Showing 12001 words to 15000 words out of 152206 words
Ta kalli ledan, ya
juya ya bar wajen ta bi sa da kallo har ya koma parlor, sauke idonta tayi, bayan few seconds ta duka ta dau
ledan ta juya ta koma dakin. Khaleesat ta bude abincin da ya kawo mata ta fara ci kenan wayarta ya fara
vibrate, mikewa tayi ta bude handbag dinta ta ciro wayar, sosai gabanta ya fadi ganin Abdul ke kiran ta,
zaunawa tayi gefen gado tana kallon screen din wayar har sannan gabanta na bugawa, kafin kiran ya katse
tayi karfin halin dagawa ta sa handsfree sannan tayi sallama cikin sanyin murya, maimakon ya amsa sai ji
tayi yace "Wato all this While ni kike jira in kiraki ko Khaleesat?" Ta sauke idonta a hankali tace "To ai
cewa kayi duk sanda kake son magana da ni zaka kirani amma kar in sake in kira ka" Yace "Don nace kar
ki kirani sai ki ki kiran nawa? Me yasa baki reason ne?" A sanyaye tace "Kayi hakuri" Yace "In ban hakura
ba ya zan yi da ke? Ai saboda baki damu da ni bane yasa kika zama comfortable without calling me all this
while, ko da bazan daga ba ai kamata yayi ki kira" Cikin sanyin murya tace "Kayi hakuri" Yace "Yaushe za
ku fara jarabawa?" Tace "Probably nan da 6 to 7 weeks" Yace "I can't wait har zuwa nan da sati bakwai ban
gan ki ba Khaleesat, idan na samu lokaci zan shigo anytime from now in sha Allah" Shiru Khaleesat tayi as
if trying to process what he just said, yace "Hello" Da sauri ta kifta ido tace "Na'am ina ji" Yace "Me yasa
kika yi shiru? Ko baki son in zo ne?" Tayi yake tace "Aa ban yi shiru ba network ne, ban ji me kace ba"
Yace "Ohk, nace you should expect me any moment from now" A hankali tace "Toh Allah ya kai mu" Yace
"Ameen, me kike yi yanzu?" Tace "Abinci nake ci" Yace "Ohk switch to video call" A hankali tace "Toh"
Mayafinta ta jawo sannan tayi yanda yace mata.
✍🏻
07087865788 for more info
[5/2, 5:50 PM] khaleesat Haiydar ✍️: ✨✨ HALYSAAH ✨✨
✍🏻
By _Khaleesat Haiydar_
5......
Wajen karfe biyar na yamma Khaleesat ta fito parlor daga dakinta, window ta nufa tana leka garage ta ga
motar Housemate dinta alamar yana gidan, juyawa tayi ta tafi kitchen zata yi disposing takeaway din da
yayi mata daxu, ta window din kitchen din ta hangosa zaune a Lawn din dake bayan kitchen din waya ƙare
a kunnensa alamar he is making a phone call, komawa baya tayi don kar ya hangota ta window din kitchen
din, ta ajiye ledan hannunta a hankali ta juya ta fita daga kitchen din ta dawo parlor, tsaye tayi tana kallon
handle na kofar living room din, sai kuma ta tafi gun da ya ajiye takardun karatunsa ta hau bincika Books
din da sauri, har ta gama dube dubenta bata ga abinda take nema ba, ta koma kitchen din tana kara lekansa,
seeing he is still on call ta dawo da sauri ta tafi corridor din dakunansu, tsaye tayi gabanta na faduwa as if
contemplating on whether to do what is on her mind or just forget it, ganin she is just wasting time ta runtse
idonta ta bude, sai kuma ta kai hannu handle din kofar dakinsa a hankali ta bude ta shiga ciki zuciyarta na
bugawa, bin dakin that was neat and tidy ta fara yi da kallo kafin ta karasa can ciki da sauri, har sannan tana
kallon ko ina na dakin, ta ma rasa daga inda zata fara duba abinda ta shigo nema, zagaye dakin ta fara yi
tana dube dube with confusion, daya wayarsa dake gefen gado yayi haske alamar shigowar sako, kallon
