Showing 75001 words to 78000 words out of 152206 words

Chapter 26 - HALYSAAH by Khlst Hydrr

13 May 2026

68

siya
mana bazai ce ya gagaresa ba" Da sauri Khaleesat tace "A'a, zan yi amfani da kudin account dina" Safiyyah
tace "Atoh dai" Khaleesat ta gaya mata haka ne kawai don bata son taje ta ma Ya Musty magana.... Jay ne
ya zo daukansu a schl din as usual, sai da ya fara dropping din Safiyyah sannan ya kama hanyar gida da
Khaleesat, daxun nan yaga Abba ya sako masa dala dubu goma wai na House rent dinta, da ya gaya ma AJ
sai cewa yayi ya masa transfer din Dala dubu biyar shi ma ya rike dubu biyar din tunda ba su suka kawota
kasar ba, shi da Jay bai tankasa ba, Jay dake driving ya ɗan kalli Khaleesat jin shirun yayi yawa, yaga
alamar tayi nisa tunanin da take, sai a sannan ya kula da idonta da yayi ja, a hankali yace "Halysaah"
Juyawa tayi ta kallesa trying to look alright ta ɗan yi murmushi tace "Na'am" Yace "Are you okay?" Tayi
yake tace "Na gaji ne kawai" Jay yayi shiru, bai sake ce mata komai ba amma yasan ba gaskiya ta fada
masa ba, a ɗan few months din da yayi da ita har ya gama studying dinta gaba daya, he knows when she is
happy, sad, bored, disturbed, and even tired, wannan karan yaga damuwa ne karara a fuskarta, ya dai ci
gaba da driving dinsa har suka isa gida, bayan yayi parking ya juya yana kallonta, a hankali yace "Me ke
damunki Halysaah?" Duk kokarinta na ganin ta nuna masa ba komai hakan yaci tura, don kawai ita ma gani
tayi kuka ya taho mata, Jay ya jinginar da kansa da kujeran motar bai ce mata komai ba, kwana biyu ya
huta da kukanta don a sanda ya dawo da ita gidan rana daddaya ne bata kuka don ma Safiyyah na taka mata
burki kuma ya ga tana ɗan jin maganar Safiyyar wani lokaci, sai da tayi kukanta me isanta sannan yace
"Sauka mu shiga ciki to" Ba musu ta bude motar ta sauka tana goge idonta, shi ma ya sauka, yana gaba tana
biye da shi suka shiga cikin gidan. Khaleesat na kwance da yamma ta shiga Hisnul Muslim dake wayar Jay
sai ga kira ya shigo wayar, a hankali ta mike zaune tayi picking call din ta kai kunne tayi shiru, daga daya
bangaren taji yace "Kin tashi?" Tace "Uhm" Yace "Kin yi sallah?" Tace "Nayi" yace "Ohk will you mind
going out to the park with me?" Khaleesat tayi shiru, sai kuma a hankali tace "Ohk, thank you" Yace "You
are welcome, i will be waiting for you at the parlor downstairs" Tace "Ohk" After almost 15 mins Khaleesat
ta sauko downstairs cikin shiri, sosai kayan jikinta yayi mata kyau sai dai ta rame sosai, shi kadai ne zaune
parlon yana jiranta, tun da suka hada ido ta sunkuyar da kanta, ya mike ya jira har ta iso parlon yana
kallonta, a tare suka fita zuwa parking space din gidan ya bude mata motar, ta ɗan kallesa tayi murmushi
tace "Thank you" Ya bude ido yace "No thanks" bayan ta shiga ya kulle motar sannan ya zaga ya shiga
driver seat, one of the best park na state din ya kai ta and she love everything about the park, the view was
so fascinating and breathe taking, she felt so refresh and relieve taji kamar bata da wani damuwa a lkcn, Jay
ya siya masu Wraps da fresh lemonade, wannan karan bata ji kunyar cin abinci gabansa ba, lkci lkci yake
daga kai ya kalleta, ita dai ta dinga kallon feral horses dake park din from a far distance, can ta kallesa tace
"Su ba a hawansu ne?" Yayi murmushi ya girgiza mata kai yace "Ba a hawa" Tace "And nobody is
controlling them?" Yace "Sort of, they are just on their own with no supervision, ko kina son in kai ki inda
zaki hau doki ne?" Er dariya tayi ta girgiza masa kai kawai, ya ɗan kalleta, kana ganinta kasan tana cikin
farin ciki a lokacin, ta kalli wraps dinsa da bai karasa ci ba tace "You are not eating?" Yace "Za ki ci ne?"
