Showing 78001 words to 81000 words out of 152206 words
ta juya ta kallesa
sai kuma ta dau popcorn daya ta matsa dai dai kusa da shi a hankali ta saka masa a baki, da sauri ta gyara
zamanta ta maida hankalinta kan movie, ya bude ido, taji yace "What a nice movie" Sai a sannan dariya ya
taho mata ta juya ta kallesa tace "Ain't you ashame of saying this?" Yana gyara zama yace "You don't like
the movie? But it's nice, i like it" Tana murmushi tace "To in ka gama baccin ka tashi mu tafi, ni na gama
kallona" Ya ɗan shafa kai trying not to smile yace "Wa yace maki bacci nake, i was only meditating duk
nasan abinda ake yi ai, ba gashi an kusa gamawa ba" Ita dai murmushi kawai take tace "Naji, tashi mu tafi,
a hanya sai ka bani labarin film din don akwai inda ban gane ba" Yayi shiru yaki cewa komai, tana danne
dariyarta ta tashi ta dau sauran popcorn dinta da nasa, tashi yayi ya bi bayanta suka fita daga Auditorium
din, lokaci lokaci take juyawa ta kallesa don ta tabbatar he is not walking and sleeping at the same time, da
sauri ya jawota ta fado jikinsa bayan tayi missing step saboda waige waigen sa da take sai kuma yayi saurin
saketa, within few seconds aka yi hakan, ta rufe bakinta da hannu don ba karamin tsorata tayi ba, yace
"Yanzu da kin fadi kika fara min kuka kilan har mu kai gida" Ta marairaice tana kallonsa, Softly yace
"Alright Sorry Halysaah" Ta juya ta fara tafiya a hankali, a haka suka fita daga cinema din bata sake waigen
bayanta ba, yana biye da ita yana kallonta har suka isa gun da yayi parking. Wajen karfe goma suka isa gida
bayan yayi parking ta juya ta kallesa a hankali tace "Thank you so much" Ya mata murmushi yace "You are
welcome House mate" A haka suka sauka daga motar tana biye da shi suka shiga gidan, kafin ta shiga daki
yace "Get me ur travelling documents" Ta kallesa zata yi magana ya daura fingers dinsa biyu a lips dinsa, ta
sauke idonta sannan ta juya a hankali ta shiga cikin dakin, after some minutes ta fito ta mika masa, ya amsa
yace "Good job, zan tura maki ticket din ta Email dina, sai da safe" A hankali tace "Allah ya tashe mu
lafiya" Juyawa tayi ta koma cikin dakin ta kulle kofar, Jay ya tafi parlon sama yaga AJ kwance kan Couch
yayi bacci, shi dariya ma yake basa, kawai mutum ya dora ma kansa wahala, juyawa yayi ya wuce dakinsa,
wajen karfe sha biyun dare Khaleesat na ta juye juye ta kasa bacci ita kanta ta rasa dalili, message taji ya
shigowa wayar Jay dake wajenta ta mike zaune ta jawo wayar tana duba message din taga Email ne ya
shigo, tana bude Email din taga ticket din ya turo mata na Turkish Airline, kuma Business class seat, bata
san me yasa taji hawaye ya cika idonta ba, ta ajiye wayar a hankali ta koma ta kwanta.
