Showing 3001 words to 6000 words out of 152206 words
for that apartment, bata karasa ba ta jingina jikin fence din dake
inda take tsaye tana kallon motar ta little space din dake between the wooden fence din, taga ya fito daga
motar ta bi sa da ido har ya shiga apartment din yana danna wayarsa, ta fi minti biyar tsaye a inda take,
daga karshe tana tafiya a hankali ta karasa apartment din ta murda kofar parlon taji ya kulle, hade rai tayi
tana kallon kofar, daga karshe da ta gaji da tsayuwa kawai tayi knocking, sau uku tana knocking sannan ya
bude kofar, yana ganinta yace "Hi" ita dai ko kallonsa bata yi ba fuskarta babu yabo babu fallasa ta bi
gefensa ta shiga parlon, direct gun wayarta dake kan kujera ta nufa ta dauka tare da reading materials dinta
dake saman kujeran, har zata dakinta sai kuma ta dawo ta tafi kitchen ta dau goran ruwa daya sannan ta nufi
dakin, sai da ta bude kofar tayi masa kallon gefen ido taga he is just busy sorting out some textbooks that
were inside a carton he came with, har ta shiga dakin nata bai juya ba balle ya kalli direction dinta....
✍🏻
07087865788
[4/29, 5:07 PM] khaleesat Haiydar ✍️: https://chat.whatsapp.com/KVY8hjs3iNq5ntSN4Z5g6V
✨✨ HALYSAAH ✨✨
✍🏻
By _Khaleesat Haiydar_
2.....
Washegari har karfe sha daya Khaleesat na dakinta bata fito ba duk da yunwan da take ji, tayi tagumi don
gaba daya ta ma rasa what is her problem particularly, ta dau wayarta jin shigowar WhatsApp message, tun
daxu suke chatting ta VN da Ummanta ta wayar makociyarsu Sha'awa, da taji shiru ta ma zata an maida ma
Aunty Sha'awa wayar nata ne, ta bude VN din tana sauraren voice din mahaifiyarta, Addu'a Ummanta ke
mata tana mata fatan nasara a karatun ta, sannan kamar ko da yaushe ta sake jaddada mata ta kula da
mutuncinta ta kula da kanta, daga karshe ta ƙare da cewa za a kai ma sha'awa wayarta don zata fita kasuwa,
Khaleesat ta sauke ajiyar zuciya ta ajiye wayar a hankali sannan ta mike ta dau hijab din sallanta ta saka ta
nufi kofa ta bude a hankali ta fita daga dakin don ta gaji da horan kanta da yunwa ita da ke breakfast da
wuri, kitchen ta tafi almost bumping into her new House mate shi kuma yana kokarin fitowa daga cikin
kitchen din, komawa baya yayi at the same time yace "Good morning" Bata yarda su hada ido ba ta matsa
gefe allowing him to pass, ya fito daga kitchen din yayi wucewarsa without looking at her, sai a sannan ta
shiga ciki, tsaye tayi tana kallon littered cups da plates din da yayi amfani da su ya bari a sink din wanke
wanke without washing them, ga bowl din fruit salad da shi ma ya ajiye bai sha ba, bin kofar kitchen din
tayi da kallon mamaki, to wa ya bari yayi masa wanke wanke? Ta fi minti daya tsaye a inda take da tunani
iri iri a ranta, wata zuciyar ta ce mata kawai tayi abinda ya kawota ta fita daga kitchen din ta bar unclean
utensils din a yanda ya bar su, amma dai kawai ta jawo liquid wash da sponge fuskarta a daure ta fara
wanke kayan wanke wanken kawai, bayan ta gama ta goggoge kitchen din ta hada shayi ta debi cookies a
plate sannan ta fita daga kitchen din ta wuce dakinta. Wajen karfe uku Khaleesat ta fito daga dakinta, tun da
ta gama breakfast take karatu sai sallah kawai ta tashi tayi da azahar, jin ko ina shiru and to be sure baya
