Showing 18001 words to 21000 words out of 152206 words

Chapter 7 - HALYSAAH by Khlst Hydrr

13 May 2026

112

ta kalli Baaba Gaje tace "Ni ce na kirata don ina ta magana bata min reply ba" Aunty Farida tace "Ai
tsabar munafurci yasa ta gaya maki ba wani abu ba" Khaleesat ta ɗan yi murmushi ta gaida Aunty Farida,
Aunty Farida ta amsa tace "Amma shi Abdul yasan Umma bata da lafiya shine ko kira ya dubata bai yi ba?"
Khaleesat ta sauke idonta kasa tace "Ni fa bai san na dawo ba Aunty" Aunty Farida tace "Wai ban gane bai
san kin dawo ba, wa ya biya maki kudin jirgin?" Khaleesat ta daga manyan idanuwanta tana kallonsu, Sai
kuma a hankali tace "Wani ne ya biya min ba Abdul ba" Umma ta kalleta da sauri tace "Wani?" Da mamaki
Aunty Farida tace "Wani a ina?" Khaleesat na kokarin mikewa tace "Neighbor dina ne" Umma ta bude baki
tana kallonta, sai kuma tace "Ko baki da hankali ne, waye ya biya maki kudin jirgi Khaleesah?" Khaleesat
tayi shiru bata ce komai ba, Gaje tace "Bude baki zaki yi ki mana bayani dalla dalla, waye shi zai biya maki
zunzurutun kudi na jirgin da naji ance ya fi miliyan daya? A ina kika san sa?" Still dai Khaleesat taki cewa
komai, Aunty Farida tace "Ke bana son rainin wayo uban wa zaki ma shiru ana maki magana? Ko baki ji
tambayar da ake maki bane?" Umma dai kallon Khaleesat kawai take da mamaki, Khaleesat ta koma baya
ta ɗan sunkuyar da kanta a hankali tace "Ni fa nace makocina ne ya biya min, kuma ai gani yayi ina ta kuka
Ummana bata da lafiya shine ya biya min jirgi in dawo in dubota" Cikin sanyin murya ta kare maganar,
Baaba Gaje tace "Atoh dama ai ko ina ana samun na Allah, Allah ya masa albarka, Bature ne ko?" A takaice
Khaleesat tace "Um" don bata son ma a ci gaba da zancen, Baaba Gaje tace "Ko da naji, ai sai baturen
dama, wani baƙin fata ne zai biya maki jirgi don yana makocinki, ai ko mutuwa uwar taki tayi iyaka ya
maki gaisuwa ya kama gabansa, to Allah ya saka masa da alkhairi, abinda ma baturen kudin jirgin ba wani
kudi bane a wajensa, ji zai yi kamar naira dubu goma ya kashe fa" Khaleesat na kallon Aunty Farida tace
"Aunty yanzu za aje asibitin ne?" Aunty Farida tace "Aa mu har mun dawo daga asibiti sai kuma na gobe in
Allah ya kai mu" a hankali Umma tace "Toh da ya biya maki kudin jirgin zuwa wa zai maki na komawa
yanzu? Kinsan dai ko hauka kike baza ki bari Abdul yaji wannan batun ba ki ja mana masifa ko?" Sai da
gaban Khaleesat ya fadi, a hankali ta sunkuyar da kanta, ita gaba daya ta ma mance ashe biyan jirgi za ayi a
koma, nan da nan jikinta yayi mugun sanyi, yanzu ina zata samu kudin ticket din komawa, she became so
weak at once, Aunty Farida tace "Toh shi Abdul din baki ce masa Umma bata da lafiya bane?" Khaleesat da
har sannan jikinta yake a sanyaye ta girgiza kai tace "Baya nan ne" Daga haka ta mike ta tafi zata shirya
don zanin da tayi wanka ne daure jikinta har a lkcn, Khaleesat na cikin saka kayanta da ta fiddo a akwati