screen din wayar take yi ganin wani matashi kamarsa a shekaru ne a fuskar wayar, ta juya ta kalli Trouser
dinsa, gabanta na faduwa ta dauka ta kai hannu aljihun wandon, Dollar ta ciro masu yawa tayi saurin
ajiyesu gefen gado, sannan ta duba daya aljihun, zaro ido tayi jin makulli da Counter a ciki, ta ciro da sauri
tana kallon makullin taga makullin kofar parlor ne, bata san sanda tayi murmushi ba ta ajiye wandon a inda
ta dauka sannan ta juya da sauri, ƙamewa tayi a spot din da take ganinsa tsaye bakin kofar dakin ya
rungume hannu yana kallonta daga sama har kasa, kawai ta juya masa baya zuciyarta na bugawa taji kamar
ƙasa ya bude ta shige ta huta, after some seconds taji yace "Sannu da aiki" Ita dai ta kasa juyowa, she felt so
ashame at that moment, she wish this never happened, sai juya makullin hannunta take with shame, Calmly
yace "Give me the key" Ta wani turo baki taki juyowa tace "To ba amfani zan yi da shi ba" Yace "Dama in
bana nan bincike kike shigowa ki min a daki?" Bata san sanda ta juyo tana kallonsa babu ko kiftawa ba jin
abinda yace, sai kuma ta ajiye makullin a gefen gado ta nufi kofa ta bi gefensa ta fice daga dakin ta shiga
nata ta tura kofar, nan da nan taji hawaye ya cika idonta ta zauna gefen gado, sai kuma ta ɗora kanta saman
pillow hawaye na sauka idonta har da shessheka. Karfe bakwai da few minutes Khaleesat na zaune kan
darduma, tun da ta idar da sallah take zaune wajen, da ta tuna abinda Housemate din nata yace mata sai taji
hawaye ya cika idonta, gaba daya taji ta tsani zaman gidan, kuma bata jin zata iya ci gaba da zama as far as
he is here, ta yanke shawaran kawai zata gaya ma Abdul ya canza mata gida kamar yanda Safiyyah ta bata
shawara tun farko taki dauka, wayarta dake gefen gado ta dauka jin ana kira, tana dubawa taga Mustapha
ne ke kiranta, ajiye wayar tayi gefenta taki dauka har ya katse, ya sake kira nan ma taki dagawa, bayan ɗan
lokaci aka sake kiranta kallon wayar tayi a bit fed up thinking it's still Mustapha sai taga Abdul ne ke
kiranta this time around, ta jawo wayar a hankali tayi picking ta kai kunne, sallama tayi masa sannan ta
gaishesa, yace "Ya naji muryarki haka?" Tayi shiru tana tunanin ta inda zata fara sanar masa the situation at
hand, muryarsa ya dawo da ita tunanin da take, a ɗan tsawace yace "Ke, baki ji na ne zaki min shiru?" Kasa
gaya masa tayi don bata ma san yanda zai fara daukar lamarin ba barin yanda taki gaya masa tun farko, Ta
ɗan yi yake tace "Ina jin ka, kawai muna da wani jarabawa ne gobe, kuma ina jin ciwon kai, and I haven't
covered up, shi yasa nake damuwa" Yace "Na ce ki dena stressing kanki da karatu, u are not dull to be
studying as if ur life depends on it, read a little and get enough rest, nasan za ki yi passing ko ma me za
kuyi gobe" Tana murmushin karfin hali a hankali tace "To" Yace "Kin ci abinci ne?" Ta girgiza kai tace
"Ban ci ba" yace "Ohk get something to eat, idan kin gama sai ki kirani ina jiran ki" Tace "Toh" Katse
wayar yayi, ta bude WhatsApp dinta tana duba ko Neighbor dinsu ta mata reply taga ta hau WhatsApp din
amma still bata yi reply ba, yau kwana uku kenan basu yi magana da Ummanta ba, Dialing din Number
Sha'awa tayi ta direct call, har ya katse ba a daga ba, sai da ta sake kira aka daga, sallama Khaleesat tayi
