Showing 54001 words to 57000 words out of 152206 words
daga
parlon wishing dama bata zo gidan ba kilan da haka bai faru ba, da tasan bala'in da za ayi kenan babu
abinda zai fara fitowa da ita daga gida, Safiyyah ta figi dankwalinta zata bi ta, Mustapha ya mata tsawa
yace "Kar ki kuskura ki fita daga gidan nan" Safiyyah ta fashe da kuka tana bubbuga kafa tace "Ni wallahi
yaya na gaji, na gaji kuma haka, na gajiiii, dubi cin mutuncin da matarka ta min daxu kace in kyaleta,
yanzu kuma daga kawata ta zo wajena in mata kitso shikenan sai ta fara kunduma mana zagi ta kamani da
dambe??" Yace "Wuce dakin ki nace" Ita dai Khaleesat tuni ta kara gaba ta bar gidan. That same day wajen
karfe biyar da rabi sai ga Safiyyah ta zo gidan Khaleesat, Khaleesat ta zauna gefenta bayan sun shigo parlor
tana kallonta tace "Ban ji dadin abinda ya faru ba yau Sophie, da na sani da ban je gidan ba ma wallahi"
Safiyyah tace "Ai abun duniya ne ya dameni kamar in hadiye zuciya shi sa nayi ta kiranki ki zo daxu, wai
fa bayan na gama yi maki gyaran gashi na koma gida matar nan kamar jirana take ta kama zagina ta uwa ta
uba a gaban mijinta wai don me zan zubar mata da sauran miyarta dake kitchen, kuma fa kar kice da miya a
tukunyar Khaleesat, wallahi ba komai ciki sai wani guntun miya da yayi tsami sai bugawa yake, ni kuma na
wanke na dafa indomie na ci kafin in taho nan daxu in maki gyaran gashi, Ya Mustapha ya hanani cewa
komai ya bani hakuri na wuce daki, a banza tunda dai shi ma har uwayensa ta zaga, shine bata daddara ba
da kika zo zata sake hadamu ta zage ga yan iska sai muyi shiru muna kallonta, ni wallahi so nayi ace ma na
cire mata hakora biyu ta dawo wawulo, amma dai a juri zuwa rafi wallahi sai na mata illar gaske kafin in
gama karatu a kasar nan, dama tun 3 weeks ago da muka zo muka kawo maki abinci da ni da Y Mustapha
ta kara kullatata ta kara tsanata tunda har yau tayi tunanin da akwai wani abu tsakaninki da Mustapha, ko
ga maciji fa bama yi da ita a gidan" Khaleesat ta sauke ajiyar zuciya ta kamo hannunta tace "Ki dai dinga
hakuri plss Sophie wataran sai labari, da ni ce ke ma wallahi bazan dinga biyeta ba a gidan nan" Safiyyah
tace "To ai ba kowa ke da matattciyar zuciyar da kare ya lashe irin taki ba, amma wallahi tayi kadan in ki
biye mata, tana ce min kule zan ce mata casss don ubanta, an gaya mata ita ta isa ta shiga tsakanina da
Mustapha? Cousin dina ne fa, Uwarsa ce ta sha nono ta bar ma uwata, Babansa kuwa Cousin din babana ne
halaq malaq, ina ga bai taɓa zaunar da ita ya mata bayanin nan dalla dalla bane, kuma ya ci sa'ar bana kai
karar abinda matsiyaciyar matarsa ke yi min gida, don wallahi da tuni an dau mataki, amma dai bari mu yi
hutu in koma Nigeria" Khaleesat ta sauke ajiyar zuciya tace "Zancen gaskiya ke ma fa kina da naki
Safiyyah, babu ta yanda za ayi kina zaune da mata ko ɗan wanke wanken nan da shara baza ki ke taya ta ba
a gidan, Abinda fa idan an mana mun san baza mu ji dadi ba to kar mu yi ma wani, she is also human, kuma
at times bacin rai ne ke triggering wani mugun halin mutum, kece kika yi triggering din halinta a gidan,
babu ta yanda zaki ji dadi wataran kanwar mijinki ta zo gidanki ta zauna bata taya ki aikin komai sai dai in
kinyi girki ta deba ta ci ta ajiye maki plate, ki duba wannan lamarin fa, mu mata muna da son kanmu wani