1000 dollar din da Housemate dinta ya bata suka fado mata a rai, ta zaro ido lkci daya taji hankalinta ya
kwanta har sai da ta sauke ajiyar zuciya, tasan probably in ta canza har da 100 dollar din da Safiyyah ta
bata kudaden za su iya maidata Amurka, she felt so relieved, nan da nan walwalarta ya dawo, tana jin
Baaba Gaje na tambayar Aunty Farida ko kishiyoyin Ummanta sun shiga dubata yau, Aunty Farida tace
"Jiya ma basu shigo dubata ba sai yau Baaba Gaje" Baaba Gaje tace "Shegu matsiyata, so fa suka yi ace ta
mutu, to shi Malam Alin ya ku ka ƙarke da shi? Ya bada kudin?" Aunty Farida tace "Aa ni fa ban bi ta
kansa ba Baaba Gaje, dama me ya tsinana kafin in zo kanon? daxu ma aka turo min sauran kudin adashina
da nake jira, duk na siya sauran magungunan" Baaba Gaje tace "Atoh dai bai taɓuka komai ba a takaice, shi
ma da zaki basa yanxu tsaf zai amshe" Har aka yi azahar su Umma da Aunty Farida na gidan, Umma har
tayi bacci ta tashi saboda maganin da take sha, har a sannan da kyar take taka kafarta daya, hannunta dai ya
sake ya dawo normal tun a jiya, Khaleesat ta shigo dakin da shinkafa da waken da ta dafa, Baaba Gaje
kuma ta shiga makota dubiya, Aunty Farida dai sai bin Khaleesat take da kallo, sosai taga ta kara kyau tayi
fresh, duk da dai tana nan a yanda take babu kiba, komawa tsakar gida Khaleesat tayi ta dauko man gyadan
da ta soya ta dawo dakin, ta fara zuba ma Umma da Aunty Farida abincin, Umma dake zaune kan darduma
tana kallonta tace "Kun fara jarabawan ne?" Aunty Farida tace "Haba dai sun fara jarabawa zata taho? Ai
bazai yiwu ba, ko ana haka ne?" Khaleesat dake sauraronsu ta girgiza kai tana ɗan murmushi tace "Da
sauran lokaci bamu fara ba tukun" Aunty Farida tace "To yanzu dai tun kan wani munafukin yasan kina
garin nan mu shiga uku yaushe za ki koma Khaleesah?" Khaleesat ta daga kai a hankali tace "Cikin satin
nan in sha Allah" Aunty Farida tace "Toh inji dai Abdul din ya rage abubuwan nan nasa da yake maki?"
Khaleesat ta ajiye masu abincin a gabansu kamar bazata ce komai ba sai kuma tace "Babu abinda ya fasa,
ni na gaji da halinsa ma yanzu" Umma ta daga kai tana kallonta, Aunty Farida ma kallonta take don bata
taɓa cewa ta gaji da halin Abdul ba, Aunty Farida ta sauke ajiyar zuciya ta fara cin abincin gabanta tace "Na
dai gaya maki babu me canza maki shi sai ke da kanki, ke macece ya kamata ace zuwa yanzu kinsan
wanene Abdul kinsan kuma yanda zaki zauna da shi" Mikewa Khaleesat tayi without saying anything don
ita yanzu taji ko zancen nasa ma bata so har cikin ranta, tun shekaranjiya da yayi fushi har yau bai kirata ba
ita kuma as far as tayi masa miss calls har biyu to bata ji zata iya sake kiransa ba unlike before da ta dinga
kiransa kenan ko da bazai daga ba, ko kuma tayi ta masa magana ta WhatsApp, to yanzu kam bata ji zata
iya ba.....