Tayi murmushi tace "A'a, na koshi, kawai naga baka ci da yawa bane" Yace "Na ci abinci daxu ne, i am
full" Ta kalli lemonade din gabansa tace "To in dauka?" Yace "A karo maki wani kenan?" Ta girgiza kai da
sauri tace "Aa fa, i just don't want it to waste ne" Ya dauki sauran lemonade din nasa ya ajiye mata a
gabanta yana kallonta, ta dau straw din ta fara shan lemonade din a hankali, dauke ido yayi daga kallonta,
wayarsa ya fara ring yana dubawa yaga AJ ne ke kiransa, yayi picking ya kai kunne, ita dai Khaleesat
kallonsa kawai take, after few seconds Jay yace "Ni sai next week probably, ban gama abinda nake ba, do
not book with me" Ajiye wayar yayi bayan AJ ya katse, ya kalli Khaleesat yace "Zaki jira har next week mu
tafi Nigeria, or you will leave before then?" Khaleesat tayi shiru at first, a hankali ta sauke idonta tace
"Yanda kace" Yana murmushi yace "Ko zaki bi AJ, he is leaving soon, yanzu ma ticket zai yi booking" Ta
daga manyan idanuwanta ta kallesa, sai kuma tace "He that dislikes me shi ne zan bi sa?" Jay yayi dariya
yace "How will you say he dislikes you Halysaah? He dislikes you shi ne yaje har apartment dinki yayi
rescuing dinki? Ke ce dai baki ganesa ba har yanzu, AJ is nice just that yana da son girma ne kuma baya
son raini, which i understand him because that's our heritage, kinga ke ko gaishesa baki yi" Tana wasa da
straw din lemonade din gabanta tace "To ai nasan ko na gaishesa bazai amsa ba, saboda na taɓa gaishesa
bai amsa min ba" Jay dai yayi murmushi yace "In kin ci gaba da gaishesa ae zae amsa" Tace "Ur frnd
doesn't like me at all, he prefer my frnd" Jay yace "Who told you he is my frnd? AJ is my cousin bro
Halysaah" Khaleesat ta daga kai ta kallesa tace "Da gaske?" Yayi murmushi yace "Ba ma kama ne?"
Khaleesat ta buda hannu tace "Ni ban wani san yanda fuskarsa yake ba ai, ban taɓa kallonsa sosai ba" Jay
yayi dariya, a hankali yace "To cousin brother dina ne, His dad is my father's junior bro" Khaleesat tace "To
amma dai ka girmesa ko?" Jay na murmushi yace "Not at all, just 3 months ne tsakaninmu, we will clock
34 next year" Khaleesat tace "Shi ne yace ya haifeni?" Jay bai san sanda yayi dariya ba sosai, sai kuma
yace "Zolayarki fa yake, but how old are you?" Ta sauke idonta kasa kamar bazata ce komai ba, sai kuma a
hankali tace "I am 20" Jay ya wara ido yace "Waw, you are still a Baby Halysaah" ta wani kallesa, yana
murmushi yace "To ai in AJ mace ne kuma an masa auren wuri ya isa ya haifeki" Yana dariya ya kare
maganar, Khaleesat dai taki cewa komai still playing with the straw in front of her, a hankali Jay yace "Are
you angry?" Ta daga kai ta kallesa, sai kuma tayi murmushi ta girgiza masa kai still looking at him, Jay ya
kwantar da murya yace "U misunderstood AJ, yana da kirki sosai, kuma yana da tausayi, just that he is a no
nonsense kuma baya son raini, sannan truly yana da girman kai na sani, but that doesn't make him bad,
kuma da kinsan wanene shi zaki san yana ma da saukin kai" Khaleesat ta karasa shan lemonade din gabanta
taki ce ma Jay komai, Jay ya kalli agogon wrist dinsa yace "Let go for horseback riding before it gets late"
Khaleesat ta zaro ido tace "A'a ni dai bazan hau doki ba" Yana murmushi yace "To mu je dai" Shi ya fara
