Showing 63001 words to 66000 words out of 152206 words

Chapter 22 - HALYSAAH by Khlst Hydrr

13 May 2026

59

"Did you throw up?" Kai kawai ta gyada masa tana maida
numfashi, gun da ya ajiye hot chocolate din ya tafi ya dauko mata yace "Pls ki sha ko kadan ne sai in baki
magani" Ta girgiza masa kai, yace "C'mon Halysaah, kadan fa za ki sha" Yana rike da cup din don kar ya
sakar mata ta zubar, a haka ta kurbi shayin kadan, sai da yasa ta kara sha sannan ya ajiye shayin ya dauko
magani, tana ganin maganin ta fara girgiza masa kai da sauri don har taji wani aman zai taho mata, bude
kofar dakin aka yi Jay ya juya, AJ ya gani tsaye bakin kofar yana kallonsu, Jay bai sake kallon inda yake ba
ya maida dubansa kan Khaleesat yace "Pls ki daure ki sha Halysaah, ko baki son ki samu relieve?" Kara
girgiza masa kai tayi hawaye ya fara sauka idonta, lallabata Jay ya fara yi akan ta sha maganin, AJ ya wani
hade rai yace "Kee baza ki amshi maganin da ake baki ba? Wa zaki ba wahala?" Jay yace "Ba ruwanka pls
AJ, get out" Ita dai Khaleesat ko kallonsa bata yi ba tana fama da kanta, Jay bai sake takurata kan ta sha
maganin ba ya mike yace "Toh ki daure ki hau kan gado ki kwanta, i am coming now" Ta gyada masa kai,
ya juya ya nufi kofa, ko kallon Ajay bai yi ba ya fita daga dakin, AJ ya tabe baki ya juya ya koma
downstairs. Haka nan Jay ya hado alluran da za mata don saukar mata da zazzabin, sai da ta ga ya dawo
dakin sannan ta daure ta koma saman gadon tana ganin jiri ta kwanta, ya tsaya gefen gadon yana rike da
alluran yana kallonta, ta marairaice ta girgiza masa kai kawai alamar bata so, ya kwantar da murya yace "To
ya kike son in maki Halysaah? Kin ki shan magani" wayarsa dake aljihunsa ya ciro jin yana ringing ganin
Salem ke kiransa ya ajiye alluran hannunsa yace "I am coming Halysaah" Fita yayi daga dakin, ya sauka
downstairs ya tarar da Salem zaune parlor, bayan sun gaisa Salem yace "Slide dina nake son zaka duba min
Jay" Shi dai AJ na zaune yana kallon kwallo ga Legend a gefensa, Jay yace "Ohk, but tunda ka zo pls zaka
yi injecting Housemate dita she is sick" Salem yace "Ayya, shi sa ta kira jiya, Allah ya bata lafiya, tana can
gidan nata ne?" Jay yace "No, she is upstairs, mu je in nuna maka dakin da take" A tare suka wuce sama, AJ
dai kallonsa kawai yake a TV kamar bai san suna parlon ba, Jay bai shiga dakin ba bayan ya nuna ma
Salem ya dawo downstairs ya zauna, Khaleesat bata yi ma Salem wani musu ba don ba ma ta da wannan
strength din duk da yanda bata son allura haka nan ta bari ya mata, tsabar zazzabin dake jikinta ko zafin
shigar alluran bata wani ji ba, Salem yayi mata Allah ya sauwake sannan ya fita daga dakin ya koma
downstairs, Jay yace "Thank you, bari in duba maka" Sai bayan kusan minti talatin Jay ya tafi dakin
Khaleesat ya sameta tayi bacci, ya sauke ajiyar zuciya ya karasa kusa da gadon ya kai hannu kusa da
goshinta sai dai bai taɓa ta ba, nan yaji temperature dinta ya fara sauka, juyawa yayi ya dau sauran shayin
da ta bari ya fita daga dakin..... Wajen karfe sha daya da rabi Khaleesat na kwance hannunta rike da wayar
Housemate dinta, tun 20 min ago ta tashi daga baccin da ya dauketa daxu, she felt a bit relieved now da
alluran da Salem yayi mata, sai dai har sannan kanta bai daina mata ciwo ba kamar ta cire ta huta, tayi
