso kusa da motar ya daga kai ya kalleta, ta sunkuyar da kai a hankali tace "Ina yini" Calmly yace "Ina
wayar da na baki?" Jakar hannunta ta nuna masa tace "Yana ciki, na sa silent ne" Driver seat ya bude ya
shiga sannan ya bude mata daya side din motar, zagawa tayi ta shiga ta jinginar da kanta ta lumshe ido, ya
tada motar suka bar Airport din, Google map yayi ta using after almost 45 mins ride Khaleesat ta fara gane
inda za su, amma kuma sae ko ina yayi mata sabo a area din ko don she is not stabilize ne bata dai sani ba,
ta juya ta kallesa shi dai driving dinsa kawai yake with the assistant of his google map, at last suka shigo
wani unguwa yayi parking ya dau wayarsa yayi dialing number, muryar Aunty Farida taji bayan anyi
picking, Khaleesat taji kamar an yaye mata ƙaso tamanin cikin damuwarta jin muryar kanwar Ummanta,
bayan few minutes sae ga ta ta fito daga cikin wani gate, tun da AJ ya hangota daga nesa ya fahimci da ita
yake waya don kana ganinta ka ga Khaleesat, yayi driving din motar har zuwa dai dai kofar gidan da ta
fito, yana parking Khaleesat ta bude motar da sauri ta sauka da sauran last strength dinta ta nufi Aunty
Farida ta fada jikita, Aunty Farida ta rikota da sauri kafin ta kai kasa, wata makociyarta ce ta taimaka mata
suka rike Khaleesat suka shiga da ita cikin gidan, shi dai AJ na tsaye kusa da motarsa yana kallonsu har
suka shiga ciki, sai kuma ya jingina da motarsa yana kallon yara dake wasa few houses away, wayarsa ya
ciro jin yana ringing ganin me kiransa ya daga yace "Ya ake ciki?" Daga daya bangaren mutumin yace
"Ranka shi dade sai daxu ya kunna wayar tasa, an kuma duba location din nasa yana cikin garin Abuja
yanxu haka" AJ yayi shiru kafin yace "Ohk, i will get back to you nagode" Daga haka ya katse wayar ya
mayar aljihunsa, sai ga Aunty Farida ta fito daga cikin gidan, yayi ƙasa da kansa ya gaisheta, ta amsa cikin
sanyin murya tace "Sannu da kokari fa, Allah ya saka da alkhairi, mu shiga ciki sai mu yi magana ko" Bai
ce mata komai ba ya bi bayanta zuwa cikin compound din, Compound ne me dauke da apartment uku self
contain each, AJ ya tsaya daga balcony din apartment din bai shiga ba har sai da Aunty Farida ta kara
lekowo ta masa magana sannan ya cire takalmansa ya shiga parlon ya zauna saman kujera yana kallon
Khaleesat da ta juya baya kan 3 seater din da take kwance, Aunty Farida ta tafi kitchen dauko masa ruwa,
ya ciro wayarsa yana dannawa absentmindedly, Sai ga Aunty Farida ta fito kitchen ta ajiye masa ruwan a
kusa da shi sannan ta zauna, da damuwa tace "Sannu da kokari Junaid, Allah ya saka da alkhairi, mun gode
sosai" AJ ya daga kansa ya kalleta yace "Amma dai kince bai san inda kike a lagos ba ko Aunty?" Aunty
Farida tace "Gaskiya bai san nan gidan ba, tsohon gidan da na baro ne dai ya sani, shi ma wani lokaci ne da
ta zo Lagos dubani bani da lafiya, ta zo da kwana uku sai ga shi shima ya zo, to yau wata hudu kenan da
barina wancan Unguwan na dawo nan" Ajay dai yayi shiru idonsa a kasa, Aunty Farida tace "Kuma ba
unguwa daya bane, shi wancan Unguwan da na baro a Ojota ne, daga can zuwa nan ma tafiya ce me zaman
kansa, ba kuma wanda yasan nan na dawo" Ajay yace "Toh shikenan, jikinta da zafi ne?" Aunty Farida tace
"Ehh na ji da zafi sosai gaskiya, makociyata da ta rike min ita muka shigo yanzu nurse ce, tace zata rubuta
min magunguna in siyo mata" Ajay yace "Ohk, bari zan fita yanzu sai in siyo magunguna da allurai da drip
ayi mata karin ruwa" Aunty Farida tace "To Allah ya saka da alkhairi, amma baka sha ko ruwa ba Junaid"
Ajay ya ɗan yi murmushi yace "Bari in je in dawo dai" A haka ya fita daga parlon ya tafi pharmacy ya
harhado mata magunguna da drip da allurai. Wata mace ce warce bazata wuce shekaru hamsin da bakwai
ba zaune wani kantamemen parlor cikin isa, mai aikinta na duke gabanta tana yanke mata kumbar
kafafuwanta, cikin fada take cewa "Banda ma naci irin naka dama ina kai ina er matsiyata? Er talakawa?