tashi sannan ita ma ta mike suna tafiya a tare, satan kallonsa tayi suka hada ido ya ciro wayarsa yace "Let's
take some pictures with this beautiful view" A hankali tace "Ok" Tana tsaye kusa da shi yayi masu hoton da
wayarsa, yana kallon hoton da yayi masu ya taɓa hancinsa yace "Ya naga hancinki yafi nawa tsayi, ya naga
kamar kin fi ni kyau" duk lokaci daya ya jero tambayar yana sake kallon hoton da kyau, ita dai Khaleesat
tayi murmushi tace "Uhm is that an irony?" Jay yayi dariya yace "I am serious Halysaah" Wata er Africa ce
ta zo wucewa ya mika mata wayarsa politely yace ta masu hoto pls, yarinyar ta amshi wayar zata masu
hoton, yanda Khaleesat taji ta uncomfortable kusa da shi, shi ma dai kamar hakan ne cause he left a little
gap between them, yarinyar ta masu hotuna masu kyau kuwa, ita kanta yarinyar sai kallon hoton take kafin
ta mika ma jay wayarsa tana kallon Khaleesat admiringly tana murmushi tace "You are so Beautiful"
Khaleesat ta sauke idonta tace "Thank you" Yarinyar ta daga masu hannu ta bar wajen, bayan Jay yayi mata
godiya, kallo daya yayi ma hotunan ya mayar da wayar cikin aljihunsa yace "Let go for horseback riding
Housemate" Wani park din ya kai su daban da ake hawa doki, duk yanda yayi da Khaleesat ta hau doki
bayan ya biya masu kudi taki wai ita bata iya ba tsoro take ji, daga karshe ta marairaice tace "Ni dai kawai
ka bani wayarka in dinga maka video sai kai ka je ka hau" Yayi murmushi kawai ya mika mata wayarsa
yace "To ai shikenan" Khaleesat was so impressed with his horse riding skills kamar irin dama ya saba din
nan, sai murmushi take masa, mutanen wajen ma suna ta kallonsa, Khaleesat's eyes were glued to him all
through, tana yi tana masa video, sai after 7 suka bar wajen, tana kallonsa kafin su shiga mota tace "Where
did you learn to ride horse confidently?" Yayi dariya yace "Back home" Tana murmushi tace "To ka taɓa
zuwa nan ne?" Jay yace "Tab ai nan wajen zuwan AJ ne, kawai dai of recent ne muka dena zuwa"
Khaleesat tayi shiru bata ce komai ba, sai da ya fara biyawa African Restaurant ya siya mata abinci, ganin
leda daya ya mika mata yace "This is for you" Tace "Kai fa?" Yace "No, i am taking tea and bread this
night" A hankali tace "Ohk, thank you" Bayan sun isa gida yayi parking, ta juya tana kallonsa a hankali tace
"Thank you so much, Allah ya saka maka da alkhairi, i appreciate you" Without looking at her yace "Amma
nace ki dena min godiya ko Housemate?" Tayi shiru, ya bude motar ya sauka sannan ita ma ta sauka, yana
gaba tana biye da shi har suka shiga gidan, AJay na zaune parlor yana shan fruit salad yana kallon kwallo,
ya juya ya kalleta don shi bai ma san bata gidan ba, suna hada ido abinda Jay yace mata daxu ya fado mata,
ta sunkuyar da kai, kamar munafuka tace masa "Good evening" AJ ya gyara zama yana kallonta yace "Kin
saba gaisheni ne zaki ce min Good evening??" Khaleesat ta ɗan kalli Jay da ya karasa cikin parlon, Jay
yace "Good night Halysaah, if you need anything you call my line" A hankali tace "Thank you" Daga haka
ta wuce sama, Jay na kallon AJ yace "Ba don na mata magana ba kana tunanin zata gaisheka ne dama? Ni
ne nan na saka ta, sai me kuma in baka amsa ba?" AJ yace "Zamana take a gidan da zata gaisheni" Jay dai
yaki tanka masa.


