Showing 42001 words to 45000 words out of 152206 words

Chapter 15 - HALYSAAH by Khlst Hydrr

13 May 2026

84

da safe kuma a gabansa, shi in bai
bata min rai ba baya jin dadi a rayuwarsa" Khaleesat tayi shiru kamar bazata ce komai ba, can dai tace "To
ai Cereal ba abinci bane, ka dai dinga ci ko kadan ne" ฦŠan murmushi kawai yayi bai ce komai ba, tace
"Shikenan, za mu koma, Allah Ubangiji ya baka lafiya" Yace "Baza ki bari Salem ya dawo yayi dropping
din ku ba?" Tace "Aa, Safiyyah nasan brother dinta ne ke kiranta a waya, kaga tun daxu muka gama
lectures bata koma gida ba" Yace "Ohk ni bari in ajiye ku" Khaleesat ta zaro ido tace "Aa kai da baka da
lafiya, za mu yi ordering Uber do not worry about us pls" Khaleesat ta mike, yana ganin haka shi ma ya
tashi, amma sai da ya dafa kujera for sometime saboda juya masa da kansa ya fara yi, A hankali Khaleesat
tace "Pls kar kayi stressing kanka, just lie down and rest" Ya dago kansa yace "No, let me see you
downstairs" Juyawa tayi ta nufi kofa, ya bi bayanta, ga mamakinta sai ta ga Safiyyah tsabar samun waje
tana zaune parlon dake upstairs tana kallo tana cin cookies ga lemo a gabanta, to a ina ta samo lemun da
cookies, Safiyyah ta washe baki ganin Khaleesat sannan ta mike tace "Shikenan mu tafi?" Jay da ta hango
ne yasa tayi tsit, Khaleesat ta nufeta suka fara sauka downstairs a tare amma gabanta faduwa yake kar su
kara ganin karen daxu, hakan yasa ta bari Safiyyah ta shiga gaba, Jay na biye da su a baya har suka sauko
downstairs, ai ko karen na ganinsu ya nufo su da gudu yana haushi, Khaleesat ta juya a tsorace zata koma
sama ta ci karo da Housemate dinta dake bayanta, ya rikota da sauri yace "C'mon, are you afraid of dog
Halysaah?" Bayansa ta koma zuciyarta na bugawa, Safiyyah kuwa sai kora karen take da jakar hannunta
fuska daure, shi dai Ajay na zaune parlor tun da ya kallesu sau daya ya dauke kai ya ci gaba da kallon
Football da yake, sai da Jay ya kori karen sannan ya juya da gudu ya koma gun Ajay ya zauna saman
kujeran kusa da shi, Jay ya juya ya kalli Khaleesat da ta marairaice ita ma tana kallonsa, ya ษ—an yi
murmushi yace "Ba abinda zai maku ai, bai san ku bane shi yasa...." ita dai bata ce komai ba, Jay ya jufi
Ajay yace "Ajay ina makullin motana?" Ajay yace "Me zaka yi da makullin mota?" Khaleesat dai tuni ta
nufi kofar fita parlon da sauri don ko kallon Ajay bata son yi, Safiyyah kam tana kallon Ajay tace "To sai
anjima, Nagode sosai" Yace "Allah ya tsare" sallama tayi ma Jay shima sannan ta bi bayan Khaleesat, Jay
yasan bazai basa makullin ba, hakan yasa ya duba aljihun Ajayn ya zaro few dollars sannan ya juya ya bi
bayan Safiyyah, duk yanda yayi da Safiyyah ta amshi kudin taki amsa, Khaleesat tuni ta kusa fita daga
gidan gaba daya, a haka Safiyyah ta bi bayanta. Safiyyah na kallon Khaleesat bayan sun shiga Lyft har sun
fara tafiya ta rike haษ“a tace "Ke ashe wannan gayen da muka yi misunderstanding da farko da muka shigo
gidan yana da kirki sosai, in gaya maki da na zauna parlon nan na sama ni kadai ya zo wucewa ya ganni sai
ya tsaya yayi powering min TV, har da kunna min wutan parlon, ya kuma nuna min fridge in dau lemo in
sha, wallahi i never expect such kind gesture from him duba da yanda ya amsa mana gaisuwanmu da muka
shigo parlon da farko, ashe mun yi misperceiving dinsa ne" Khaleesat tayi kamar ma bata ji abinda
Safiyyah ke cewa ba.


