Showing 72001 words to 75000 words out of 152206 words

Chapter 25 - HALYSAAH by Khlst Hydrr

13 May 2026

83

parlor tare da Abba da Aunty, cikin nutsuwa Abba ke masa magana
amma shi gaba daya hankalinsa na sama kan Halysaah don tun da gari ya waye bai je wajenta ba, kawai dai
Cook din gidan ne ya kai mata breakfast, AJ ya shigo parlon daga reading nook da yake zaune ya nufi
dinning area zai yi breakfast, Abba ya bi sa da kallo, after a while yace "Baka yi breakfast din bane" Jay ya
ɗan kalli AJ, Aunty kanta kallonsa take ita ma, without turning back AJ yace "Ban yi ba" Aunty tace "To ai
naga cook din gidan ya kai maka Breakfast din sama daxu" Ko tankata AJ bai yi ba ya tafi dinning ya
zauna, Abba na kallon Jay calmly yace "Is he Okay?" Jay ya ɗan shafa kai yayi kasa da murya yace "I think
supervisor dinsa ne bai yi approving Article din da yayi publishing ba tukunna" Aunty tace "To banda abun
sa ai ba wani abu bane he should add in more effort to his work kawai" Shi dai Jay bai ce komai ba, haka
shi kansa Abba, after a while Jay ya mike ya tafi sama, direct part din AJ ya nufa bayan yayi sallama ya
tura kofar dakin ya shiga. Wajen la'asar AJ na zaune parlorn dake sama, gaba daya he look moody, dama
jiya da daddare a nan parlorn ya kwana tsabar takaici, har zuwa yanzu yaki ce ma Jay komai a gidan, Jay
kuwa ko a jikinsa don ko kallonsa ma baya yi, su biyu ne kadai a gidan don Abba ya fita tare da Aunty da
autarta zuwa gidan wani prominent friend dinsa a garin, da yake gobe da safe za su bar kasar zuwa Nigeria,
AJ ya gyara zama yana bin Jay da kallo trying to be sure of what he is holding in his hand, he was very
shock ya dai bi sa da kallo har yaga ya nufi bangarensa, ya tallabi chin dinsa yana girgiza kafa, sai bayan da
Jay ya fito for the first time since yesterday AJ yace "Wallahi i will never forgive you for these Jawwad, i
promise you am not forgiving you" Jay dai ya dake bai yi dariyar da ya basa ba, kuma yaki tankasa yayi
wucewarsa ya bar sa zaune a gun, da daddare Khaleesat na duba laptop dinta Jay ya shigo dakin da sallama
ta daga kai tana kallonsa ya zauna kan kujeran dakin yace "Hope you are better now?" Ta gyada masa kai,
yace "Toh Allah ya sauwake, amma ki tabbatar kin sha maganin so that u get enough night rest" Tace "Zan
sha" Yace "Alright Good night Housemate, bacci nake ji" Ta ɗan yi murmushi tana kallon agogo dake nuna
karfe goma tace "Ai baka ma yi da wuri ba" Yayi murmushi kawai yace "Saura kar ki kwanta saman gadon
yau" A hankali tace "Zan kwanta" Yace "Good" Daga haka ya fita daga dakin, shi kansa yasan tunda ta
dawo gidan yake tauye ma kansa bacci, kuma ba wai baccin baya damunsa bane kawai daurewa yake yi,
har ciwon kai yake yawan yi yanzu saboda baya bacci sosai, Khaleesat ta kashe laptop dinta ta ajiye sannan
ta mike a hankali ta dauko maganin da ya kawo mata daxu ta sha sannan ta kwanta saman gadon, amma fa