*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment
07087865788 👈🏻, it's better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don
littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*
[5/26, 9:45 AM] khaleesat Haiydar ✍️: Washegari Wednesday da yamma Jay na zaune parlon dake sama
tare da AJ da ya maida parlon wajen kwanansa, don tun da Khaleesat ta kwana dakinsa tsakaninsa da dakin
kawai ya shiga ya dau kaya, ko bandakin dake dakin baya shiga, Jay dake kallonsa yace "Yanzu dai zan iya
dawowa dakinka kenan tunda ka tashi a dakin?" AJ yayi banza da shi yana ci gaba da hada few kayansa da
yake yi a tsadadden box dinsa da zai yi tafiya gobe, Jay yace "To wai kayi booking flight din ne da naga
kana hada akwati?" AJ yace "Bana son Airline din da na gani jiya, anjima zan siya Ticket din Turkish
Airlines" Jay yace "How many hours connection time for the layover?" AJ yace "Baya wuce 2 to 3 hours,
ko ma bazai kai haka ba" Jay yace "Will you mind travelling same plane with my Housemate? I just
remembered I will be meeting my Mami at the UK, tare za mu koma Nigeria da ita daga can" AJ yace "Of
course I will mind Jawwad, because my OCD will never allow me board the same plane with her, ga
Airline kala-kala ka nemi wani ka siya mata ticket mana, what is my business with her da zaka hadani da
ita sai kace ni na kawota America, there is this Airline na mance sunansa Economy class ticket dinsu naga
is just 600 dollars, you can get her the ticket as the Good Samaritan that you are" Mikewa Jay yayi bai ce
masa komai ba ya bar parlon. Wajen karfe biyar da rabi Jay ya kwankwasa ma Khaleesat kofa, bayan ta
bude yace "Ba abinda zaki dauka a can apartment din da zaki koma da shi Nigeria Housemate?" Khaleesat
tace "Ohk, zan dau wasu kayan" Yace "To ki shirya sai in kai ki can ki dauka" Khaleesat na kallonsa a
hankali tace "Pls kar kace zaka siya min ticket ina da kudi a account dina, i will get the ticket" Yayi
murmushi yana kallonta yace "To Hajiya me kudi, kudin zai isa ki mana booking har ni da AJ?" Tana
murmushi ta fara wasa da gefen gyalenta tace "Sae dai kai kadai, ni ai ban san wani AJ ba" Akan kunnen AJ
da ya taho daga parlor zai sauka downstairs, ya tsaya yana kallonta babu fara'a, Jay ya juya ya kallesa yana
murmushi yace "Je ki shirya ina jiranki downstairs Halysaah" Juyawa tayi ta tura kofar dakin a hankali, ko
da Khaleesat ta sauko downstairs ta tarar da Jay yana jiranta, and it's almost 6pm, ya mike suka fita daga
parlon, bayan sun bar compound din a motarsa ya ɗan kalleta yace "Kinga kin kara tsokanar AJ ko?" Ta
marairaice tace "To ni ai ban san yana wajen ba, why is he always eavesdropping?" Jay yayi dariya yace
"Ni dai ba ruwana" Ita dai tayi shiru bata ce komai ba, she can't even wait ta dena ganin AJ she is already
exhausted with him and his problem, she can't wait to stop seeing him, suna isa apartment dinta abinda ya
faru ya dawo mata fresh, kawai sai take ganin kamar trauma din ya dawo mata sabo a kwakwalwarta, lkci
daya duk jikinta ya mutu, haka dai jikinta ba kwari ta tafi dakinta ta fara hada kayan da zata hada shi kuma
Jay ta bar sa parlor yana jiranta, sau uku Safiyya na zuwa gidan debo mata kayanta kwanaki kuma duk