mata sannan ta gaisheta, Sha'awa ta amsa tace "Lafiya lau Khaleesah, ya karatu?" Khaleesat tace
"Alhamdulillah ya gida ya su Kamilu?" Sha'awa tace "Duu lafiyansu lau wallahi" Khaleesat tace "Su
Ummanmu suna lafiya..." Sha'awa tace "Kwana biyu kinyi magana ta wassap kinji shiru ko, to Ummanku
dai bata da lafiya amma da sauki yanzu" Nan da nan Khaleesat taji hankalinta ya tashi don dama tun da taji
shiru for days tasan ba lafiya ba, don ko bata yi ma Ummanta magana ba ita zata mata ta wayar Sha'awa taji
ko tana lafiya, Hankalinta a tashe tace "Aunty Sha'awa tun yaushe?" Sha'awa tace "Ina jin yau kwana uku,
ai an ma ce kar a gaya maki, shi yasa ko mayar maki da sakon da kika yi ta wassap din ma ban yi ba,
yanzun ma kar ki wani ce zaki kira kowa kiyi ta mata addu'a kawai Allah ya bata lafiya" Khaleesat taji
hawaye na sakko mata ta kasa cewa komai, Sha'awa tace "Wai daga ta tashi zata fito daki tayi alwalan
magariba shi ne fa ta yanke jiki ta fadi a bakin kofar dakin, duk kwanan nan ina rabata da saka ma kanta
damuwa tunda tasan matsalarta na hawan jini, to kinga ai irin haka ake gudu gashi kuma ya faru, Farida ma
ta taho daga legas tun jiya ta iso, kar ki wani tada hankalinki don jikin da sauki" Cike da karfin hali
Khaleesat tace "Suna asibiti ne yanzu?" Sha'awa tace "Wani asibiti? To har sai da Farida ta zo sannan ta kai
ta asibiti jiya in gaya maki, amma duk kwanakin nan tana gida gashi ko taɓata kika yi a daya barin jikinta
bata ji wai, ko magana ma in tayi sai kin sa kunne sosai zaki ji, ke abun fa ba kyau, har yanzu hankalinmu a
tashe yake, an dai ce kar a gaya maki kar hankalinki ya tashi...." Khaleesat in hankalinta yayi dubu ya tashi
a lkcn, ta kalli Screen din wayarta jin kiran ya katse alamar katin ta ya kare, ajiye wayar tayi ta fara rera
kuka kamar an sanar mata da mutuwa... Har karfe goma na dare Khaleesat ta kasa tashi daga kan darduman
da take, sosai ta shiga damuwa ba kadan ba, a inda take zaune Abdul ya kirata sau biyu amma ta kasa
picking call din nasa, karfe goma da rabi taji anyi knocking kofar dakinta, ta juya ta kalli kofar tana share
hawayen dake idonta amma bata tashi ba sai ma hade rai da tayi, after a while ya sake knocking still dai
bata tanka ba, sai kuma taji yace "Assalamu alaikum" kawai ji tayi ya bude kofar dakin ta juya da sauri
daga inda take zaune suka hada ido, daga nan bakin kofar ya tsaya yana kallonta, ita dai taki yarda ta sake
hada ido da shi, ya karasa ciki ya tsaya still leaving enough distance between them, calmly yace "Maganar
da na maki yasa kike kuka? But i was only pulling ur legs Halysaah, i am sorry about that, was just joking"
Wasu hawaye suka cika idonta sai kuma ta fara kuka, bude ido yayi alamar mamaki sosai yana kallonta, can
dai ya kwantar da murya yace "Look, do not take my words serious Halysaah ni wasa nake maki wallahi"
Ta rufe fuskarta da Hijab din jikinta tana kuka a hankali, dukawa yayi da mamaki sosai yana kallonta ya ma
kasa cewa komai, after few seconds da taji shiru ta ɗan bude fuskarta don tunaninta ya fita daga dakin, suna
hada ido ta daure fuska tace "Ni saboda kai nace nake kuka?" Yace "Toh why are you crying?" Shiru tayi
bata ce komai ba wasu sabbin hawayen na cika idonta, Yace "Tell me Halysaah, what is making you cry?"
