Showing 66001 words to 69000 words out of 152206 words
kofar Jay
ya shigo, kallon Khaleesat yake yace "Kin sha maganin Housemate?" Ta gyada masa kai without looking at
him, Safiyyah ta kallesa cike da damuwa tace "Ashe kuma iftila'in da ya faru kenan jiya Yaya Housemate?
To Allah Ubangiji ya tsare na gaba, ku kuma Allah ya saka maku da alkhairi ya baku ladan hidimar da ku
ke yi da kawata don bata da kowa a garin nan sai Allah sai ni da ku, kuma she is not longer safe in this state
don Abdul can be cunning, azzalumi ne mugu, nasan har yanzu yana labe garin nan bai tafi ba, kuma ba
imani ne da shi ba ina jin tsoron next move dinsa, Allah kadai yasan sau nawa ya koma apartment din nan
yaga babu kowa ciki" Jay dai ya ɗan yi murmushi yace "She will remain here har ta gama exams dinta in
sha Allah" Khaleesat ta kallesa ta girgiza kai cikin sanyin murya tace "Bazan iya exam din ba, Nigeria nake
son tafiya" Safiyyah ta mata wani kallo kamar zata ce in tana da kudin jirgi ta tafi sai dai kuma kawai tayi
shiru tana hararanta, Jay ya kwantar da murya yace "Saboda me baza ki iya exam ba Khaleesat, stop saying
that pls, in sha Allah zaki yi jarabawan ki lafiya, in kun gama sai ki koma Nigeria" Safiyyah tace "Atoh shi
dai na gani, kan wani tantirin ɗan iska take son lalata future dinta, duka duka fa shekarar karshe za mu
shiga yanzu a makarantar" Khaleesat ta sauke idonta hawaye na sauka idonta don tasan baza su gane abinda
take nufi ba, Jay ya sauke ajiyar zuciya yace "Try calming her down Safiyyah, and naga tun jiya bata wani
ci abinci ba ban san ko tafi son abincin Nigeria ne ba, nasa cook din gidan yayi ordering ingredient din har
an kawo, i don't know ko zaki girka mata a kitchen tunda kina nan" Safiyyah tace "To ba damuwa, let me
cook for her" Yace "Alright" a tare suka bar dakin Khaleesat ta bi su da kallo hawaye na bin fuskarta.
Tunda suka shigo kitchen din Safiyyah ke bin ko ina da kallo don the kitchen is so big and well equipped,
irin modernize kitchen din nan, bayan Jay ya fita cook din gidan ya nuna mata ingredients din shinkafa da
miya sannan shi ma ya fita, tuni ta hau girkin a kitchen din. Wajen karfe biyar Safiyyah na daki tare da
Khaleesat hira kawai take mata kamar ba abinda ya faru, ita dai Khaleesat tayi shiru tana kallonta amma
gaba daya hankalinta baya kan hiran, wayar Safiyyah ya fara ring ta jawo jakarta ta ciro wayar ganin
Mustapha ke kiranta ta wani turo baki sannan tayi pick ta sa handsfree tace "Ina wuni yaya" Ko amsa
gaisuwar bai yi ba yace "Waye ya zo ya daukeki a mota Safiyyah?" Safiyyah ta bude baki tace "Ohh haka
matar taka tace maka? to ta manta a jirgi aka zo aka daukeni ba a mota ba, kuma munafurcinta zai kare
mata wallahi" Tsawa ya daka mata yace "Ina maki magana kina min maganar banza? Are you okay?" Ta
wani murguda baki tace "Toh ba ina hanya bane wai, haka kawai dai babu dalili bazan kama hanya in fito
cikin sanyin nan ba yaya, ko ka manta jibi za mu fara exams ne?" Kashe wayarsa yayi, Safiyyah tace
"Allah dai ya tsine ma Surayya albarka, kuma wallahi kafin mu gama exam mu bar kasar nan sai na mata
abinda bazata taɓa mantawa ba a rayuwarta, ko da wasa kuma bazan ma gaya masa abinda ya faru dake ba
kar yayi burgan cewa ki dawo gidansa ya kara ma matarsa extra nama" Ita dai Khaleesat tayi shiru bata ce