Wanda cin yau da kyar na gobe da kyar, ai kai ba class dinta bane ta ko ina, you just stoop ur self so low
Abdul, babu wanda ya isa da kai babu wanda zai baka shawara ka dauka, na rasa irin wannan taurin kai
naka, tun asali i am against you marrying that poor wretched girl, kuma har gobe ba wai nayi na'am bane
kawai bani da yanda zanyi da kai ne Babana, baka jin maganata ko na ubanka balle na yayarka, yanxu ina
amfanin kaskantar da kai da matsiyaciyar tayi cikin talakawa yan uwanta a gaban gidan cin abinci, abu har
police station, da mutuncinka da iliminka a maka haka? In zaka dau shawarata yanzu gwara kawai ka
saketa case ya dawo sabo fil, uban me zaka ci da ita kuma bayan wannan abun da ta maka a idon duniya?
Idan yarinya kake so ni duk inda zan shiga zan je in samar maka yarinya karama da ta fi ta komai kuma er
gidan arziki ba tsiya ba, kai ko Nijar din ne ma ni sai in shirya inje da kaina in samo maka wata buzuwar er
gidan arziki ba talakawa ba, kai ga ma er wata kawata shuwa Arab yanda kaga ita wannan da makale ma ita
ma haka take tass da ita, ga gashi, sannan su ba talakawa bane" Wata matashiya ce er shekara 39 dake
zaune parlon ita ma ta juya da sauri ta kalli warce ke magana tace "Momy ban gane abinda kike nufi ba?
Wai nufinki ya saketa kenan?" A fusace Momyn tace "Toh uban me zai ci da ita idan bai saketa ba Meema?
Er talakawa ce fa, a kanta aka fara kyau a duniya ne da bazai rabu da ita ba?" Warce ta kira da Meema ta
girgiza kai tace "A'a wallahi Momy, ai idan ya rabu da ita yanzu ma ita da iyayenta ne suka ci riba, duk
uban hidimar da yayi mata sai kice ya saketa daga karshe ko tausayinsa ba ki ji ba Momy? Ae wallahi bata
isa ya saketa ba, ko don mu kuntata mata yanda ta kuntata ma Abdul baza mu yi fatan ya saketa ba, dole sai
ta shigo gidan nan, balle shi ba mahaukaci bane da zae saketan, yarinyar da ya tura har America karatu duk
don dai ta zama presentable cikin mutane kar a mana dariya daga karshe ta saka masa da wannan walakanci
da tijara haka?" Abdul dake zaune parlon shi ma duk yana sauraronsu ya mike yace "In har aka ga na saketa
to bana numfashi ne a duniya, kuma duk inda ma take zata dawo hannuna nan ba da jimawa ba kuwa, a nan
ne zata gwammaci bata taɓa sanina a rayuwarta ba, i will make life a living hell for her" Momy ta tabe baki
tace "Shi dama talaka ai bai gaji abun arziki ba, shi yasa babu ruwana da su ko da wasa, hanyar jirgi daban
ta mota daban, kai ne da jajibe jajibenka kasa ubanka ya tafka asaran kusan miliyan dari akan matsiyaciyar
yarinyar nan" Tuni Abdul ya fice daga parlon, Meema na kallon uwarsu tace "Ai ki ma dena maganar
asaran miliyan dari Momy, don yanxu babu wannan zancen asaran nake ji" Momy dai ta tabe baki tana
kallon me aikinta tace "Ke kar fa ki yanka ni inyi mugun bata maki rai yanzu, ya zaki dinga gaftare min
naman yatsu" Hakuri mai aikin ta hau bata. Wajen karfe biyar na yamma Khaleesat ta ɗan kishingida a 3
seater, hannunta rike da bowl din pepper soup din da Aunty Farida tayi mata, gaba daya ta kasa shan pepper
soup din Offals din, don jinsa take kamar magani a bakinta gashi har sannan jikinta babu kwari ga ciwon
kai, ta kalli drip din dake hannunta taga ko quarter bai yi ba amma har ta gaji ta rasa inda zata sa kanta taji
dadi, tun da AJ ya kawo magungunan da drip ya ajiye ya bar gidan har sannan bai dawo ba, ga abincinsa
Aunty Farida ta zuba a cooler ta ajiye a tray tun daxu tana jiransa, tambayoyi ne da yawa ke yawo a zuciyar
Aunty Farida tana son tambayar Khaleesat ko shine ya taɓa biya mata jirgi kwanaki da Umma bata da
lafiya amma ganin yanayin da Khaleesat ke ciki ta bar duk tambayoyin nan a zuciyarta, Aunty Farida ta
kalli Khaleesat tace "Ki daure ko kadan ne ki sha, ko in dama maki custard?" Khaleesat ta girgiza mata kai,
dai dai nan aka kwankwasa kofar parlon, Aunty Farida ta mike ta yafa gyalenta sannan ta tafi ta bude kofar
