Showing 15001 words to 18000 words out of 152206 words

Chapter 6 - HALYSAAH by Khlst Hydrr

13 May 2026

87

kira ki na gaya maki ba i will be leaving for Nigeria by
3pm" Da mamaki Safiyyah tace "Zaki tafi Nigeria? Abdul ne ya siya maki flight ticket?" Khaleesat ta sauke
idonta tace "Uhm" Safiyyah tace "Is it that critical Khaleesat?" Khaleesat tace "To da sauki dai, amma
kinsan bazan samu rest of mind ba in ban je ba" Safiyyah tace "To kina airport yanzu ne?" Khaleesat tace
"Aa ina jiran Lyft ne yanzu zan tafi" Safiyyah tace "Toh shikenan mu hadu a can kawai sai mu yi sallama,
bari in nemi Uber nima" Khaleesat tace "To nagode Sophie" Da haka suka gama wayar, Khaleesat ta mike
bayan Lyft dinta ya iso, tana rike da trolley dinta da handbag ta fito daga dakin ta kulle kofa, sanye take da
Maroon Abaya sai veil dinta, tana tafiya a hankali ta karaso cikin parlorn, ya ajiye wayar da yake yace "Kin
shirya?" Without looking at him tace "Eh" yace "Kin yi ordering ride ai?" Tace "Eh" yace "Ohk" Mikewa
yayi ya ciro 1000 Dollars ya mika mata yace "Sort ur self out with this" Girgiza masa kai tayi tace "Aa
Nagode" Yace "C'mon, u didn't beg me Halysaah" Ƙin kallonsa tayi kuma taki amsan kudin, ya dau
handbag dinta da ta ajiye saman trolley din gabanta ya bude zip din jakar ya sa mata kudin tare da wani
farin takarda, ta ɗaga kai tana kallonsa, ya koma ya zauna yace "Allah ya tsare, my regards to ur Mom and
everyone back home, Allah ya bata lafiya" Da kyar tace "Ameen nagode" Yace "Zaki ga digit na rubuta
maki a takarda, idan kun sauka Airport sai ki kira number kice masa kun sauka" Ta kasa cewa komai, after
few seconds ta dau handbag dinta cikin sanyin murya tace "Nagode " Yace "U are welcome, wishing u a
Safe trip" Tana jan trolley dinta a hankali ta nufi kofa, tana bude kofar ta fita ta daga kai tana kallonsa taga
Idonsa na kan wayarsa da yake dannawa, kulle kofar parlon tayi, taga Lyft din dake jiranta ta nufi wajensa.
A Airport Khaleesat suka hadu da Safiyyah, Safiyyah na rike da hannunta tace "Tun yaushe ne Umman bata
da lafiya?" Khaleesat tace "Jiya Aunty sha'awa ke gaya min" Safiyyah ta sauke ajiyar zuciya tace "To Allah
Ubangiji ya bata lafiya" Khaleesat tace "Ameen" Safiyyah tace "Lallai Abdul ya fara hankali da yayi
tunanin biya maki jirgi kije ki duba Umma, nayi mamaki sosai wallahi" Khaleesat ta ɗan yi murmushi da
iyakarsa lips, Safiyyah tace "Yanzu kwana nawa za ki yi?" Khaleesat tayi shiru at first, sai kuma tace "Sai
dai naje tukunna in sha Allah" Safiyyah tace "Toh Allah ya kai ku lafiya, don Allah ki gaida min Umma da
jiki" Safiyyah na fadin haka ta jawo handbag din Khaleesat ta saka mata dala dari tace "Plss manage this
kawata" Khaleesat ta ɗan bude baki tace "Haba meye haka Sophie" Sophie bata tsaya ta saurareta ba ta
daga mata hannu tana murmushi ta bar ta tsaye wajen, Khaleesat dai ta bi ta da kallo. Khaleesat was more
than shock bayan ta amshi boarding pass dinta ganin ticket din Business Class ya siya mata, Business class
fa? Kikkifta ido tayi ta sake kallon ticket din sosai to confirm, taga Business class din dai ne still, sosai
jikinta yayi sanyi, tana jan kafa da kyar ta shiga jirgin, this is the first time she will be traveling Business
class, wata Flight Attendant that gave her all the maximum attention ta yi leading dinta har zuwa Seat dinta
a cikin jirgin da fara'a tana welcoming dinta, bayan wani ɗan lokaci jirgin ya tashi, Khaleesat ta ajiye
Amenity kit da aka bata ko duba abinda ke ciki bata yi ba tana bin ko ina na Business class din da ido, the
Flight from Baltimore Washington International to Amsterdam Schiphol Airport in North Holland for
Layover was smooth and comfortable, duk zuwanta Amurka bata taɓa tafiya feeling so comfortable like
this ba, bayan few hours aka sauya masu jirgi zuwa Nigeria a nan North Holland, Khaleesat tayi shiru da
mamaki jin announcement na cewar Lagos Nigeria jirgin ya nufa, ticket dinta ta sake dubawa taga ashe
haka ne a jiki, bayan tafiyar kusan awa bakwai jirgin nasu ya sauka a MMI Airport Lagos.