*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment
07087865788 👈🏻, it's better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don
littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*
[5/26, 9:47 AM] khaleesat Haiydar ✍️: Khaleesat na zaune gefen gado tana kallon Jay dake kulle mata
akwatunan ta, yana dagowa ta juya a hankali tana kallon window dake dakin, ya dau boxes din biyu yace
"Let me get them in the car" Daga haka ya fita daga dakin, ta jinginar da kanta jikin gadon dakin har ya
dawo, yana kallonta yace "Hope you didn't forget anything Halysaah" Ta gyada masa kai, yace "Ok, you
know what? in dai muka fita kika hadu da AJ thank him and tell him you are leaving" With a smile on his
face ya kare maganar yana kallonta, ta sauke idonta tana wasa da fingers dinta a hankali tace "Ohk" Yace
"Good gal, mu tafi" Mikewa tayi ta bi bayansa tana rike da karamin handbag dinta walking slowly, suna
fitowa walk way din babban corridor din sama sai ga AJ ya taho daga parlorn dake nan sama, Jay ya kalli
kayan jikinsa ganin iri daya suka sa kuma tun safe ba wai sun hadu bane kawai coincidence, tunda AJ ya
kallesu sau daya ya ci gaba da tafiyarsa, Khaleesat ta ɗan kalli Jay, ya gyada mata kai sannan ya nufi stairs,
ita dai tana tsaye ta jira har AJ ya iso kusa da inda take sannan ta sauke idonta a hankali tace "Good
morning, i want to thank and appreciate you for everything, i will be leaving today in sha Allah" Without
looking at her yace "Jay dai zaki ma godiya ni me na maki" Ta bi sa da kallo har ya fara sauka downstairs,
sai bayan da ya sauka sannan ta tabe baki ta bi bayansa tana tafiya a hankali, parlor ta tarar da Jay zaune
yana jiranta, Jay ya bi AJ da kallo yace "Flight din naka na gobe ne amma?" AJ yace "I am leaving for the
airport now" Jay yace "Ohk, zaka jira inyi dropping Housemate dina sai in dawo in kai ka airport din?" AJ
yace "No, don't bother" Daga haka ya fita daga parlon tare da daya daga workers din gidan wanda da alama
shi zai yi dropping dinsa airport din, Jay ya daga kai ya kalli Khaleesat, ya lura tunda gari ya waye jikinta
yake a sanyaye, yana kallonta yace "Are you Okay Halysaah?" Ɗan murmushi tayi tace "Sure" yace "Kin
gaya ma kawarki yau zaki tafi?" Khaleesat ta gyada masa kai tace "Na gaya mata" Yace "Ok, ita yaushe
zata tafi?" Khaleesat tace "Yayanta yace ta bari ranan lahadi" Jay yace "Kin tabbatar baki mance komai ba
kuwa a sama?" Ta gyada masa kai, yace "Je dai ki sake dubawa Housemate" Bata masa musu ba ta juya
zata koma sama yace "Toh ki ajiye jakar taki mana" Ta dawo ta ajiye jakarta a kan kujera sannan ta wuce
sama, Mikewa Jay yayi ya tafi gun jakar ya dauka ya bude sannan ya ciro Dala dubu daya a aljihunsa ya sa
mata a jakar ya kulle ya mayar ya ajiye mata ya koma ya zauna, ba a dau lokaci ba Khaleesat ta dawo
downstairs tace "Ban manta komai ba" Yace "Good" Mikewa yayi bayan yaji fitar motar AJ don dama jira
yake yaji sun fita daga gidan, yana kallonta yace "Mu je, ur Flight is in an hour time in sha Allah"
Khaleesat ta gyada masa kai ta dau handbag dinta, tana biye da shi suka fita daga parlon gidan, har gari ya
fara duhu, suna shiga motarsa ta mika masa wayarsa dake hannunta kar ta manta, a hankali tace "Thank you
so much" Ya amshi wayar sannan ya dauko pin a motar ya cire sim card din cikin wayar snn ya mayar mata
yace "Your ticket is on the phone, in kin koma Nigeria sai kiyi SIM card replacement, in kuma baki son