โœ๐Ÿป
07087865788
[5/12, 6:46 PM] khaleesat Haiydar โœ๏ธ: Read My Book "HALYSAAH" on
ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=681294ff01c6bd900451c8e6


โœจโœจHALYSAAHโœจโœจ
โœ๐Ÿป
By _Khaleesat Haiydar_




15.....

Wajen karfe takwas na dare Khaleesat na zaune parlor tana duba wani reading material dinta wayarta ya
fara vibrate, daukan wayar tayi taga number Salem, ita dai kallon screen din kawai take at first, after some
seconds ta daga ta sa Hands-free tayi shiru tana saurare, daga daya bangaren aka mata sallama, muryar
Housemate dinta ta ji, ta amsa sallamar tare da gaishesa, yace "Ya kika je gida Halysaah?" Tace "Lafiya
lau" Yace "How about Safiyyah?" Tace "Tana can gidansu" Yace "Good, thank you so much for the visit" a
hankali tace "Allah ya kara lafiya" Yace "Ameen Housemate" Daga haka yayi mata sallama ya katse wayar,
bata kai ga ajiye wayar ba wani kiran ya sake shigowa ta ga Abdul ne, sai a sannan ta tuna damuwar da take
ciki for days now, nan da nan mood dinta ya canza, tayi picking call din ta saka hands free sannan ta ajiye a
gefenta tana ci gaba da duba reading material dinta a hankali ta gaishesa, yace "Didn't you see the money i
sent to you?" Ta girgiza kai tace "Ban kula ba" yace "To ki duba" Katse wayar yayi ta jinginar da kanta
jikin kujera with many thought running her mind.... Washegari da yamma bayan Khaleesat ta idar da sallah
tana zaune tayi dialing number Salem, yana fara ring ya daga, bayan sun gaisa tace "Dama abinci ne zan
ma Housemate dina yace min yana so, ban san ko zaka iya zuwa karfe biyar sai ka tafi masa da shi ba,
that's if you are available and u don't mind doing so pls" Yace "Oops naje Pennsylvania daxu da safe, but za
ki iya zuwa gidan ki kai masa ai, he is at home" A hankali Khaleesat tace "Ohk" Yace "Yeah, ki kai masa
kawai can gidan" Tace "To nagode" a haka suka yi sallama ta ajiye wayar, Allah ya so bata dora girkin ba
don ta san babu abinda zai sake maida ta gidan nan dai, tayi zuwan farko tayi na karshe. Khaleesat na zaune
tare da Safiyyah bayan sun gama lectures din su na ranan, Safiyyah tace "Are you checking on ur
Housemate even if ta waya ne kuwa Khaleesat?" Khaleesat ta kalleta tace "I don't have his number ai"
Safiyyah ta dinga kallonta da mamaki, can ta girgiza kai tace "Ni ban san me yasa kike haka ba, why won't
u ask that guy Salem ya baki? It's almost 10 days now da muka je gidan dubasa tunda kika ga har yanzu bai
zo apartment dinku ba kinsan kilan ko bai ji sauki bane" Khaleesat tace "There was a time da muka yi waya
da Salem din yace zai turo min lambarsa kuma bai turo ba shi sa har yau ban sake masa magana ba naga
kamar baya son tura lambar ne, sannan kawai i assume kilan wannan arrogant guy din ne na gidan yayi
stopping dinsa from coming to the house, i suspect they are kind of related or something like that" Safiyyah
ta tabe baki tace "To ko in raka ki mu sake zuwa dubasa ne?" ko rufe baki bata yi ba Khaleesat tace "I am
going no where, sai dai in ke zaki je sai in masa tuwo ki kai masa, dama ranan da muka je yace min yana
son tuwo da miyar kuka, but for me babu abinda zai sake maidani gidan nan wallahi" Safiyyah ta dinga
kallonta, can tace "Gaskiya zuciyarki kamar dutse yake Khaleesat, wato har ce maki yayi yana son cin tuwo