[5/3, 6:15 PM] khaleesat Haiydar ✍️: ✨✨HALYSAAH✨✨




✍🏻
By _Khaleesat Haiydar_




6.....


Bayan Khaleesat ta dau trolley dinta a cikin airport after going through custom ta tsaya cikin airport din
tana tunanin yanda zata yi cause karfe shidda saura ne na asuba, should she check for available flight to
Kano? To nawa ne ma a account dinta before she think of doing so, ko dai kawai ta tafi Motor park ta hau
mota zuwa kano, dollars din da Housemate dinta ya bata ne ya fado mata a rai don gaba daya ta ma mance,
ta bude handbag dinta ta ciro kudin tana kallo, takardan da ya saka mata hade da kudin a jaka ya fadi kasa,
ta duka ta dau takardan tana kallon numbers din jiki sai kuma ta mayar cikin jaka tare da Dollars din,
masallacin dake cikin Murtala Muhammad International airport ta tafi don yin sallan asuba, tana ta zaune
cikin masallacin bayan ta idar da sallah tana azkar dinta, can ta ciro wayarta a handbag ta duba agogo taga
karfe bakwai da minti goma, dollars din jakar ta sake cirowa ta kirga taga dala dubu ce, kallon kudin ta
dinga yi jiki a sanyaye don bata yi tunanin har haka ya bata ba, ta dau white paper din dake dauke da digit
tana tunanin to ko digit dinsa ne wannan din, kati ta siya ta Ussd sannan tayi dialing number a wayarta, sai
da ya kusa katsewa aka daga, daga daya side din aka yi sallama ta amsa, amma sai taji kamar ba muryarsa
bane, ta dai ce "Ina kwana?" Yace "Hajiya ko kece kika taho daga America?" Tace "Eh" Yace "To barka da
isowa Hajiya, ina ta sauraren kiran naki dama tun daxu, kina cikin airport din ne yanzu?" Tace "Eh" Yace
"Ohk to gani nan tahowa ba da dadewa ba in sha Allah" Bayan ya katse wayar ta kalli screen dinta, to waye
kuma wannan, maida kudin tayi jaka ta ciro nose mask dinta ta saka sannan ta mike ta fito daga Masallacin
da trolley dinta with handbag, bayan wasu mintoci sai gashi ya sake kiranta, ta fito outside of the airport,
yana hangota ya nufota ya gaisheta da ladabi har da bowing kansa yace "Ya hanya Hajiya?" Ta sauke idonta
tace "Lafiya Alhamdulillah" With respect yace "Ga mota can Hajiya, zaki je hotel ki huta zuwa karfe daya
na rana don Flight dinki zuwa kano na karfe Biyu ne in sha Allah..." Khaleesat was speechless ta dinga
kallonsa babu ko kiftawa cike da mamaki, can kuma ta kalli lafiyayyen motar da ya nuna nata, tuni ya
karasa ya amshi trolley dinta ya tafi ya bude booth ya saka, sannan ya bude mata bayan mota yace
"Bismillah Hajiya" Sauke idonta tayi kasa taji kafafuwanta sun mata nauyi amma a haka tana tafiya a
hankali ta tafi ta shiga back seat sannan ya kulle motar, ya zaga ya shiga driver seat, Hotel me tsada sosai
that isn't far away from the airport ya kai ta, sai da ya tabbatar tayi check in har zuwa dakinta sannan ya bar
hotel din, tana shiga babu jimawa wata ma'aikaciyar hotel din ta kawo mata lafiyayyen Breakfast, ita dai
Khaleesat ba um bare um um, gaba daya kanta ya gama kullewa, tashi tayi ta bude trolley dinta ta dau
Shower gel zata yi wanka. Khaleesat na bacci wajen karfe daya da minti ashirin vibration din wayarta ya
tasheta, ta jawo wayar a hankali tana duba me kiranta taga mutumin da ya kawota Hotel ne, ta mike zaune
sannan tayi picking call din ta kai kunne tayi shiru, daga daya bangaren yayi mata sallama sannan yace
