Showing 93001 words to 96000 words out of 152206 words

Chapter 32 - HALYSAAH by Khlst Hydrr

13 May 2026

63

babban mota ne, babu garin da baya zuwa da kaya a babban mota a fadin Nigeria, kuma
motar tasa ce iyaka idan kana da lodi ya kai maka kayan ka har inda kake so sannan ka biyasa, har Nijar ya
sha shiga da kaya daga nan Nigeria ta haka ma ya hadu da yayata Aunty Zahra'u warce ita ce mahaifiyar
Khaleesat, don mu yan Nijar ne mahaifinmu har yanzu yana nan da ransa mahaifiyarmu ce dai Allah yayi
ma rasuwa shekarun baya, to bayan ya auri yayata ya kawota Kano Nigeria ya ajiyeta cikin matansa biyu,
bayan en watanni da auren shine na dawo wajen yayata tunda bata da kowa a Nigeria bata san kowa ba, nan
rikona ya dawo hannunta a lkcn ina da shekara goma, tsangwama da kyara babu irin wanda ban sha ba a
wajen kishiyoyin yayata, gashi bata iya ce masu komai tunda ita ma ba barin ta suka yi ba, mace ce me
hakuri da kauda kai, in zanyi magana ma sai ta hanani, a haka ta samu makaranta ta saka ni tunda a can
kasarmu ina karatu aka daukoni aka kawo mata, sai da tayi shekara biyar a gidan sannan Allah ya bata
Khaleesat, Mahaifin Khaleesat na da rufin asirinsa sosai don haka bamu rasa komai a gidan ba sai zaman
lafiya da kwanciyar hankali daga kishiyoyinta wani lokacin har da uwar mijin, jifa jifa mu kan kai ziyara
Nijar gun iyayenmu da yan uwa da abokan arziki, bayan shekaru 12 da auro yayata a lkcn Khaleesat na da
shekara bakwai sai abokan Mijin yayata da yan uwa suka dinga zugasa akan ya shiga siyasa ya nemi wani
babban mukami zai samu tunda yana da jama'a sosai, kuma ba laifi yayi karatunsa, matansa ma suka dinga
zugasa akan ya fito takara, yayata tayi kokarin ganin ta hanasa tunda bai rasa komai ba a sana'arsa ta dreban
mota amma ya ki, haka nan ya daga babban motarsa ya siyar har da sabon gidan da ya fara ginawa a nan
Ɗan Ladi na sidi, ya daga duk en kadarorinsa ya siyar ya shiga siyasa gadan gadan, duk matansa sai da ya
biya masu Hajji suka tafi da mahaifiyarsa, ya kuma canza ma ko wacce kayan daki, ya ba kowa kudi a
hannu, kusan mutane goma sha biyu ya biya ma Hajji a lkcn, banda matasan anguwa da ya dinga biya ma
kudin makaranta, yayi ta facaka da kudi a karshe dai ya zo ya fadi zabe, duk wa enda suka dinga zugasa
suka juya masa baya, Allah ya rufa masa asiri bai amshi bashin banki da wani abokinsa ke ta zugasa ya
amsa ba kasancewar da zaben ya gabato bashi da kudi kuma a hannu, bayan faduwarsa zabe aka shiga
yanayi na babu a gidan, cin yau da kyar na gobe da kyar ga yayata na da cikin yan biyu, dama gidan da
yake haya me tsada tuni ya saki bayan kudin hayan sun kare muka dawo mariri gidan gadonsa da ya bari a
walakance don saura kadan ya kyautar lokacin da yake campaign sai gashi gidan ya mana amfani ya rufa
mana asiri, makaranta me tsada da yaran gidan ke zuwa duk ya ciresu suka dawo gida suka zauna babu
karatu, iyayen basu yi dubaran mayar da su na gwamnati ba, duk muka shiga mawuyacin hali a gidan, sai
sanda ya samu mota yake lodin kaya ya kai a biyasa, sanda babu mota kuma sai dai kowa ta ciyar da kanta
a gidan, yana kuma fin wata da watanni bai samu ko da karamar mota ba, duk ka zo kofar gida zaka gansa a
zaune babu abun yi shi ma duk ya fita hayyacinsa, tuni yayata ta siyar da kayan dakinta ta fara sana'a ina
