Showing 147001 words to 150000 words out of 152206 words

Chapter 50 - HALYSAAH by Khlst Hydrr

13 May 2026

94

hankali yace "Kiyi hakuri, amma Allah ya sani ina son ki, in ma baki
yarda ba i owe you no explanation tunda Allah shi ya sani, kuma today should be ur first and last warning
Khaleesat.... I mean in ur life do not ever ever dare compare me with any stupid guy born of a woman, kar
ki sake kawo min zancen wani ɗan iska ko shi wanene a kunne na, sannan bazan yi taking zaman da ku ka
yi tare da shi and whosoever da kuma alakar ku personal ba because you are my wife now, duk wannan ya
zama pass and shi ne looser, kuma har abada babu wata alaƙa da zai sake hada ki da shi don ubansa har
duniya ta nade kuwa, ba wai ban ji zafin alakar da kika yi creating da su a America bane a raina, fadin zafin
da naji ma is just an understatement wallahi, amma considering the fact that you are my wife yasa nayi
letting bygone to be bygone, so let me keep using that to calm my self kar in masu abinda ke raina...." Wani
mugun tsanarsa ne ke karuwa a ran Khaleesat jin kalmomin da ke fitowa bakinsa, wasu hawaye masu zafi
suka dinga sauka idonta tana tausayin kanta da irin monster din da Allah ya bata as miji, kokarin kwace
kanta take yi a jikinsa zata sauka daga kan gadon yaki saketa yace "Ohk bokare min za kiyi don ina baki
hakuri? But i said i am sorry, and i promise i won't hurt you again, na dena dukan ki...." Ƙin ce masa komai
tayi tana kuka a hankali, ya kwantar da ita kirjinsa yana shafa gashinta a hankali yace "Billah ina son ki
Khaleesat, duk abinda kika ga ina maki saboda ina son ki ne, but kin ki bani hakkina saboda ke akwai wani
plan din a xuciyarki, probably ma su suka koya maki haka" Daga kai Khaleesat tayi ta kallesa tsabar bakin
ciki bata san sanda tace "Ai ba kowa ne bashi da aikin yi kamar ka ba" Shiru yayi yana kallonta babu ko
kiftawa, ita kanta shirun tayi gabanta na faduwa don bata san sanda kalman ya fito bakinta ba, Instead sai ji
tayi yayi kasa da murya kamar me rada yace "Where is the Lubricant?" Sosai gabanta ya fadi jin abinda
yace, yana rungume da ita jikinsa ya bude bedside drawer kamar yasan nan din ta ajiye kuwa, ya laluba ya
dauko, shesshekan kuka ta fara yi zuciyarta na bugawa, yayi kasa da murya yace "Kinsan tsinuwar Allah
kike tara ma kanki kuwa?" Cikin kuka tace "To ai ba ni bace" Yace "To waye?" Muryarta na rawa tace
"Wallahi ban sani ba" Cikin kwantar da murya yace "Promise me today will be different plss Baby" Ta kasa
cewa komai hawaye masu zafi na sauka idonta ga faduwan da gabanta yake yi, gently ya fara cire kayan
baccin jikinta yana kallon kwayar idonta cikin duhun dakin, a wannan dare Abdul bai yi bacci ba tsabar
bacin rai, sai dai bai hantareta ba bai zageta ba, bai kuma doketa ba, haka ya mike ya fice kawai ya bar
mata dakinta ya koma nasa, ya shiga bandaki ya sakar ma kansa ruwan sanyi duk da mugun sanyin da ake a
garin, bayan ya fito ya saka Pajamas dinsa ya kunna karatun qur'ani a wayarsa ya kwanta amma ko rintsawa
bai yi ba har asuba. Tunda Khaleesat ta idar da sallan asuba take zaune kan darduma bayan ta gama azkar
dinta, gaba daya jikinta a sanyaye yake, zuwa yanxu kam sosai lamarin nan ya fara bata tsoro, ko baccin
kirki bata yi ba daren jiya tsabar yanda abun ya tsaya mata a rai, kawai tayi deciding tayi amfani da