"Hajiya fatan kin shirya in taho in dauke ki, flight din naki nan da minti talatin ne in sha Allah" a hankali
Khaleesat tace "Toh" Yace "Gani nan tahowa yanzu da izinin Allah" Yana katse wayar Khaleesat ta sauka
daga saman gado taje tayi alwala a bandaki, tana idar da sallan Azahar sai ga kiransa, ta dau trolley dinta da
handbag ta bar dakin hotel din ta sauko downstairs, yana hangota a Reception din hotel din ya tafi da sauri
ya amshi trolley din hannunta, ya karbi makullin dakin ya kai ma Receptionist, sannan suka fita haraban
hotel din ya bude mata back seat bayan ya saka trolley dinta a booth, cikin mintuna kadan suka isa MMI
Airport, sai da ya tabbatar ta amshi boarding pass dinta sannan yayi mata sallama da murmushi fuskarsa
yace "Toh Allah Ubangiji ya tsare Hajiya, idan kun sauka kanon za a karasa dake gida in sha Allah... We
will keep in touch" a hankali Khaleesat tace "Toh Nagode, Allah ya saka da alkhairi" Yace "Ameen Hajjaju,
nagode kwarai, Allah Ubangiji ya kai ku lafiya" A haka suka rabu ta nufi Departure lounge walking slowly,
bayan kusan minti ashirin jirginsu ya tashi zuwa garin kano. Suna sauka kano Khaleesat ta fito daga cikin
airport gabanta na faduwa, sai gyara nose mask din fuskarta take tana waige waige, yanzu ina ma ta nufa
tukun, tasan ko da wasa bazata nufi gida ba dai, wayarta ya fara ring ta duba da sauri gabanta na ci gaba da
faduwa, wata lamba ce ke kiranta tayi picking tayi shiru, taji an mata sallama ta amsa, mutumin ya gaisheta
yace "Hajiya Hamisu ne ya aiko min lambarki, naga jirgin ku ya sauka yanzu, yace za a karasa dake gida,
kina ta ina yanzu?" Tace "Na fito outside of the airport" Tahowa taga mutumin yayi zuwa inda take tsaye
bayan ya hangota, nan ya kai ta har motar dake jiranta, motar shigen wanda ta shiga a Abuja ne, mutumin
ya bude mata back seat ta shiga tace "Nagode" Yayi bowing kansa yayi mata sallama yace "Allah ya kai ku
lafiya" Tace "Ameen Nagode" Drivern dake mazaunin driver ya gaisheta yana tambayarta ya hanya sannan
ya tada motar suka fita daga airport din yace "Ina muka nufa Hajjaju?" Khaleesat ta ɗan yi shiru kamar me
nazari, sai kuma tace "Hotoro zaka kai ni" Yace "To Allah ya kai mu lafiya" Suna isa dai dai kofar gidan da
ta nuna masa ya tsaya, ya bude motar ya sauka don fiddo mata Trolley dinta a booth, bude motar tayi ita ma
ta sauka tana gyara facemask dinta, ta amshi akwatinta a hannunsa sannan tayi masa godiya ta shiga cikin
gidan da sauri, Baaba Gaje dake zaune tana tankade garin tuwo ta daga kai tana kallonta, Khaleesat ta ɗan
sauke Facemask dinta tana murmushi tace "Baaba sannu da aiki" Baaba Gaje ta ajiye rariyar hannunta tace
"Khaleesatu? Daga ina kuma haka?" Khaleesat ta duka nan gabanta har sannan tana ɗan murmushi tace
"Makaranta" Baaba Gaje tace "Ikon Allah, to ai ko minti ashirin banyi da dawowa daga gidanku ba kuma
ba ace min kina hanya ba" A hankali Khaleesat tace "Baaba ya jikin Ummanmu fa?" Baaba Gaje tace
"Kaddai ba a san kin biyo hanya ba kika taho Khaleesatu?" Khaleesat ta gyada mata kai kawai, Baaba Gaje
tace "Ikon Allah, to ai jikin nata da sauki er nan, shi Awdul din ne ya biya maki kudin jirgi kika dawo?"