kokarin ta tashi ma ta tafi bandaki amma ta kasa, she is so weak kamar warce ta dade tana ciwo, hakan yasa
kawai ta jawo wayar Jay, da har zata shiga gallery dinsa to while away time amma sai taga it's not proper ta
shiga hotunansa, hakan yasa ta shiga wani game da ta gani kawai tana yi daga kwancen da take, bude kofar
dakin aka yi ta daga idonta, Jay ne ya shigo dakin AJ dake bayansa yaki karasowa ciki ya tsaya daga bakin
kofar, Jay ya nufota yace "Ashe kin tashi, how are you feeling now Halysaah?" Ta gyada masa kai a hankali
tace "Good morning" Yace "Morning Housemate, are you feeling much better now?" Kai kawai ta gyada
masa, yace "Ohk bari a kawo maki breakfast, idan kinyi sai ki daure ki sha magani kin ji" Ita dai bata ce
masa komai ba ya juya ya nufi kofa ya fita ya mika ma AJ wayarsa sannan ya sauka downstairs zai kawo
mata breakfast, shi dai AJ daga sama har kasa yake kallonta, ta ɗan saci kallonsa to see if he is still standing
by the door ko ya tafi, hada ido suka yi ta dauke idonta tana ci gaba da game dinta da take, after a while ta
kara satan kallon bakin kofar taga ya bar wajen, sai ga Jay ya shigo ya ajiye mata tray din breakfast ta dinga
kallon plate din baked beans irin na turawa a gefe da soyayyen kwai a gefe, with veggies, sai sausages, ga
cup din hot chocolate with few slices of bread a gefe su ma, ita dai tasan ba iya cin wannan abincin zata yi
ba, yana kallonta yace "Can you give me ur frnd Safiyyah's Home address?" Ta sauke idonta ta gaya masa
address din, yace "Ohk, na ma san area din, i have a frnd there" Ita dai tayi shiru, ya dauko mata maganin
da taki sha daxu ya ajiye kusa da ita yace "Pls ki daure kiyi breakfast din, sai ki sha drug din kafin in dawo"
A hankali tace "Toh nagode" ya mata murmushi ya juya ya fita daga dakin ta bi sa da kallo. Jay ya tarar da
AJ zaune a waje gurin shan iska dake compound din yanna danna wayarsa, hakan yasa ya nufesa ya zauna
kujeran dake facing dinsa yace "AJ, i think i am confuse at this point, what do u suggest about this young
girl's issue?" AJ ya daga ido ya kalli Jay yace "My suggestion is that... ka barta ta tafi duk inda ma zata ka
cire hannunka da bakinka cikin wannan case din babu abinda ya shafe ka, a cikin kunnenka kaji tace shi
gayen ne ke sponsoring dinta, babu kuma ta yanda zai yi sponsoring dinta without the consent of her
parent, kaga they are comfortable with that, so who are you to intrude Jawwad? Baka san komai akan ta ko
kan saurayin ba don me zaka zakalkale haka? Tare fa ka gansu, da can baya zuwa America din ya sameta ne
a gidan? sai yanzu tasan yana molesting dinta? Girl's can be very cunning fiye da tunaninka, don't start
what u can't finish Jawwad" Jay dake ta kallonsa yace "So now what are you insinuating?" AJ yace "Since
you are daft kar Allah ya sa ka gane abinda nake insinuating" Jay dai kallonsa kawai yake, after a while a
hankali yace "But duba da abinda ya faru tsakaninka da guy din kasan zai iya hurting dinta idan nace ta
koma gidan nan AJ, she is no longer safe in that apartment, ka dai ga ba ma cikakken hankali ke gare gayen
ba, ka duba fa wuka yaje ya dauko a kitchen" AJ ya gyara zama yace "Sai kayi mata hanyar komawa gun
iyayenta as the good Samaritan that you are from Samaria, kaga in ta koma sai ta gaya ma iyayen nata
