Showing 81001 words to 84000 words out of 152206 words

Chapter 28 - HALYSAAH by Khlst Hydrr

13 May 2026

91

Karfe shidda da yan mintuna drivern
ya sake zuwa ya daukesu ya maida su airport, daga nan kuma suka hau jirgi zuwa garin kano, inda suka
sauka airport din Aminu kano karfe tara saura na dare, this time around ma sai da drivern da ya zo daukan
AJ ya sauka yayi mata magana tare da kai akwatunanta booth, ita dai tana ta tsaye don taxi kawai ta so
dauka da zai kai ta gida, ganin drivern ya bude mata back seat ta karasa jiki a sanyaye ta shiga motar, sai da
suka fita daga Airport din drivern ya kalleta ta madubi yace "Ranki shi dade wani anguwan za a ajiye ki?"
Khaleesat ta ɗan kalli AJ dake zaune gaban motar yana danna wayarsa, sai kuma ta kalli drivern tace "Inda
zan je da nisa, kar in bata maku lokaci gashi dare yayi, duk inda ka samu kawai ka ajiye ni zan samu abun
hawa" Sai a sannan AJ yace "Ce maki yayi sauri yake?" Khaleesat tayi shiru, sai kuma tace "Ni Mariri zan
je" Driver yace "Toh Allah ya kai mu lafiya Hajiya" Bayan tafiyar kusan minti arba'in suka iso Maririn, A
hankali Khaleesat dake kallon drivern tace "Zan iya sauka a nan sai in karasa cikin layin saboda kar ku
shiga baku samu wajen juyawa ba...." Drivern yace "Layin baya bulla ne? In dai yana bulla babu damuwa
za mu samu hanya in sha Allah" Tace "Toh shikenan, nagode" Nan ta nuna masa inda zai bi ya shiga
unguwan, shi dai AJ kallon ikon Allah kawai yake without uttering a word, haka jama'an anguwan suka
dinga bin motar da ya dalle ko ina da haske da kallo, ba ko wani mai mota bane zai yarda ya shiga hanyar
nan da motarsa cause driving is uncomfortable there in baka yi hankali ba sai ka goge motarka, gashi gidan
nasu can ciki ciki ne, at last dai tace "Kawai in ka samu waje a nan zan sauka, ga gidan can" Drivern yace
"Toh shikenan Hajiya" Haka ya samu yayi parking motar, sannan ya sauka zai dauko mata akwatunanta a
bayan booth, ta bude motar ta sauka tana kallon kofar gidansu hankalinta ya ɗan kwanta ganin bata ga
Babanta a kofar gidan ba, kan kace me yara yaran anguwan da suka ga ita ce a motar suka taho da gudu ana
mata oyoyo, haka dai ta samu ta hadasu da akwatunanta sannan ta zaga zuwa side din da Ajay yake, tana
wasa da gefen gyalenta ta kasa kallonsa tace "Thank you so much Allah ya saka da alkhairi" yace "Wanda
ya hada ki jirgi daya da ni zaki ma godiya, Jay kenan" Sai a sannan ta ɗan kallesa, bata dai ce komai ba ta
juya tana tafiya a hankali ta bar wajen, godiya tayi ma drivern ta masa kwatancen unguwan da zai shiga
wanda a nan zai samu hanyar billa zuwa titi, yayi mata godiya shima ya shiga mota sannan ta nufi cikin
gidansu gabanta na faduwa, a hankali tayi raising sack din cement that was use as barrier between the door
and inside of the house zata shiga cikin gidan ta ci karo da kanninta da suka fito yi mata oyoyo da gudu
bayan yara sun shiga da akwatunan ta, a haka suka shiga cikin gidan tare tana Rungume da su, zazzaune
taga kishiyoyin ummanta biyu da 'ya yansu rakacaa a tsakar gidan har a lkcn ba a sauke tuwon dare ba
gashi ana neman karfe goma, kananun yaransu ne kawai suka taso yi mata oyoyo da gudu, muryar wata
makociyarsu dake zaune cikin gidan taji tana cewa "Ikon Allah sannu da zuwa Amarya ashe dai kina hanya