ta koma gefe, da sallama Ajay ya shigo parlon yana kallon Aunty Farida yace "Tare da brother dina muke"
Aunty Farida tace "To ku shigo mana" a hankali Khaleesat ta gyara zamanta tana kallon Jay babu ko
kiftawa, ganinsa ta dinga yi kamar a mafarki, Jay ya sauke kansa ya gaida Aunty Farida ta amsa da fara'a,
sannan ya juya yana kallon Khaleesat shi ma babu ko kiftawa, lkci daya hawaye ya cika idonta tana
kallonsa, walking slowly ya karasa har cikin parlon ya duka gabanta yana kallonta, a hankali yace "Are you
feeling better now Housemate?" Da sauri ta gyada masa kai hawaye na sauka idonta, and truly she felt
better immediately, shi dai AJ na tsaye yana kallonsu, haka Aunty farida da ta koma one sitter a sanyaye ta
zauna, Jay yayi kasa da murya still looking at her yace "Kiyi hakuri, everything will be okay soon in sha
Allah, i promise you" Ta gyada masa kai da sauri with so much hope from his assurance, yana kallon bowl
din hannunta Softly yace "Take ur soup" Ba musu ta dau spoon din ta fara shan pepper soup din a hankali,
Aunty Farida ta kalli Ajay tace "Baka zauna ba Junaid" Ajay ya sauke kansa ya karasa 2 seater ya zauna,
Aunty Farida ta share hawayen da ya cika idonta, da kyar tace "Mu ma duk ba da son ran mu bane
abubuwan nan ke faruwa haka ba, ba mu da yanda za mu yi ne kawai, amma babu nagartattun iyayen da za
su dau er su su ba Abdul aure"
[5/29, 8:10 PM] khaleesat Haiydar ✍️: Sai da Jay yaga Khaleesat ta ci pepper soup din me ɗan yawa sannan
ya mike ya koma kusa da Ajay ya zauna, After a while Ajay yayi breaking din silence din da ya ziyarci
parlon yace "Iya daukar nauyin karatun ta kawai yayi Aunty?" Aunty Farida zata yi magana wayarta ya fara
ring, dauka tayi ganin Umma ce ke kiranta ta wayar makociyarsu Sha'awa, ta mike ta tafi dakinta don daga
wayar, Ajay dai kallon Khaleesat yake kamar yanda Jay ke kallonta don har ta shanye pepper soup din, ta
ajiye bowl din kasa tana kokarin disconnecting drip din hannunta ta yanda zata bar cannula din kawai, Jay
ya mike yana kallonta yace "What happened? Do u want to ease ur self" Da kyar tana girgiza masa kai tace
"I think i want throw up" Ya karasa cikin hanzari yayi disconnecting din mata, ta tashi ta wuce bandakin
Aunty Farida da sauri tana toshe bakinta, sai ga Aunty Farida ta fito daga daki, ta kalli inda Khaleesat ke
zaune ganin bata nan ta kalli kofar bandaki, zaunawa kan kujera tayi a sanyaye tana kallonsu tayi kasa da
murya tace "Yanzu yayata ta kirani wai an zo an tafi da mahaifin Khaleesat" Da mamaki Jay da Ajay ke
kallonta, Ajay yace "Kamar yaya kenan?" A sanyaye Aunty Farida tace "Baban Abdul din ne yasa aka je
aka tafi da shi" Daga Ajay har Jay kallonta suke with confusion da kuma mamaki, fitowar Khaleesat daga
bandaki ya sa Aunty Farida tayi shiru bata sake cewa komai ba, bayan Khaleesat ta kwanta kan 3 sitter din
Aunty Farida ta juya tana kallonta tace "Ko zaki shiga daki a maida maki drip din?" Khaleesat ta gyada
mata kai don ita ma ta gaji da kwanciyar kujeran, Aunty Farida ta mike tace "Bari in ma makociyata
magana sai ta sa maki a daki" Daga haka ta fita daga parlon, after some minutes sai ga ta ta dawo da
Neighbor dinta Bayerabiya, Khaleesat ta tashi ta koma dakin Aunty Farida, Bayerabiyar ta bi ta ciki ta sa
mata drip din, ita dai Aunty Farida na zaune parlor tayi nisa tunanin da take har makociyarta ta fito ta tafi,
Aunty Farida ta kalli su Ajay a hankali tace "To abinda yayata ta kirani ta gaya min kenan" Ajay yace "So
suke a biya su kudin makarantar da ya dinga biya mata?" Aunty Farida ta girgiza kai tace "Ai ba iya kudin
makaranta bane Junaid" Ajay yayi shiru yana kallonta, Jay yace "Bayan makaranta akwai wani abu na kudi
da ya hadasu ne?" Aunty Farida tace "Kwarai kuwa.... Shekarun baya Malam Ali wanda shi ne mahaifin
Khaleesat dreban