lkcn..." Safiyyah ta dakatar da ita tace "Ohh wato goyon bayanta ma kike kenan Khaleesah? you are trying
to say duk abinda take min yayi dai dai ko?? To nagode, dama ke baki taɓa goyon bayan mutum a duk halin
da yake ciki, in dai mutum zai kawo maki damuwarsa to ya kara dulmiya kansa cikin damuwa ne, ni kuma
ban taɓa kin supporting dinki ba no matter the situation, ko Abdul da nake zagi kullum kamar ɗa na nake
goyon bayanki an gaya maki kema baki da naki baƙin halin ne wani lkci? Dama mistake nayi ma na zo
gidan nan asirina a rufe da gidan Sandra na wuce da ba a kara bata min rai ba" Tana fadin haka ta mike ta
figi jakarta ta nufi kofa kamar zata tashi sama, Khaleesat ta mike tace "Safiyyah" Banza da ita Safiyyah tayi
har ta fice daga parlon ta kullo mata kofa, Khaleesat ta sauke ajiyar zuciya ta koma ta zauna, a hankali tace
"Ae shikenan"
✍🏻
07087865788
[5/15, 7:17 PM] khaleesat Haiydar ✍️: Read My Book "HALYSAAH" on
ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=681294ff01c6bd900451c8e6
✨✨ HALYSAAH✨✨
✍🏻
By _Khaleesat Haiydar_
19....
Ranan friday wajen karfe sha daya na safe Khaleesat ta gama Laundry da take a kitchen ta fito, a reading
nook din parlon ta tarar da Housemate dinta yana duba textbooks dinsa, cikin few seconds ya dau wanda
zai dauka ya dawo cikin parlon yana kallonta yace "Har kin gama kenan" Kai kawai ta gyada masa ta fara
tidying din parlon, rana na farko kenan da ta fara ganinsa yayi shiga irin ta Hausa cikin fararen kaya, Taji
yace "Hope you are studying well Halysaah" kai kawai ta gyada masa, yace "Alright, till later" Ta ɗan
kallesa tace "Are you Nigerian?" Ya buda ido yace "Why do u ask?" Tace "Kawai nayi zatan ko daga Chad
kake, or Niger" Dariya yayi yace "Hope it's fine now tunda kin rama?" Hanyar dakinta ta nufa ba tare da ta
basa amsa ba, ya dau makullin motarsa ya nufi kofar parlon, sai bayan da ya fita sannan ta dawo cikin
parlon ta tafi gun window ta ɗan bude drapery din jiki tana leka garage, ganin har ya tafi ta ci gaba da aikin
da take yi a parlor. Wajen karfe biyar na yamma Khaleesat na kitchen tana girki at the same time suna waya
da Abdul, tun 40 mins ago ya kirata suke magana har sannan, duk kwanan nan dai lafiya suke waya da shi,
ya kuma ɗan rage mata wasu abubuwan da yake mata, he is being a little caring these days, a rana sai su yi
waya sau biyu wani lkcn har sau uku har hakan na bata mamaki kamar dai ba shi ba, yanzun ma shi ne yayi
encouraging dinta ta tashi ta fara girkin da take yi don bata yi niyyar girki ba, for weeks now kullum
Housemate dinta ke masu takeaway na dinner wani lkcn har lunch, this made her soo lazy to go to the
kitchen, breakfast dama tea and cookies take ci yawanci ko kuma ta ci da bread idan Housemate dinta ya
siyo, wani lkcn ta ci french fries da kwai ko ketchup, kwankwasa kofar parlor taji ana yi, ta ɗan zaro ido
sanin bazai wuce Housemate dinta ba, kilan ya mance makullinsa ko kuma yayi misplacing dinsa as usual,
ta kalli wayarta dake ajiye a kan kitchen cabinet har sannan Abdul was on the line kuma a handsfree ta sa
wayar, tana ɗan kame kame tace masa "Can u excuse me pls, i will call u back in the next 2 minutes pls"
Abdul yace "Why? Me zaki yi? Is the call hindering you from doing anything?" Da sauri tace "Noo" don
bata son tayi laifi, sai kuma a hankali tace "Just want to round up the cooking ne, na kusa gamawa ai" Yace