abinda ke faruwa da abinda selfishness dinsu ya ja mata a kasar mutane, sai su yi sorting kansu a can
kawai" Jay yace "Kar kace haka, we know nothing about why they allowed him to sponsor their daughter,
we shouldn't judge them har sai mun san dalilinsu AJ" AJ yace "Dalilin banza, babu responsible parent din
da za su damka ma kato irin wannan mutumin er su ya kai ta wata kasa da sunan karatu, it doesn't even
make sense, sai kace ba musulmai ba, ko da cousin brother dinta ne ma abun bai yi tsari ba balle babu ko
wani relationship na jini tsakaninsu, who does that" Jay ya sauke ajiyar zuciya yace "Duk da haka dai ni
bazan yi judging dinsu ba tare da nasan komai ba, let give them benefit of doubt" AJ yace "Sai kayi ta basu
ai, ni kam bazan bayar ba" Jay yace "But komawarta Nigeria yanzu bazai yiwu ba AJ, ba shine solution ba,
Monday za su fara exams, John Hopkins university take ita ma fa" AJ yayi dariya har da kyakyatawa yace
"Tabb, lallai gayen ya kashe kudi ba na wasa ba" Jay dai kallonsa kawai yake, AJ yace "Toh za a fara
exams me kake nufi kenan? Naji ka ce apartment din nata is not safe for her anymore..." Jay yace "She will
remain here har su gama exam kafin ta koma Nigeria wajen iyayenta" AJ ya wani kallesa da sauri yace
"What do you mean? Kana nufin mu zauna gida daya da balagaggiyar yarinya da ba muharramar mu ba
kamar wasu jahilai marasu tsoron Allah? Kai da wa za ku yi wannan nonsense din??" Jay yace "Duk yan
iskan turawan da kake kawowa gidan nan ka basu daki su zauna dama muharramanka ne ban sani ba?" AJ
yace "Turawa kace ai, kuma babu komai tsakanina da su kai ma ka sani, i am only helping most of them
tunda ba a garin nan suke ba" Jay ya mike yace "Ita ma haka za mu yi helping dinta tunda ba a garin take
ba, take it or leave it" yana kai wa nan yayi wucewarsa inda yayi parking motarsa, Ajay ya bi sa da wani
kallo, can yace "Sai dai ku je can ku biya wani apartment din ku zauna tare, babu wanda zai takurani a
gidan nan wallahi, dama ai kun saba zama gida daya tare, it's not a new thing, dole ne sae ta zauna gidan
nan cikinmu mu ba maguzawa ba" Shi dai Jay ya shiga motarsa ya fita daga compound din ya kama hanyar
gidansu Safiyyah....


*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment
07087865788 👈🏻, it's better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don
littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*
[5/20, 5:24 PM] khaleesat Haiydar ✍️: Jay na isa unguwan da gidansu Safiyyah yake sai ya mance
apartment din da Khaleesat ta gaya masa, hakan yasa ya kira wayarsa dake wajenta, Khaleesat na zaune
saman gado har sannan tana playing game da wayar, sosai gabanta ya fadi ta dinga kallon screen din wayar
ganin image din hotonsa da number da yayi appearing, sai taga kamar shi din ne a gabanta take gani, sai da
kiran ya katse ta zaro ido bayan tayi realizing bata yi picking ba har ya katse, bayan few seconds ya sake
kira, dagawa tayi ta sa handsfree tayi shiru, yace "Halysaah" Tace "Na'am" Yace "I think i forgot the
apartment u told me" Gaya masa ta sake yi yace "Thank you" Daga haka ya katse wayar ya ci gaba da
driving dinsa, dai dai gaban apartment din yayi parking don motar Mustapha baya nan, yana tsaye bakin
kofa yayi knocking gently, after a minute aka bude kofar parlon, komawa baya Safiyyah tayi tana kallonsa
