Showing 24001 words to 27000 words out of 152206 words
a parlon"
Khaleesat ta dau spoon ta fara cin abincin tace "Ko dai kin san sa ne Safiyyah?" Dariya Safiyyah tayi tace
"Ina kuwa na san sa, kawai so nake in gansa ne wallahi, irin wannan kayan alatu a kitchen haka, where is
he even getting the money shi da ya zo ta scholarship" Khaleesat dai cin abincin gabanta kawai take taki ce
mata komai, Safiyyah ta dau spoon ta fara cin abincin ita ma, basu jima da fara cin abincin ba sai ga shi ya
fito daga dakinsa, bai kalli direction din da suke ba ya nufi kofa rike da laptop dinsa, Safiyyah ta bi sa da
kallo kamar idonta zai fita ya bi sa, ita dai Khaleesat kallo daya tayi masa ta ci gaba da cin abincinta har ya
fita daga parlon ya kulle masu kofa, Safiyyah ta ajiye spoon din hannunta tace "To fa, shi kuma haka yake?
Ji wani ɗaga shoulders da yake ko kallon inda muke bai yi ba, haka yake maki a gidan dama?" Khaleesat
tace "You can be funny Safiyyah" Safiyyah ta hade rai tace "No like seriously haka yake feeling kansa? Ko
don abincin da yake ajiye maki na yan gayu a kitchen ne ya ja haka? Ta yaya zai wani wuce mu babu ko Hi,
ni fa bana son harkan walakanci" Khaleesat tace "Look Safiyyah ni ba shi ya ajiye min duk abinda kika
gani a kitchen ba, shi baya ma zaman gidan nan, jifa jifa kawai nake ganinsa, beside ai mun gaisa da ya
shigo kina kitchen, to kuma kallon me zai yi mana don zai fita?" Safiyyah zata yi magana wayarta ya fara
ring, mikewa tayi ta dauko wayar, ta ɗan buda ido tana kallon Khaleesat tace "Ke Abdul ne ke kirs" Sosai
gaban Khaleesat ya fadi ta ajiye cokalin hannunta ta dinga kallon wayar Safiyyah, Safiyyah ta rike haɓa
tace "Ikon Allah, ko ya kiraki baki daga bane? Let me pick dai inji me zai ce" Da sauri Khaleesat ta kamo
hannunta zuciyarta na bugawa tace "Safiyyah kar ki ce masa naje Nigeria plss cause bai sani ba wallahi"
Safiyyah ta saki baki tana kallonta hangangan, da mugun mamaki tace "Ban gane bai sani ba? To wa yayi
sponsoring tafiyar taki? Ina kika samu kudin tafiya" Sosai hankalin Khaleesat ya tashi a lkcn, tana girgiza
ma Safiyyah kai tace "Just don't tell him pls, nace maki bai sani ba" Safiyyah da mamaki ya kasa barin ta
tace "Ai kiran nasa ma ya katse" Khaleesat taji gaba daya abincin ya fita ranta, sai ga kiransa ya sake
shigowa wayar Safiyyah, Safiyyah ta gwalo ido tace "Abdul ne da kirana har sau biyu? Anya lafiya"
Khaleesat tayi gathering courage tace "Just pick, in ya tambayeki ni kawai kice masa bani da lafiya yanzu
ma kika baro gidana" Safiyyah tace "Ohk" Picking call din tayi ta saka handsfree, ita ta masa sallama ya
amsa yace "Ya kike?" Safiyyah tace "I am good" yace "Are you together with Khaleesat?" Babu bata lkci
Safiyyah ta sanar masa exactly abinda Khaleesat tace ta gaya masa, ya dan yi shiru at first, sai kuma yace
"Tun yaushe ne bata da lafiya?" Safiyyah ta kalli Khaleesat, da sauri Khaleesat tayi mata alamar sati daya
da fingers dinta, Safiyyah tace "Yau ina jin sati daya kenan" Daga daya bangaren yace "Sati daya? Me yasa
ba a gaya min ba, and what's wrong with her?" Safiyyah tace "Oh ni na zata ai ta gaya maka" Abdul yace
"Wani irin rashin lafiya take haka dake hindering dinta from picking calls?" Safiyyah ta wani yamutse
fuska jin useless question din da yake yi taki basa amsa tana kyabe baki, ita dai Khaleesat gabanta sai