dama" Khaleesat dai kallonta kawai take jin abinda tace, taji kishiyoyin ummanta na cewa "Ai ko dai, kinga
mu da muke gidan ma ko gaya mana ba ayi ba balle mu shiga mu fita tahowar nata ya fasu, kinsan haka aka
maida mu a gidan, to ga dai ta mun ganta kamar an jefota, mun kuma yi murna" Khaleesat ta gaishesu
without waiting for response ta shige dakin Ummanta, zaune ta ganta a bakin kofa Umma dake kallonta
cike da damuwa tace "Khaleesat me ya samu wayarki kusan wata daya? Dama kina hanya shine Abdul din
bai gaya mana ba?" Khaleesat ta rungumeta a hankali tace "Umma lalacewa wayar yayi" Umma ta dago
kanta tana kallonta tace "To shi ya dauko ki a tashar jirgin?" Khaleesat ta sauke idonta tace "A'a" Muryar
kawar Ummanta da taji a dakin yasa ta daga kai don bata ma san tana ciki ba, Khaleesat ta gaisheta da
murmushi, Mama Salame ta amsa da fara'a tace "Ashe dai kina hanya amarya" Khaleesat tace "Amarya
kuma Mama?" Mama Salame tace "Au shi Awdul din bai gaya maki ba dama, ai yau ana saukowa sallan
juma'a aka daura auran ku"




*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment
07087865788 👈🏻, it's better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don
littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*
[5/26, 9:48 AM] khaleesat Haiydar ✍️: Khaleesat ta kwala wani karan da ya gigita Ummanta da Mama
Salame, Umma ta mike da sauri tana kallonta a kidime, haka ma Mama Salame da tace "Innalillahi wa inna
ilaihi raji'un, menene haka Khaleesah?" kishiyoyin Umma duk suka yo dakin a guje su ma don Khaleesat
bata fasa ihun da take kwalawa ba cikin tashin hankali take cewa "Wallahi bana son shi bazan iya zaman
aure da shi ba, na shiga uku na lalace, don Allah Umma ku min rai ku rufa min asiri, wallahi bana son sa"
Umma dai sake baki tayi tana kallon Khaleesat tashin hankali karara a fuskarta gashi ta kasa cewa komai,
daya daga kishiyoyin Umma da ake kira Mama Shatu tana gyara zaninta da ya kusa kwancewa saboda
gudun da suka yi tace "Ji wani gulma da kinibibi? Shi Abdul din ne da ya daukeki ya kai ki kasan turai
karatu yayi ta kashe kudadensa ne baki so yau? A ajiye batun ubanki a gefe, ke abinda ya kashe maki yau
ko kaf kasar da uwarki ta baro za a siyar za a iya biyansa aka ce maki?" Ita ma daya Co-wive din da suke
kira Mama Zubaida tace "A'a rainin wayo mana Shatu, gwara ai a rena mana hankali, don uwarta kasuwa
ne nan da zata cika mana gida da ƙuwa, wannan ai iskanci ne da walakanci" Khaleesat bata fasa kuka da
ihun da take a dakin Ummanta ba tana surutai ita kanta bata san takamaiman abinda take cewa ba tsabar
tashin hankali, Kanninta Noor da Islam kuwa har sun fara kuka su ma a dakin, kan kace me har makota sun
fara tururuwan shigowa gidan, aka tsaya cirko cirko bakin kofar dakin Ummanta ana salallami, Mahaifinta
ne Malam Ali ya shigo gidan yana zazzare ido, shi ma ya karaso da sauri yana tambayar abinda ke faruwa a
gidan, Mama Shatu ta tabe baki tace "Wai er da ta fi kowa ce ta sauka yau daga Amurka shine uwar ke
sanar mata ai an daura aurensu da shi wanda ya kai ta waje karatu har ta dena ganin kowa da gashi, shine fa
ta cika anguwa da ihu da koke koke wai ita bata son auren bazata zauna da shi ba, ga jama'a na ta shigowa
an zata gobara muke, wannan ai tsabar sangarci da iya shege ne" Juyawa Malam Ali yayi ya nufi gun da