✍🏻
07087865788

*Still on free pages*
[5/4, 8:14 PM] khaleesat Haiydar ✍️: ✨✨HALYSAAH✨✨
✍🏻
By _Khaleesat Haiydar_




7.....

Kwanan Khaleesat hudu yau a garin kano, kuma har a sannan babu wanda yasan da zuwanta a cikin yan
gidansu, ko nan da can bata fita a gidan Baaba Gaje don ma kar tsautsayi ya sa ta hadu da daya daga cikin
yan gidan nasu, a kwanaki hudun nan sau biyu Ummanta da Aunty Farida suka zo gidan Baaba Gaje
dominta, zuwa sannan Umma ta warware gaba daya tafiyarta ya dawo normal, tun kwanaki biyu da suka
wuce ta gama amsan treatment dinta a hospital sai magunguna da take sha kawai, har zuwa ranan kuma
Abdul bai kira Khaleesat ba, ita kuwa kawai taji ko a jikinta da ya kira da kar ya kira, there wasn't an atom
of disturbance a tattare da ita, ko ta WhatsApp bata yi gigin yi masa magana ba Unlike before da bazata iya
hakuri ba sai ta masa, tana bakin murhu tana dafa shinkafa da wake ga turmi gabanta tana ɗaka yajin da za
ayi amfani da shi wajen cin shinkafa da waken, Su Ummanta da Baaba Gaje kuma na can uwar ɗaka,
tunanin yanda zata fara shirye shiryen komawa USA take don suna da wani presentation nan da kwana uku,
daxu da safe ta duba available flight da farashinsu online and she is hoping in ta canza dollars din da
Housemate dinta ya bata zai isheta ta koma, Khaleesat ta bar daƙan yajin da take yi bayan taji Aunty Farida
na kwalo mata kira, mikewa tayi ta wuce dakin tana amsawa, tun da ta zo gidan Baaba Gaje ta sakar mata
aikin komai, hatta jikokinta ita ke masu wanka kan su tafi makaranta, ita taga kamar har ta ɗan yi duhu
tsabar girki cikin rana da take yi tun zuwanta, Aunty Farida tace "Ana kiran wayarki" nan da nan mood din
Khaleesat ya canza ta karasa gun wayar without much interest, duk tunaninta Abdul ne cause she isn't
expecting any call from anybody, Number mutumin da ya tarbeta a Airport din Lagos ta gani a gaban
Screen din wayarta, ta dinga kallon number bata ko kiftawa, duk da bata yi saving ba amma ta gane nasa
ne, daukar wayar tayi ta fita daga dakin ta koma bakin murhun sannan tayi picking ta kai kunne, sallama
yayi ya gaisheta da ladabi, tace "Ina yini?" Yace "Alhamdulillahi Hajiya, ya jama'ar gidan?" Tace
"Alhamdulillah" Yace "To maa sha Allah, dama na bugo ne inji ko zaki kara kwanaki nawa nan gaba kan ki
koma America?" Khaleesat tayi shiru trying to understand why he is asking her that, yace "Hello?" Tace
"Ina jin ka, ban gane tambayar bane" Calmly yace "Aa so nake in san ranan da zaki koma ne Hajiya, in ya
kama ayi rescheduling din ticket dinki sai ayi hakan in sha Allah" Khaleesat was speechless, a ranta tace
Ticket kuma? Kasa cewa komai tayi with surprise, taji ta ma kasa ci gaba da tsayuwa, jin ya sake cewa
"Hello" ta kifta ido da kyar ta duka kusa da turmin da take daka yaji tace "Ina ji" Yace "Ina ga a bari duk
sanda kika shirya zaki nemeni ta waya ko Hajiya?" Sauke idonta tayi kasa, lokaci daya jikinta yayi sanyi
sosai, cikin sanyayyen murya tace "Ranan Lahadi nake son zan koma idan Allah ya yarda" Yace "To Maa
sha Allah, dama booking din ranan aka maki da zaki taho, flight din karfe daya ne, za ku tashi ta Airport din
Abuja in sha Allah" Ita dai Khaleesat ta kasa cewa komai, yace "Sai kin ji ni in sha Allah Hajiya" A hankali
Khaleesat tace "Nagode" Khaleesat na zaune dakin Baaba Gaje tana jujjuya shinkafa da waken dake
gabanta da cokali, gaba daya ta kasa cin abincin, ita kanta ta rasa dalili, ko tsabar yanda jikinta yayi sanyi
ne tun bayan da suka yi waya da mutumin daxu da ya sanar mata da ticket dinta na komawa America
sannan tana gama aikin da take ta bude WhatsApp taga ya aiko mata da Flight Ticket dinta which was also