da mamaki daga sama har kasa, ya ɗan mata murmushi yace "Hi Safiyyah" Ta bude ido sosai tana leka
motarsa da taga yayi parking thinking may be he is together with Khaleesat, ganin motar ba kowa ciki tace
"Hi, good afternoon" Yace "How are you doing Safiyyah?" Lokaci daya tace "Ko dai Khaleesat bata da
lafiya ne?" Da damuwa sosai tayi tambayar, Yace "Yeah bata da lafiya" Tace "Wallahi yanzu na gama
shiryawa nake son in ci abinci inje gidan naga miss call dinta jiya ina ta kira har yau wayar baya shiga, and
i am disturb" Yace "Shi yasa na zo in dauke ki idan ba damuwa so you can be together with her she is sick,
probably idan kin mata magana zata ci abinci ta sha magani" Da sauri Safiyyah tace "Sure, bari in dauko
gyalena" Juyawa tayi da sauri ta koma cikin gidan, shi kuma ya koma parking space, Surayya dake zaune a
parlon ta kasa kunne duk tana jin conversation dinsu kafin Safiyyah ta shigo, Safiyyah ko kallon direction
dinta bata yi ba ta tafi dakinta da sauri ta dauko jakarta da gyale sai wayarta sannan ta fice daga gidan,
ganin Jay cikin motarsa yana jiranta ta bude gaban motar ta shiga tana cewa "Tun jiya ne bata da lafiyan?
Kuma me yasa ta kashe wayarta?" Jay yace "Tace wayar ya fada ruwa ne" Safiyyah tace "Ohk" Sai da suka
dau hanya sannan Jay yace "Amma tana can gidanmu fa, can za mu je yanzu" Safiyyah ta juya da sauri tana
kallonsa da mamaki tace "Gidanku? Why? What happened?" Calmly yace "Before then za mu fara zuwa
apartment dinmu sai ki dau mata kayanta da zata yi amfani da shi, we left yesterday with nothing" Safiyyah
bata sake cewa komai ba tunani iri iri na yawo a ranta, to me ya faru? ta yaya Khaleesat da ta sani me
shegen taurin kai ta yarda har ta bi sa can gidan nasu? Ko dai rashin lafiyar nata is critical ne haka? Da
tunane tunanen nan suka isa apartment din, suka shiga ciki tare da Jay ta nufi dakin Khaleesat shi kuma ya
zauna a parlor, bayan few minutes ta fito tace "Kala daya zan dau mata kayan ai ko?" Jay ya mike yace
"No, 3 to 4 will be okay" Duk da confusion din da Safiyyah ta shiga bata dai ce masa komai ba ta juya ta
koma cikin dakin, ta dau akwati ta saka ma Khaleesat kayanta da duk abinda zata bukata a ciki, tana fitowa
daga dakin Jay ya mike yace "Kin dau mata duk abinda zata bukata?" Safiyyah ta gyada masa kai, suka fita
daga parlon, duk ta kagu taje wajen Khaleesat ita dae, silently suka yi tafiyar har suka iso gidan, bayan Jay
yayi parking ya sauka Safiyyah ma ta sauka, ya fiddo akwatin sannan suka nufi entrance din apartment din
Safiyyah na biye da shi, bai ga motar AJ a gidan ba alamar ya fita, suna haurawa sama Jay ya tafi dakin da
Khaleesat take yayi knocking, ya mika ma Safiyyah akwatin yace "Zaki iya shiga, zan je inyi sallah"
Safiyyah ta amshi box din tace "Ohk" Bude kofar dakin tayi Khaleesat ta dinga kallonta har ta shigo,
Safiyyah ta ajiye box din hannunta ta nufeta da sauri tace "Me ya sameki Khaleesat?" A hankali Khaleesat
ta sauke idonta ta kasa cewa komai don bata ma san ta inda zata fara ba, sai ga hawaye. Safiyyah na tsaye
dakin kusa da window bayan Khaleesat ta bata labarin duk abinda ya faru, tsabar yanda labarin ya kidima
Safiyyah kasa ci gaba da zama tayi gefen gadon, Safiyyah tayi shiru for almost 2 minute tana tsaye jikin