komai ba, Safiyyah ta mike ta dau jakarta da gyale tace "Sai na zo gobe in sha Allahu, saura kar ki karasa
cinye abincin ki zauna kina asaran hawayenki akan ɗan daba, ga lambata na sa maki a waya in da wani abu
ko kuma kina bukatar komai kawai ki kirani" Daga haka ta fice daga dakin, Khaleesat ta sauke idonta kasa,
Downstairs Safiyyah ta hadu da AJ wanda shigowarsa gidan kenan tana ɗan murmushi ta gaishesa ya tsaya
ya amsa yana danna wayarsa yace "How are you doing" Tace "Alhmdlh ya karatu" Yace "Fine, ya naki"
Tace "Muna ta fafatawa dai, to fa mun gode da hidima yaya, Allah ya saka da alkhairi da abinda ku ka ma
kawata, Allah ya biya ku" Sai a sannan ya daga kai ya kalleta jin wai tana masa godiya, ita dai ta ci gaba da
godiyar ta ba kakkautawa, Yace "Ameen" Tace "Yaya Housemate din ya fita ne, ni zan koma gida ne
yanxu" Sai ga Jay ya shigo parlon from outside, ganinta yace "Ohk zaki koma Safiyyah?" Tace "Eh wallahi
yamma tayi amma in sha Allahu zan shigo gobe da safe" Yace "To Allah ya kai mu, mu je inyi dropping
dinki" Tuni AJ yayi wucewarsa sama, Safiyyah ta bi bayan Jay suka fita daga parlon tana mamakin inda
karen gidan yake bata gansa ba tun daxu, sai bayan da suka dau hanya tace "Yaya Housemate...." Dariya ta
ba Jay bai jira me zata ce ba yace "I am Jawwad Safiyyah" Tace "To ni dai don Allah kayi dubara ka amshe
wayar da ka ba Khaleesat kar taje ta kira yan gidansu su gigita ta, kaga bamu san ko Abdul din na kasar nan
ba ko ya koma Nigeria, in ta kira suka gaya mata wani maganar da kyar ta iya abun arziki a jarabawan nan"
Jay yayi shiru cause he reason with what Safiyyah is saying, can yace "Haka ne kuma, i will tell her not to
speak to anyone for now, amma bazan iya amsan wayar ba naga kamar it's whiling away her time" Safiyyah
tace "To in da kati a wayar don Allah ka kone sa, in da WhatsApp kayi uninstalling dinsa kaga ta haka babu
wanda zata ma magana, the exams is just for a few weeks, kamar gobe ne za mu gama" Yace "Sure i will do
so Safiyyah" A haka suka isa gidansu ta sauka daga motar ta masa godiya yace "Ki gaida mutanen gidan"
Tace "To za su ji" Yayi reverse ya dau hanyar gida hoping Khaleesat bata riga ta ma kowa magana back in
Nigeria ba. Washegari da safe Jay yayi booking appointment na ganin likita saboda daren ranan ma
Khaleesat dai bata yi bacci ba, yasan dai ba lallai su samu ganin likitan a ranan ba, so he was just helping
her to manage her self with the drugs available, da Safiyyah kuma ta zo sai taji ta nemi zazzabin ta rasa
dama kadaici ne da damuwa suka mata yawa. Ranan monday da safe Jay yayi dropping din Khaleesat
school for her first exam, and he stayed behind har zuwa sanda za su gama don su koma gida tare, kawai
shi dai baya son barin ta ita kadai, Jay is trying his very best na ganin Khaleesat ta sake ranta domin tayi
karatun jarabawanta da kyau kar ta samu matsala, ga kuma Safiyyah dake encouraging dinta a gefe ita ma,
kuma hakan yayi tasiri sosai don ta ɗan sake ranta tana karatun, AJ dai tun ranan da ya shigo ya ganta
zaune a daki har bayan da suka yi Exams uku bata sake saka shi a ido ba, bata san ko yana gidan ba ma ko
baya gidan, ita dai 24/7 tana daki, hatta abinci cook din gidan ne ke kai mata sama yayi knocking ta fito ta