a dar dar take saman gadon, Jay na isa parlorn dake sama ganin AJ kwance kan kujera yana danna wayarsa
yace "Do you care sharing my room with me today?" AJ yaki tankasa yana danna wayarsa, Jay ya daga
kafada yayi wucewarsa dakinsa, after like an hour AJ ya mike zaune jin muryar Abbansa, Abba dake
kallonsa yace "Is everything Alright Ahmad? Why are you lying down on the Couch?" AJ ya fara sosa kai
yace "Eh yanzu zan tafi daki Dad, ban san sanda bacci ya daukeni ba" Yana fadin haka ya mike tsaye ya
dau wayarsa ya nufi dakinsa, Khaleesat ta juya jin an bude kofa don ba bacci take ba, yana shigowa dakin
kuma ya kulle kofar ya tsaya nan bakin kofar, rufe har kanta tayi da duvet, ya tafi gaban madubi ya tsaya
yana tunanin Jay bai taɓa cutarsa ba irin na wannan lokacin, sosai abun nan ya tsaya masa a rai, ita dai
Khaleesat tana ta sauraren taji ya bude kofar ya fita daga dakin amma taji shiru, hakan yasa ta sauke duvet
din kanta a hankali suna hada ido ya watsa mata kallo yace "Meye kike kallona?" Ta wani kallesa, sai kuma
ta juya masa baya bata ce komai ba, after almost 5 minutes ya bude kofar dakin ya fice, tsabar yanda bai
yarda da neatness din duk dakunan dake gidan ba ya sa ya gwammace ya kwanta a parlor instead of going
into any of the room. Da Asuba Jay ya fito dakinsa kenan zai sauka downstairs su yi sallah da Abba, tunda
Abba ya zo tare suke sallah amma banda AJ da baya saukowa ayi sallan da shi sai dai yayi shi kadai a
sama, Jay ya hadu da Abba yana haurowa sama, Abba yace "This shows baku sallah tare a gidan nan
Jawwad, ma'aikatan gidan nan guda biyu duk Musulmai ne, ga ka ga Junaid, amma ace baza ku hadu ku yi
sallah ba?" Da sauri Jay yace "Muna yi Abba..." Abba bai ce masa komai ba ya nufi bangaren AJ, Jay ya
buda ido sosai, sai kuma ya bi sa da sauri yace "Zan kira maka shi Abba..." Abba yace "Jiya da nace ka
kirasa ya sauko?" Jay ya kasa cewa komai, duk tunanin Jay za su ga AJ a Parlor a kwance amma sai yaga
baya parlon, nan hankalin Jay ya tashi ya tsaya a inda yake tsaye ya kasa ci gaba da bin bayan Abba, he
wish Junaid bai cire code din nambobin kofar dakinsa ba, Abba na tura kofan sai ga AJ da ya shiga
bandakin dake parlorn da suka baro yayi alwala ya taho zai dau pray mat, shi ma zaro ido yayi yana kallon
Abba kamar yanda Jay ma ya tsaya kallonsa, AJ ya juya suka kalli juna da Jay, tunda Abba ya kunna wutan
dakin ya tsaya for like a minute bakin kofar dakin yana kallon Khaleesat dake bacci, sai kuma ya juyo ya
fito closing the door gently, Daga AJ har Jay suka sunkuyar da kai a tare kamar munafukai, Abba dai sai
kallon AJ yake, after 30 seconds of silence, speaking Calmly Abba dake kallon Jay yace "Abinda ke faruwa
gidan nan kenan Jawwad, and you told me nothing about it?" Jay ya kasa cewa komai kuma ya kasa barin
su hada ido da Abba, cikin nutsuwa babu fada Abba yace "Magana nake maka Jawwad" Da kyar Jay ya
