Showing 132001 words to 135000 words out of 152206 words
dakin Umma ta
fito da sauri jin sunan wanda Noor ta kira, Khaleesat ta tafi ta rungumeta ta fashe da matsanancin kuka,
Farin ciki wajen Aunty Farida ba a cewa komai don duk tunanin su Ajay ne suka dawo da ita gida, sallaman
Abdul yasa duk suka juya suna kallon hanyar shigowa gidan da mamaki, nan da nan fara'ar Aunty Farida ya
bace, su Mama Shatu ne kawai suka amsa masa sallaman, ya karaso cikin compound din, Aunty Farida ta
saki Khaleesat ta tafi ta zauna kusa da Umma fuskarta babu yabo babu fallasa, Mama Zubaida ta mike da
sauri ta shimfida masa tabarma ita da Mama Shatu na masa sannu da zuwa, ya zauna kan tabarman yana
kallon Umma ya gaisheta, Umma ta amsa tace "Sannu da zuwa" Aunty Farida ta mike ta shige dakin
Umma, Abdul ya gaida su Mama Zubaida dake ta washe baki, duk suka amsa da fara'a, Ita dai Khaleesat na
durkushe kusa da Ummanta kanta a kasa, Abdul ya kalli Umma yace "Baba baya nan ne" Umma tayi karfin
halin cewa "Eh bai dawo ba" Ko rufe baki bata yi ba sai ga Malam Ali ya shigo gidan da rabin buhun
dankalin Hausa a hannunsa, ajiyewa yayi ganin Abdul da Khaleesat, yace "A'aa, ikon Allah, baki mu ka yi
yau a gidan" Abdul ya tashi ya tafi har inda Malam Ali ke tsaye ya gaishesa, Malam Ali ya amsa yana kame
kame, ya tafi da sauri ya dauko tabarma ya kara shimfida ma Abdul yace "Yi zaman ka a nan, bari in zubo
mana ruwa a buta lokacin Magariba yayi" Da sauri ya tafi ya dauko butoci biyu ya tafi zai debo ruwan,
Umma ta mike ta shige dakinta, Khaleesat ta bi bayanta, Nenne ce ta shigo gidan da sallama tace "Allah me
hikima, sannunku da zuwa Awdul" Abdul ya gaisheta, ta jawo kujera ta zauna tana facing dinsa tace "Lafiya
lau wallahi, ya iyayen naka, ina kokarin daura sanwa kenan sai ga wani almajiri da gudu ya zo ya sanar min
ai kun zo, kasan ɗan albarka ne almajirin nan duk wani abu da ke faruwa a gidan Ali kamar kiftawan ido
yake rugowa ya sanar min, ni kuma in ina da er dabino kwara uku in basa la'ada, nayi farin cikin ganin ka
wallahi, ina matar taka, in ji tare ku ke?" Yace "Tare mu ke" Sai ga Malam Ali da ruwa a butoci yace "Ai
ina jin tana dakin uwarta" Nenne tace "Kai kuma lafiya? ina zaka da butocin ruwa ko karfe shidda bai yi
ba?" Malam Ali yace "Au? To to bari a ajiye, na zata magariba ta yi" Da sauri ya koma ya ajiye butocin ya
dawo, Nenne tayi kasa da murya tana kallon Abdul tace "To Awdallah, ka dubi girman Allah ka rike amanar
da muka baka, yanxu kai ne uwarta kai ne ubanta, duk ta kuskure maka ka kawota wajena ni zan san yanda
zan yi da ita, kuma albarkacin auren da ya shiga tsakaninka da jikata ka kara ba Mahaifinka hakuri ya yafe
ma Malam Ali komai ya wuce a wajensa don girman Allah, don yanxu kam duk mun zama daya tunda ga
aure har ya shiga tsakani, Allah Ubangijin ya baku zaman lafiya ya kauda duk wata fitina ya kawo zuri'a
dayyaba" Abdul yace "In sha Allah Kaka" Nenne na murmushi tace "To madallah, gashi ko tuwon dare ban
yi ba balle in zubo maka" Yace "Ba komai, can gidanmu za mu wuce yanxu yamma tayi" Nenne tace
"Gaskiya kam, bari in fito maka da ita ku tafi, go slown hanyar nan bata da kyau" Tashi Nenne tayi ta nufi
dakin Umma, kuka kawai Khaleesat take Umma tayi tagumi tana kallonta ta ma rasa abun cewa amma
daurewa kawai take ita ma hawayen bai zubo mata ba, don bakin ciki Aunty Farida na jingine jikin bangon