abubuwan da Nenne ta kawo mata zuwa anjima, sai da gari ya waye sosai sannan ta mike tana tafiya a
hankali ta fita daga dakin zuwa parlor, sosai gabanta ya fadi ganinsa zaune a parlon da cup din shayi a
gabansa, ta sunkuyar da kanta zuciyarta na bugawa ta tafi ta durkusa ɗan nesa da shi a hankali tace "Ina
kwana" Maimakon ya amsa sai ji tayi yace "Meye nake perceiving a cikin kitchen kamar maganin
gargajiya?" Khaleesat ta daga kai ta kallesa, shi ma kallonta yake fuskarsa babu yabo babu fallasa, rasa me
zata ce masa tayi tana wasa da fingers dinta, a fusace yace "Bakya ji na ne?" Bakinta na rawa da kyar tace
"Nenne ce ta kawo min" A takaice yace "Na menene?" Ta sauke idonta tace "Magani ne kawai, dama ta
saba bani in dinga amfani da shi a gida" Mikewa yayi yace "Mu je ki bani su" Ta shi tayi kamar munafuka
ta nufi kitchen din ya bi bayanta, ita kanta taji kamshin itatuwan da ta shiga kitchen din, ta bude inda ta
ajiyesu ta dauko, ya mika hannu, ta karasa ta basa, yace "Ba a min amfani da irin wa ennan abubuwan a
gida" Kai kawai ta gyada masa, fuska daure yace "Kin ji me nace maki? Kar ki sake amsa idan ta baki" A
hankali tace "Na ji" Juyawa yayi ya fice daga kitchen din ya koma parlor ya zauna, ya ajiyesu nan kasan
tiles, tana fitowa daga kitchen yace "Get ready za mu fita, kuma kar ki bata min lokaci" Cikin sanyin murya
tace "Toh" Dakinta ta tafi, bayan kusan minti talatin sai ga ta ta fito cikin shiri, dai dai nan shi ma ya fito
daga dakinsa rike da wayarsa da car key, yana gaba tana biye da shi suka shigo parlor, ya dau ledan
magungunan da Nenne ta kawo mata ya nufi kofar fita daga parlon ita dai tana biye da shi a baya, a booth
dinsa ya saka ledan magungunan, sannan ya zaga zuwa driver seat, ita ma ta shiga front seat, bayan ya
gama warming motar ya fita daga gidan. A sanyaye Khaleesat ta fito daga Office din Dr Mariya with
different thoughts running her mind, ta ɗan juya ta kalli Abdul da ke bayanta shi ma ya fito office din
likitan, ƙin kallonta yayi, hakan ya sa ta ci gaba da tafiyarta slowly, sai ga Dr Mariya ita ma ta fito daga
Office din zata masu rakiya zuwa parking space, hira suke yi kawai da Abdul suna tafiya a tare, ita dai
Khaleesat na can gabansu, har dai suka fita daga reception din hospital din suka karasa parking space, Dr
Mariya na kallonta tana murmushi tace "To amarya plss inji labari opposite of this kin ji? There is nothing
wrong with you, In kinyi amfani da duk shawararin da na baki komai zai tafi dai dai in sha Allahu, hakuri
kawai za ki yi it's always like that dama, Allah Ubangiji ya bada zaman lafiya, in dai na samu lokaci zan zo
har gida mu gaisa" a hankali Khaleesat tace "To Nagode Aunty, Allah ya kawo ki lafiya" Dr Mariya na
murmushi tace "Ameen" Sai kuma ta kalli Abdul tace "To Barrister ku gaida gida, ina kuma tabbatar maka
in sha Allah matsalar ta zo karshe tunda kaga mun dade ina magana da ita, kuma hopefully ta dau duk
abinda nace mata" Yace "Thanks for your time Dr" Zagawa yayi ya shiga driver seat, Khaleesat kuma ta
shiga front seat, ya tada motar suka bar hospital din, har suka yi nisa bai ce mata komai ba, ita ma dae shiru
tayi tana ta tunane tunane, sae da taga unguwan da suka shigo tayi realizing gidansu ya kawosu, bayan yayi
parking ya sauka motar, ita ma ta sauka, booth ya tafi ya bude ya ciro ledan da Nenne ta kawo mata, da