girgiza kai yace "I know nothing about it Abba" AJ ya bude baki yana kallon Jay da yaki kallonsa, Abba ya
gyada kai yace "Ohk then, ku mu je mu yi sallah lokaci na wucewa" Daga haka ya juya ya bar su tsaye a
wajen, Jay ya bi bayan Abba da sauri, AJ ya bi sa da kallo baya ko kiftawa, tuni har Abba ya sauka
downstairs hakan yasa Jay ya tsaya Parlor sai ya tuna tuggun da AJ ya hada masa gun Hadeeyah just 3 days
back, bai san sanda dariya ya taho masa ba, sai ga AJ da jikinsa yayi sanyi ya shigo parlon yana kallonsa,
hakan yasa Jay ya danne dariyarsa ya hade rai ya sauka downstairs da sauri, AJ ya bi sa da kallo, sai kuma a
hankali ya zauna saman kujera ya kai hannunsa baki, ganin abinda Jay yayi masa yake kamar a mafarki, bai
taɓa shiga shock irin na wannan lokacin ba. Da safe kamar babu abinda Abba ya gani a gidan don bai sake
masu maganar baz kuma da alama ko Aunty bai gaya ma ba, Jay ma yasan bazai taɓa gaya mata ba, karfe
sha daya jirginsu zai tashi zuwa Nigeria don haka har sun gama shirin tafiya Airport, Abba ya kalli Jay yace
"Junaid bai sauko yayi Breakfast ba ko an kai masa sama ne?" Jay yace "I don't really know" Abba ya dau
wayarsa ya kira AJ, ba a dau lkci ba sai ga AJ ya sauko parlor shi dai ya kasa hada ido da Abbansa, Abba na
kallonsa yace "Kayi breakfast ne, naga baka sauko ba" Without looking at his Dad yace "Na yi" Abba yace
"Ohk, za mu tafi airport ne yanzu, get ready" a hankali AJ yace "Ohk" Daga haka ya juya ya koma sama,
sai da AJ ya fara zaunawa a parlon sama for almost 5 mins, gaba daya jikinsa a sanyaye yake, gashi ya tsani
shirun Abbansa don ba alkhairi bane shirun, gwara ace ma fada yayi ta masa ba kakkautawa da wannan
basarwan da yayi kamar bai ga komai ba, his next move might not be funny, Jay ya cucesa, bai taɓa zaton
haka daga Jay ba, to ko yace ma Abba bai santa ba ta yaya zai yarda da shi tunda a dakinsa ya ganta ba
dakin Jay ba, ganin bata lkci kawai yake ya mike yana tafiya a hankali ya tafi dakinsa don dauko kayan da
zai sa, yana shiga dakin Khaleesat na fitowa daga bandaki da hijab dinta har kasa ta fito wanka, ya wani
kalleta daga sama har kasa fuskarsa a daure, ita dai tunda suka hada ido ta dauke kanta bata sake yarda ta
kallesa ba tana dai tsaye hanyar shiga bandakin, ya dau kayan da zai dauka ya karasa gaban madubi ya dau
tsadadden turarensa ya fice daga dakin, ta wani kyabe baki ta karasa shigowa cikin dakin. Har Abba suka
isa Airport bai ce ma AJ komai ba akan daxu da asuba, kuma da alamar babu abinda zai ce masa, he was
just speaking about something different in the car, a haka suka rabu normal normal a airport kamar babu
komai, AJ yaki jiran Jay ya ja mota ya bar airport din ya kama hanyar gida, dole sai Uber Jay ya samu da
zai maida shi gida, ko da ya isa gida ya ga AJ zaune a compound da non alcoholic wine a gabansa trying to
use it to calm himself down at the same time trying to figure out wani hukuncin Abbansa zai ce zai dauka a
kansa.....