business Class kamar dai yanda ta zo, this made her so weak, gaba daya ta ma rasa gane feeling din dake
ranta a lokacin, bata taba tunanin Housemate din nata zai mata ticket din komawa ba, Duk Ummanta na
lura da sauyawanta lkci guda, Aunty Farida ta gama shafa powder din da take zata leka gidan wata kawarta
Maman Fu'ad a nan hotoron, ta dau jakarta da mayafi tana kallon yayarta tace "To sai na dawo Umma"
Umma tace "Amma kar ki dade don Allah Farida" Aunty Farida tace "Haba ai yamma tayi bazan zauna ba
Umma" Daga haka ta fita daga dakin tayi ma Baaba Gaje dake waje tare da bakuwarta sallama sannan ta
fita daga gidan, Umma ta daga kai tana kallon Khaleesat tace "Menene kika saka abinci a gaba kika kasa ci
Khaleesat?" Khaleesat ta daga kai da sauri tana kallon kyakkyawan fuskar Ummanta, babu wanda zai ce
Umma ce ta haifeta sai dai ma yayi tunanin yayarta ce don kama suke ba na wasa ba kamar an tsaga ƙara,
Khaleesat tayi murmushin yake ta kai shinkafa da waken baki tace "Babu komai fa Umma" Umma tace
"Yaushe za ki koma? Kuma yaya za ayi da batun kudin jirgi? Har yanzu Abdul din bai san kina nan ba?"
Khaleesat ta girgiza kai tace "Umma ai nace baya nan kuma ba a samunsa ta waya, ranan lahadi zan koma
in sha Allah" Umma tace "Ranan Lahadi? To ina za ki samu kudin komawa?" Khaleesat ta gyara zamanta
tace "Makocin nawa ai tare ya biya min na zuwa da dawowa" Kallonta Umma ta dinga yi da alamar tuhuma
ga mamaki kwance fuskarta, Khaleesat taki yarda ta bari su hada ido sai tura abincin gabanta take, Umma
tace "Khaleesah" Da kyar Khaleesat ta daga kai gabanta na faduwa, Umma tace "Meye tsakaninki da
wannan mutumi da ya biya maki kudin jirgin zuwa har da na komawa?" Khaleesat ta hadiye sauran
shinkafar da ya makale a throat dinta da kyar tace "Wallahi Umma babu komai, makocina ne kawai shi,
kuma don yaga yanda na daga hankali baki da lafiya shi ne yasa yayi hakan, ni kaina sai bayan da ya biya
min na sani, amma ki yarda dani Umma babu komai tsakanina da shi" Kamar zata yi kuka ta kare maganar,
Ummanta ta sauke ajiyar zuciya tayi shiru, bayan some seconds tace "Toh shikenan, amma dai kinsan in
Abdul ya samu labarin nan da matsala ko?" Khaleesat ta sunkuyar da kanta bata sake cewa komai ba, jin
Umma tayi shiru alamar ta fada duniyar tunani Khaleesat ta daga kai a hankali tace "To ai Umma babu
wanda yasan na zo kano har yanzu, don haka bazai sani ba" Umma ta sauke wani ajiyar zuciyar tace "To
gudun kada hakan ya sake faruwa kar ki sake yarda ko wata mu'amula ta hadaki da shi makocin naki
Khaleesat, ki rufa mana asiri" Khaleesat bata ce komai ba sai kuma ta jawo handbag dinta ta ciro dala dubu
dayan da Housemate dinta ya bata ta nuna ma Umma cikin sanyin murya tace "Wannan ma shi ya bani da
zan taho" Umma ta dinga kallon kudin duk da bata san ko nawa bane ta dai ce "Ki kula don Allah
Khaleesat kar ki ja mana magana kin dai san wanene Abdul kin san kuma waye Babanki" Khaleesat dai tayi
shiru, tasan Umma bata san har nawa bane Dollars din in an canza zuwa Naira, ita dai tayi shiru bata gaya
mata ba kar ta kara daga mata hankali. Washegari da wuri Khaleesat ta shirya ta saka Nikab dinta ta fita don
zata je canza dollar din nata ta dan yi siyayya, bayan ta canza dalolin taga har ya wuce yanda take tunani a
Naira, nan ta fara zuwa inda zata siyi waya, ta siya ma Ummanta da Aunty Farida sabbin wayar Android iri
daya na dubu dari da hamsin each, Ganin Baaba Gaje ma bata da waya kuma ba iya amfani da Android zata
yi ba ta siya mata karamar waya na dubu ashirin, daga nan ta karasa kasuwa tayi siyayyar yan abubuwan da
zata koma USA da shi, ta siya ma siblings dinta twins mata sabbin school bag da schl shoe da socks, ta siya