amsa, in ta gama still shi yake zuwa ya amshi tray din, bayan sati biyu da fara exam dinsu ranan suna da
interval Safiyyah ta zo gidan da yamma, abinci ta kawo ma Khaleesat, Khaleesat taji dadi sosai ganin tuwo
ne don dama tun jiya take sha'awan tuwon, Safiyyah tace "Kinga ba dadewa zan yi ba yanzu zan tafi kafin
mutumin can ya fara kirana kamar Surayya ce ta bar gida" A hankali Khaleesat tace "Baza ki bari anjima
kadan ba pls" Safiyyah tace "Wallahi yanzu Ya Mustapha zai fara kirana, bai ma san na fito ba, kuma nayi
order din Lyft ma da zai maidani gashi nan ya kusa karasowa nan, tashi ki rakani kofar gida" Khaleesat ta
girgiza kai tace "Kawai ki tafi za mu hadu schl tomorrow in sha Allah" Safiyyah tace "Wai ke baki gajiya
da zama ke kadai a daki, don Allah ni dai tashi ki rakani kema ki ɗan yi strolling kafafuwanki" a hankali
Khaleesat tace "Baza ki gane ba Sophie, wallahi i am not comfortable staying in this house, na kagu mu
gama jarabawan nan in koma Nigeria" Safiyyah tace "Ae ranan Housemate dinki ya gaya min wai kince
masa zaki koma apartment dinki nace lallai baki da hankali, Allah ma yasa Abdul bai sake gidan ba" Tana
dariya ta kare maganar, sai kuma ta kwantar da murya tace "Kiyi hakuri kawata, nan da sati kadan zaki ga
mun gama exams din in sha Allah, ki kwantar da hankalinki pls, yanzu dai tashi ki rakani" a hankali
Khaleesat ta sauko daga kan gadon ta dau gyalenta suka fita dakin tare da Safiyyah, suna saukowa
downstairs suka tarar da AJ a parlor da Jay, Khaleesat dai ta sunkuyar da kanta don sai yau taga AJ for
almost 2 weeks, ita ta zata ma baya gidan ne, Jay na kallon Safiyyah yace "Are you going soon Safiyyah?"
Safiyyah tace "Eh wallahi Yaya Jawwad Lyft dina yana hanya ya kusa" Yace "Alright, ki gaida mutanen
gidan" Tace "In sha Allah za su ji" Sallama tayi ma AJ ya amsa mata, sannan ta kama hannun Khaleesat
suka fita daga parlon, suna tsaye waje suna jiran karasowar Lyft wata mota ta shiga gidan bayan matukin
motar ya fito daga cikin motar ya bude gate, Safiyyah tayi kasa da murya bayan sun shiga ciki tace "Ke
kinga wani Ride me suna ride Khaleesat? Su dai da masu kudi kawai suke harkar su a kasar nan, in kin
bibiya abokansu ne 'ya yan masu kudi irinsu" Khaleesat dai bata ce komai ba, bayan kusan minti uku sai ga
Lyft din Safiyyah ya iso, Safiyyah ta bude bayan motar ta shiga, Khaleesat ta daga mata hannu, Safiyyah na
mata murmushi tace "Sai mun hadu a schl kawata, kiyi karatu da kyau fa" Kai kawai Khaleesat ta gyada
mata sannan ta koma cikin gidan, duk a dar dar take tafiya a babban compound din gidan, har yau ita dai ta
kasa sakin jiki a gidan nan gani take kamar a kaya ma take she is so very uncomfortable, a haka ta isa
parlon gidan ganin baki biyu dake parlon tare da su Jay wanda da alama abokansu ne Khaleesat ta sauke kai
ta gaishesu, suka amsa da fara'a, ita dai ta nufi stairs, daya daga frnds din nasu taji yace "Bakuwa ku ka yi a
gidan" AJ dake shan fruit salad yace "Eh, yarinyar wani abokinmu ne a Nigeria ta zo jarabawa" Jay ya saki
baki yana kallon AJ da ke ta shan fruit salad dinsa ko ajikinsa, Ita kanta Khaleesat sai da ta ɗan juya ta
kallesa sannan ta wuce sama, abokin na gyara zama yace "Waow, amma da gani da wuri abokin nan naku
yayi aure, ya huta abunsa gashi mu duk mun kasa har yanzu" AJ dai ya ci gaba da shan fruit salad dinsa
