Showing 102001 words to 105000 words out of 152206 words

Chapter 35 - HALYSAAH by Khlst Hydrr

13 May 2026

52

ta shigo ta cire mata drip din
bayan ya kare, ta daga kai ta kalli Aunty Farida a hankali tace "Aunty su Housemate dina sun tafi ne?"
Aunty Farida tace "Waye kuma Housemate din ki?" Khaleesat ta sauke idonta tayi shiru, Aunty Farida tace
"Junaid din ne Housemate din ki?" Khaleesat ta girgiza mata kai tace "Wanda suka zo tare" Aunty Farida
tace "Ohk, tun daxu ai suka tafi kina bacci, ta yaya ya zama Housemate din ki?" Khaleesat na juya fruits
din gabanta a hankali da fork tace "Gida daya muke da shi a America" Aunty Farida ta ɗan buda ido da
confusion tace "Gida daya kuma? Kamar yaya? Amma ba kin ce makociyarki mace bace?" Khaleesat tace
"Eh daga baya ta tashi daga apartment din, shi ne shi ya dawo gidan" Aunty Farida tace "Ikon Allah, shi
kuma Junaid din a ina kika san shi?" Khaleesat tace "Cousin brothers ne ai, dalilin Housemate dina na san
shi" Aunty Farida ta kafe ta da ido, Khaleesat ta sauke kanta bata boye ma Aunty Farida duk abun da ya
faru tun daga dawowar Housemate apartment dinta, yanda ya biya mata kudin jirgi to and fro ta dawo
Nigeria ta duba Umma, irin zaman da suka yi da shi da kirkin da yayi ta mata, har zuwa lkcn da Abdul ya
zo kasar a karo na biyu da kuma abinda ya faru tsakaninsa da Ajay, da yanda suka maidata gidansu har ta
gama Exams, babu abinda ta boye ma Aunty Farida hawaye na zuba idonta, Aunty Farida ta kasa cewa
komai sai kallonta kawai take jiki a sanyaye, after almost a minute Aunty Farida ta sauke ajiyar zuciya tayi
tagumi don she is just speechless bata san ma me zata ce ba, amma ta fahimci wani abu a labarin da
Khaleesat ta bata..... Washegari wajen karfe goma na safe Jay ya bude kofar dakin Ajay ya samesa tsaye
yana buttoning din shirt dinsa ya gama shiryawa, Jay ya jingina da jikin kofar dakin ya rungume hannu
yana kallonsa calmly yace "You know what Ajay?" Ajay ya dau face cap dinsa ya saka, yana kokarin daura
agogonsa a hannu yace "All ears" Jay yace "I think we shouldn't say anything to Abba akan kudin da muka
yi magana jiya" Sai a sannan Ajay ya juya ya kallesa yace "Why?" Jay yace "Kasan zai yi querying dinmu
about what we are using that huge amount of money for, i think gwara in amshi kudi wajen Mamina kawai,
cause you know i can't lie to Abba idan yayi insisting akan abinda za mu yi da kudi haka, zan iya gaya masa
me za muyi da kudin if he insist" Ajay ya masa wani kallo daga sama har kasa yace "Sannu saint, ita
Mamin ce bazata yi querying dinka akan me zaka yi da huge sum of money din ba?" Jay yace "Yeah, but i
know how to convince her" Ajay yayi wani murmushi yace "Mamin ce zaka yi convincing, i see" Bai jira
amsar da Jay zai basa ba ya dau makullin mota da wayar sa ya bi gefensa ya fice daga dakin ya sauka
downstairs, Jay ya bi sa da kallo, after a while ya jawo kofar dakin ya kulle sannan ya bi bayansa, Ummi
dake zaune parlor ta bi su da kallo ganin alamar fita za su yi tace "Ina kuma za ku da safen nan?" Without