taimaka mata, ta kuma saka Khaleesat a makarantar da zata iya biya don Khaleesat ta taso da kwazo da
hazaka ga ta yarinya ce me shiga rai ko don kalan fatarta, don a unguwan ma gidan buzaye ake kiran
gidanmu, hatta Mahaifinta kiri kiri yake nuna yafi sonta a cikin sauran yaransa wanda hakan ya ja mata
tsana da kyara a gun matansa da yan uwanta, ko sanda yake da mota a hannu tsaraba na musamman yake
ma Khaleesat ko da bazai yi ma uwarta ba, ana haka yayata ashe duk cinikin da nake sai ta kwasa ta ba
mijinta a boye ban sani ba, ga dai matansa duk da hali na babu da aka shiga a gidan basu bar yayata ba,
kullum cikin hada mata tuggu da makirci ake wajen miji da uwarsa, cikin wannan yanayi yayata ta haifi
yan biyunta wanda haihuwan da tayi na karshe kenan a gidan, a lkcn matsaloli har sun fi na da, jarin yayata
ya karye kuma babu wani abu da zata siyar ta tada jarin, ga jegon yan biyu tana yi ga yunwa wani lkcn sai
makota ke zubo abinci a kawo mata, iyayenmu a can Nijar ba masu karfi ba balle su taimaka mana, a haka
na bi wata kawata zuwa nan garin Lagos tana siyar da abinci, kafin nan fa nayi aure har na fito, duka auren
bai cika shekara daya ba, na auri wani abokin mahaifin Khaleesat, karayar arziki na samun Malam Ali na
dinga fuskantar matsaloli gun mutumin da matansa uku wanda daga karshe ya sakeni dama ba saboda Allah
yayi auren ba saboda kalan fata ta yayi, ina nan Lagos nake tallafa ma yayata da 'ya yanta uku, don bana
son karatun Khaleesat ya tsaya duk da ta samu Foundation sosai sbda makarantar da ubanta ya sa ta ma a
sanda yake da rufin asirinsa yafi na sauran yan uwanta tsada, na zo Lagos da yan shekaru yayata ta kirani
wataran wai gashi an ba Baban Khaleesat babban mota har zai kai kaya kudu, matsaloli sun fara
warwarewa tunda har an biyasa kudin kai kayan kuma kudade masu tsoka gashi har ya siya kayan abinci
masu yawa ya ajiye a gida, tace in Maza in dawo gida kawai dama ita hankalinta ba a kwance yake da
zamana a lagos ina sana'a ba, a haka ta takurani har sai da na dawo Kano, a sannan Khaleesat na da shekaru
sha shidda tana kuma gab da gama secondary don da wuri aka sakata a makaranta, na dawo da wasu
kwanaki ranan muna zaune tsakar gida da yamma sai ga mahaifin Khaleesat an shigo mana da shi ranga
ranga ko motsin kirki bai yi, wanda duk gaba daya mun zata yana hanyar kudu har ya kusa Lagos, ga dai
shi babu ko kwarzanen ciwo a jikinsa kuma wa enda suka
kawosa suka ce ai daga asibiti ma aka taho da shi a can wajajen garin yarbawa, sannan kwanansa uku a
asibiti aka sallamosa wasu mutane da suka shaidasa tunda dreba ne suka biya kudi aka sako sa a mota aka
dawo da shi Kano, sosai hankalinmu yayi mugun tashi a wannan lokacin, sae da Malam Ali yayi kwana
biyu a gida ana ta addu'a da neman taimako kafin ya farfado gaba daya har yana iya magana, nan fa yake
sanar mana barayi ne suka kwace Trailer da kayan mutane a ciki bayan sun shaka masa wani farin abu,
tashin hankalin da duk muka shiga bazai misaltu ba a lokacin, daga Trailern har kayan cikin trailern ya
doshi miliyan dari da tamanin" Shiru Aunty Farida tayi tana goge hawayen dake zuba idonta, Jay that was
shock ya kalli Ajay dake kallon Aunty Farida babu ko kiftawa jin zunzurutun amount din da ta kira, Aunty
Farida na share idonta ta ci gaba tace "A ranan yan sanda sun kusa goma suka zo a motoci, a haka aka sa