wayar sai in sa a kai maki sabo a Nigeria" Tayi murmushin karfin hali tace "Saboda me zance bana so,
nagode sosai, Allah ya saka da alkhairi" Yace "To ai nasan ku mata da son sabon abu" Ta girgiza masa kai
kawai tana murmushi bata ce komai ba, a haka suka bar gidan suka dau hanyar airport da tunani iri iri a ran
Khaleesat, ko baccin kirki bata yi ba daren jiya ga wani daren, ko me zata je ta tarar a Nigeria sai Allah, it's
now that reality is dawning on her, bayan sun isa airport Jay ya juya ya kalleta yace "You can sort ur self
out ba sai na shiga ciki ba ai ko?" Ta gyada masa kai, da kyar tayi karfin halin cewa "Thank you so much
Housemate, Allah ya saka da alkhairi da abubuwan da ka min" Kasa ci gaba tayi saboda hawayen da ya fara
sauka a idonta she just can't thank him enough, gani take words aren't enough to thank him, shi dai Jay
kallonta kawai yake with surprise, can yace "C'mon Halysaah, to menene abun kuka?" Ta kasa basa amsa ta
rufe fuskarta da gyalenta tana kuka a hankali, Jay ya kwantar da murya yace "Pls ki dena wannan kukan, in
nasan abinda zaki yi kenan i will have just order either Lfyt or an Uber that will be taking you to the
airport" Dena kukan tayi tana goge hawayen da yaki tsaya mata tana kallonsa, ya bude motar ya sauka ta bi
sa da ido taga Luggages dinta dake booth zai dauko, a hankali ta bude side dinta ta sauka daga motar tana
bin sa da kallo, daya daga porters dake wajen ya ba luggages din nata ya shigar mata da shi ciki ya hada
masa da tip dinsa, ita dai Khaleesat kallonsa take, ya juya ya dawo kusa da ita yace "Alright safe trip
Halysaah, idan kinyi replacing Sim card dinki sai ki min magana ta WhatsApp, my regards to everyone
back home" Ta sauke idonta a hankali tace "I will miss you" sai bayan da ta fada haka ita kanta tayi
realizing abinda ta fada, sai kuma ta kasa dago kanta, ya ɗan yi murmushi yace "I will miss you too
Housemate, in sha Allah next week i will be in Nigeria too" Bata iya ta kallesa ba ta gyada masa kai kawai
ta juya a hankali ta bi bayan porter din da ya shigar mata da luggages dinta zuwa check in counter for her
Boarding pass, kasancewar Business class ticket gareta all the processes were smooth and straight for her,
daga karshe ta nufi waiting lounge don in 15 mins time za su fara boarding jirgi, tunda ta shiga lounge din
take kallon wanda ta gani zaune da mamaki, ta kalli boarding pass dinta sannan ta kalli na hannunsa taga iri
daya, wayarsa kawai yake dannawa, ganin bai ganta ba ta juya a hankali ta koma wani wajen daban ta
zauna ta inda ma bazai ganta ba, bata sake waigen inda yake ba, iya drink kawai ta amsa a lounge din
unlike wasu da ke ta cin abinci duk a cikin kudinsu, gaba daya ta nemi appetite dinta ta rasa saboda
damuwa, da ta tuna inda zata sae taji har wani juya mata kanta yake kamar bata da lafiya, ta saƙa wancen a
ranta ta kwance har daga karshe aka fara boarding din jirgi, sai da Khaleesat ta jira AJ ya fara tafiya sannan
ta mike ta bi bayansa walking slowly, Har seat dinta wata Flight Attendance da ke welcoming dinta da
fara'a ta kai ta, hada ido Khaleesat tayi da AJ that was sitting few seats away from hers, ta sunkuyar da
kanta ta zauna Seat dinta tana mayar da Amenity kit din da aka ajiye mata a gefe, AJ ya kasa daina kallonta
fuskarsa babu yabo babu fallasa, he can't even explain what he is feeling at that moment don bai taɓa ganin