faduwa yake, Yace "Where is she now?" Sounding uninterested with the conversation Safiyyah tace "Tana
gidanta mana" Da sauri Khaleesat tayi typing a wayarta sannan ta nuna ma Safiyyah, bayan Safiyyah ta ga
abinda Khaleesat ta rubuta tace "Jikin nata dai da sauki sosai fa" A takaice yace "Thanks" Daga haka ya
katse wayar, Safiyyah ta ajiye wayarta tace "Tirrrr, ki ji wani magana gatsau gatsau kamar dan daba, ko
tashi hankalinsa fa bai yi ba, ni wallahi da ina da yanda zanyi ku rabu rabuwa na har abada da Abdul din
nan wallahi yi zan yi, ko kadan bashi da features din miji na gari, babu caring babu tausayi babu affection,
so pompous and full of himself always, nonsense and ingredient, wallahi in wani mutumin kirki ne da
yanzu hankalinsa ya tashi duk ya birkice min a waya amma kiji yanda yake magana a tsattsaye kamar
ubana daga karshe wai Thanks, kamar wanda nayi ma albishir me dadi wai Thanks, ke ki ji fa wai thanks" a
hankali Khaleesat tace "Baza ki gane ba Safiyyah, nima naji i am fed up with him, na gaji da halinsa yanzu"
Safiyyah ta rike haba da sauri tace "Ke Khaleesat, anya kece ke fadin haka kuwa?" Khaleesat ta wani taɓe
baki ta jawo abinci ta fara ci tace "Kawai naji na gaji all of a sudden wllhi" Safiyyah ta sako baki tana mata
kallon mamaki, can tace "Ni ba wannan ba ma, Khaleesat wa yayi sponsoring flight dinki zuwa Nigeria?"
Khaleesat ta daga kai tana kallonta amma tayi shiru, Safiyyah tace "Kin yi shiru, waye ya biya maki kudin
jirgi?" Khaleesat ta sauke idonta kamar bazata ce komai ba sai kuma tace "Housemate dina ne ya siya min
Ticket" Safiyyah ta gwalo ido da wani expression na mamaki sosai tace "Ban fahimta ba Khaleesat,
Housemate dinki as how?" Khaleesat ta sauke ajiyar zuciya tace "Eh shi ne ya biya min ticket din jirgin...."
Khaleesat bata boye ma Safiyyah duk yanda aka yi Housemate din nata yayi sponsoring tafiyarta ba,
Safiyyah was totally speechless and Surprise, after few seconds tace "Did you know what flight ticket is
saying from USA to Nigeria Khaleesat?" Khaleesat tace "I went to Nigeria in business class and came back
in Business class Sophie" Buda baki Safiyyah tayi ba tare da ta san tayi hakan ba tana kallon Khaleesat
kamar idanuwanta za su fito, a hankali tace "Business class fa kika ce Khaleesat?" Khaleesat ta gyada mata
kai, Safiyyah ta fara bin gidan da suke ciki da kallo that is for the average here in America, da wani
Expression tace "Business class? To me yake yi a wannan gidan if he is doing this well that he can afford to
pay for business class to and fro? Dama ni tun daga irin abubuwan da na gani a kitchen nasan wannan
mutumi might be trying to disguise himself for a reason best known to him, idan ba haka ba why share an
Apartment bayan zai iya affording shi kadai ya zauna a gidan, beside zai iya samun wanda ma yafi wannan
in a more better area" Ita dai Khaleesat kallon Safiyyah kawai take ganin yanda tayi concluding lokaci
daya, Safiyyah ta wani juya ido tace "Or did he have any mission here da bamu sani ba?" Khaleesat ta
girgiza kai tace "Daga sanda nayi misplacing makullina ne ya fara kwana gidan nan tunda yasan bani da
makulli, amma tun da yayi move in zuwa gidan nan i can count sau nawa ya kwana if i remembered well,
baya kwana nan wallahi, ba har na gaya maki ba...." Safiyyah tayi dariya tace "But i am trying to
understand me yasa yake zaune a gidan nan, ko dai ya sanki from somewhere ne shine ya dawo nan saboda