masu atamfofi kala uku each da mayafai da takalma masu kyau da inner wears, jikokin Baaba Gaje ma ta
siya masu takalma da inner wears gaba dayansu, pharmacy ta shiga da takardan da aka rubuta magungunan
Ummanta ta siya mata na wata biyu duk da tsadar magungunan, kusan Azahar ta koma gidan Baaba Gaje ta
tarar su Ummanta basu zo ba. Washegari asabar Khaleesat na shanya kayan jikokin Baaba Gaje da ta
wanke, Baaba Gaje kuma na shirin fita kasuwa Ummanta suka shigo gidan tare da Aunty Farida da Siblings
dinta yan biyu Islam da Noor that are just 11 years old, da gudu suka tafi suka rungumeta suna mata oyoyo,
sosai kannin nata ke kama da ita, Khaleesat was so happy seeing her twins Siblings wanda su uku kawai
Ummansu ta haifa, Baaba Gaje tace "Basu tafi islamiyya bane?" Umma tayi kasa da murya tana kallon
Gaje tace "Sun ma kwana biyu rabonsu da zuwa, ba a biya kudin wata ba" Baaba Gaje tace "Ikon Allah to
Alin ca yayi bazai biya ba kenan?" Umma tace "Cewa yayi in dora masu talla kamar yanda yan uwansu ke
yi tunda su ba 'ya yan Gwal bane, dama ba fa shi ke biya masu ba wannan karan ne bani da kudi duk jarin
ya lalace shine nace su tambayesa" Baaba Gaje tace "To Allah ya kyauta, amma Ali dai haƙƙin 'ya ya da
kyar ya bari ya jiyo kamshin aljanna balle yaje kusa da ita" Ita dai Khaleesat a sanyaye ta kama hannun
kannin nata zuwa dakin Baaba Gaje, tana jin Baaba Gaje na cewa "Amma de suna zuwa bokon?" Umma ta
sauke ajiyar zuciya tace "Ina fa, islamiyya ma da ya zama dole ba aje ba sae wani boko" Aunty Farida ta
girgiza kai cike da takaici tace "Allah de ya kyauta, shi fa bakin cikin bata dora ma yaran talla kamar yanda
sauran matansa ke dora ma nasu 'ya yan talla ba yake" Sosai jikin Khaleesat yayi sanyi don duk sanda ta
tambayi Ummanta ko kannen nata na zuwa boko da Islamiyya ta wayar Sha'awa sai tace mata eh suna
zuwa, ashe basa zuwa, Umma dai bata ce komai ba suka shiga dakin gaba daya, Baaba Gaje tace "Kun ga
bari inje kasuwa in dawo" Su Umma suka mata Allah ya kiyaye ta figi gyalenta ta fita daga gidan,
Khaleesat ta fiddo duk siyayyan da tayi jiya, daga Ummanta har Aunty Farida kallonta suka tsaya yi, Aunty
Farida ta rike haɓa tace "Haka kudin suke da yawa da kika canza? Kuma wa ya aike ki kashe kudi haka mu
da muke da sabga a gabanmu Khaleesat? Maimakon ki bada a ajiye maki ko kujeru da setin gado ne da
kudaden? Kin de san ko tsintsiya mahaifinki ba lallai ya siya maki da sunan a kai ki dakinki da shi ba ko?"
Khaleesat tayi murmushin karfin hali bata ce komai ba, Umma dai ta ma rasa abun cewa, Aunty Farida tace
"Ni da kin yi shawara da ni duk baza ki yi wannan siyayyan ba, iyaka ki siyi abinda zaki koma can Amurka
da shi, in suka tado da maganar aure me garemu da za a kai ki da shi Khaleesah?" Khaleesat na murmushi
tace "Allah zai rufa asiri zuwa sannan Aunty" Aunty Farida tace "Yanzu duk kudin sun kare kenan?"
Khaleesat ta girgiza kai tace "Aa, saura dubu dari biyar" Daga Aunty Farida har Umma bude ido suka yi
sosai suna kallonta with shock, Aunty Farida ta gyara zama tana zaro ido tace "Har nawa ya baki haka? Ko
dai baki da hankali ne" Khaleesat ta kauda zancen ta hanyar cewa "Har fa da kudadena duk na canxa"
handbag dinta ta jawo ta bude ta ciro sauran kudaden da suka rage don har wanda Safiyyah ta bata ta canza,
ta kirga dubu dari a ciki ta ware, sannan ta kirga dubu dari da hamsin shi ma ta ware, kallonta kawai Umma
da Aunty Farida suke, ta ba Aunty Farida dubu dari tace "Aunty kiyi kudin mota da wannan idan zaki koma
Lagos sannan ki kara jari" Ta ajiye ma Umma 150k tace "Umma ki rike wannan a biya kudin makarantar su
islam da Noor a kuma canza

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login