window tana girgiza kafa, ita dai Khaleesat goge hawayen dake sauka idonta kawai take, can Safiyyah ta
sauke wani ajiyar zuciya me cike da takaici tace "A baya da nake gaya maki Abdul ɗan daba ne ba kin
maida maganata abun wasa ba? Tunda uwata ta haifeni ban taɓa ganin ɗan iska kamar Abdul ba, yanzu da
baki samu lambar kowa ba haka zai lalata maki rayuwa babu digon tsoron Allah a ransa? Ya kashe uban
kudin zuwa USA kawai don ya zo yayi lalata? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, amma naji haushi da ɗan
uwan Housemate dinki bai sumar da shi ba an maida sa Airport a haka, tirr da Abdul, tirr da halinsa, i am so
happy that things turn out this way, in sha Allahu karshensa ne ya zo a rayuwarki" Khaleesat ta fashe da
kuka tace "Sophie ban san next action dinsa ba idan ya koma Nigeria, i am so restless" Safiyyah tace "Next
action dinsa? Sai ya koma ya gaya masu uban da ya kawosa USA da Intention dinsa, ke in zaki dena
wannan crocodile tears din naki ki dena don ba tausayinki zan ji ba, tunda dai bai samu nasaran lalata maki
rayuwa ba ni duk abinda zai faru ma ya dade bai faru ba, kukan uban me kuma kike ma mutane? Ko
nasaran da bai samu a kanki bane ya dame ki? Kuma wallahi ya ci sa'ar baki sameni a waya ba don kafin in
karaso gidan sai 911 sun riga ni, tuni zan kirasu ince gashi can za ayi fyade, banda iskanci duk karuwansa
basu ishesa ba sai ya zo ya kara dake? Gaskiya ki rike Housemate dinki da ɗan uwan nan nasa da kyau don
mutane ne su wallahi, da ba don su ba da yanzu wani zancen ake ba wannan ba, don da na kai maki ruwan
zafi yafi a kirga zuwa bandaki yanzu" Khaleesat dai bata sake ce mata komai ba tana share hawayen da
yaki tsaya mata, Safiyyah ta rike haɓa har sannan tana mamakin Abdul, can tace "Kamar irin ya zo wajen
matar nan tasa, ni wallahi da yaji suka barbada masa mu ga ta iskanci, shege kawai prostitute" Duk tashin
hankalin da Khaleesat ke ciki sai da tayi dariya don ita bata taɓa jin inda aka ce ma namiji prostitute ba sai
yau a bakin Sophie, Safiyyah tace "Ga dai katon daki an baki, kiyi karatun exams dinki cikin kwanciyar
hankali, nima in abun duniya ya isheni in taho nan in sameki kafin dare yayi in koma den dina, don ko da
wasa bazan ce ki dawo gidanmu ba ni kaina ban tsira gun tsinanniyar matar Yaya Musty ba kuma yaki
kwatar min en ci, da zai bar ni ba nima sai in dawo nan kusa dake ba tunda ba rasa abincin da za su bamu
mu ci za su yi ba, wannan dakin ai ya ishemu rayuwar America, bari kiji Khaleesat dama Allah ya riga ya
rubuta Abdul ne silan zuwan ki Amurka ki hadu da mutanen arzikin ki, babu me canza haka ko yaki ko ya
so dole sai ya kawoki ya hadaki da mutanen arzikin ki tunda Allah ya rubuta haka, iya role dinsa kenan a
rayuwarki, kuma Allah ne zai basa ladan hakan bamu ba, ba shikenan ba?" Khaleesat dake ta kallonta ta
girgiza mata kai tace "Ni bazan zauna gidan nan ba Sophie" Safiyyah na mata wani kallo tace "Ohk,
Apartment din naki zaki koma ki kai ma Abdul din kanki kenan?" Khaleesat ta sauke idonta kasa muryarta
na rawa tace "Bazan iya jarabawan ba Sophie, gwara kawai in koma gida, i want to go home, i want to go
to my mother" Safiyyah zata yi magana aka yi knocking kofar dakin, Safiyyah ta amsa aka bude

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login