ma mahaifin Khaleesat ankwa ana jan sa kamar barawo aka fita da shi yaransa da matansa na kururuwa
suna ihu, Khaleesat kadai ce bata motsa daga inda take zaune da littafi a hannunta ba sai hawaye kawai,
duk aka cika kofar gidanmu babu masaka tsinke kai kace barawon gaske aka zo dauka, mun shiga tashin
hankalin da baya faduwa a wannan rana, kuma duk mutanen da yayi ta biya ma Hajji a sanda yake da hali,
da kuma mutanen da ya taimaka ma aka rasa wanda zai bi yaga inda ma aka kai sa, ashe daga kano Abuja
aka nufa da shi, bayan dogon binkice aka gano trailern an yasar a wani gari an kuma juye duk kayan cikin
trailern, dama me trailer daban, me kaya daban, adadin kayan cikin trailern kuma zai yi na miliyan dari, to
ba kowa bane me kayan cikin trailern nan illa mahaifin Abdul, sam ba a yarda babu sa hannun Mahaifin
Khaleesat a juye kayan cikin trailern ba, dama kuma yan unguwa na jin haushin ya samu lodi me yawa
haka ya tafi kai kayan shi kadai ko yaron mota bai dauka ba, kuma ko wani dreba an san sa da yaron mota
daya ko biyu, nan aka yi ta zuga baban Abdul akan kar ya yarda wai dama planning Baban Khaleesat yayi
don ya taɓa yi ma wani mutum haka da dadewa yace barayi sun kwace kaya a hanya sai yafewa mutumin
yayi, kuma wai don yaga Alhaji Musa wato mahaifin Abdul me kudi ne sosai shi yasa zai cucesa yace an
sace kaya tunda yanxu ta kare masa bai da komai, kuma wallahi sharri ne ba haka Baban Khaleesat yake
ba, bai cin kayan wani baya taɓa abu in ba nasa bane, beside bai taɓa sanin Baban Abdul ke da kayan ba sai
da iftila'in ya faru sannan yaga me kayan, shi dai kawai ance masa ga Lodi zai kai lagos ya kuma amince
tunda sana'ar sa kenan kuma kullum fatan samun Lodi yake, ko da babu zugin yan anguwa baban Abdul bai
yi kama da mutumin da zai iya yafe kudinsa ba don kana ganinsa kasan bashi da mutunci bashi da kirki, sai
da Mahaifin Khaleesat yayi wata uku bamu sa shi a idonmu ba kafin aka dawo da shi kano duk ya rame
yayi baki ya dawo kamar ba shi ba, da kyar aka bari muka gansa a fursin da aka ajiyesa na nan kano, ranan
duk bamu yi bacci ba bayan mun dawo gida, yayata ta shiga tashin hankali mara misaltuwa don tun dauke
mahaifin Khaleesat dama ta fara alalan siyarwa don mu rufa ma kanmu asiri saboda ɗan jarin da nake da
shi nima duk ya karye bani da komai, kafin ma a dawo da mahaifin Khaleesat kano sau uku muna zuwa
gidan Alhaji Musa a Nassarawa GRA domin mu basa hakuri ko zai dubi halin da muke ciki ya taimaka a
sake mana Baban Khaleesat amma duk aka mana koran kare, na farko masu gadi ne suka kore mu, na biyu
Matarsa ranan ta rako baƙinta ta gan mu tayi mana cin mutunci ni da yayata da Baaba Gaje ta sa aka kore
mu, na uku kuma ɗan cikinsa Abdul wanda dama shi kadai ne namiji a 'ya yansa, ana haka aka shiga kotu
ko lauya baban Khaleesat bashi da tunda bamu da halin daukan Lauya, rana na farko da aka kawo Malam
Ali kotu daga prison ni da Khaleesat da kishiyar yayata Mama Shatu ce muka je kotun don sauraron karan,
to a ranan Abdul yaje kotun shi ma a matsayin daya daga lauyoyin mahaifinsa ashe shi ma Lauya ne, sarai
na ganesa da na gansa a kotun don ranan karshe da muka je gidansu har ce ma masu gadi yayi in muka sake
dawowa su rike mu yan sanda ne za su zo su tafi da mu, zaman kotu da akayi a wannan rana babu wani