Kamar bazata ce komai ba sai kuma tace "My mother is sick" Yace "Hasbunallah, what's wrong with her?"
bata sake ce masa komai ba tana goge idonta, After few seconds ya sauke ajiyar zuciya yace "Amma ai ba
kuka zaki zauna kina yi ba, addu'a zaki mata Allah ya bata lafiya" Nan ma dai bata ce komai ba, ya mike
yace "Allah ya bata lafiya" Sai a sannan tace "Ameen" Yace "Are you going back home to check on her?"
Ta daga kai ta kallesa amma bata ce masa komai ba, yayi shiru shima, can yace "Are you from kano?" Ta
gyada masa kai, Yace "Allah Ubangiji ya bata lafiya, and try getting something to eat for Dinner" Ta
sunkuyar da kanta kawai, ya juya ya fita daga dakin ya kullo mata kofar gently. Wajen karfe sha biyu na
dare Khaleesat na kwance taji ya sake knocking kofar dakinta, juyawa tayi ta kalli kofar, bayan wasu yan
sakwanni ta mike zaune tana kallon kofar, sai da ya sake knocking sannan ta sauka daga saman gadon ta
dau hijab dinta ta saka ta nufi kofar ta bude, yace "Are you still crying?" Ta hade rai ta girgiza kai without
looking at him, yace "Ok naga baki fito kinyi dinner ba and it's past 12, ki nemi abinda za ki ci kar ki
kwanta haka" Ita dai bata ce komai ba, yace "Hello" Daga kai tayi ta kallesa tace "Naji" Yace "Good" Kullo
kofar dakin nata tayi ta nufi kitchen tana tafiya a hankali, sai da yaga ta shiga kitchen din sannan ya shiga
dakinta yana bin ko ina da kallo, after a while Khaleesat ta fito daga kitchen din with a cup of tea and some
cookies, tsaye ta gansa corridor, bayan ta karaso yace "Kin ga nima Ummi na bata da lafiya amma ban
zauna ina kuka ba kamar yanda kika yi" Khaleesat bata kallesa ba ta shige dakinta ta kulle kofa, tana gama
shan shayin ta koma saman gado ta kwanta, tasan yau da kyar ta iya bacci, she wish she can just see herself
in Nigeria, but how?? Wasu hawaye ne suka zubo idonta ta lumshe ido, after a while ta jawo wayarta a
hankali tayi dialing number Abdul bayan ta tuna ya kirata har sau biyu daxu bata iya tayi picking ba, har
kiran ya katse bai daga ba, ta sake kiransa nan ma bai daga ba, tasan as usual yayi fushi kenan, ko uxuri
bazai mata ba, ajiye wayar tayi ta juya zuwa daya side din gadon. Washegari da safe Khaleesat na zaune
daki tana ta kokarin kiran Aunty Farida amma baya shiga, har Sha'awa sai da ta kira ita ma wayarta baya
shiga, ta rasa wa kuma zata kira, ta kalli agogon wayarta dake nuna karfe goma sha daya ta ajiye wayar tayi
tagumi, tun daga daren jiya har yau bata da sukuni, ko schl din ma yau tasan bazata iya zuwa ba, juyawa
tayi jin knocking a kofar dakinta, tana dai zaune har sai da ya kwankwasa kofar sau uku sannan ta sauka
daga saman gado, walking slowly ta tafi ta bude kofar, Yace "Good morning Halysaah, how was ur night?"