Khaleesat ta girgiza kai gabanta na faduwa tace "Bai san na dawo ba Baaba" Baaba Gaje tace "Ikon Allah,
to bari in kira Parida, ko kuma ke ki kirata da kanki, Gwara da kika yi dubaran zuwa nan kada Salubabben
uban nan naki ya sa ki a bakin duniya mu shiga uku, Ga tabarma taho ki zauna ki huta, irin wannan tafiya
me nisa haka, naji ance Amurkan har yapi legas nisa ko? Kira Paridan mu ji yanda za ayi" Khaleesat ta
zauna gefenta ta bude handbag ta ciro wayarta, duk da yanda gabanta ke faduwa haka tayi dialing din
lambar kanwar Ummanta Aunty Farida, Baaba Gaje tace "Auu to ai Parida ba waya a hannunta wai an sace
a mota" Khaleesat ta daga kai tana kallonta, Baaba Gaje tace "Abinda zai faru kawai ga garin tuwon nan ki
karasa tankade min ga can murhu na dora ruwan tuwo in yayi ki min talgi ki tuka tuwon in ya silala ki
kwashe, ga kuma kayan miya can bai dai da yawa ki jajjaga ki kada min miyar kuka, ni kuma sai in koma
can Mariri yanzu in sanar ma Ummanku kin zo" Khaleesat tace "Toh Baaba" Mikewa Baaba Gaje tayi ta
figi yakunennen gyalenta a igiyar shanyan dake ɗan karamin tsakar gidan ta yafa tace "Bara inje, dama ina
da canjina dari da hansin sai in roke masu ɗan sahu su kai ni ko Farawa ne sai in karasa Maririn da kafa ta"
Khaleesat ta bude handbag dinta amma sai taga Dollars kawai, ta daga kai ta kalli Baaba Gaje tace "Wallahi
bani da kudin Nigeria a nan Baaba, amma bari in ciro a POS yanzu sai in baki kudin adaidaita sahun"
Baaba Gaje tace "Aa yi zamanki kiyi aikin da na sa ki, minti nawa ne nan da Mariri, kawai dai ga wanke
wanke can bakin kwararo ki wanke min har su, ki share tsakar gidan nan, in yaran nan suka dawo islamiyya
ki dauraye masu Uniform dinsu, dakin ma na nan sunyi kaca kaca da shi babu kyan gani" Daga haka ta fice
daga cikin gidan bayan ta saka slippers dinta, Khaleesat ta cire mayafin abayan jikinta ta dora kan
akwatinta sannan ta ci gaba da tankaden da Baaba Gaje ta bar mata, Baaba Gaje makociyarsu ce a can
unguwansu Mariri kafin 'ya yanta su siya mata wani ɗan kararramin gida a nan Hotoro Tsamiyar boka ta
dawo tana zaune da jikokinta biyar tana dubasu, zaman mutunci da amana Baaba Gaje suka yi da
Mahaifiyar Khaleesat da ta dauki Gajen tamkar uwa. Wajen karfe shidda saura Khaleesat ta gama duk aikin
da Gaje ta loda mata sannan ta dora ruwan da zata yi wanka a sauran rushi, zaunawa tayi kan tabarma ta
jingina da bango don ta gaji likis, Housemate dinta ne ya fado mata, ta dai yi shiru staring into space, after
a while ta sauke idonta a hankali ta mike ta shiga da kwanukan da ta wanke cikin dakin Gaje, dai dai nan
Gaje ta shigo cikin gidan da Aunty Farida, Khaleesat ta tafi da gudu ta rungume Aunty Farida cike da
murnan ganinta, Aunty Farida na kallonta tace "Ke kuma da wa kika yi shawara kika biyo hanya
Khaleesah? Abdul din ne yace ki taho?" Gaje ta daga hannu sama da sauri tace "Aaaa tace bai ma sani ba"
Aunty Farida na kallon Khaleesat da mamaki tace "Ban gane bai sani ba??" Khaleesat ta marairaice ta
kauda zancen ta hanyar cewa "Aunty ya jikin Ummanmu?" Aunty Farida ta kamo hannunta suka zauna
saman tabarma tace "Ai jikin Umma da sauki sosai Khaleesat, gashi har an sallamemu a asibiti, wa yace
maki bata da lafiya ne ma tukun?" Khaleesat da har hawaye ya ciko idonta tace "Aunty Sha'awa" Gaje tace
"Lahh ha ila, wato Sha'awa bazata dena munafurci ba ko? Wato bazata canxa hali ba ko? Da kaina fa sai da