*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment
07087865788 👈🏻, it's better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don
littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*
[5/26, 9:45 AM] khaleesat Haiydar ✍️: Khaleesat felt so much relieve after leaving AJ's room, tana biye da
Jay ta koma dakin da take, ba tare da Jay ya kalleta ba bayan ya ajiye laptop dinta dake hannunsa yace "Kin
ji sanda aka bude kofa da asuba ne?" Khaleesat na kallonsa ta girgiza kai tace "I am not sure, may be ina
bacci sannan, banyi bacci da wuri ba" Yace "Ohk" Tace "Why are you asking?" Ya juyo yana kallonta, ya
ɗan mata murmushi yace "Nothing" Tace "But ai frnd din ka yana shigowa ya dau stuffs dinsa wani lkcn"
Jay yace "Ohk" Har ya juya sai kuma ya sake dawowa yace "Kince baki yi bacci da wuri, ciwon kan ke
damunki har yanzu?" Ta girgiza kai tace "A'a, kawai baccin ne dai bai zo ba" Yace "Ohk" Khaleesat ta bi sa
da ido har ya fita daga dakin sannan ta zauna gefen gado a hankali, har cikin ranta take jin kamar ta jawo
ranan talata, she is so tired tana bukatar kawai ta ganta kusa da Ummanta, she need her Mom's hug, Jay na
fita ya kira ma'aikatan gidan su gyara ma AJ dakinsa, Jay made sure the workers left nothing untouched a
dakin duk da babu abinda dakin yayi, amma irin gyaran da aka ma dakin da bandakin ba na wasa bane, sai
da ko ina ya dawo yana sparkling tsabar gyara sannan Jay ya koma downstairs, amma still a ranan ma AJ
bai kwana dakin ba, yayi kwanciyarsa a parlor kan kujera. Washegari which was monday AJ na zaune usual
spot dinsa a compound da Coke din gwangwani a gabansa, har a sannan yaki ce ma Jay komai a gidan, not
even Jay hatta ma'aikatan gidan duk ba wanda yake yi ma magana he is just keeping straight face, Jay ya
fito daga cikin gida ya karasa har inda yake zaune, ko kallon direction dinsa AJ bai yi ba yana juya counter
din hannunsa, Jay na kallonsa yace "Abba wants to speak to you" Yana fadin haka yace "Abba gashi nan"
Ya ajiye wayar gaban AJ, Calmly Abba yace "How are you doing Junaid" AJ ya sauke idonsa ya gaida
Abba, Abba ya amsa yace "You didn't call to know if we arrived safely" AJ yace "Ayi hakuri" Abba yace
"It's fine, yaushe za ku dawo hutu" AJ yace "Ran Thursday zan dawo in sha Allah" Abba yace "What about
Jawwad" A takaice AJ yace "I don't know" Abba yace "Hand the phone over to him" Jay ya dau wayarsa
sitting in one of the chairs beside AJ yace "Na'am ina ji Abba" Abba yace "Kai yaushe zaka dawo" Jay ya
ɗan yi shiru, sai kuma yace "Probably next week in sha Allah" Abba yace "Ohk Allah ya kai mu, earlier
today you said you have something to tell me unfortunately ina tare da baƙi a lkcn, so what is it Jawwad"
Jay ya ɗan shafa kansa thinking of where to start, can dai yace "Abba dama it's about the girl u saw
yesterday" Abba yayi shiru at first, sai kuma "Ohk, what about her?" Jay yace "Abba ni ne na kawota gidan
ba AJ ba, she is a student of John Hopkins also, she is having issue with House rent and she's writing exam,
so shine kawai na kawota gidan nan zuwa sanda zata gama jarabawan...." Abba ya dakatar da shi yace "Did
you and Junaid birth me or i birth you both?" Jay ya girgiza kai da sauri yace "Billah Abba i am not
cooking up stories, believe me, all what i am saying is the truth ai kasan bana maka karya Abba, kawai dai
ni na kai ta dakin AJ ne without even his knowledge cause Aunty will definitely see her in the house, part
din AJ ne kawai nasan bazata shiga ba, kuma because of this... AJ parlor ya dawo yake kwana, wallahi babu
komai tsakaninmu da ita kawai taimako ne, you can even speak to her to confirm ranka ya dade" Abba yace
"If she is having rent issue don menene baza ku bata kudin hayan ta biya ba ko kuma ni ku min magana, na