looking at her a takaice Ajay yace "Bar beach" Ummi tace "Dama ana zuwa Bar beach da safe?" Ajay yace
"Eh" daga haka ya fice daga parlon, Ummi ta kalli Jay tace "Wai Beach za ku?" Jay ya ɗan sosa kansa yace
"A'a sai da yamma, yanxu dai kawai yawo za mu yi a gari" Ummi ta tabe baki tace "Ai shikenan, traffic ma
kadai ya isheku, Mami ma suna hanya yau in sha Allah, sun ma kusa sauka" Jay ya sauke kansa yace "Eh
haka tace min" Ummi tace "To sai kun dawo" Jay yace "Allah ya sa" Daga haka ya fita daga parlon, ya
tarar da Ajay a mota yana jiransa, yana shiga motar Ajay yace "Ko ina ruwanta da inda za mu, ni bana son
sa ido a rayuwata, shi yasa bana sauka gidanta a garin nan, i hate what i don't like" Jay yace "Ikon Allah,
what's wrong with her asking us where we are going?" Ajay yace "That's very wrong, we are not kids da
zata dinga tambayar mu inda za mu idan za mu fita, ko Abba baya controlling din mu yanda matar nan take
yi, i don't think i am going back to that house zan je in kama hotel kawai" Jay ya girgiza kai yace "Kai fa
matsala ne da kai kamar gidan haya, ni ban ga wani abu ba don ta tambayemu inda za mu da safe, it's
normal ai" Ajay ya kallesa yace "To ni ba kai bane da ake controlling yanda aka ga dama a family, kai da
kaga za ka iya sai ayi ta controlling dinka Jawwad" Jay bai sake ce masa komai ba, Ajay ya ja motar suka
fice daga gidan. Da sallama Safiyyah ta daga buhun dake makale kofar shiga compound din gidansu
Khaleesat, Mama Shatu da Mama Zubaida ne tsakar gida ko wacce na zaune bakin murhunta ana girka
abincin talla hayakin icce duk ya cika ko ina na gidan, Mama Zubaida sai mita take an siyo masu jikakken
icce, gaishesu Safiyyah tayi suka amsa ana mata wani kallo kasa kasa, Safiyyah ta tsaya suka gaisa da
Labiba dake wanke robobin da za a zuba abincin siyarwa, sannan ta nufi dakinsu Khaleesat ta daga labulen
ta shiga da sallama, zaune ta tarar da Umma ta jingina da bango hannunta rike da carbi ga kawarta Mama
salame da wata Zaliha makociyarsu sai Sha'awa ita ma makociyarsu zaune dakin ko wanne yayi jigum,
zaunawa Safiyyah tayi tana kallon Umma ko gaisheta bata yi ba ganin yanayinta tace "Umma baki da lafiya
ne?" Umma tayi karfin halin cewa "Sannu da zuwa Safiyyah" Safiyyah ta gaisheta sannan ta gaida sauran
mutanen dake dakin, ta sake maida dubanta kan Umma kan tace komai Mama Salame da ta san kawar
Khaleesat ce ita tayi kasa da murya tace "Tsakaninki da Allah Sapiya baki san inda kawarki Khaleesah take
ba?" Safiyyah ta zaro ido tace "Kamar yaya Mama?" Sha'awa ta gyara zama tace "Ae tun ranan asabar
rabon da a saka Khaleesat a ido, daga ta dawo kasar waje ta tarar an daura mata aure da audallah washegari
Asabar aka nemeta aka rasa, babu inda ba a shiga neman Khaleesah ba amma babu ita babu labarinta, jiya
jiya yan sanda suka zo suka tafi da Malam Ali" Safiyyah da ta shiga wani shock jin wai an daura ma
Khaleesat aure da Abdul ta ajiye jakarta a gefe ta dafe kirji tace "Wani Abdul din aka daura mata aure da?"