yace "Ai kam ya huta, mu ma da munyi auren da wuri duk da mun haifi kamarta ai"
*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment
07087865788 👈🏻, it's better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don
littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*
[5/21, 6:02 PM] khaleesat Haiydar ✍️: Khaleesat na zaune da daddare tana duba course din da za su yi
washegari a laptop dinta, sosai take kewan Ummanta tasan kilan tana ta mata magana ta WhatsApp taji
shiru, she just pray everything is alright back home in Nigeria, duk in wannan tunanin ya fado mata sai taji
ta kasa karatu, haka nan dai ta tsura ma laptop dinta ido, knocking din kofar dakin aka yi ta mike a hankali
ta karasa gun kofar ta bude don tasan Jay ne, sau da yawa sai dai yayi mata knocking bai fiye shigowa
dakin ba, daga nan bakin kofa yake tsayawa yayi mata duk maganar da zai mata, yana kallonta bayan ta
bude kofar yace "Are you sure u are studying for ur next course Halysaah?" Ta gyada masa kai tana
kallonsa, ya ɗan jingina da bangon wajen yace "Erm, sorry about what you overheard AJ saying few hours
ago Halysaah, kinga dalilin da yasa nake barin masa gidan shi kadai ya karata kenan, he is a serious
nuisance... Kiyi hakuri da abinda yace kin ji Housemate?" Khaleesat ta ɗan yi murmushi tana wasa da
gefen gyalenta kamar bazata ce komai ba, sai kuma tace "Ai ni ban ma san tsoho bane sai yau" Jay couldn't
help it but laugh out loud, Khaleesat ta daga idanuwanta tace "Allah kuwa ban san shi tsoho bane, don
wanda ya isa haifata ai tsoho ne" akan kunne AJ da ya fito daga parlon dake sama, tsaye yayi yana kallonta,
tana hada ido da shi ta kulle kofar dakin gbamm, AJ ya kalli Jay dake ta dariya, can ya juya fuuu ya bar
wajen, Jay dai ya bi sa da kallo still laughing, har ransa yaji dadin abinda Khaleesat tace akan kunne Ajayn.
Jay na dakinsa wajen karfe goma da rabi yana duba laptop dinsa AJ ya shigo dakin, sau daya ya kallesa ya
ci gaba da abinda yake, AJ yace "That brat will not continue staying in this house anymore, ka samar mata
wani alternative kawai in ba haka ba in kira gida in fada masu ka kawo mana yarinya tana rayuwa cikin
gidan nan" Jay ya daga kai ya kallesa yace "Ni ai na zata har ka kira ka gaya masu, kuma tunda ba gidanka
bane baka isa kace bazata zauna ta gama exams dinta ba" AJ yace "Ohk zaka sha mamaki" Daga haka ya
fice daga dakin, Jay ya ja tsaki ya ci gaba da abinda yake. Washegari tare Jay ya dauko Khaleesat da
Safiyyah ya kawo su nan gida bayan sun gama exams din ranan, bai shiga compound din ba ya tsaya a waje
yace "I will be going out now, sai na dawo later" Khaleesat ta sauka daga motar tana kallonsa, a duk sanda
baya gidan sai taji gidan duk babu dadi, duk da ko yana nan yawanci yana dakinsa sai in da wani abu ne
yake zuwa kofar dakinta ya mata magana, but she prefer him to be at home always ko da baza su ga juna
ba, duk sanda ya fita sai ta shiga kadaici wani lkcn har da damuwa, kuma in dai zai fita din sai ya gaya
mata zai fita, yau kam she felt relieved tunda tare suka dawo gidan da Safiyyah, yana kallonta yace "Zan
kiyi girkin yau tunda ga kawarki sai ta taya ki?" Khaleesat ta sauke idonta tace "Ohk" Yace "Alright take
care" ta gyada masa kai ya ja motarsa ya wuce, ita da Safiyyah suka shiga gidan, Safiyyah tace "Kai na