ke?" Khaleesat tace "Ji fa wani magana, bai san ni a ko ina ba wallahi, ni bamu taɓa haduwa da shi ba,
ranan da suka fara zuwa gidan i overheard him asking if his housemate is a Male or female, lkcn ina
dakina, kilan he is in a haste to settle down ne shi yasa kawai he opt for this, amma bai san ni ba wallahi"
Safiyyah dai tayi wani murmushi tace "Ae shikenan we shall see" Sai kusan karfe bakwai Safiyyah ta bar
gidan shi ma saboda azababben kiran da Ya Mustapha ke mata ne, tana mita haka ta bar gidan, bayan
Khaleesat ta rakata ta dawo tayi sallahn magarib a nan parlon tana zaune saman darduma bayan ta gama
azkar ta dau wayarta don dubawa ko Ummanta tayi mata reply, tun Safiyyah na nan suke Voice chat da
Ummanta da kannenta, ganin Umma bata yi reply ba ta gane wayar ya mutu don dama Umma tace mata
babu caji wayar ta kusa mutuwa, mamakin Abdul kawai Khaleesat ke yi a ranta, duk da ce masa da
Safiyyah tayi bata da lafiya amma har yanzu bai kira wayarta ba, ko ta Whatsapp bai mata magana ba, tana
cikin wannan tunanin taji an bude kofar parlon, juyawa tayi Housemate dinta ya shigo, sallama yayi ganinta
a parlon, ta dauke idonta ta amsa, ya karaso cikin parlon without looking at her ya tafi inda Books dinsa
suke yace "Kawar taki ta tafi kenan...." Khaleesat tace "Ina yini" Yace "Good evening Halysaah" Bayan ya
gama daukan text books da zai dauka ya dawo cikin parlon yace "Alright Good night" Ta bi sa da kallo, sai
da ya nufi kofa ya sake juyowa yace "Sai da safe" Ta sauke idonta tace "Allah ya kai mu lafiya" Daga haka
ya bude kofar ya fita tana jin ya kulle kofar da makulli daga waje. Washegari Khaleesat bata da karatun da
za su yi a makaranta, don haka har karfe goma bata fito parlor ba tana kwance, ita har sannan fa ta kasa
daina mamakin Abdul don har sannan bai kirata ba, tashi tayi daga karshe ta shiga bandaki tayi wanka ta
shirya, wajen karfe goma da minti arba'in ta fito daga dakinta, kwance taga Housemate dinta saman 3 seater
yana bacci, kulle kofar da tayi ne yasa ya bude ido a hankali, walking slowly ta karaso cikin parlon, juyawa
yayi bayan ya sake rufe idonsa as if murmuring yace "Good Morning Halysaah" Tace "Ina kwana" Bai
bude ido ba bai kuma amsa ba alamar ya ci gaba da baccinsa, ita dai ta wuce kitchen. After an hour
Khaleesat ta fito daga kitchen bayan ta gama girkin da take, zaune ta gansa a parlon ya dafe kansa, tsayawa
tayi tana kallonsa, ya daga kai suna hada ido ta ɗan koma baya tace "Is everything okay?"
✍🏻
07087865788
[5/6, 4:37 PM] khaleesat Haiydar ✍️: ✨✨HALYSAAH✨✨
✍🏻
By _Khaleesat Haiydar_
9.....
Still bai dago kansa ba yace "Tashi na kika yi" Ta ɗan bude ido tana kallonsa tace "How?" Ya koma ya
kwanta ya rufe ido yace "With the noise ur utensils were making in the kitchen" At first kamar bazata ce
komai ba, sai kuma tace "To ai ba nan ya kamata ka kwanta kana bacci ba" Ya bude ido yace "Ok u
intentionally woke me up kenan?" tace "Ni ban ma san kana parlon ba ai..." Murmushi kawai yayi bai ce
mata komai ba, tana ɗan kallonsa a hankali tace "I made some breakfast, you can have some" Yace "Ok
thanks, baki je schl yau ba?" Tace "Ba mu da lectures" Yace "Ohk, wani school kike?" Shiru tayi tana
kallonsa, ya mike zaune yace "University of Maryland Baltimore? Loyola University Maryland? Morgan
state University? Stevenson University? Johns Hopkins University?" Tace "Duk kuma a nan garin su ke?"