Sha'awa na gyara barkakken zaninta tace "Audullah saurayinta dai da kika sani, ranan juma'an nan da ta
wuce aka daura masu aure, tana dirowa kasar aka sanar mata shine ta gudu har yau babu ita babu labarinta,
gashi an tafi da Malam Ali an kullesa" Safiyyah tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Mikewa tayi tsaye
ba tare da tasan tayi hakan ba tsabar shock din da ta shiga maganganun Sha'awa na yawo a kanta, hawaye
ne ya cika idonta tana girgiza kai ta kasa cewa komai, ina jin bayan Khaleesat da tayi bakin cikin auren da
aka daura mata da Abdul idan aka cire su Jay babu wanda yayi bakin ciki kuma irin Safiyyah, don ji tayi
kamar an aza mata katon dutse a kirji tsabar bakin cikin wannan labarin, kawai ta fashe da kuka cike da
tausayin kawarta, Abdul fa?? Housemate din Khaleesat ne ya fado mata a rai, nan Safiyyah ta dinga rera
masu kuka kamar ita ce Khaleesat din, muryar Nenne suka ji a tsakar gida tana kunduma ma su Mama
Shatu da Mama Zubaida zagi tana cewa "Wato har sararin kunna rubabbun murhun ku kuka samu a gidan
nan baku dubi bala'in da ake ciki ba, ai in dai ɗa ne kowa ma ya haifa wallahi, yanda ku ke nuna halin ko in
kula da abinda ya samu ɗa na ku ma dai kun haifi 'ya yan nan naga, shegu masu fararen kafafuwa tunda ɗa
na ya auro ku yake shiga bala'i sinka sinka a duniya amma saboda baku da imani da tausayi ko wacce ta
zauna bakin shegen murhun ta" Mama Zubaida ta kauda kai tana tabe baki tayi kasa da murya tace "Sai
kuma yunwa ta kashe mu saboda yan sanda sun zo sun dauki Malam" Ita dai Mama Shatu sai juya miyarta
take kar ya kone taki ko kallon inda Nenne take, Nenne na huci ta nufi dakin Umma ta dage labulen tana
kallon cikin dakin tace "Saka dogon hijabi da rike carbi ba shine mafitarki ba Zahra'u, duk inda kika tura
yarinyar nan waya kawai zaki buga masu ki ce ta dawo tun lamari bai lalace mana gaba daya ba, in ko ba
haka ba wallahi sai a wanke daya daga kanninta a ba ma Awdul din tunda abinda yayi ta shi yayi su, in jar
fata da gashi irin ta buzaye ne su ma duk suna da shi, babu abinda zata gwada masu sai shekaru tunda ta
basu shekaru bakwai, don bazan zuba ido a karo na biyu ɗa na ya koma fursin ya tagayyara ba, Allah kadai
yasan nawa na kashe wajen shige shige har Allah ya bamu mafita a wancan lokacin da aka kullesa, tun asali
bata san bata son Awdul din ba sai bayan da ya kashe mata uban dukiya da bazai lissafu ba? Wace masifa
ku ke son ja ma ɗa na ke da er ki a garin kano? Shi kadai fa ya rage min namiji sai mata, wallahi ki fito da
ita Zahra'u in ya so su riketa a sake min ɗa na, nasan har da hadin bakin makirar tsohuwar can Gaje, yanxu
kuma zan kama hanya in tafi Hotoron duk inda ku ka boye Khaleesah sai kun fito da ita baza ku kara ja min
salalan tsiya ba, sha'awa taso ki rakani gidan tsohuwar banzan can Gaje" Da sauri Sha'awa ta mike ta figi
baƙin gyalenta ta fita daga dakin ta bi bayan Nenne dake huci suka fita daga compound din gidan, Mama
Zubaida da Mama Shatu suka saki guda a tare bayan Nenne ta fita, Mama Shatu ta kyalkyale da dariya tace
"Ana yi muna hura murhu, ma ga dai karshen wannan dirama me dadin kallo a gidan nan, su buzuwa sai a
koma dajin da aka shiga aka nemo maganin farin jini ayi ma Malam bayanin lamari ya kwabe, ba dai 'ya
yanmu bane munana masu baƙin jini, maji ma gani dai" Umma dake jin duk abinda suke cewa ta jinginar
da kanta da bango hawaye na sauka idonta Mama Salame na bata hakuri, Safiyyah dai jingina tayi daga