positive outcome da ke nuni da cewar da nasara a case din, kwata kwata babu alamun nasara tunda Malam
Ali ba kowa bane, kuma ba shi da kowa bai da komi, bashi da wanda zai tsaya masa, haka aka dage shari'ar
zuwa wani watan shi kuma za a maidasa prison cikin motar da ta kawosa ko belinsa anki badawa,
Khaleesat ta dinga kuka sosai a haraban kotun tana kallon yanda aka shigar da babanta motar prison, nima
ina rungume da ita ina hawaye, wanda wannan ne ya ja hankalin Abdul da fitowarsa daga kotun kenan
zuwa kanta, ba shi ba hatta sauran jama'an wajen kallonta suke, Alhaji Musa babban mutum ne kuma me
kudi wannan yasa har da yan jaridu a haraban kotun, wani ɗan jarida ya nufo mu yana tambayar me za mu
iya cewa game da zaman da aka yi yau a kotu, budan bakin Khaleesat cikin kuka sai cewa tayi Allah ya
saka ma babanta sharrin da aka masa, ina tunanin a nan ne Abdul ya fahimci er gidan wanda suke ƙara ce
Khaleesat, duka duka shekarunta sha shidda a sannan amma duk wanda ya kalleta sai ya sake kallonta,
ranan ma tsautsayi yasa ta fito babu Nikab duk da ba a shiga da Nikab amma duk inda zata bata fita babu
Nikab, in ma bata sa ba uwarta zata tilastata ta saka, hatta nima bana fita babu shi haka Mahaifiyarta saboda
bakin jama'a, kun ji inda Abdul ya fara ganin Khaleesat, a sannan kuma kawai motarsa ya shiga, sai wani
Lauya me zaman kansa ya nufo mu, ya ja mu gefe yana kokarin calming din Khaleesat, nan ya tambayeni
me ya faru, me ya kawo mu kotu, nayi briefing din masa komai nima ina kuka, ya tambayeni zuwa yaushe
aka daga karan, na sanar masa, yace to in basa lambata in sha Allah anjima zai kirani yaga abinda za ayi
akan case din kuma mu kwantar da hankalinmu, ko wayar bani da shi a sannan, instead sai na basa Address
din unguwanmu Mariri, ita dai kishiyar yayata na zaune karkashin bishiya tayi tagumi, a haka muka bar
kotu ranan rai babu dadi muka koma gida, bayan kwana biyu ranan da yamma wajen karfe shidda muna
zaune tsakar gida ko wacce na fafutukar abinda zata dora ta ciyar da kanta da yaranta, don yanzu kowa
takai takai a gidan, kishiyoyin yayata har sun sake 'ya yan su maza kanana suna fita almajiranci suna ciyar
da kansu, matan kuma a dora masu talla su tafi can bakin kasuwa, yayata dama ina taimaka mata muna
sana'a a gida, kudin waec din Khaleesat ne dai muka kasa hadawa gashi saura kwanaki kadan a fara, kamar
daga sama sai ga Mahaifin Khaleesat ya shigo gidan kamar an jefosa, Khaleesat ce ta fara ganinsa ta tafi da
gudu ta rungumesa, duk muka mike tsaye a tsorace muna kallon ikon Allah baki bude, yayata tayi karfin
halin tunkararsa tana tambayarsa daga ina yake haka, kar dai gudowa yayi daga gidan yari, Baban
Khaleesat yace kawai shi dai ce masa aka yi an bada belinsa daxu da rana, sai gashi kuma aka daukosa aka
kawo har gida aka ajiyesa, tsabar mamaki duk muka kasa cewa komai a tsakar gidan, yayata ta kama
hannunsa hawaye cike idonta ta kai sa dakinsa don shi ma duk a firgice yake kana ganinsa kasan ba
karamin wahala ya sha ba, sai a sannan yaran gidan suka fara ihu suna murnan dawowan mahaifinsu suna
ta tsalle tsalle, sauran matan duk suka bi bayan yayata zuwa dakin Baban Khaleesat"
[5/30, 7:48 PM] khaleesat Haiydar ✍️: Khaleesat na zaune hall din da jama'a ke jiran Luggages dinsu a
Arrival, duk da bata da kayan da zata jira amma rashin sanin inda ta nufa yasa ta zauna wajen tana bin