ake ajiye itacen girki da sauri ya suri daya ya dawo ya nufo dakin Umma yana cewa "Ina take..." Matan
makota dake tsakar gidan suka hau basa hakuri suna don Allah ya kyaleta, yaki sauraron kowa yana zazzare
ido, Khaleesat na hangosa ta tafi bayan Ummanta da gudu tana kuka ta rungumeta, kanninta ma suka yi
bayan Umma gaba daya suna kuka, Mama Salame ta tsaya tayi bake bake gabansa tace "Haba haba, haba
Malam Ali, meye haka kake kokarin yi?" Yace "Salame ki bar ni dai inci malfar ubanta a wajen, mu zata
tona ma asiri? Ni zata ja ma sabon bala'i da fitinan da ya girmeni?" Mama Salame tace "A'a wallahi baza ka
doketa da wannan rafkeken icen ba ita ba jaka ba, mu je waje Malam Ali" Ita dai Umma kanta na kasa bata
ce komai ba, haka Mama Salame ta samu ta tasa keyarsa ya fita daga dakin tana biye da shi, Mama Zubaida
ta rike haɓa tace "Ikon Allah, mu muke ganin kinibibi iri iri a gidan nan, to in aka bibiya wani ta kyallara
ido ta gani a Amurkan shine zata tona ma uban asirinsa da ke rufe, da can menene yasa ta hakura zata
aurensa? Sai ranan da aka daura aure ta nemi tara mana mutan anguwa tace bata san zance ba? Yau ni nake
ganin iskanci, to ta tsotsi nonon buzuwa ba dole ta iya makirci da kissa ba" Ita dai Khaleesat kuka kawai
take a jikin Ummanta siblings dinta na kusa da ita suna taya ta, Mama Salame ta sake labulen dakin Umma
duk don matan dake tsaye bakin kofar su kama gabansu, Umma ta juya tana kallon Khaleesat gaba daya ta
kasa cewa komai, zamewa kasa Khaleesat tayi ta hade kanta da gwiwa tana kuka kamar ranta zai fita tana
cewa "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, na shiga uku na lalace" a sanyaye Umma ta tafi gefen katifar dakin
ta zauna ta kasa cewa komai. Karfe biyun dare Umma na zaune kan darduma da carbi a hannunta,
Khaleesat ta tsallake kanninta ta fito daga cikin net din da take kwance bayan ta tuna ko isha'i bata yi ba,
tunda Mama Salame ta daura mata net tace ta shiga ta kwanta wajen karfe sha daya take kwance duk da ba
bacci take ba, don ko bacci barawo bata gani ba, amma tayi shiru cikin net din tunani iri iri na yawo a
kanta, gaba daya ta ji kamar hawayenta ma ya kafe, har a lkcn babu maganar da ya hadata da Ummanta,
tana jin jiri da zazzabi ta nufi kofa zata fita ta dauro alwala, Umma dai ta bi ta da kallo, bayan ta dauro
alwalan ta dawo ta saka hijab dinta ta tada sallah, bayan ta idar tayi nafila raka'a biyu, tana zaune kan
darduman ta jingina da bango tayi nisa tunanin da take, gani take kamar a mafarki ake sanar mata an daura
mata aure da Abdul amma ta ki farkawa daga mummunan baccin nan har yanzu, muryar Ummanta yaji ta
kirata a hankali, Khaleesat ta juya ta kalleta amma ta kasa amsawa, Umma ta mike ta koma kusa da ita ta
zauna tana kallonta, cikin sanyin murya tace "Me ya faru kuma tsakaninki da Abdul din Khaleesat? Wani
abun ya kara maki? Me yasa kika ce baki son auren?" Khaleesat ta fashe da kuka a hankali tace "Umma
wallahi bana son sa, bazan iya zama da shi ba, in aka ce za a kai ni gidansa zan iya mutuwa wallahi, don
Allah Umma ku taimakeni ku yi min rai" Umma ta kasa ce mata komai hawaye ya cika idonta ta fara
gogewa da hijab dinta, Khaleesat ta daura kanta kan kafadar Ummanta tana kuka me tsuma zuciya tace