gidan ta nufi kofar parlon zata bude taji an kulle da makulli, dakinta ta koma ta dauko makullinta ta bude
kofar tana duba garage taga babu motarsa a ciki, komawa cikin gidan tayi ta kulle kofar sannan ta tafi
kitchen, tun shekaranjiya take son cin shinkafa da miya amma kasancewar she is not comfortable tun da ya
dawo gidan yasa ta hakura da girkawa, yanzu da taga baya nan kawai tayi deciding tayi shinkafa da miyar,
bayan ta daura shinkafar, ta fara hada miyar dama tana da sauran chicken thighs a fridge, fitowa parlor tayi
da sweeper zata yi shara, ta ajiye sweeper din hannunta to tidy the couch first, dukawa tayi tana kallon
takardun Housemate din nata da ta gani, sai kuma ta kyabe baki ta bar su nan yanda ya bari a kan kujeran,
share rug din parlon ta fara yi bayan ta dauke makullin da ta gani a kasa, ta dinga juya makullin ganin
kamar na Bedroom ne, kafin minti arba'in ta gama girkin da take ta tsaftace ko ina na gidan, ta debi
abincinta ta tafi daki da shi, sai da ta fara yin sallahn Asr sannan ta dau wayarta tana dubawa, sosai gabanta
ya fadi ganin miss call din Abdul, nan da nan taji abincin ya fita ranta gaba daya, ta zauna gefen gado a
hankali tana kallon wayar, ta fi minti goma zaune a haka, she was soo worried, to yanzu me zata ce masa
ma in ta kirasa, daga karshe ta daure tayi dialing number nasa, har ya katse bai daga ba, ta sake kira nan ma
bai daga ba, duk da yunwan da take ji haka nan taji abincin ya fita ranta, ta tsani duk wani abu da zai sa
Abdul ya daga mata hankali, haka tayi forcing din kanta ta ci abincin sannan ta kwanta side din gado, bata
san sanda bacci ya dauketa ba a haka.... knocking kofar dakinta da ake yi ne ya farkar da ita daga baccin da
take, ta mike zaune da kyar tana murza idonta tana kallon kofar at the same time tana mamakin me zai sa
ya dinga bubbuga mata kofa haka, to ko dai bashi da kai ne?? ta jawo wayarta tana duba agogo taga karfe
shidda da mintuna, bata yi tunanin ta dade tana bacci haka ba, sake knocking da aka yi yasa ta mike tsaye ta
saka hijab fuska daure tace "What is that??" Ta ji yace "Ohk i think i misplaced my keys, just want to know
if you saw it while tidying up the parlor?" Sai a sannan ta tuna makullin da ta gani a parlor daxu da take
shara, tana tafiya a hankali ta karasa kofar dakinta ta murda key din jiki sannan ta bude door din, tuni har ya
bar corridor din ya koma parlor ya tsaya yana jiranta, da alama dawowarsa gidan kenan a lkcn, ta karaso
cikin parlon ba tare da ta kallesa ba, shi dai duba message din da ya shigo wayarsa yake with all his
attention, ta tafi inda ta ajiye makullin sannan ta dawo ta ajiye masa kan takardunsa dake kan kujera tace
"Here" Yace "Ohk" dakinta ta koma ta shiga tana mamakin wai Ohk, ba ma thank you ba kamar irin ya
ajiyeta din nan, kwafa tayi ta saka ma kofarta key, bayan Khaleesat ta idar da isha ta sake kiran Abdul bai
daga ba, sau hudu kenan tana kiransa tun karfe bakwai bai yi responding ba, yanzu dai tafi tunanin yana
bacci don dare ne sosai a can kasar, even at that tasan she is in soup, mikewa tayi ta dau plate din da ta ci