amma kika kasa yi ki kai masa saboda wani banzan dalilinki, gaskiya you are not nice at all sorry to say"
Khaleesat ta mike tace "Ki kirani ko ma me zaki kirani amma wallahi bazan koma wannan gidan ba as far
as that bossy Man is in the house, kawai sai in kama hanya in sake komawa don yaji dadin kara raina min
hankali ya walakanta ni, in dai ke zaki je zan yi girkin in baki, after all kince the arrogant guy is nice to you
ai" Safiyyah bata tanka ta ba ta fara danna wayarta kawai, a haka suka rabu ko sallaman kirki basu yi da
juna ba, har Khaleesat ta isa gida a lyft bata san sun iso ba, a duk kwanakin nan Allah ya sani Housemate
dinta na ranta don babu ranan da zai zo ya wuce bata tunasa a zuciyarta, ba willingly taki zuwa gidan ta
dubasa ba kawai wannan mutumin ne bata son ta sake haduwa da, sannan she is afraid of the huge dog in
the house, kar ma taje mutumin ya sakar mata karen ta shiga uku, amma a ko da yaushe Housemate dinta
yana ranta tana kuma son sanin how he is feeling, a hankali ta bude motar ta sauka duk jikinta a sanyaye ta
nufi apartment dinta ta bude kofar ta shiga, turus tayi a living room din ganinsa kwance kan 3 seater yana
bacci, juyawa taga yayi with his eyes still close yace "Good evening Halysaah" Sauke idonta tayi daga
kallonsa, walking slowly ta karasa cikin living room din ta nufi can kusa da single sitter ta tsaya still
looking at him, a hankali ya bude ido ya fara bin parlon da kallo alamar he is looking for her, suna hada ido
calmly tace "Good evening" Mikewa zaune yayi trying to recover fully from his sleep yana shafa fuskarsa
yace "How are you?" Tace "Alhamdulillah, ya jikin?" Yace "Naji sauki ai" Shiru tayi kamar me tunanin
abinda zata ce, can kuma dai tana rike da edge din gyalenta cikin nutsuwa tace "Naga baka zo bane, i
thought jikin ne har yanzu...." Ya girgiza kai without looking at her yace "Abbana ne yasa na je Nigeria, we
spent 6 days in Nigeria, jiya muka dawo" Yana fadin haka ya daga kai yaga kallonsa take, da sauri ta kauda
kanta tana nodding tace "Ohk" Daga haka ta juya ta nufi dakinta kamar munafuka, ya koma yayi
kwanciyarsa. After almost an hour Khaleesat ta fito parlor, ta samesa zaune ya gama baccin yana danna
laptop dinsa, kanta a kasa ta karasa cikin living room din ta dan kallesa suka hada ido tana kame kame tace
"Dama tambayarka zan yi in maka tuwon ne yanzu zaka ci?" Yace "Tuwo kuma? Aa kinga you just came
back from school, ki bari next time in sha Allah" Tace "Ohk" Daga haka ta tafi kitchen to make a light
dinner, bayan ta gama girkin ta fito parlor, har sannan yana nan zaune, ta ษ—an kallesa tace "You care for
some?" Ya kalli hanyar kitchen din sai kuma yace "Let me dish it my self" Daga haka ya ajiye laptop dinsa
ya mike ya tafi kitchen din, ita dai tana tsaye ta bi sa da kallo, bayan few minutes ya fito da bowl din pasta
din ya zuba very little quantity, with another plate of the pasta, ita dai kallonsa take, ya mika mata na plate
din ta sauke idonta ta amsa, ya zauna ya ajiye bowl din nasa, a hankali tace "Wannan ne zai isheka?" Yace
"Eh" juyawa tayi zata bar wajen, yace "Bedroom za ki je ki ci abincin kenan" Ta gyada masa kai tayi
tafiyarta daki. Wajen karfe tara na dare Khaleesat ta saka hijab dinta jin yana knocking kofarta sannan ta