"Don Allah ku taimakeni Umma, bazan iya ba wallahi" Umma ta rungumeta tana patting bayanta ita ma
hawayen na sauka idonta amma bata iya ta ce mata komai ba, they sat there for almost 40 mins, jin tana
sauke numfashi a hankali Umma ta gane bacci tayi, a haka Umma ta zauna wajen Khaleesat na jikinta don
bata son tashinta har kusan lokacin sallahn asuba. Da safe wajen karfe tara Umma ta shigo dakinta rike da
cup din kunu da kosai a roba, ta karasa kusa da Khaleesat dake kwance gefen katifarta ta ajiye mata sannan
ta zauna cikin kwantar da murya tace "Ta so ki ci ko kadan ne Khaleesat" Khaleesat dai kallon cup din
kunun kawai take, lkci daya hawaye ya cika idonta, Umma dai ta sunkuyar da kai, Islam ce ta shigo dakin
rike da paracetamol da Umma ta aiketa ta siyo ma yayar tata, ta zauna kusa da Umma tace "Umma ga
maganin na siyo ma Aunty" Umma ta amsa ta ajiye a gefenta tace "Tashi ki je ki karasa min aikin da na sa
ki" Islam dake kallon Khaleesat ta mike a hankali ta fita daga dakin, Umma ta maida dubanta kan
Khaleesat tace "So kike ki sa ma kanki wani ciwon ne Khaleesat nima ki sa min damuwa? Ki tashi ko
kunun ne ki sha" Khaleesat ta girgiza mata kai cikin rawan murya tace "Ni bazan iya sha ba Umma" a
sanyaye Umma tace "Toh ya kike son in maki Khaleesat?" Umma ta kasa ci gaba hawaye ya fara sauka
idonta ta dafe kanta, kuka kawai Khaleesat take tana kallon Ummanta, Umma ta dake tana share idonta tace
"Ko wajen Nenne zaki sai ki gaya mata ki ji abinda zata ce, ni kin san babu abinda zan iya yi akan lamarin
nan Khaleesat" Ita dai Khaleesat bata ce komai ba, Umma ta mike a sanyaye ta fita daga dakin don juye
mata ruwan wankan da ta dora mata a kan wuta yana ta tafasa, a haka ta ta dawo ta samu ta lallabata ta ɗan
sha kunun sannan ta tafi waje yin wanka, kafin ta fito har Umma ta fiddo mata kayan da zata sa tayi tagumi
tana jiranta, karfin hali kawai Khaleesat take amma ji take kamar zata iya collapse at anytime, bayan ta
shirya Umma tace "Amma bana son yan gidan nan su san inda zaki, kar su gaya ma Malam" Khaleesat ta
jinginar da kanta da bango, a hankali tace "Umma bazan iya zuwa ni kadai ba don Allah ki rakani" Umma
tayi shiru, can tace "To zan fita in shiga gidansu Er Lami in jira ki a can, bana son su ga mun fita tare,
bayan na fita da minti goma kema sai ki fito" Kai kawai Khaleesat ta gyada mata, Umma ta mike ta dau
hijab dinta ta saka sannan ta dora nikab ta fita daga dakin, Su Mama Shatu da Mama Zubaida suna ta girka
abincin siyarwansu da yaransu za su fita talla da shi, tace masu zata shiga makota sannan ta fita, duk suka
bi ta da kallo sun tabe baki, Mama Shatu tace "Ma ji ma gani dai, a sanda ake mana fafa an tura 'ya kasar
waje ga namu yaran a zube ai babu bakin cikin da ba a kuntsa mana ba" Mama Zubaida tace "Sun gana
tattatse ɗan mutane rana daya su fito su ce basu san zance ba, ke ina kika taɓa ganin anyi haka? Ai na so
Malam ya rarrade shegiya jiya da daddare, to dai ba kanta kadai zata ja ma babban magana ba, har shi
Malam din" Duk Khaleesat na jin su, ita dai tana zaune ta jinginar da kanta da bango tana sauke numfashi a
hankali, bayan minti goma da fitar Ummanta ta tashi da kyar ta fiddo gogaggen Hijab dinta ta saka sannan
ta dora Nikab ta fita daga dakin, tunda ta fito suke kallonta, a haka ta nufi hanyar fita daga tsakar gidan tana