Yace "Ohh, kina gari baki san makarantun dake garin ba?" Ta girgiza masa kai kawai still looking at him,
shi dai bai kalleta ba yace "To ke wanne kike zuwa a cikinsu?" Ta sauke idonta tace "Na karshen da ka
kira" Ya ɗan yi murmushi yace "John Hopkins kenan? Buh ni ban taɓa ganin ko me kama dake a schl din ba
ai" Yayi dariya yace "Just joking kafin ki fara min kuka" Ta wani kallesa, duk wannan abun bai kalli
direction dinta ba yana magana ne yana kallon agogon wrist dinsa, yace wani course kike yi?" Tace
"Pharmacology" Sai a sannan ya kalleta yace "Really?" Ta gyada masa kai, yace "That's a very good
course, year what kike yanzu?" Calmly tace "Year 3" Ya gyada kai yace "Good, Allah ya bada sa'a" Ta
sauke idonta tace "Ameen" Yace "Ban yi tunanin makarantar kike ba da na dinga dropping dinki in zan je
ai, ko da yake ba lallai sanda zan je kina da Class ba...." Sunan wani lecturer dinsu ya kira mata, kawai ta
ɗan yi murmushi tana kallonsa cause he is one of her favourite lecturer, yace "He took us during our
Undergraduate Degree, and Master's degree also, that was 3 years back, and he is still among my
Supervisors currently...." Khaleesat dai sai kallonsa take, ta kasa hakuri har sai da tace "And you are still a
student till date?" Ɗan murmushi yayi yace "I am a Medical Dr, pursuing my PhD on Cardiology"
Khaleesat couldn't stop staring at him, Yace "I have been studying since i was a baby" Tace "Amma lecturer
kake son zama?" Er dariya yayi yace "Not at all Halysaah...." Khaleesat dai tayi shiru bata ce komai ba tana
kallonsa, ya dau wayarsa da ake kira ya mayar ya ajiye yace "Kin ci abincin ne a kitchen naga ban ganki da
plate ba as usual?" Ta wani kallesa bata ce komai ba ta juya tayi wucewarta daki, shayi ta sha da cookies a
kitchen sanda take girki, bayan ta gama girkin kuma taji bata ma jin yunwan shi sa bata zuba abincin ba,
Khaleesat ta koma dakinta da kusan 45 minutes tana duba wani course dinsu ta laptop taji kamar ana
knocking din kofar parlor, ta mike ta fito parlorn, tsaye taga Housemate dinta bakin kofar living room din
har ya bude kofar, Safiyyah ce ta shigo parlon tana kallonsa tace "Hello" Ya dauke idonsa yace "Hi"
Komawa daki Khaleesat tayi, Safiyyah tace "Pls is Khaleesat around?" Yace "Sure...." Dakin Khaleesat ta
nufa, shi kuma ya tafi ya ci gaba da karatun da yake a parlor, Khaleesat ta mike tana kallon Safiyyah bayan
ta shigo dakinta tace "Why are you looking this way Sophie?" Safiyyah tace "Wallahi kwanan nan zaki ji
nayi ma matar can duka a kasar nan" Khaleesat tayi murmushi tace "Me kuma tayi maki again?" Gefen
gado Safiyyah ta zauna kana ganinta kasan ranta a bace yake tace "Tun fa da kika je gidan mugun halinta
ya ninku akan wanda take min a baya Khaleesat, she is trying all possible best to make the house miserable
for me, dama yanzu ta dena ajiye min abinci kwata kwata, cornflakes da Golden morn sai ta boye a dakinta
da sunan taje hada ma yaronta ne duk don kar in sha...." Khaleesat ta sauke ajiyar zuciya tace "To Allah ya
kyauta, ko zaki dawo nan?" Safiyyah tace "In dawo nan for what reason? ashe ma riba ta ci kenan idan na
bar mata gidan, ai we die together with her in that house, babu inda zan dawo wallahi, kawai rabon ta ci
duka ne ba wani abu ba" Lkci daya expression din Safiyyah ya canza daga bacin rai ta kamo hannun
Khaleesat tana washe baki tace "Kee naga Housemate dinki ido da ido yau, dama haka yake gayen? Wallahi