"But my call isn't preventing you from doing so, wayan ba a ajiye yake ba? Continue with ur work kawai"
Knocking ta sake ji, ta ma san Housemate dinta ne cause haka yake knocking dinsa, ta kalli wayarta tace
"Ohk then" Abdul ya ci gaba da maganar da yake mata, a hankali ta dau wayar ta fita daga kitchen din
almost tiptoeing kamar tana tsoron yaji sound din tafiyarta, ta nufi kofar parlon ta bude at the same time
tana kokarin yi ma Housemate dinta alamar da yayi shiru ta hanyar dora finger dinta daya a lips dinta, lkci
daya taji komai nata ya tsaya cak, a hankali ta zame finger dinta daga lebbenta tana kallonsa bata ko
kiftawa zuciyarta na bugawa, ta cire wayar dake kunnenta looking speechless and Surprise at the same
time, Calmly yace "Ko in koma ne?" Ta zaro ido cikin in ina tace "No, no, not at all, i... i was just being
surprise, sannu da zuwa" Da sauri ta koma gefe zuciyarta na bugawa da karfi, Ya katse wayar dake kare
kunnensa sannan ya shiga parlon, ta bi sa da kallo still shocked, gani take kamar she is daydreaming, ta
kikkifta idanuwanta ta bude to be sure but still she is still seeing him, har sai da ya karasa cikin parlon ya
zauna sannan ta bi bayansa, a hankali ta duka kusa da shi tana yaƙen karfin hali tace "Wai dama all this
while kana garin nan ne? I am so confuse" Yace "Gashi kin gan ni, in baki yarda ba sai ki taɓa ki ji don ki
tabbatar" Still feigning smile tace "I am seriously surprise, this is the least thing i expected today wallahi..."
Sai kuma ta tashi da sauri tace "Let me get u water" Kitchen ta tafi zuciyarta na bugawa, sai da ta jingina
jikin cabinet ta dafe kirjinta a hankali tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, na shiga uku" Tasan at anytime
Housemate dinta zai iya shigowa gidan don yamma yayi sosai, cikin hanzari ta bude fridge ta dauko masa
ruwan gora da drink with glass cup sannan ta fita da sauri, tana kirkiran murmushi ta durkusa gabansa ta
ajiye masa tace "Tun yaushe kake garin nan amma?" Ya dau ruwan goran yana kallo yace "You are buying
expensive water now? Sannu er gayu" Tayi dariyar karfin hali tace "Not at all, miyar ma ya kusa yi sai in
zuba maka abincin, ko dama shi sa kace sai nayi girki?" Kawai murmushi yayi bai bata amsa ba, ta mike ta
koma kitchen, gaba daya she is confuse on what to do, ta fara dube duben wayarta ta tuna ta ajiyesa kan
kujera a parlor, fitowa ta sake yi ta tarar Abdul yayi picking din kiran da ake masa ta waya, cikin dubara ta
dau wayarta ta nufi dakinta da sauri tana kallonsa ta gefen ido taga attention dinsa na kan wayar da ya fara,
bandakinta ta shige ta kulle tace "Na shiga uku" Da ta tuna bata ma da lambar Housemate din nata ta sake
jin mugun tashin hankali, yanzu ya zata yi? Da sauri ta fara dialing number Salem, ai ko yana fara ring ya
daga, murya can kasa ta gaishesa without waiting for his full reply tace "Plsss how can i get in contact with
my Housemate? ina son zan masa magana ne urgently" Salem yace "Ohk, muna ma tare, gashi nan" Bata
san sanda ta sauke wani irin ajiyar zuciyar relieve ba, taji muryar Housemate dinta yace "Hello Halysaah, is
everything alright?" Ta girgiza masa kai da sauri kamar yana ganinta tace "Plss i am sorry amma kar kace
zaka dawo yau, my fiance is around, he just came without notice" Yace "Tohhhh, haka kuma aka yi ashe?"