dakin ita ma ta kasa cewa komai, a haka Nenne ta shigo dakin ta same su, taɓe baki tayi tace "Ta so ki fita
mijinki na waje na jiranki" Ita dai Khaleesat bata ce komai ba tana kuka kamar ranta zai fita, Nenne tayi
kasa da murya tace "Wato a yanda kanwar uwarki ke zube ba mashinshini shekara da shekaru haka kema
kike son ki zauna mana tunda kyau kawai gare ku amma babu farin jini, banda samun waje ki samu miji
zankadede kamar Awdul amma son zuci irin taki da na uwarki da kanwarta bazai sa ku yi farin ciki da
hakan ba, in a baya Awdul ɗan iska ne dama Allah ya taɓa halittar da bai shiryar ba in yayi niyya? Daga
yanda Awdul ke magana a kintse na gane ya shiryu wallahi, to ko kawota da yayi ta gaishemu kadai ya isa
mu shaida shiriyarsa, wallahi ku dinga jin tsoron Allahn da ya halicce ku, duk wanda burinsa ya raba aure
to tsinuwar Allah ne zai tabbata a garesa, kuma in sha Allahu Khaleesat tayi aure kenan mutuwa kadai ne
zai rabata da mijinta tunda duk mun san yana sonta, tashi ki fita gun mijinki ku tafi munafuka kawai, duk
da can baki san baki son shi ba sai da ya aika ki kasar turawa idonki ya bude a can" Cikin kuka Khaleesat
tace "Ni wallahi bana son sa, bana son sa, bazan iya zama da shi ba" Nenne tace "Aikin banza, to uban me
ya rage kuma bayan ya kwana da ke? Ai duk rashin son da kike masa dole ki zauna da shi tunda ya kwana
dake yau kusan satin ki daya a gidansa ba kuma ajiye ki zai yi yana kallo kamar hoto ba tunda shi ba ɗan
iska bane, kuma gidan Ali ba Obalande bane da za a tara masa fararen zawara har biyu a gida, Farida ma
kadai ta ishemu, tashi ki fita ki bani waje ko in tafi in kira maki Ali yanxun nan ya fitar min da ke, tun da
uwata ta haifeni ban taɓa ganin er da bata son kwanciyar hankalin ubanta ba sai ke" Umma ta share
hawayen dake zuba idonta tana kallon Khaleesat tace "Ta shi ki je Khaleesah, Allah ya maki albarka, Allah
kuma ya baku zaman lafiya" Mikewa Khaleesat tayi tana kuka sosai ta fita daga dakin Ummanta, Nenne
tace "Atoh dai, iya addu'ar da za mu yi mata kenan a matsayin mu na rikakkun musulmai, tun da muka ga
haka to Allah ne kadai ya san hikimarsa nayin hakan, kuma dama an gaya min aurenta da Awdul aure ne me
kyan gaske in har zata kwantar da hankalinta, gashi mun shaida yana son ta, kuma ta dalilinta arzikin
ubanta duk zai dawo har ma ya fi na da, wallahi haka aka ce min, kawai dai babba ba a son yayi ta surutu
ne shi sa nake jan bakina nayi shiru" Har suka bar gidan da Abdul hawaye ne kawai ke zuba idon
Khaleesat, dubu talatin ya ba kishiyoyin ummanta ko wacce 15k, ya ba Islam 50k, Nenne ya bata 20k,
Malam Ali kuwa bai amsa kudinsa ba sai ajiye masa Abdul yayi kan tabarman dake bakin kofar dakinsa,
babban tashin hankalin Khaleesat yanxu period dinta da ya dauke, don kafin su taho kano a dari dari tayi
sallahn Azahar kar ya shigo ya ganta, tasan yau dai ƙaryar ta ya kare kawai, a haka suka iso gidansu Abdul
bayan sallan magrib, Driver na shiga babban compound din da mota Khaleesat taji gabanta ya tsananta
faduwa, bayan yayi parking a space din parking Abdul ya sauko daga motar yana kallonta, da kyar ta iya
saukowa daga motar zuciyarta na bugawa sosai wanda ita kanta bata san dalilin hakan ba all of a sudden, ya
fara tafiya tana bin sa har suka isa entrance din shiga parlorn gidan....