mamaki tana kallonsa tace "Ina zaka kai wannan?" A takaice yace "Momy zan kai ma, naga tana dealing da
irin abubuwan nan, she can use it if she want, ke dai baza kiyi amfani da su ba a gidana" Khaleesat ta
marairaice masa tace "Noo pls, ni dai gwara kayi disposing dinsu don Allah" Fuska daure yace "Bazan yi
disposing din su ba" Bata san dama haushinta ne fal zuciyarsa ba bayan Dr Mariya ta dubata ta tabbatar
masa lafiyarta qlau babu wani abu da yake hindering passage dinsa, everything is normal, kawai hadin kai
taki basa, Khaleesat ta sunkuyar da kai a sanyaye bata sake cewa komai ba, ya nufi entrance din gidan nasu,
tana tafiya a hankali ta bi bayansa har suka shiga parlorn gidan, da mamaki Momy ke kallonsu tace "A'a,
daga ina ku ke da safen nan, sannun ku da zuwa" Abdul ya zauna ya gaisheta, ta amsa tana kallon Khaleesat
da ta zauna kasan carpet tana gaisheta, Momy ta amsa da fara'a sosai fuskarta tana welcoming dinta, Momy
na kallon Abdul tace "Amma ba daga gida ku ke ba ko" Yace "Eh, daga asibiti mu ke" Da mamaki Momy
tace "Asibiti kuma, waye ba lafiya?" A takaice yace "Bata ji dadi bane, amma da sauki" Momy na kallon
Khaleesat tana murmushin karfin hali tace "Allah sarki, sannu Mamana, Allah ya kara lafiya" Sai kuma ta
kalli Abdul tace "Ko wajen Dr Mariya ku ka je?" Yace "Eh" Mikewa yayi ya ajiye mata ledan magungunan
kusa da ita yace "Kakarta ce ta kawo mata wnn jiya, ni kuma kin san bana son irin abubuwan nan na
gargajiya shi ne na kawo ko zaki yi amfani da su ke" Momy tayi kuri da ido tana kallon ledan da mamaki,
sai kuma ta dauka ta bude da sauri, lkci daya ta saita kanta tana murmushin karfin hali tace "Allah sarki, ai
kam nasan halin ka baka san itatuwa, zan ko yi amfani da su dama nawa sun kare tas" Ita dai Khaleesat
kasa dago kanta tayi, Momy was shock har cikin ranta amma tayi karfin hali take wayancewa, can ta kalli
Khaleesat tace "Amma baki fara amfani da su ba ko" Khaleesat ta girgiza kai ba tare da ta kalli Momy ba
tace "A'a jiya ta kawo min banyi amfani da komai ba" Momy tace "To to, hakan yayi" Ta kalli Abdul tace
"In dai an samu wasu a dinga kawo min kawai" Mikewa yayi yace "Za mu koma Momy" Momy tace "Da
wuri haka? To wai ka koma aiki ne?" Yace "Ban koma ba tukun" Momy tace "Toh shikenan, Allah ya tsare
nima in sha Allahu ina nan shigowa in kawo mata turarrukan wuta da na jiki" Shi dai bai ce komai ba ya
nufi kofa, Khaleesat ta mike tana yi ma Momy sallama, Momy duk fa a rude take ta gyada mata kai kamar
kadangariya tace "To Mamata, sai na shigo, ku gaida gida, maza bi sa ku tafi" Daga haka Khaleesat ta bi
bayan Abdul da har ya fita daga parlon, Momy ta dau wayarta har tana tuntube ta shiga dakin dake
downstairs ta fara kiran Dr Mariya don family Dr dinsu ce for long, Dr Mariya na dagawa suka gaisa da
Momy cikin fara'a, Momy tace "Yanxu Abdul ya zo min da matarsa yace daga asibiti suke, naga duk ba shi
da walwala nasan yana da zurfin ciki bazai gaya min ko menene ba, shi ne na kira inji lafiya dai ko Dr? Ko
juna biyu gareta? kinsan dama yace bai son haihuwa da wuri, in dai juna biyu ne da ita gwara in yi dubara
in dawo da ita wajena don ni dai ina son ganin jikana, kar yaje ya bata wani abu da zai lalata cikin taje ta
sha" Dr Mariya tayi dariya sosai, bata boye ma Momy komai ba tayi mata bayanin dalilin zuwansu Asibiti,