bango a inda take tsaye hawaye na zuba idonta ita ma, ganin abun take kamar a mafarki wai an daura auren
Khaleesat da Abdul, to amma ina Khaleesat zata tafi tun ranan Saturday ita da tasan Khaleesat ko kawaye
bata da su a kano, Housemate ne ya fado mata, ta dau jakarta da sauri tana share hawayenta ta fita daga
dakin Umma, Umma ta bi ta da kallo hawaye masu zafi na bin idonta daga ranan asabar zuwa yau har ta
rame, ko abinci bata iya ci ta kira Aunty Farida yafi a kirga akan ta zo gareta ko zata ji saukin radadin da
take ji a zuciyarta, Mama Zubaida da Mama Shatu suka bi Safiyyah da wani kallo suna tabe baki har ta fita
daga compound din, Mama Zubaida ta matsa kusa da Mama Shatu da yake murhunsu kusa da kusa yake,
tayi kasa da murya tace "Kin ga ki hakura da dafa waken nan da kika ce don gaskiya zai bata mana lokaci
ga waje da nisa, gwara mu je a kara kada hankalinta taji ta tsanesa da auren kuma taki dawowa, in ya kama
a kadata ta shiga duniya duk sai mu ce ayi, kudi ne dai zai yi kuka ba wani abu ba, kinga daga karshe in ma
Labiba ko Lamisah duk wanda yace a basa duk daya ne a wajen mu babu banbanci, babu abinda zata
gwada masu sai farin fata da uban gashi kamar na doki, in idanuwa ne su ma suna da shi, sannan suna da
hancinsu dai dai gwargwado, tun asali kece kika yi ta makon fiddo kudi da ba a kai ga haka ba ma wallahi"
Mama Zubaida ma tayi kasa da murya tace "Wallahi ban taba zaton aikin mutumin na ci haka ba Shatu,
kinsan Malaman Jabu sun yi yawa yanzu sai dai ka kai masu kudinka su yi cefanen gidansu, shi sa kika ga
ina ta ja da baya naki sakin kudi dama jarina ba jarin arziki ba, kinsan tun bayan rasuwar Malamin nan da
yayi mana aiki kan Parida naki sakewa da Malamai don asaran kudi kawai mutum yake shi din dai ne
malami gangariya amma mutuwa ta dauke mana shi kwatsam, gashi har yau duk uban kyan parida babu
mashinshini tana can tana tuwo tuwo a Legas tana aiko ma yayar kudi kuma in sha Allahu a haka zata kare
ga dai kyan da diri da komai amma babu mashinshini, to in anyi duniya don manzon Allah haka Khaleesar
ma zata kare, amma yanxu tunda muka samu sabon Malamin nan naga aiki da cikawa kema kin san fiddo
kudi bazai kara min wahala ba, ba gashi har na sa an amso min adashina ba daxu, in sha Allah sai mun
karkato da hankalin Abdul kan 'ya yan mu, ko Labisah ko Labibah, ba dai kyau suke takama da shi ba wai
su buzaye, to wallahi sai dai su ga ana aure....." Shiru Mama Zubaida tayi ganin Salame ta fito daga dakin
Umma ta ci gaba da juya miyarta with serious face, Safiyyah na fita kofar gida ta ciro wayarta a jaka don
tana da number Housemate, tayi dialing numbersa gabanta na faduwa tana hoping yasan whereabout din
Khaleesat, jin Khaleesat take a ranta kamar er uwarta ta jini, she can't imagine halin da take ciki yanxu,
yana fara ring Jay dake mota tare da Ajay ya daga wayar ganin Safiyyah ke kiransa yayi picking ya kai
kunne calmly yace "How are you Safiyyah?" Da kyar Safiyyah tace "I am fine, ina kwana?" Yace "Lafiya
lau, kin dawo Nigeria kenan?" Ta gyada kai da kyar tace "Pls tambaya nake son in maka Ya Jawwad" Jay
yace "Ina jin ki Safiyyah" Safiyyah tace "Don Allah kasan whereabout din Khaleesat, wai tun Saturday ta
bar gida har yanxu ba a san inda take ba, yanxun nan na zo gidansu nake samun labarin" Hawaye na zuba
idonta ta kare maganar, a hankali Jay yace "Halysaah?" Lkci daya Ajay ya juya ya kallesa, sai kuma ya
fixge wayar ya katse ya ajiye, Jay dai kallonsa kawai yake, can yace "Kawarta ce fa" Ajay yace "And so?