na jaddada mata kar ta gaya maki ko kin mata sako ta wassol don kar hankalinki ya tashi, ashe sai da
munafukar ta zaga ta fada maki" Aunty Farida tace "Toh Allah ya kyauta, kwata kwata Sha'awa bazata
canza ba" Khaleesat da hawaye ke cika idonta tace "To Aunty ta yaya zan ga Ummanmu yanzu?" Aunty
Farida tace "Kar ki damu kiyi zaman ki nan wajen Baaba Gaje, gobe da safe in za mu tafi asibiti sai mu fara
biyowa ta nan da Umman tunda asibitin Malam Aminu kano ne" A hankali Khaleesat tace "Toh Allah ya kai
mu Aunty" Sai bayan Magrib Aunty Farida ta bar gidan bayan ta ci tuwon da Khaleesat tayi ma Gaje, sosai
Khaleesat taji ta samu rest of mind bayan taji jikin Ummanta da sauki, bayan Isha Gaje ta gyara mata ɗan
lungun da zata kwanta a dakin ta daura mata net din sauro tace "Allah dai ya rabaki da cinnaku" ita dai
Khaleesat tayi murmushi kawai bata ce komai ba, ita matsalarta ma zafi, ko ya zata yi da zafi yau gashi
karamin dakin wani ɗan mitsitsin window ne kawai ke garesa, su bakwai kuma zasu kwana a ciki,
Khaleesat ta gama shirin kwanciya don tayi wanka sannan ta shiga net din ta kwanta, ta amshi maficin da
gaje ke mika mata ta cikin net din, tun dawowarta sai a sannan tayi subscription ta shiga WhatsApp dinta,
Message din Safiyyah dake tambayarta ko ta isa lafiya kadai tayi ma reply, bata yi mamakin rashin ganin
message din Abdul ba don she isn't even expecting his message, ajiye wayar tayi ta gyara kwanciyarta ta
lumshe ido, Housemate dinta ne ya fado mata, she have no access to him balle ko godiya ma tayi masa,
bata yi tunanin da ta fito zata tafi airport bazai tambayeta phone number dinta ba, ko Airport din ma bata yi
tunanin bazai yi offering yace zai kai ta ba, juye juye kawai take yi a net din idonta a rufe, after a while of
thinking bacci ya dauketa. Washegari Khaleesat ta gama yi ma Baaba Gaje duk aikace aikacen gidan, ta
hura gawayi ta daura ruwa tayi ma kananun jikokinta wanka sannan ta dama kunu, Baaba Gaje ta fita siyo
masu kosai a titi, har karfe goma Khaleesat bata ga Aunty Farida sun zo gidan da Ummanta ba, gaba daya
ta damu taga Ummanta, Baaba Gaje tace "To ke sai ruwan ya salance zaki je kiyi wankan? Ba fa wani
gawayin" Khaleesat tace "Zan yi" Daga haka ta mike ta tafi yin wankan, tana fitowa daga wanka taga
takalmin da Aunty Farida ta zo da shi jiya a bakin kofa da wani takalmin daban wanda ko ba a fada ba tasan
na Ummanta ne, da sauri ta shiga dakin Baaba Gaje taga Ummanta da Aunty Farida a zaune, tsallake Aunty
Farida tayi ta tafi gun Ummanta da gudu cike da farin cikin ganinta ta durkusa gabanta ta rungumeta, Aunty
Farida tace "Ko dai baki da hankali ne?" Baaba Gaje tace "Toh da sauki dai kam" Ita dai Umman sai kallon
Khaleesat take, gaba daya Khaleesat ta ma mance wai Umma bata da lafiya tsabar farin cikin ganinta, a
hankali Umma tace "Meyasa zaki biyo hanya Khaleesah? Abdul din ne yace ki dawo?" Khaleesat ta kamo
hannunta cike da damuwa tace "Umma ya jikin?" Umma tace "Naji sauki Alhamdulillah" Khaleesat tace
"Aunty Sha'awa tace min ko magana fa baki yi" Baaba Gaje ta rike haɓa tace "Oh ni 'ya su, kun ji er iska
ko? Wallahi Sha'awa da kyar taga annabi, babu yanda bamu yi da ita ko da wasa kar ta gaya maki ba ashe
sai da ta zaga ta fada, har ce mata nayi tace maki tayi tafiya ko da zaki buga nata wassol" Khaleesat ta daga
kai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login