Momy ta sauke wani irin ajiyar zuciya ba tare da tasan tayi hakan ba, sai kuma ta bige da cewa "Innalillahi
wa inna ilaihi raji'un, kinsan yarinya ce fa, duka duka Allah yasa tayi shekara ashirin, har da yarinta abun
nata dae" Dr Mariya tace "Wallahi nima haka nace masa don dae in kwantar masa da hankali kar ya dinga
jin haushinta, amma shekara ashirin ai ba yarinya bace Hajiya, aka ma er shekara sha biyar aure ta zauna
balle er shekara ashirin, ni dai na bata shawarwari Allah ya sa tayi amfani da shi, kar tun yana hakuri da ita
hakurinsa ya kare a fara samun matsala gaskiya" Murmushi kawai Momy take tana Allah Allah su gama
waya da Mariya ta kira Godiya, daga karshe Momy tace "To Allah ya sa ta dau shawaran naki Dr, kuma zan
yi ma yayarsa magana ita ma taje gidan anjima ta kara nutsar da ita in sha Allahu" A haka Momy suka yi
sallama da likitan, Momy tayi wani dariya tana girgiza kai sannan ta fara dialing number Godiya, aikin
miliyan biyu ai ba wasa bane, sun dade suna waya da Godiya a waya, daga bisanni suka yi sallama, Momy
na ta murmushi ita kadai bayan Godiya ta sake jadadda mata Malamin yace lokacin ma da ya dibar masu za
ayi sakin baza a kai haka ba, don gab ake da yin sakin cikin kwanan nan kuwa, Meemah da ta shigo dakin
ta tarar Momy na waya ta zauna duk tana sauraron conversation dinsu har suka yi sallama tace "To
shikenan Momy yanxu haka zai saketa ba mu ci ubanta ba na huce haushin abinda yayi min a kanta?"
Momy tace "Ke wa ke ta wani cin ubanta? Ance maki shi ne a gabana sai kace wata yarinya? Ni dai in na
samu Abdul ya rabu da ita an gama min komai, kuma hakan kadai ne a gabana yanxu ba shashanci irin naki
ba, ke kinsan menene hada iri da talaka kuwa? Ke kiji matsiyaciyar kakarta har ta fara shige shigen
malamai tana kawo mata asiri banda Allah yasa Abdul din ya gani, to karyarsu ta sha karya wallahi, cikin
kwanan nan zai kora masu ita bayan ya saketa" Mikewa Meemah tayi ta fita daga dakin don kwata kwata
ba haka ta so ba ita, so kawai tayi a bar ta tayi ma Khaleesat dukan mutuwa ko zata jin sanyin abinda Abdul
yayi mata a kanta.
[6/25, 8:35 PM] khaleesat Haiydar ✍️: Bayan Khaleesat sun koma gida tayi wanka sannan ta canza kaya
tayi sallan azahar ta fito ta dora lunch a kitchen, tana ta zaune parlor bayan ta gama hada komai na girkin
tayi tagumi tayi nisa tunanin da take bata san sanda ya fito daga dakinsa ba, ya karaso parlon yana kallonta
yace "Burden din mutane nawa ne a kanki da kike tagumi haka" Juyawa tayi ta kallesa tana gyara zamanta
amma bata ce masa komai ba, tunda suka dawo gidan sai yanxu yake mata magana bayan ya gama cika da
batsewan sa kenan, Yace "I am asking you" Shiru tayi still bata ce komai ba, ya zauna kan kujeran dake
facing dinta yace "Mutane nawa kike ciyarwa da kike tunanin yanda za ki yi?" Bata san sanda tayi
murmushi ba tana wasa da fingers dinta, kamar bazata ce komai ba, sai dai a hankali tace "Ba ina son zan yi
magana da frnd dita Sophie ba kace bazan yi ba" Yana kallonta yace "Kiyi magana da ita ki ce mata me?" A
hankali tace "Babu komai, i am just missing her kawai" Wayarsa dake hannunsa ya cire ma lock sannan ya
mika mata yace "Speak to her in my front" Amsan wayar tayi ta shiga contact dinsa ta duba number
Safiyyah sannan tayi dialing, yana kallonta yace "Sa a handsfree" Ba musu Khaleesat ta saka kiran a