wanda ya gama rena masa wayo a duniyar nan kamar Jay ba, jiya wajen karfe sha biyun dare ya farka ya
gansa yana duba masa waya ashe ticket din da ya siya yake dubawa, he felt like just leaving the plane at
that moment, after a while kawai ya dauke kai yana kara gyara barrier din da zai sa ko hangota bazai dinga
yi ba, Ita ma Khaleesat ko by mistake bata sake kallon direction din sa ba, a haka jirgin ya tashi, Khaleesat
bata taɓa jin motion sickness ba tun da ta fara tafiya a jirgi amma yau ko don saboda pressure din da ta saka
ma ranta ne kawai sai ji tayi as if she wants to throw up tun da jirgin ya daga, ta cire seat belt dinta da sauri
ta mike ta nufi Lavatory din jirgin almost running, shi dai ya bi ta da kallo, Flight Attendance din da ta
kawo mata Hot towel kafin tashin jirgin ne ta bi bayanta tana tambayar if she's okay, Khaleesat ta gyada
mata kai kawai bayan ta fito daga Lavatory din, AJ ya bi ta da kallo har ta koma seat dinta ta zauna sannan
ya tabe baki, Flight Attendance din ta duka kusa da ita tana tambayarta ko tana bukatar wani abu ne,
Khaleesat ta girgiza kai tana murmushin karfin hali tace "Thank you, i am okay" Matar ta sake tafiya sai ga
ta ta dawo da ruwa da orange drink, sai kuma wani drink daban duk a glass daban daban akan tray daya, ta
duka tana mika ma Khaleesat ta dauki wanda take so, glass din ruwa kawai Khaleesat ta dauka ta mata
godiya sannan ta sanar mata bazata ci abinci ba all throughout the flight don ma kar matar ta sake dawo
mata, gani take tana cin abu zata yi aman da bata yi ba daxu, gyara kujeranta tayi ta kwanta ta lulluba da
blanket din da jirgin yayi providing for business class passengers, nan da nan bacci ya dauketa, da za su
sauka Turkey wajen karfe hudun asuba sai da wata Flight Attendance daban ta zo ta tasheta ta sanar mata
jirgi zai sauka, Khaleesat ta mike zaune da kyar don ciwo kanta ke mata, tayi fastening seat belt dinta,
bayan sun sauka Istanbul ta bi AJ da kallo har sai da ta daina hangosa sannan ta mike ta dau handbag dinta
da waya ta bi bayansa tana tafiya da kyar leaving her Amenity kit behind, jiran awa biyu za su yi a Business
Class waiting lounge na airport din kafin a canza masu jirgin da zai kai su Nigeria, ta riga AJ shigowa
lounge din kilan masallaci ya tafi, ita ma tana ganin lokacin sallahn asuba yayi ta tafi tayi sannan ta dawo ta
zauna a business lounge din, after like 15 mins sai gashi ya shigo, not far away from her ya zauna da ruwan
gora a hannunsa, Ita dai ta jinginar da kanta jikin kujeran da take zaune ta daura handbag dinta a kafarta,
she is having a terrible headache a lokacin, after almost 30 mins of sitting wani ɗan Nigeria ya dawo kusa
da ita ya zauna, wanda shi ma daga nan Turkey zai je Nigeria a Business class, kuma jirginsu daya kamar
yanda ta ga ticket irin wanda ta amsa bayan sun sauka Istanbul din a hannunsa shima, yana kallonta yayi
mata sallama cikin nutsuwa, ta ɗan kallesa sannan ta amsa, yace "Guess you are coming from America
right?" Tace "Uhm" Yana kallon Flight ticket dinta yace "Oops you are having the same name as my Mum,
can i call you Jiddah instead of the real name?" Khaleesat dake sauraronsa without looking at him tace
"Ohk" Yana murmushi yace "Alright, are you traveling alone Jiddah?" Ta girgiza kai tace "No" Ya buda ido
yace "Ohk with who?" Ta kalli direction din AJ, shi ma mutumin ya kallesa suka hada ido don kallonsu