menene sai kun kawota nan gida cikin ku ta zauna? Is that ur home training? Dama addininku ya yarje
maku da haka?" Jay ya sauke ajiyar zuciya a hankali yace "Kayi hakuri ka gafarce mu Abba, she will be
rounding up her exam on Tuesday, and she will leave in sha Allah" Abba yace "Kaga da ba don nasan baza
ka min karya ba Ahmad i won't listen to you, da Junaid ne ya tsaya mun wannan bayani bazan yarda da shi
ba, and my plan was to start making arrangement na samar masa mace da zan aura masa a kai masa ita can
ƙasar, tunda ka min wannan bayanin naji na kuma yarda amma daga kai har shi sati biyar na baku kacal ku
gabatar min da macen da za ku aura, ita kuma i will send you some money to sort out her House rent" AJ ya
daga kai yana kallon Jay bayan yaji abinda Abbansa yace, sai kuma ya mike kamar zai tashi sama ya bar
wajen, shi dai Jay was speechless this was the least thing he was expecting to hear from Abba, jin Abba ya
katse wayar ya zuba ma screen din ido, ya basu 5 weeks?? jay ya fi minti goma zaune a wajen kafin daga
karshe ya sauke ajiyar zuciya ya mike ya dau wayarsa ya shiga cikin gida. The next day Khaleesat suka
gama jarabawansu na karshe and she was so happy amma kuma da ta tuna wasu abubuwa kawai sai mood
dinta ya canza, suna zaune tare da Safiyyah a cikin makarantar ganin yanayinta da yanda ta sauya lokaci
daya tayi shiru, Safiyyah ta kalleta tace "Why are you like this Khaleesat?" Khaleesat ta daga kai ta kalleta,
a hankali tace "I don't have the means of going back to Nigeria Sophie, the burden i am placing on my
Housemate is too much ba shi ya kawo ni kasar nan karatu ba, he knows nothing about me, don me zan yi
ta dora masa nauyina har haka?" Safiyyah tace "To ya za kiyi Khaleesat, tunda ba ke kika rokesa ya maki
ba ai kawai addu'a zaki masa Allah ya saka masa da alkhairi, he is ur God sent Angel, ba gashi with or
without Abdul kin gama jarabawanki lafiya ba" Khaleesat ta sauke idonta jin hawaye ya ciko mata,
Safiyyah ta hade rai tace "To meye na kuka kuma?" Muryarta na rawa tace "Ni dai bana son yace zai sake
kashe min kudi masu yawa in koma Nigeria, i am feeling guilty" Safiyyah ta wani kalleta, can tace "Kya
rube a kasar nan kuwa, ke kina da hanyar komawa ne? Ko kuma aikatau zaki nema a kasar ki tara kudin
komawa Nigeria? In ba dai kudaden Abdul dake account dinki zaki yi using ki biya kudin jirgi ba" Safiyyah
na kai wa nan ta kyalkyale da dariya tace "Ko ya kwashe en kudaden nasa ne?" Ita dai Khaleesat tayi shiru
taki ce mata komai, Safiyyah tayi dariyarta me isarta sannan tace "Allah ba batun wasa ba, ya kwashe
kudaden nasa ne?" Khaleesat ta girgiza kai a hankali tace "Suna nan" Safiyyah tace "Miliyan nawa ne ma?"
Khaleesat ta sauke idonta tace "Almost 9.5 Million" Safiyyah tace "To kawai ki siya Ticket abunki tunda
dai yasan ba uban wani gareki a kasar ba da zai baki kudin komawa Nigeria ba, bayan shi kawo ki, in nice
ke ma har shopping sai nayi na komawa Nigeria a cikin kudin wallahi, ai bazai san kin taɓa ba tunda ba shi
ke ganin alert ba" Safiyyah na dariya ta kare maganar, ita dai Khaleesat bata tanka ta ba, Safiyya tace "Naji
kinyi shiru ko baza ki taɓa ba? Wallahi yanzun nan in raka ki shopping mu fatattake kudin" Khaleesat tace
"Ai ba nawa bane da zan fatattake su" Safiyyah ta kwashe da dariya tace "To ai sai kiyi ta zama a kasar,
dama gulma ce yasa kika kawo maganar ba wani abu ba don nasan Jay kike saka ran ya biya maki ticket"
Khaleesat dai kallon Safiyyah kawai take ta kasa ce mata komai, amma ita kadai tasan abinda take ji a
zuciyarta, Safiyyah tace "In kuma in ma Ya Musty magana to, don dai Economy class ticket da zai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login