abinci daxu ta nufi kofa ta fita daga dakin, a parlor ta ga sabon Housemate dinta yana tattara takardunsa at
the same time yana answering phone call taji yana cewa "I am on my way now" Daga haka ya katse wayar
ya mayar aljihunsa ya dau takardunsa da makullin mota ya mike tsaye, ido hudu suka yi for the first time
tunda ya dawo gidan, ita dai ta dauke kai kamar bata ma gansa ba ta karaso cikin parlon zata tafi kitchen
taji yace "I ate a little out of the food you cook, and...." Yayi pointing takeaway din da ke kan kujera yace "I
am taking some to my frnd too" duk wannan abun bai kalli inda take tsaye ba yake magana, sai ita ce ma da
ta dinga kallonsa da mamaki babu ko kiftawa, ya dau takeaway din ya nufi kofa cikin hanzari, yace "Good
night" Ta bi sa da kallo har ya fita ya kulle gidan da makulli ta waje, mamaki yasa ta kasa karasawa kitchen
din, after some seconds ta tafi kitchen din, da plate din da ya ci abincin, da cup din da ya sha coffee, da
bowl din da ya sha fruits salad duk suna ajiye a sink babu wanki, ta jingina da kofar kitchen din ta rungume
hannu tana kallon sink din kamar zata fashe don bakin ciki, can ta karasa ciki tana duba shinkafar da ya bar
mata, taga da kyar in zai yi spoon uku, gashi duk yayi littering din wajen da shinkafar wajen diba kuma ya
bar shi haka, haka nan ta juye er shinkafar da ya rage a karamin bowl, ta wanke duk utensils din, ta gyara
ko ina ta goge sannan ta hada shayi ta koma daki da bowl din sauran abincin, zaunawa tayi gefen gado ta
dau wayarta tayi dialing number Safiyyah, sai da ya kusa katsewa Safiyyah tayi picking daga daya
bangaren tace "Allah da gaske baki da kirki Khaleesah, to ko baki kira ba dai na isa Virginia cikin koshin
lafiya" Khaleesat ta ɗan yi murmushi tace "Dama nasan kin isa lafiya ai, hope you are doing good?"
Safiyyah ta tabe baki tace "Oho dai, wannan ba matsalar ki bane" Khaleesat tace "Amma don Allah ina kika
ce ma Ya Musty za ki?" Safiyyah tace "Ahaf tsaya wasa, sai kace baki san ni ba, munafukar matarsa da
yake ba son zamana a gidan take ba ita ce ma ta kara convincing dinsa, duk zatonsu ina gidanki muna
group reading with some of our Coursemate" Khaleesat tayi murmushi tace "To ai shikenan, yanxu yaushe
zaki dawo?" Safiyyah tace "Gobe ne birthday din ai, in sha Allah i will be back on Monday" Khaleesat tace
"Toh Allah ya kai mu, kinsan mene?" Safiyyah tace "Aa" Khaleesat ta sauke ajiyar zuciya tace "Wallahi in
gaya maki Abdallah ne ya kirani nayi missing call dinsa as i am speaking to you now tun daxu nake
kiransa yaki picking, nasan fushi yayi sosai, ni kuma...." Safiyyah ta dakatar da ita tace "Ke kuma me?
Shikenan rayuwa babu uxuri dama?" Khaleesat tayi kasa da murya tace "He warned me times without
number kar in sake missing call dinsa Safiyyah, kuma wallahi ina kitchen sanda ya kira wayar kuma na
daki ba da gangan nayi missing kiransa ba" Sounding so pissed off Safiyyah tace "Wai don Allah me yasa
kika dauki tsoron duniya kika dora ma mutumin nan ne Khaleesat? For how long will things continue this
way? Yaushe za ki fara nuna masa ke fa mace ce? yanzu haka za ku yi auren ya maida ki slave a gidansa
tunda kin nuna masa kina mugun tsoronsa tun a waje? wannan wani irin gantalallen relationship ne?