kawai Ajayn yake yana jin conversation dinsu, mutumin na murmushi ya tashi yaje ya gaisa da AJ sannan
ya koma ya zauna, shikenan Khaleesat ta samu lafiya, don bai sake ce mata komai ba kawai danna wayarsa
yake tayi tunda shi dai bai san ko waye Ajayn a gunta ba, daga karshe ma ya tashi ya bar wajen, at last aka
fara boarding din jirgin da zai kai su Lagos Nigeria daga Istanbul, Usman ya juya ya kalli Khaleesat da ta
mike tana rike da handbag dinta, har AJ ya wucesu sai kuma ya tsaya amma bai juyo ba, ita dai tana tafiya a
hankali har ta isa inda yake tsaye sannan ya ci gaba da tafiya tana biye da shi, har jirgi ya tashi Usman dake
zaune not far from Khaleesat but close to AJ bai ce mata komai ba, this time around ma dai bacci kawai
tayi har zuwa Nigeria. Karfe hudu saura suka sauka Nigeria washegari Friday, ita dai Khaleesat tun da ta
ganta Lagos bayan ta gama da Custom da Immigration ta fara tunanin kuma yanda zata yi, to ko dai kawai
ta tafi gidan Aunty Farida tunda a nan Lagos take, to ko tace zata je bata da sim din da zata kirata don ba
gane anguwan zata yi ba kuma bata da lambarta a kai balle ko waya ne ta ara ta kirata a airport din, sai
kuma tayi tunanin kiran Ummanta tunda tana da numberta a kai sai tace ta turo mata number Aunty Farida,
gun wata mata warce taga kamar Bahaushiya ce ta nufa, ta gaisheta sannan tace "Don Allah Aunty wayarki
zaki ara min in ɗan yi kira nawa ba caji" Matar ta fara kallonta daga sama har kasa, sai kuma ta bude
handbag dinta ta ciro wayarta ta mika mata, Khaleesat ta amsa tace "Nagode" Dialing number Umma tayi
ta kira taji a kashe, sosai jikinta yayi sanyi, ta kira har sau uku duk ana ce mata a kashe, a hankali ta zame
wayar a kunnenta ta mika ma matar tace "Nagode, wayar ma a kashe yake" sai da matar tayi dialing wayar
ta tabbatar eh a kashe din yake, kana ganin matar kasan she is not comfortable giving off her phone,
Khaleesat na jan trolley dinta a hankali ta fito daga cikin airport din tana tunanin yanda zata yi, ko dai
kawai ta tafi tashan da zata samu mota zuwa kano, since she have some money in her bank account, wani
mutumi ne taga ya nufota, ya gaisheta da ladabi yana mata barka da zuwa, sannan ya nuna mata mota yace
"Ke mu ke jira ki fito dama" She was looking at him with confusion, can ta kalli motar, shi ko har ya amshi
Akwatunanta yayi booth din mota da su, sannan ya dawo ya bude mata back seat, zata yi magana sai ta
hango AJ zaune front seat din motar, ta ɗan yi jim, sai kuma ta fasa cewa komai, ta tafi ta shiga motar, hotel
drivern ya kai su kasancewar next available flight to lagos na karfe bakwai na magrib ne, dakin da aka biya
mata na downstairs, shi kuma AJ sama taga ya tafi, All this while kuma bai ce mata komai ba, ita dai tana
son ce masa ta gode amma bai bar space din hakan ba, ko tsayawa bai yi ba balle tayi godiyan, sai da driver
din ya amshi passport din ta da zai mata booking din jirgi tare da AJ zuwa kano sannan ya bar hotel din,
bayan Khaleesat ta shiga dakin babu dadewa aka kawo mata lafiyayyen lunch, duk da tana jin yunwa bata
iya ta ci da yawa ba she is just restless, taje bandaki ta wanke baki tayi wanka ta dauro alwala ta fito, bayan
ta saka wasu kayan tayi sallah sannan ta dau handbag ta bude zata ciro lip gloss dinta, a nan taga kudin da
Jay ya saka mata, ta dinga kallon kudin ko kiftawa bata yi a sanyaye.