[6/18, 7:34 PM] khaleesat Haiydar ✍️: Khaleesat na tafiya a hankali ta shiga parlon tana karanto addu'o'i a
ranta don irin faduwar da gabanta yake yi isn't normal, ga tsikar jikinta sai tashi yake, she was so
uncomfortable and restless at the same time, Abdul ya kulle kofar parlon ya kalli mahaifiyarsa dake zaune
cikin parlor ita da kanwarta Aunty karima da Meemah, ko wannensu da bowl cike da farfesun kayan ciki a
hannu, Khaleesat ta sunkuyar da kanta ganin gaba dayansu zubo mata ido suka yi suna kallonta fuskarsu
babu yabo babu fallasa, amma kana kallon kwayar idanuwansa babu abinda zaka gani sai tsantsan
kiyayyarta, da kyar ta karasa tsakar parlon kamar zata harde ta fadi, ta duka kasa cikin sanyin murya ta
gaishesu gaba daya, instead Momy sai ta dauke kai tana kallon Abdul tace "Flight din sai na dare ka samu
kenan Babana, bayan tun sassafe Meemah tayi maka text" Aunty Karima ta hau kwalo ma mai aiki kira ta
zo ta karo mata farfesu, Abdul bai ce ma Momy komai ba ganin babu wanda ya amsa gaisuwar Khaleesat
cikinsu ya kalleta yace "Ta shi mu je" Khaleesat ta ɗaga kai ta kallesa amma bata tashi ba ga zuciyarta sai
bugawa yake, Momy tace "Ta tashi ku je ina? Wacece ita din tukunna?" A takaice yace "Matata ce" Aunty
Karima ta gyara zama da mamaki tace "Ikon Allah, ita ce er gidan barawon da yayi ma Alhaji sata har na
miliyan dari kenan?" Meemah tace "Kwarai kuwa gashi kin gane ma idonki, ita ce dai er matsiyatan da
Abdul ya makale ma saboda rashin sanin darajan mahaifinsa bai dubi rashin kirkin da aka yi ma Daddy a
kotu akan hakkinsa ba ya koma ma yarinyar, dama yawon ta zube uwarta ta shigo yi Nigeria shi ne ta hadu
da ubanta bayan sun yi watsewarsu ya aureta...." Katse ta Abdul yayi a fusace yace "Idan kika ci gaba da
voicing gibberish zaki sha mamakin abinda zan maki a nan Amina, bridle ur tongue" Aunty Karima ta bude
baki da mamaki tace "Amina kai tsaye? Ko ka fara shaye shaye ne Abdul? Akan shegiyar yarinyar nan kake
nema kayi ma yayarka rashin kunya?" Abdul ya kalleta yace "Kar ki sake sako min baki tunda ba dake nake
ba, stay out of anything that concerns me, Momy ce dolen ki ba ni ba" Momy tayi wani murmushi tace
"Rabu da su Babana, take her inside ta huta, sannunku da zuwa" Tana fadin haka ta tashi ta taho kusa da
Khaleesat ta dafa ta tace "Welcome my daughter, ku je sama kin ji" Da kyar Khaleesat ta mike tsaye duk
jikinta a sanyaye ta bi bayan Abdul, Momy ta koma ta zauna ta bi ta da kallon gefen ido, har ta ga sun haura
sama sannan ta kalli su Meemah tayi kasa da murya tace "Sam baku da hankali baku da tunani, haka muka
yi da ku daxu?" Meemah da ke huci tace "Ni matsala ta kinsan ban iya pretending bane Momy, wallahi ban
iya ba ko nace zan yi" A fusace Momy tace "To in kin san ruguza min plan za ki yi ki ja min asara to tun
wuri ki tattara ki tafi gidan Suwaiba bana son hauka, duk ba ke kika ja mana wannan bala'i ba? da sa
hannun ki fa abubuwan nan suka faru, ai wallahi sati daya yayi ma yarinyar nan yawa a gidan nan in dai ni
na haifi Abdallah, don haka duk wanda bazai iya abinda nace yayi ba to ya bar gidan nan kawai kar ya ja
min asara" Aunty Karima tace "Toh Momy kar kuma fa yace zai koma can gidansa da ita, kin san babu me
sa shi babu me hanasa idan yayi niyyar yin abu" Momy tace "Ku dai ku zuba min ido kawai ku ga ikon
Allah, ance maku ni mahaukaciya ce warce bata san abinda take yi ba irin ku? Ai ni ba yarinya bace nasan
me nake yi" Mikewa Momy tayi tana tafiya gansan gansan ta nufi staircase, Meemah ta kyabe baki tace
"Wallahi ji naki zuciyata bazata iya wani pretending ba akan shegiyar yarinyar nan me kamar sadaka yalla,