tafi ta bude kofar, yace "Sai da safe Halysaah, i am going home" at first shiru tayi, can kuma a hankali tace
"Why are u having two home?" Ya ษ—an buda ido yayi murmushi yace "One is a home, the other... a comfort
zone" Ta langwabar da kai tace "U said two same thing ai, A Home is also known as a comfort zone"
Dariya yayi yace "Not in my case Halysaah, they are two different thing to me" Shiru tayi kafin tace "So
now, which is home and which is comfort zone?" Yayi murmushi yace "Kema dai kamar er jarida, how is ur
frnd?" Tace "She is fine" Yace "And ur Bossy boyfriend, hope ya daina saka ki kuka dai yanzu?" Ta wani
kallesa zata kulle kofarta da sauri yace "Wait, it's just a harmless question Halysaah" Tace "To da nace
maka kuka yake sa ni?" Yace "Ohk, Allah sa kar in zo ina baki hakuri kwanan nan bayan ya saka ki kukan,
and before i forget me yasa baki cin cookies dake kitchen?" Tace "Nawa ne da zan ci?" Yayi shiru kamar
bazai ce komai ba, can kuma yace "To ki dinga ci daga yau duk abinda kika ga na siya ki dauka idan kina
bukata, I didn't buy them all because of my self alone, ko da namiji ne a gidan nan ko wata mace daban in
zan siya abu in ajiye zan siya ne in surplus not for only me, kin gane ko? Har bottle water ina siya mana ne
mu biyu ba ni kadai ba, after all there is love in sharing" Ita dai idonta na kasa bata ce masa komai ba, Yace
"Good night" juyawa yayi ta bi sa da kallo har zuwa parlor, sai kuma ta kulle kofar dakinta a hankali.
Washegari Asabar Khaleesat ta gama laundry da take a kitchen, tayi tidying din duk gidan sannan taje tayi
wanka ta fito parlor tana tunanin abinda zata girka kafin ta fara karatu cause it's almost 12pm, tun karfe
goma Housemate dinta ya shigo gidan ya wuce Bedroom dinsa, ta ma san bacci, ita kam mamakin yanda
baya gajiya da bacci take, knocking kofar parlon aka yi, she is expecting Safiyyah dama amma bata yi
tunanin da wuri zata zo ba, ta karasa gun kofar ta bude a bit relieve ta samu me taya ta girki, da mamaki ta
bi sa da kallo bayan ta koma gefe don da ta ci gaba da tsayuwa wajen taga alamar bangajeta zai yi ya shiga
parlon, direct taga ya nufi dakin Jay ya bude ya shiga, kasa rufe baki tayi tsabar mamaki, tana jin sa yana
ma Jay bala'i a dakin, ita dai bata ji muryar Jay din ba, Jay ne ya fara fitowa daga dakin, kamar yanda ta
zarga kuwa baccin yake, laptop din da ya bari kan kujera da ya shigo daxu ne ya dauka, Ajay na fitowa ya
mika masa laptop din, a mugun fusace Ajay yace "What the hell should i do what with it again bayan lokaci
ya kure? Kasan implications din da abin nan da kayi zai ja min kuwa?" A karo na farko Jay yace "Kai dalla
wayar a silent yake, kuma ni ban san akwai recent aikinka a ciki ba, da bazan taho da shi ba ai" Ajay dai
kallonsa kawai yake kamar ya shaฦ™o sa, Jay ya zauna kan kujera ya jinginar da kansa tare da lumshe ido,
banda hararan Ajay babu abinda Khaleesat da ke tsaye parlon take yi, lkci daya Jay ya mike yace "Hey let
me see you off, wanka zan yi" a takaice Khaleesat tace "And pls Housemate warn him not to ever barge
into someone else's apartment like this again, this isn't a shopping Mall da zai shigo kai tsaye" A tare suka
juya suna kallonta gaba dayansu, Ajay yayi facing dinta calmly yace "Ke, da ni kike wannan maganar ko