Ta wani turo baki kamar yana ganinta, yayi murmushi yace "Alright Halysaah, keep ur cool, duk sanda ya
tafi sai ki sanar min" A hankali tace "Thank you" Yace "Not a problem" Shi ya fara katse wayar, ta kalli
screen din sannan ta sauke ajiyar zuciya ta fito da sauri bayan ta bar wayar a dakinta, har sannan ta tarar
Abdul bai gama wayar da yake ba, da alama business call ne, Khaleesat na tafiya a hankali ta tafi kitchen
don saka masa abincin da ta girka, har sannan she is shock, babban damuwarta yanzu kasantuwarsu su biyu
kadai a gidan, a da bata jin tsoron kasancewa da shi guri daya and that was almost 4 years back, but not
anymore, he is complete changed all of a sudden in just a year, da tunanin nan ta fito daga kitchen, ta karasa
har gabansa ta ajiye masa abincin, yana kallonta yace "How about ur Housemate, bata nan ne?" Ta ɗan yi
murmushin karfin hali tace "Yeah bata nan" Ta mike ta koma edge din kujera ta zauna kamar bakuwa a
gidan, a hankali tace "Ya su Momy da Aunty Hafsah?" Yace "Lafiya lau" Bata sake cewa komai ba, Ya kalli
abincin da ta ajiye masa yace "I am full, ki rufe sai dai anjima" A hankali tace "Ok tafiya zaka yi da shi?"
Yana dubanta yace "In tafi da shi ina?" Ta kirkiri murmushi tace "A'a ai tambaya kawai nayi" Yace "Na riga
nayi lodging out of the hotel, i was in Maryland since morning" Khaleesat was speechless, bata gane yayi
lodging out of the hotel ba, to ina zai kwana ko kuma wani hotel din zai kama? kai bata ma yarda ba don in
yayi lodge out to ina trolley din kayansa yake, Tana murmushi da kyar tace "To ina akwatin ka?" Yace
"Tana cikin mota" Ta hadiye abu da kyar tace "Motar wa?" A takaice yace "Ban sani ba" sunkuyar da kai
tayi bata sake cewa komai ba, yace "Ko kina da plans ne yau? Naga kinyi mamakin zuwana da gaske" Ta
zaro ido tace "Not at all wallahi, ai kai ma kasan daga schl babu inda nake zuwa, kawai dai nayi mamakin
muna ta waya tun daxu ashe kana garin nan" Ya mike yace "To ki dena mamaki tunda ba ke kika siya min
ticket din ba" Ta sunkuyar da kanta tayi shiru, dakinta ya nufa yace "Let me take a shower" Khaleesat ta
gyada masa kai kawai ta bi sa da kallo, a very tall and masculine guy he is, just like her Housemate, and
they are all handsome in their own different ways kamar su suka yi kan su, sai dai ita tafi ganin kyan
Housemate dinta ko me yasa, a zahiri duk macen da ta samu Abdul in dai mayyar kudi ce kuma tana son
namiji me tsantsan kyau ga kuma qualities na cikakken namiji pertaining to body structure not behavior... to
duk walakancin da Abdul zai dinga mata zata jure tayi ta shanyewa don mijin nuna ma sa'a ne shi din, that
is if behavior isn't included, amma Khaleesat dai dai da rana daya qualities din nan biyu na Abdul bai taɓa
dada ta da kasa ba, a haka stepsisters dinta ko ga maciji basa yi da ita all because of Abdul, kiri kiri suke
nuna mata jealousy dinsu daga su har iyayensu a fili, ba su kadai ba hatta wasu daga sa'aninta a anguwa sun
dena kulata saboda shi, basu san baƙin cikin da take kunsa day by day ba, she wish zai koma ma daya daga
stepsisters din nata da ita kam ta huta, kwantar da kanta tayi jikin kujera tana jin hankalinta na kara tashi,