ban taɓa jin tsanar mutum a duniya irin yanda na tsaneta ba, Abdul bai taɓa min kalan tijaran da yayi min
akan ta ba, kuma fa a gabanta yayi min haka tana ji tana kallo" Aunty Karima ta sauke ajiyar zuciya tace
"Nima ba gashi yayi min ba Meemah, fatan mu kawai komai ya zo karshe cikin gaggawa, mu yi yanda
Momy tace kawai" Khaleesat ta dinga bin dakin da Abdul ya kawota da kallo wanda babu tantama dakinsa
ne, a hankali ta zauna saman kujeran dakin tana kallonsa yana cire agogon wrist dinsa alamar zai shiga
bandaki yayi alwala, abinda aka yi mata a parlor ne kawai ke yawo a kanta, tayi nisa tunanin da take yi sai
gashi ya fito daga bandakin yana kallonta yace "Shiga kiyi alwala" Sosai gabanta ya fadi ta daga kai tana
kallonsa, ta dake tace "Ai ban gama ba" Wani tsawan da ya gigitata ya daka mata, yana mata wani mugun
kallo yace "Kar ki raina min hankali, is it going to take u forever to finish ur period? Karya kike yi kin
gama" Tsabar yanda ta tsorata jikinta har bari yake ta ma rasa me zata ce masa, yace "Idan na dawo
masallaci i will check for my self" Daga haka ya fice daga dakin kamar zai tashi sama, hawaye ya fara
zarya a idonta, wannan moment din take ta tsoro gashi ya zo kuma babu yanda ta iya, shesshekan kuka ta
fara yi cikin tashin hankali, bayan ya fita da kamar minti biyu taji an bude kofar dakin, ta juya da sauri
gabanta na faduwa, Momy ce ta shigo dakin ta sakar mata murmushi ta nufota tace "Ya sunanki daughter?
Mu sai yace mana Khaleesat, ni dai nace Khaleesat ai ba sunan yanka bane" Khaleesat ta sauke idonta
zuciyarta na bugawa a hankali tace "Sunana Hauwa" Momy tace "Maa sha Allah, ashe uwata ce, welcome
to the family my dear, taso mu je kiyi sallah" Khaleesat felt a bit relieve da gesture din Momy toward her,
ta mike tsaye Momy ta kama hannunta suka fita daga dakin, can bangarenta ta tafi da ita har cikin Bedroom
dinta sannan ta nuna mata bandakin dake dakinta tace "Ki shiga ciki kiyi alwala, amma kafin nan let's do a
mother and daughter talk first my dear" Khaleesat ta daga kai tana kallon Momy, Momy ta nuna mata kan
kujera tana mata murmushi tace "Get sitted Mamana" Khaleesat ta zauna kan 2 seater dake dakin Momy ta
zauna gefenta tana facing dinta tace "Kar ki boye min komai mamata, ki daukeni tamkar mahaifiyarki, ki
gaya min gaskiya wani abu ya shiga tsakaninku da Abdul ne tun bayan da ya dauke ki?" Sosai Khaleesat
taji tambayar yayi mata nauyi a kai, hakan yasa ta kasa kallon Momy ta sunkuyar da kanta kawai, Momy ta
kwantar da murya tace "Akwai dalilin da ya sa nake tambayarki haka ne Mamana, kar ki ji kunya ki boye
min komai, open up to me" Girgiza mata kai kawai Khaleesat tayi ba tare da ta bari sun hada ido ba, Momy
ta kamo hannunta tace "Kar fa ki ji kunyata ki boye min komai mamana, gaskiya zaki gaya min" a hankali
Khaleesat tace "Gaskiya na gaya maki Momy" Momy ta dinga kallonta kamar dai bata yarda ba, can tace
"To saboda me? Anya kuwa gaskiya kike gaya min Mamana?" Khaleesat bata dago kanta ba tace "Period
nake yi ne" Momy tace "Toh kin gama yanxu?" A hankali Khaleesat tace "Daxu na gama" Momy ta sauke
boyayyen ajiyar zuciya tace "To naji dadin jin hakan mamana, don nasan irin daukan da Abdul ya tafi ya
maki bayan dawowar ki daga makaranta, hakan bai ba iyayenki daman yi maki duk abubuwan da ya
kamata su maki ba a matsayinki na budurwa kafin ki tare gidan mijinki, basu samu daman yi maki shirin
xuwa gidan miji ba, amma tunda ya kawo ki nan in sha Allah zan maki duk abinda ya kamata diyata...." Ita
dai Khaleesat tayi shiru har sannan bata dago kanta ba, Momy ta mike tace "Ta shi mu je bandaki ki ga...."