ji kamar iska zai kadata ta fadi. Gidan da Ummanta tace zata jirata ta nufa, ta samu Ummanta a tsakar gida
tana jiranta yan gidan ma duk basa nan, Umma ta taso suka fita daga gidan, tafiyar kusan minti sha biyar ne
zuwa gidan Nenne daga gidansu, Nenne ta ajiye tsintsiyar hannunta tace "Dawowa yayi da ita daga inda
take karatun don an daura aure?" Umma ta zauna kan tabarman tsakar gidan ta cire Nikab din fuskarta ta
gaida Nenne, Khaleesat ta zauna gefen Ummanta, Nenne ta amsa tace "Ai dama nace ko da ta dawo sai ta
huta an kintsa ta kafin ayi maganar wata tarewa tunda yace baya bukatar taron komai, amma baza mu dau
yarinya haka kawai ace an je kai ta ba" Umma dai tayi shiru bata ce komai ba, a hankali Khaleesat ta cire
Nikab din fuskarta ta ajiye, Nenne ta ɗan duka tana kallonta tace "Lapiya naga idanuwanta sun kumbura
haka, me ke faruwa?" Umma ta sauke ajiyar zuciya ta kasa cewa komai, A fusace Nenne tace "Magana
nake ku ka min shiru fa? Meye haka aka shigo min da ita da kumburarrun ido" Cikin rawan murya
Khaleesat tace "Nenne ni bana son sa, bana son auren..." Nenne ta saki baki tace "Baki son auren kuma?"
Khaleesat ta gyada mata kai hawaye wasu na bin wasu a kuncinta, Nenne ta nemi waje ta zauna tace "Atoh
dai, ni dama shegen bai taɓa kwanta min ba, amma abun dubawa a nan shine na isa da Alin? Ashe ma ba er
banza bace ni a gunsa kenan" Nenne ta mike ta shiga dakinta ba a dau lokaci ba ta fito ta dire wani babban
ledan hannunta sannan ta bude tace "Kun dai ga duk wata shegiyar kyautarsa da yake kawo min ban taɓa
amfani da ko daya ba duk na tara masa kayansa waje daya, ga atamfofinsa nan da turarurruka da tarkace, ba
ruwana ban yi amfani da su ba, ke ma Zahra'u inda abunsa da kika san ya taɓa baki ki tattaro su waje daya,
shi Ali ina ma yayi amfani da nasa shi ya sani, sai ya shiga kasuwa da wuri wuri" Ita dai Umma tayi shiru
bata ce komai ba, Khaleesat kuwa kuka take a hankali, Cikin sanyin murya Umma tace "Kin mance abinda
ke kasa ne Nenne, ai yanzu ba maganar wai abinda ya bamu bane damuwar" Nenne tace "Yo ina ruwana da
abinda ke ƙasa, ko ina ruwan yarinya da abinda ke kasa? Sai a ma jikata auren dole kike nufi kenan? Ni fa
tun asali katon mutumin nan bai min ba sam, ayi mutum ba fara'a ya shigo maka sandan sandan ya fita
gansan gansan? A duba fa wannan lamari, da kyar kaga murmushinsa kamar rikakken ɗan ta'adda da aka
kusa yi ma preedom, yo wannan uban kudi na ubansa wa ma yasan ko ta'addancin suke da garkuwa da
jama'a, hatta ruwan gidana gansamemen mutumin nan bai taɓa sha ba, yanda na ajiye masa haka yake barin
min tsiyata bai san yarana mata ruwan gora suke siya min ba ya zata durawa nake, haka zai zauna maka
kamar sarki yayi ta danna waya ga gidan er banza ya shigo, to ban isa da Ali ba kannensa mata ma basu isa
da shi ba, shi kawai ta kansa yake a rayuwar nan baya duba makomar er da ya haifa a cikinsa, ko dan yaga
yaran rakacaa an haifa masa ne ba kwantrol oho, gashi ba jin maganar yayyin uban nasa zai yi ba balle ince
ku je ku samesu, in kuma muka ce mu tafi mu kai rahotu gidan yan sanda daga karshe mu za a kulle, to ni
Ramatu ya zan yi? Amma dai ba komai zan aika a kira min Alin anjima, hatta batun daurin auren sai jiya da
za a daura muke samun labari"

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login