wa?" Ta wani kauda kai fuskarta a daure tace "In baka son ayi da kai kar ka sake shiga gidan mutane babu
Excuse, after all ba tare muke renting apartment din ba da zaka shigo min gida without notice, idan wajen
abokinka ka zo maturely sai ka jirasa a waje, you don't have to push ur way into people's apartment like it's
a shopping complex" Ajay that was speechless ya kalli Jay, Jay ya shafa kansa yace "Why didn't u knock
and wait for me outside, after all she is saying the truth" Khaleesat tace "Ni in ya sake shigo min gida haka
wallahi 911 zan kira masa..." Ajay ya ciro wayarsa a aljihu yana mika mata yace "Call them immediately"
Ta jefa masa wani kallo tayi hanyar dakinta, Yana kallonta da kyau yace "I will definitely deal with you" Ita
dai tuni ta shige dakinta ta kulle kofar da makulli, Jay na kallonsa yace "Me yasa zaka shigo mata gida
kamar tsohon barawo?" Ajay yace "Za kayi bayanin me kake yi da mace under the same roof in America,
macen ma da ka kusa haifa, i promise to report you back home, ita kuma i will teach her the lesson of her
life" Yana kai wa nan ya fixge laptop dinsa a hannun Jay, Jay dake murmushi yace "Babu abinda ka isa kayi
mata don ta gaya maka gaskiya Malam, kai waye da baza a gaya ma gaskiya ba" Tuni Ajay ya fice daga
parlon, Jay ya zauna kan kujera ya dafe kansa yana dariya, the incident was just funny to him, kallon kofar
dakinta yayi yana mamakin dama wai haka yarinyar nan take amma take ma saurayinta kuka? Mikewa yayi
ya nufi dakin nata yayi knocking kofar yace "Halysaah" sai da ya kirata sau uku sannan ta bude kofar a
hankali tana leka parlon kana ganinta kasan a tsorace take, dariya yayi yace "Kinsan waye shi da kika masa
rashin kunya Halysaah?" Ta wani turo baki tace "To ni ina ruwana da koma wanene shi, saboda me zai
shigo min gida kamar wani barawo, where is it done that way? Ni dai wallahi kar ya sake zuwa min gidan
nan in ba haka ba in kira 911" Jay dai sai sauraronta yake, can yayi murmushi yace "So dama kina da baki
haka amma kike ma saurayin ki kuka?" Khaleesat ta wani kallesa ta hade rai tace "Ni bana son haka" still
smiling yace "Ok, sorry" keeping a straight face tace "Ya tafi?" Jay ya juya zai bar wajen yace "Ya tafi
mana" Da sauri tace "Plss ni dai kayi masa magana kar ya sake zuwa, if there is anything ai sai ya kira kaje
can gidanku ka samesa kawai ba sai ya zo nan ba" Jay dai murmushi kawai yake yace "Ohk" parlor taga ya
tafi, ta koma dakinta ta zauna bakin gado, har sannan gabanta faduwa yake, ita kanta bata san inda ta samu
courage din gaggaya masa abubuwan da ta gaya masa ba, ko don dama tana jin haushinsa ne yasa ta samu
irin wnn courage din oho, bata fito daga dakinta ba sai da tayi sallan zuhur, a hankali take tafiya ta shigo
cikin parlorn, gani take kamar zai sake dawowa gidan at anytime, ai ko wallahi yan sanda zata kira masa,
Zaune taga Jay a parlon yana danna wayarsa, tana tsaye bayan kujera tace "Did u warn him not to come
back plss?" Jay yace "To ke meye damuwarki ba kin masa warning kar ya sake dawowa ba, ai bazai dawo
ba" Kamar zata yi kuka tace "Wallahi zai iya dawowa, kuma in ya dawo baka nan ya zan yi?" Dariyar da
yake dannewa ne ya taho masa yace "Ina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login