Handsfree, yana fara ring Safiyyah ta daga, a hankali Khaleesat tace "Sophie" Safiyyah tace "Omg
Khaleesat? Wallahi I've been expecting your call for so long kawata amma shiruu, Ya Allah, number Abdul
din ne wannan?" Khaleesat ta ɗan kalli Abdul da ya kafeta da ido tace "Um, nasa ne" Lkci daya har
Safiyyah ta gane wayar a handsfree yake sanin wanene Abdul, a hankali tace "Ohk then, ki gaida min shi
sosai pls, but can i come over in gan ki if he will permit that pls?" Cikin sanyin murya Khaleesat tace "I
will speak to him about it" Safiyyah tace "Alright dear, take care of ur self, i will be waiting for ur
feedback" Khaleesat tace "In sha Allah" a haka suka yi sallama, safiyyah ta kalli wata aunt dinta dake kusa
da ita cike da bakin ciki tace "Wallahi nasan yana gefenta shi yasa ban tofa nawa ba, Innalillahi wa inna
ilaihi raji'un, Her marriage and Abdul is the worst thing that have happened to me last year, yanxu shikenan
ta zama matarsa duk guje mata hakan da na dinga yi, ba irin addu'an da ban sa ta akan Allah ya rabata da
Abdul ba, nayi ta mata sha'awan Housemate dinta amma Allah ya riga ya kaddara Abdul ne mijinta, dubi
yanda take min magana kina jin muryarta kinsan tana cikin damuwa da matsin rayuwa, gashi karshen watan
nan za mu koma school ban kuma ga alamar zai bar ta taci gaba ba" Safiyyah ta fara matsar kwallan bakin
ciki, ita dai tana jin babu wanda ya kai ta bakin ciki da auren Khaleesat da Abdul, Abdul ya amshi wayarsa
da Khaleesat ke mika masa bayan tayi sallama da Sophie, a hankali tace "Thank you" ajiye wayar yayi yace
"Sai hankalin ki ya kwanta yanxu tunda kin yi magana da kanwar Baabarki ko" Cikin sanyin murya tace
"Plss ina neman favour din ka barta ta zo wajena don Allah, i am missing her so much" A takaice yace
"Baza ta zo ba, in barta ta zo ta ji dadin zuga ki kamar yanda ta saba? you think i don't know saboda tasan
wayar a Handsfree yake shi yasa tayi composing words dinta without saying anything silly yanxu, duk ba
ita bace ta fara ruining tunanin ki, very stupid girl" Khaleesat dai kallonsa kawai take hawaye cike idon ta,
kawai tayi deciding tayi masa maganar abinda ya tsaya mata a rai all this while, hoping Allah zai sa yayi
considering din request din nata, cike da karfin hali tace "Amma don Allah Yaya Abdul kar kace bazan
koma makaranta ba, we are resuming end of this month kuma kasan wannan shekaran kadai ya rage min
plss kar ka bari inyi asaran shekarun da nayi a baya, kayi considering expenses din karatun plss, in kuma
zai yiwu kawai a min transfer ba lallai sai can kasar ba..." Hawaye na sauka idonta ta kare maganar tana
kallonsa, ya mike yace "You think i am stupid da zan bari ki kara komawa America ki ci gaba da karatu? to
ai kai ki can ma da nayi tun farko i deeply regret doing so, nayi da na sanin kai ki karatu America da har ya
bude maki ido, kuma tunda ba kudin ki ko kudin wani naki aka kashe ba all this past years ina ruwanki da
asaran da za ayi? How is the lost going to affect you da kike nagging akan expenses din? Ina ce kudina ne
sai ko kudin mahaifina? So babu ruwanki, na gwammace inyi asaran duk abinda na kashe maki da dai ki
koma kasar nan, kuma kika kuskura kika sake kawo min maganar karatu sai nayi mummunan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login