Khaleesat ta mike tsaye ta bi bayan Momy har zuwa bandakinta, Momy ta nuna mata wani babban flask
tace "Kin ga wannan flask din? To zaki dinga tsiyayan ruwan ciki ki sirka da ruwan zafi a pampo ki dinga
tsarki da shi" Momy ta dauko wasu ɓakakken sabulai dake nannade a leda ta mika mata tace "Sabulan nan
su ma tsarki zaki dinga yi da ko wannensu, in kin yi sai ki ajiyesa inda kika ga na dauko yanzu don naki ne"
Momy ta nuna mata wani roba dake rufe a bandakin shi ma tace "Wannan ma diba zaki yi kiyi tsarki da shi,
kin ji?" A hankali Khaleesat tace "Toh Momy" Momy ta dauko wani kwalba dake boye a cikin bandakin,
Khaleesat dai bin ta kawai take da kallo ta bude flask din ta tuttule abinda ke cikin kwalban, sannan ta mike
tace "Yauwa mamana, duk ki tabbatar kinyi amfani da su yanda nace, sai kiyi alwala ki fito" A hankali
Khaleesat tace "Toh Momy" Daga haka Momy ta fito daga bandakinta ta shimfida ma Khaleesat darduma,
sannan ta zaune kan kujera ta jirata har ta fito daga bandakin, Momy ta mike ta nuna mata darduman tace
"In kin idar da sallan kar ki fito, kiyi zamanki zan kawo maki abinci" Khaleesat tace "To Momy" Daga
haka Momy ta fita daga dakin ta kulle da key ta tafi da makullin tana ɗan murmushi, a corridor ta hadu da
Abdul ya taho daga dakinsa bayan ya shiga bai ga Khaleesat a ciki ba, Momy tace "Har ka dawo masallacin
Babana?" Yace "Na dawo, tana ina ne Momy?" Momy ta ja kunnensa tace "Yanxu abinda kayi ma yayarka
ya kamata Babana? Kasan ta fa wani lokacin ba hankali ya ishi yayar taka ba, da sai kayi hakuri ka kyaleta
da halinta kawai" Ya hade rai yace "Dukanta fa take kokarin yi Momy? A ina ta san ta ko kuma me tayi
mata da zata zageta kuma ta nemi ta doketa??" Momy ta kama hannunsa suka shiga dakin baƙin dake kusa
da su tana kallonsa tace "Ai na mata fada sosai Babana, yanxu ma haushin abinda kayi mata ne yasa tayi
abinda tayi a parlor amma kayi hakuri kaji Babana" Yace "Naji, ina Khaleesat din take?" Momy tace
"Bazan fa baka matar ka ba sai zuwa jibi in ma zaka cire ido a kanta ka cire, tun da baka bari iyayenta sun
gyarata yanda ya kamata ba to ni zan gyarata" With confusion Abdul yace "Gyarata kamar yaya Momy?"
Momy tace "Ka taɓa ganin inda aka dau mace budurwa aka kai ta gidan miji haka nan? To fin karfin
iyayenta da kayi kuma suna shakkar ka shi yasa suka baka ita haka babu yanda suka iya maka, amma a
al'adar mu ta Hausa babu inda ake yin haka, ni kuma kaga bazan baka ita ba sai nayi mata duk abinda ya
kamata na gyarata, in kuma rashin kunya zaka yi min to yi Babana, Khaleesah dai bazan baka ita ba sai
zuwa nan da jibi