he is so well flavoured komai yaji, ina masa magana ma ko kallona bai yi ba amma ya amsa min cikin
girmamawa, wallahi ya burgeni" Tana blushing ta karasa maganar nata, Khaleesat dai ta saki baki ta kasa
cewa komai, can ta kalli kofar dakinta da sauri don ta tabbatar a kulle yake kar ace yana jiyo Safiyyah, sai
kuma tayi kasa da murya fuska daure tace "Meye haka Safiyyah what if yana jin ki?" Safiyyah tace
"Wallahi raina a bace yake amma yana bude kofar kawai na mance da abinda er iskar matar can ta min, a
very calm gentleman, yace min Hi nace Hello... kuma kuna Hausa da shi ko turanci ku ke? Ni sai nake ga
kamar ba bahaushe bane ba fa" Khaleesat ta hade rai sosai tace "Don Allah ki rufa mana asiri Sophie,
What's all this?" Safiyyah tayi dariya tace "Ni dai kinyi girki? Don wallahi yunwa nake ji" Khaleesat ta
mike ta nufi kofa ta fita daga dakin, a corridor ta gansa zai shiga dakinsa, bai kalli ma wanda ya bude kofa
ba yayi shigewarsa daki, Khaleesat ta tafi kitchen ta dibar ma Safiyyah abincin da ta girka, jin alamar har
ya fito daga dakin nasa ta dawo parlor ta tsaya sai gashi ya shigo parlon, makullin motarsa taga ya dauka da
wani littafi, ya daga kai suka hada ido ta fara kame kame tace "Ain't you eating the food?" Yace "Oh, ok na
manta" Kitchen din taga ya nufa ta bi sa da kallo, sai da ya shiga sannan ta bi bayansa zata gaya masa kar
ya bar mata plate bai wanke ba, tsaye ta gansa kusa da abincin ya dau spoon ya bude tukunyar sannan ya
debi shinkafar kadan ya kai baki, kallonsa kawai take da mamaki, ya juya ya kalleta yace "Bad habit right?"
Sake dibar abincin yayi ya kai baki, daga haka ya rufe tukunyar yace "Kinga ni ba yunwa nake ji ba, I am
full" Ta dinga kallonsa, bata san sanda tace "Ko in zuba maka ka tafi da shi?" Ya bude fridge ya ciro bottle
water yace "Aa in na dawo anjima zan ci" Daga haka ya fita daga kitchen din ya nufi kofar living room ya
bude, sai a sannan ya juya, ta dauke idonta, yace "See yah" Fita yayi ya kulle kofar daga waje. Sai wajen
karfe shidda na yamma Khaleesat ta raka Safiyyah zata hau Uber da tayi ordering, Safiyyah na kallonta
tace "Ya Mustapha dai ya hakura dake, jiya nake gaya masa gaskiya kina da wanda zaki aura a gida, don
nima na gaji da damuna da yake yi shi sa kawai na gaya masa, ai ko ina gaya masa yace to shikenan dama
tun farko ai da kin gaya masa he will understand" Khaleesat ta sauke ajiyar zuciya tace "To ai kinga gwara
haka" a haka suka rabu Khaleesat ta koma cikin gida, har goma na dare bata ji shigowar housemate din nata
ba hakan yasa ta gane bazai dawo gidan ba ranan. Washegari da safe ta shirya ta tafi makaranta, bata dawo
gidan ba sai kusan karfe hudu na yamma, tana shiga living room ta gane ya dawo gidan da bata nan,
bedroom dinta ta wuce bayan tayi wanka tayi sallah ta canza kaya ta fito kitchen zata yi ɗan wake don shi
ne a ranta, bayan ta gama hada duk ingredients din taji an bude kofar parlor, ta dai ci gaba da abinda take,
kitchen din ya shigo ya ajiye ledan hannunsa yace "Good evening Halysaah" Tace "Ina yini?" Yace "Lafiya
lau, Are you baking?" Ta kalli flour din da take kokarin kwabawa tace "No" Yace "What are u using flour
for?" Bata yarda su hada ido ba tace "Dan wake" Da mamaki yace "Meye shi?" Ta wani kallesa ganin da
gaske jiran amsarta yake tace "Dan waken ne baka sani ba?" Yace "Ban san shi ba" Tace "Toh zaka gansa"
Turning stick ta dauko ta fara kwabin danwaken shi dai