Gaskiya ina jinjina maki Khaleesat, don wallahi in nice bazan iya ba Allah ma ya gani sai dai duk abinda
zai faru ya faru" Cikin sanyin murya Khaleesat tace "I have no choice nor option Safiyyah...." Tana fadin
haka hawaye ya fara gangarowa idonta, a ɗan fusace Safiyyah tace "To wai ke kadai ce mace a gidanku ne
da ya gani? Naga ga Labibah da Lamisah, ina ce sati biyu kika ba Labibah a shekaru, ita kuma Lamisah
wata daya, ga kuma yayyinki Samira da salamatu, to wai halan su ba mata bane sai ke??" Khaleesat dai
bata ce komai ba tana goge hawayen dake zuba idonta, Safiyyah ta sauke ajiyar zuciya tace "Ai shikenan,
but u really need to speak up for ur self Khaleesat, ni dai nasan their worst mistake is sending you to school
abroad, aje dai zuwa, ke kuma in har baki waye kin kwatar ma kanki 'yanci daga karshe ba to sorry to say
this, wallahi u will live a miserable life in the nearest future Khaleesat, this is just the fact i am saying, na
gaji da lamarin so called Abdul din ki" Cike da karfin hali Khaleesat tace "Ki daina cewa haka pls Safiyyah,
ke me tayani addu'a ce kan Allah ya kawo min komai da sauki amma ba ki dinga fadin wa ennan
maganganun ba...." Safiyyah ta taɓe baki bata dai ce komai ba, a hankali Khaleesat tace "Pls ko zuwa gobe
da safe ki masa magana ta Whatsapp ki tayani basa hakuri cause nasan bazai daga kirana ba no matter
what..." Safiyyah tace "To naji, Allah ya kai mu goben" Khaleesat tace "Ameen" Sallama suka yi,
Khaleesat ta ajiye wayarta. Karfe goma saura na safe Khaleesat ta fito daga dakinta rike da wayarta don kar
ma Abdul ya kira by mistake tayi missing call dinsa, tun jiya take makale da wayar duk don kar ya kira bata
sani ba, kuma sau uku tana kiransa bayan da tayi sallan asuba bai daga ba still, yanzun ma da ta tashi sae da
ta kirasa sau daya nan ma no answer, zaune taga new Housemate dinta a ɗan reading nook da aka tanadar a
living Room din studying with a huge textbook dake gabansa, she had no idea ma ya shigo gidan, don
bayan da tayi sallan asuba ta fito ta hada shayi ta sha da cookies a nan parlon sannan tayi karatu har zuwa
bakwai na safe, daga nan ta shiga daki ta kwanta sai kuma yanzu da ta tashi feeling hungry, sau daya ya
kalleta yana ci gaba da duba Textbook din gabansa yace "Good morning" Ta karaso cikin living room din a
takaice tace "Ok" Ajiye wayarta tayi kan 1 sitter ta nufi kitchen, Ya daga kai yana kallon direction din da ta
bi da harshen turanci yace "In baki yi breakfast ba, ga wani nan ki dauka....." Tsayawa tayi sai kuma ta juya
ta kalli Centre table da yake nuna mata, ledan abinci ne kan table din duk da bata san wani kalan abinci
bane a ledan, ta kallesa taga ya ci gaba da karatun da yake, girgiza kai tayi with no interest tace "No, tnx"
Daga haka tayi wucewarta kitchen, ta fi minti uku tsaye kitchen din tana tunanin me zata yi, seeing her
House mate sitted in the living room yasa ta zama uncomfortable to cook anything, hakan yasa kawai ta
dauko kwalin cereals da bowl zata hada cornflakes, wayarta ta ji yana ring a parlor don tun jiya ta cire
wayar a silent, bata san sanda ta saki both d bowl and the Cereal din hannunta ba ta fito daga kitchen din
within few seconds, House mate dinta ya bi ta da kallo har ta nufi gun wayarta ta dauka da sauri, sai da
gabanta ya fadi ganin Abdul ne ke kiranta, babu bata lokaci ta daga call din, zuciyarta na bugawa tayi masa
sallama, jin shiru tace "Hello" kallon wayar tayi ta sake maidawa a kunnenta har sannan bata daina cewa
Hello ba, House mate dinta dai ya ajiye Textbook dinsa gefe ganin yanda ta rude ya maida duk
concentration dinsa akan ta, Khaleesat ta sake kallon Screen din wayar jin shiru Abdul ya ki ce mata komai
kuma tana jin maganar mutane a background, marairaicewa tayi ta duka nan kasan living room din ta saka
wayar a handsfree tace "I know u can hear me pls, don Allah kayi hakuri, i am making u this promise hakan
bazai sake faruwa ba wallahi, don girman Allah kayi hakuri" Sai a sannan yayi magana da husky voice yace
"Hold on to ur promise malama, sau biyar kenan kina missing call dina within a short period, are you out of
ur senses or is anything wrong with ur brain?" Da sauri ta girgiza kai kamar zata yi kuka tace "Wallahi ina
kitchen ina girki san da ka kira jiya, kuma...." Cutting dinta yayi yace "ke, bana bukatar jin komai daga gare
ki, none of ur lies and excuses will convince me, naga kamar u are beginning to take me for granted this
days.... Kinsan Allah kika sake missing call dina zaki sha mamakina wallahi cause it will take me nothing
to be in America...." Hawaye ya cika idonta cikin sanyin murya tace "Amma me yasa baka min uxuri?"