Housemate dinta ne ke kawota, after a while Khaleesat ta gama daukan abubuwan da zata dauka a
akwatinta, sauran kayan dakin duk ta haɗa su waje daya, ko zata dawo kasar ko bazata dawo ba ita dai bata
sani ba, ta kuma bar ma Allah komai, ta gama tidying ko ina a dakin sannan ta fito wajen karfe shidda tana
jan akwatinta a hankali zuwa parlor, kwance taga Housemate dinta kan doguwar kujera ya fara bacci, ta
tsaya tana kallonsa, sai kuma ta tafi kusa da kujeran still looking at him ta ɗan tapping din jikin kujeran
gently, a hankali ya bude ido sai kuma ya mike zaune yace "Kin gama ne?" Tace "Are you sleeping?" Yace
"A'a, kawai na kwanta ne ina wani tunani, it's even time for magrib bari inyi sallah, kema kije kiyi"
Bandakin dake parlor ya shiga ita kuma ta koma dakinta, sai bayan wani minti sha biyar din suka bar gidan,
tunda suka fito gidan Khaleesat tayi shiru, shi ma kuma bai ce komai ba, amma ya lura mood dinta ya
canza, kawai ya sa a rai bazai tafi da ita gida a haka ba, after a while ya ɗan kalleta yace "Would you mind
watching a movie in Cinema tonight?" Khaleesat ta juya ta kallesa, sai kuma ta sauke idonta bata ce komai
ba, yace "Ko baki kallo?" Tace "Ina yi, amma ba sosai ba" Yace "To yau za ki yi" Waje ya samu yayi
parking, ya dau wayarsa ya shiga website din Cinema din dake Maryland to check their schedules for that
day, yayi selecting movie din da za su kalla, da lokacin da za su kalla sannan ya siya masu ticket aka turo
masa ta online, ita dai Khaleesat kallonsa kawai take, yana daga kai tayi saurin dauke idonta daga kallonsa,
ya ci gaba da driving dinsa, without looking at her yace "I hope you will enjoy the movie" Ita dai bata ce
komai ba har suka isa Cinema din, ya siya masu popcorn and lemonade, sannan suka nufi cikin Auditorium
din da za a haska film din da ya siya masu ticket, in some minutes kuma za a fara haska film din, wannan
ne zuwan Khaleesat Cinema na farko a rayuwarta duk da a baya babu irin takuratan da Safiyyah bata yi
akan su je tare da frnds din Safiyyar amma ita dai bata yarda taje, suna shiga Jay ya fara cin popcorn dinsa
kamar abinda ya kawosa kenan, ita dai Khaleesat dama bata wani damu da popcorn ba hakan yasa take ɗan
ci jifa jifa tana kallon film da ake, she is beginning to like the film hakan ya sa ta tattara gaba daya
hankalinta kan film din, after almost 35 mins da fara film din ta juya ta kalli Jay taga bacci yake, ta dade
abu bai bata dariya haka ba, she couldn't believe he is seriously sleeping abun sa, ta rufe fuskarta da
hannunta tana dariya a hankali, she don't know why she feel relieve a duk sanda take tare da shi, there is
never a boring moment with him, gently ta kai hannu kusa da shi ta dauki popcorn dinsa daya, he was still
sleeping ta dinga kallonsa maimakon film din da ya kawota ta kalla, idan yana bacci komawa yake so
gentle and calm, a nan ne kuma ainahin handsomeness dinsa ke fitowa, if there is the sleeping princess then
he will be the sleeping prince, har awa daya da fara film din Jay baccinsa yake kuma ta kyalesa bata tashesa
ba, she watched the movie har sai da ya kusa karewa and she really enjoyed every bit of it,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login