Assignment din announcing whereabout dinta aka baka ne? Me yasa baka da sirri ne kai?" Jay yace "But
it's nothing, kawarta ce kuma tana sonta sosai, nasan bazata gaya ma kowa komai ba" Ajay ya dau wayar
jin ya fara ringing, yayi rejecting call din Safiyyah sannan ya saka wayar a silent ya zura a aljihunsa yace
"Dama ka saba tona ma mutane asiri kayi ruining plan dinsu ai" Jay yace "Bani wayata malam" Calmly
Ajay yace "Bazan bayar ba" Dai dai sanda Ajay yayi parking a kofar gidan Aunty Farida ya kashe motar ya
sauka ya bar Jay a ciki. Nenne na isa kofar gidan Gaje tare da Sha'awa er rakiyarta suka ga yan sanda biyu
kofar gidan Gaje da motarsu, ga yan unguwa sun tsaya cirko cirko ana salallami, Nenne ta ja burki inda
take tsaye tana gwaggwale ido sai ga wata er sanda ta kado keyar Gaje sun fito daga cikin gidan, Gaje na
rusa kuka cikin rudewa take cewa "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, wallahi ban san inda take ba tsakanina
da Allahn da ya halicce ni, in nasan inda take Allah ya tsine min albarka, Al-qur'anin Allah babu abinda na
hada da ita ba dangin iya ba na Baba haduwar gidan duniya ne kawai, don manzon rahama ku min rai ban
hada komai da ita ba" Er sandar tace "Amma ai an ganta ta shigo gidan ki ranan asabar da daddare, iya
gaskiyar ki kadai ne zai cece ki a wannan case din aki kai ki furson, in kuma kika ce zaki ci gaba da karya
zaki ga illar karya kuwa" Cikin tashin hankali zufa na keto ma Gaje ta ko ina tace "Wallahi zan fada
gaskiya ku tsaya ku saurareni, tsakanina da Allah ta zo gidana da daddare wajen karfe goma tace in rufa
mata asiri amma bata gaya min abinda ke faruwa ba, ni kuma da na tashi sai na kai ta gidan wata er dakina
Sadiyah Chamo, Sadiyah ce ta bata mafaka a gidanta ta kwana, kashegari kuwa ta kira wani gingimemen
mutumi a wayarta ya zo da katuwar motarsa ya dauketa suka tafi inda ban sani ba, idan na maku karya a
wannan zance kada Allah yayi min rahama" Er sandar tace "Ina gidan Sadiyar yake?" Jiki na rawa Baba
Gaje ta nuna hanyar gidan Maman Fu'ad, er sandar tace "Shiga mota mu je ki nuna mana gidan" Gaje ta
rushe da kuka tana cewa "Na shiga uku na lalace ni Al-haqqatu na ja ma kaina masifa a garin kano" Bayan
mota aka bude ma Gaje tana kuka ta shiga er sandar ta dago mata yakunannen gyalenta dake jan kasa ta
dora kan cinyarta sannan ta shiga bayan motar ita ma, tuni Nenne ta juya sum sum tun ba a lura da ita ba ta
shige wani layi, sai juyawa sha'awa tayi taga gefenta wayam babu Nenne.....


Next update at night in sha Allah.
[6/2, 8:30 PM] khaleesat Haiydar ✍️: A hankali Khaleesat ta ɗan bude curtain din dakin Aunty Farida tana
leko cikin parlon ta hada ido da su gaba daya, sauke idonta tayi ta shigo parlon walking slowly ta tafi ta
zauna kan kujera kanta a kasa, tun da taji sallama ta tashi ta tafi dakin Aunty Farida don saka Hijab dinta,
gaishesu tayi still not looking at them, Jay ne kawai ya amsa yana kalllonta calmly yace "How are you
feeling now Housemate?" Sai a sannan ta daga kai ta kallesa a hankali tace "I am much better now" Kallon
Ajay tayi suna hada ido ta sunkuyar da kanta tace "Ina yini?" Yana danna wayarsa yace "Fine" Aunty
Farida ta shigo parlon daga kitchen ta ajiye masu tray din Can drink da ruwa da taje dauko masu, sannan ta
zauna kan kujera tana kara gaishesu, Jay yace "Ya me jiki" Aunty Farida tace "Da sauki, abinci ne dai bata
ci har yanxu" Jay ya daga kai ya kalli Khaleesat, sauke idonta tayi ta dau

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login