dade banga mutumin me kirki irin bawan Allahn nan ba, he is just extra nice, ni dai Allah ya sa it's what i
am thinking" Khaleesat ta kalleta, Safiyyah ta washe maki tana wani murmushi, Khaleesat taki tanka ta,
Safiyyah tace "Kinga kamar jiya muka fara exams gashi saura mana course biyu mu gama, baki ga farin
cikin da nake ba za mu koma gida" Suna shiga parlon gidan suka ga AJ a zaune da kare a gefensa, sosai
gaban Khaleesat ya fadi don tun da ta zo gidan ita dai bata ga karen da idonta ba sai da taji haushinsa wani
lkcn, karen ya mike tsaye yana kallonsu AJ ya masa umarnin ya koma ya zauna, tuni Khaleesat tayi
wucewarta sama, Safiyyah ta tsaya ta gaida AJ da fara'arta, ya amsa yace "How was ur exam?" Tace
"Alhamdulillah, sauran mu kwara biyu, kawai intervals din ne ke da tsayi" AJ yace "Allah ya bada sa'a"
Tace "Ameen" Daga haka ta wuce sama, dakin da Khaleesat take ta shiga, ta rike haɓa tana kallonta tace
"Ni fa karfin halinki mamaki yake ban Khaleesat, ya kina gidan mutane zaki zo ki wani wucesa babu
gaisuwa? Me yasa kike yin haka ne?" Khaleesat ta cire mayafinta without looking at her tace "Don baki ji
abinda yayi min bane jiya, frnds dinsa suka zo gidan yace masu ai ni yarinyar abokinsa ce na zo exam"
Safiyyah ta kyalkyale da dariya har da kyakyatawa tace "To meye a ciki, in bai fadi haka ba so kike su yi
zaton zaman kanki kike cikin maza? Ai nan kare maki mutunci yayi, kinga dai ai abokan za su yi tunanin
baban naki ne da kansa ya kawo ki gidan abokansa ki zauna kiyi exams" Khaleesat ta wani kalleta tayi
shigewarta bandaki, Safiyyah ta zauna gefen gado tana kyakyala dariya tace "To duka duka shekararki
nawa da bazai ce ke 'yar su bace, ni dai ban ga laifinsa ba" Bayan duk sun yi sallah Safiyyah tace "Kin ga
ki tashi mu je in taya ki girkin kafin mutumin can ya fara doka min kira yanzu kamar makaho" a hankali
Khaleesat tace "Ni kamar ma kar inyi girkin, i don't want to go downstairs" Safiyyah tace "Amma ai ko don
saboda Housemate dinki sai kiyi, tunda kika ga haka kilan shi ma yana son cin tuwon da vegetable soup ne"
Khaleesat ta marairaice tace "To ai ni i am not comfortable ne, ban ma taba shiga kitchen din ba fa" Safiyya
ta mike tace "Mu je, ai ni na taɓa shiga har nayi girki" A haka ta ja Khaleesat suka sauka downstairs, da ba
don Safiyyah tace kilan Housemate dinta na son cin abincin ba da babu abinda zai sa ma ta yarda tayi
girkin, har sannan AJ na parlon amma babu karen a kusa da shi, shi dai wayarsa kawai yake dannawa bai
kalli direction dinsu ba, a haka Safiyyah ta ja ta har zuwa kitchen din gidan, after a while suka gama girkin,
Safiyyah tayi take away din wanda zata tafi da shi gida tana kallon Khaleesat tace "Ke ba yanzu zaki ci
abincin bane naga baki zuba ba?" Khaleesat ta girgiza kai tace "Sai anjima" Safiyyah ta tabe baki tace "To
mu je, Allah dai ya sa Yaya Musty bai kirani ba" Suna fitowa main parlor suka tarar babu kowa a parlon,
suka haura sama, kafin su karasa hanyar dakin da Khaleesat take aka bude kofar wani Bedroom din wata
mace da bazata wuce 23 years ba ta fito, English dressing ne jikinta amma kana ganinta kaga Hausa Fulani,
she is so beautiful, yarinyar ta bi su da kallo da mamaki, Safiyyah na murmushi tace "Hi dear" Yarinyar ta
mayar