Yace "Baza ayi uxurin ba, ni za ki gaya ma uxuri? A kanki aka fara karatu?" Shiru tayi bata ce komai ba,
yace "Wato ke kin fi karfin ki bude baki ki bada hakuri ko" Kasa cewa komai Khaleesat tayi don tun da ta
daga kiransa ta fara basa hakuri bata kuma san wani hakurin yake nufi ba, A takaice yace "Anyway, i called
to warn you to stop disturbing me with unnecessary calls, na biyu kuma ki ja ma kawarki kunne she should
never come into my DM and tell me nonsense again don zan dau mummunan mataki a kanta, ke kuma duk
sanda yayi suiting dina i will call you, don't try calling my line again" Yana kai wa nan ya katse wayar,
Khaleesat ta dinga kallon screen din wayar hawayen dake makale idonta ya gangaro, House mate dinta ya
ɗan yi murmushi wanda iyakarsa lips after paying attention to their conversation, mikewa Khaleesat tayi
tana share hawayen dake sauka idonta, sai a sannan ta lura da shi a parlon, dauke kai tayi da sauri bayan
sun hada ido, gaba daya ta ma mance yana parlon, taji yace "Is that ur Father?" Wani kallo ta jefa masa tayi
wucewarta dakinta wasu sabbin hawayen na zuba idonta, ruf da ciki tayi kan gadonta tana kuka har da
shessheka, ta kusa minti arba'in kwance a yanda take, zuwa sannan ta dena kukan da take kawai ta lumshe
ido, knocking din kofar dakinta da taji anyi at the same time aka bude ne yasa ta mike zaune da sauri don
bata san bata kulle kofar ba, hada ido suka yi da new Housemate dinta, yayi dropping ledan hannunsa ya
jingina jikin kofar dakin ya rungume hannu yana kallonta da kyau, calmly yace "Like seriously, Namiji
kika kwanta kike yi ma kuka?" Ta wani hade rai ta kauda kanta zuwa wani direction din daban, how did he
even know she understands Hausa?? yana juya counter din hannunsa as if counting his words yace "It's...
funny" Ta juya ta kallesa har sannan fuskarta a daure tace "Excuse you, why will u barge into someone
else's bedroom just like that?" Ya daga kafadarsa yace "Zan yi shisshigi in baki shawara ni dai, run for ur
dear life cause u are dating a monster as a boyfriend" Yana kai wa nan ya juya ya fita daga dakin closing
the door behind him, Khaleesat ta dafe kanta da yayi mata nauyi, daga karshe ta mike ta kulle dakinta da
makulli sannan ta shiga bandaki, karfe sha biyu da yan mintuna ta gama shiryawa don wanka tayi, kallon
ledan da ya ajiye mata tayi ta dauke kai sannan ta nufi kofa ta bude ta fita, satan kallon kofar bedroom
dinsa tayi ta karasa living room, tana tafiya a hankali ta tafi kofar parlon