Without looking at him tace "Fine" Yace "Ya jikin Mama? Kun yi communicating da su?" Kai kawai ta
gyada masa bata ce komai ba kuma bata kallesa ba, Paper da pen din hannunsa ya mika mata yace "Can i
get ur Email Address?" Ta daga kai ta kallesa da mamaki tace "I don't understand" Yace "I mean ur Email
Address" wayarsa ne ya fara ring ya mika mata takardan da pen ya daga kiran sannan ya juya ya bar wajen,
ita dai ta bi sa da kallon mamaki, can ta juya ta koma daki ta ajiye takardan da pen da ya bata, after some
minutes sai gashi ya dawo yayi knocking yace "Can i get the paper" Tasowa tayi ta bude kofar bayan ta dau
pen da takardan tace "Why are you asking for my Email Address?" Yace "Ki dae rubuta ki bani" Shiru tayi,
sai kuma ta jinginar da paper din jikin kofa ta rubuta sannan ta mika masa ya amsa ya juya ya bar wajen,
yana fita da few minutes taji message ya shigo wayarta, ta dau wayar ganin E-mail ne ya shigo ta bude,
kallon Image din da ta gani as Email din ta dinga yi babu ko kiftawa, she look shocked and confused at the
same time, ta daga kai tana kallon kofar dakinta babu ko kiftawa, dai dai sanda taji sallamarsa, kasa tashi
tayi daga inda take zaune, har sai da yayi knocking sau biyu tayi karfin halin mikewa ta isa kofar ta bude
tana kallonsa, Yace "I don't know if you find this okay and a good idea" Ita dai bata fasa kallonsa ba
looking speechless, Yace "Hope they won't be Mad at this back home Halysaah?" Jin bata basa amsa ba ya
gyada kai yace "I guess it's a bad idea, I should have ask for ur opinion first before doing this" Nan da nan
hawaye ya cika idonta ta sunkuyar da kanta, yace "Ok it's fine, i will get the ticket cancelled" Daga kai tayi
da kyar tana kallonsa hawaye na zuba idonta tace "Thank you so much, i appreciate" Yace "Sure??" Ta
gyada masa kai, yace "Ohk, u can order a Lyft that will be taking u to the airport later, ur flight is at 3pm
today" Sauke idonta tayi cause she is totally speechless, ya mika mata travelling documents dinta, amsa tayi
cike da mamakin how he got them, ya juya ya bar wajen, komawa cikin daki tayi ta kulle kofar tana kallon
inda take ajiye travelling doc din nata a dakin, did he come to her room to check ne, to ai throughout babu
inda taje, ta karasa gefen gado har sannan jikinta a mugun sanyaye ta zauna, kallon screen din wayarta ta
sake yi tana kallon ticket din don ganin abun take kamar a mafarki, tana kara duba taga tun daren jiya ya
siya ticket din and kamar yanda yace the flight is by 3pm today, ta ma rasa ko farin ciki zata yi ko kuma
wani reaction zata yi, amma da ta tuna she is going back home to see her Mom which was her wish since
yesterday sai taji wani farin cikin da tunda take bata taɓa jin irinsa ba a rayuwarta, 80% a cikin dari na
damuwarta ya ragu cikin lokaci kankani, kallon agogo tayi taga sha daya ya wuce sosai, the weakness she
is been feeling since this morning immediately vanished, mikewa tayi tana share hawayenta ta dau medium
box din kayanta.... Karfe biyu Khaleesat ta gama duk abinda take, har sallan zuhur tayi, Lyft din da tayi
ordering kawai take jira, tana zaune gefen gado xuciyarta fal da tunani kala kala, babban burinta a yanzu
bai wuce ta ganta kusa da mahaifiyarta ba, in yaso koma me zai faru daga baya sai ya faru, kallon wayarta
tayi taga Safiyyah ce ke kiranta, tun daxu da safe ta kirata amma sbda damuwar da take ciki ko picking bata
iya tayi ba, Khaleesat ta daga kiran ta kai kunne, Safiyyah tace "Khalee me yasa baki shigo schl ba yau?
Are you okay?" Khaleesat ta sauke boyayyen ajiyar zuciya tace "Ummanmu ce bata da lafiya Sophie"
Safiyyah tace "Subhanallah, amma ya jikin yanzu?" Khaleesat tace "Da sauki" Safiyyah tace "To Allah ya
bata lafiya, plss nasan ki kar ki sa ma kanki damuwa kawata addu'a kawai zaki dinga mata, nasan kilan kina
nan kina ta kuka ko?" Khaleesat dai tayi shiru bata ce komai ba, Safiyyah tace "In sha Allah in mun gama
lectures zan taho" Khaleesat tace "I am sorry ban