kowa da kallo, tun 15 mins ago jirginsu ya sauka Abuja, daurewa kawai take don wani bacci take ji tare da
gajiya, vibration taji a jakarta dake cinyarta alamar ana kiran waya, a hankali ta bude jakar ta ciro wayar da
AJ ya bata tana kallon screen din, har ya katse bata daga ba don number kawai ta gani ba ayi saving ba bata
san ko ta daga ba ko kar ta daga, kiran wayar da ake ta yi continuously ne yasa tayi picking tayi shiru tana
sauraron me magana taji namiji ne, ta amsa sallaman da yayi mata, sannan yayi introducing kansa ya sanar
mata shi ne ya zo daukanta Airport, a hankali Khaleesat tace "Ohk" Mikewa tayi ta fita daga Arrival din
tana kalle kallen inda yace mata yake a Airport din, sai ga shi ya nufota bayan ya gane ita ya zo dauka,
gaisheta yayi da ladabi yace "Babu kaya ko Hajiya?" Khaleesat ta gyada masa kai kawai, yace "Bismillah,
Motar na can nayi parking" Tana biye da shi suka isa inda motar yake, ya bude mata back seat ta shiga ya
kulle sannan ya zaga ya shiga driver seat, Ita dai Khaleesat ji tayi kawai yana sanar mata sun iso, bata san
for how long suka yi tafiyar ba don bacci ne ya dauketa throughout the journey, gyara zama tayi tana kalle
kallen compound din gidan da suke ciki, ta kalli Drivern da ya bude mata back seat, ta sauko a hankali tace
"Nagode" Gida ne babba irin na zamani, tana biye da shi ya kai ta har zuwa Entrance din shiga babban
parlon gidan ya danna bell, ba a dau lokaci ba aka bude kofar wata budurwa ce warce bazata wuce ta ba ta
gani tsaye, da ladabi Drivern yace "Bakuwar da na dauko Airport ce Hajiya" Yarinyar ta ɗan yi murmushi ta
koma gefe tana kallon Khaleesat tace "Sannu da zuwa sister, come in" Khaleesat ta shiga parlon yarinyar ta
kullo kofar tana nuna mata kujera ta zauna, bayan Khaleesat ta zauna yarinyar na kallonta tace "I am
Inteesar" Khaleesat ta daga idanuwanta ta kalleta tace "Sunana Khaleesat" Yarinyar tace "Welcome
Khaleesat, bari in ma Ammin mu magana" Daga haka ta juya ta bar parlon, after a while sai ga ta sun shigo
parlon da wata dattijuwa that is in her middle 50, zamowa kasa Khaleesat tayi a hankali tana gaisheta, da
fara'a matar da ake kira da Ammi ta dagota tace "A'a, koma kiyi zamanki kan kujera diyata" Khaleesat ta
koma ta zauna kan kujeran, Matar ta zauna kusa da ita tace "Sannu da zuwa, ya hanya?" Khaleesat tace
"Alhmdlh, ina yini" Ammi tace "Lafiya lau, ya kika baro mutan gidan?" Khaleesat tace "Suna lafiya lau"
Ammi tace "Ai na zata tare da Yariman ku ke, ashe ke kadai ce" Ita dai Khaleesat ta sunkuyar da kanta tayi
shiru tana wasa da gefen hijab dinta, Ammi ta kalli Inteesar tace "Inteesar ki kai ta daki ta huta" Inteesar
tace "Ohk" Tare suka tafi dakin Khaleesat na biye da ita, Ammi ta bi su da kallo. Wajen karfe takwas na
dare Khaleesat na zaune daki tare da Inteesar da ta mayar da ita Television, ita dai a hankali take cin fruit
salad din gabanta, tun zuwanta gidan in dai ta kalli Inteesar by mistake zata ga kallonta kawai take, da sun
hada ido kuma sai Inteesar ta mata murmushi, Khaleesat wasn't bothered da kallon don farkon haduwarsu
da Sophie haka ita ma take mata, tayi ta kallonta a makaranta ko gajiya bata yi kuma da sun hada ido sai ta
mata murmushi, bayan sun zama best of friends ne Sophie ke gaya mata she is soo beautiful shi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login