yana nufin kenan bazai tafi anytime soon ba? kilan ma yace nan zai kwana fa? Sosai hankalinta yayi mugun
tashi da tunanin hakan, after a while ta mike a sanyaye ta dau abincin da ta zubo masa ta tafi da shi kitchen
ta rufe, ana haka har lkcn sallan magarib yayi bai fito daga dakinta ba, Khaleesat dake ta zaune a parlor
kamar bakuwa a gidan ta kalli kofar dakin nata a sanyaye, sai kuma ta tashi walking slowly ta nufi dakin, a
hankali tayi sallama sai da ya amsa sannan ta bude, ta samesa zaune saman darduma alamar sallah ya idar
yana danna wayarsa, gaba daya dakin ya cika da kamshin turarensa, murmushin karfin hali ta kirkiro ta dau
hijab dinta tace "Sallah zan yi" Sai kuma ta juya zata fita yace "Ina zaki yi sallan?" Ta sake juyowa cikin
sanyin murya tace "Parlor" Mikewa yayi ya bar kan darduman yace "Pray here, dama kin saba sallah a
parlon ne?" Ya koma gefen gado ya zauna still pressing his phone, da kyar ta karasa kan darduman ta fara
sallan, bayan ta idar ta dinga addu'ar Allah ya taɓa zuciyarsa ya tashi ya tafi ya bar mata gidan ita dai,
muryarsa taji yace "Make me a cup of hot chocolate" Ta gyada masa kai tace "To" Mikewa tayi ta nufi kofa
ta fita zuwa kitchen, abinda yace tayi ta masa sannan ta koma dakin rike da mug din, bedside drawer ta
ajiye masa tace "In kawo maka abincin?" Yace "Aa bazan ci abinci ba, me yasa kike yawo da Hijab kamar
matar liman" Tana murmushin karfin hali da kyar tace "Aa ina jiran lkcn isha ne" Yace "Cire Hijab din nan"
Ba musu ta cire a hankali ta linke ta ajiye, yace "Ke kin ci abincin ne?" Duk da bata ci ba ta gyada masa kai
don gaba daya ta nemi appetite dinta ta rasa, gun reading material dinta ta tafi ta zauna ta kunna laptop
dinta tayi kamar karatu take, ya gama danne dannensa a waya ya dau chocolate dinsa ya fara sha, gaba daya
Khaleesat bata fahimtar me take dubawa a laptop din gabanta, sun kusa awa daya a yanda suke, ita dai har
sannan tana gaban laptop taki tashi, ta gefen ido ta kallesa ganin ya mike daga inda yake zaune, taga sallan
isha zai yi, sai da ya idar sannan ita ma ta tashi ta tafi tayi sallan, nan ma babu kalan addu'ar dabata yi ba
kan Allah ya taɓa zuciyarsa ya koma hotel dinsa, after a while ta mike ta dauke darduman ta linke ta ajiye,
ya mike ya kamo hannunta yana kallonta yace "Why are you uncomfortable kamar kina tare da stranger a
gidan nan ne Khaleesat?" Tayi dariyar yake tace "Stranger kuma Ya Abdul? Ai kai ba stranger bane, kai
yayana ne, kuma da ai ka sha kwana gidan nan farkon da na zo kasar, kana kwanciya a parlor ni kuma in
kwanta a daki" Yace "Kinsan da haka kike dari dari?" Ta sunkuyar da kanta ganin kallon da yake mata,
zuciyarta ya dinga bugawa, har ji take kafafuwanta suna neman kasa daukarta, ya matso da ita dab da shi
har tana iya jiyo breathing dinsa, calmly yace "Kinsan menene yasa nake kwanciya a parlor a sannan?" Ta
girgiza masa kai without looking at him don she is soo uncomfortable with him drawing her closer to
himself, yayi kasa da murya yace "Saboda u were still a baby sannan" Ta daga idanuwanta da kyar ta
kallesa amma ta kasa cewa komai, yace "Yanzu kuwa ke ba baby bace,