Showing 105001 words to 108000 words out of 152206 words

Chapter 36 - HALYSAAH by Khlst Hydrr

13 May 2026

64

plate din abincin da Aunty Farida
ta zuba mata not long ago, ta bude murfin ta ajiye sannan ta dau spoon ta fara cin abincin a hankali, Aunty
Farida na kallonsu tace "Bari in kawo maku abinci" Ajay ya kalli Jay, Jay yace "A'a mun yi breakfast
Aunty, mun gode" Aunty Farida tace "To ai rana tayi yanzu" Bata jira taji me zai ce ba ta tafi kitchen zata
zubo masu abincin, ita dai Khaleesat a hankali take cin abincin hannunta, mikewa Ajay yayi, Jay ya sa
hannu a aljihunsa ya ciro wayarsa, Ajay yace "Zan yi waya a waje" Daga haka ya fita daga parlon kafin
Aunty Farida ta fito daga kitchen, Jay yayi murmushi bai dai ce komai ba, bude wayarsa yayi yaga miss
calls din Safiyyah har shidda, yayi dialing number dinta ya saka handsfree, yana fara ring Safiyyah ta daga
kamar jira take, yayi kasa da murya yace "Can you hear me Safiyyah?" Tace "Ina jin ka, plss ba a san inda
Khaleesat take bane tun ranan asabar, kuma ni nasan bata da inda zata je a garin kano" Yace "Where are
you at now?" Da sauri tace "Nima a kano nake ai, jiya da yamma na dawo daga Maryland shi ne na zo
gidansu yau nake samun labari she is away from home tun ranan Saturday after receiving the news of her
marriage with Abdul, wai Abdul fa aka daura mata aure da" Safiyya na kai wa nan ta fashe da kuka, Jay
yace "I mean are you at home or where?" Cikin kuka tace "A'a yanxu na baro gidansu, ina bakin titi ma
haka, i am just confuse, Khaleesat bata da kawaye bata zuwa ko ina, i don't know where she will be now, i
am disturb don Allah in kasan inda take kar ka boye min plss Ya Jawwad trust me" Calmly yace "Look, this
should be confidential Safiyyah, i trust you are saying nothing to anybody about this...." Da sauri Safiyyah
tace "Na rantse babu wanda zan ce ma komai Ya Jawwad, trust me, i am also not in support of the fruitless
marriage" Jay yace "Ohk, here is ur frnd speak to her....." Mikewa yayi ya mika ma Khaleesat wayar, ta
amshi wayar tana kallon screen din dama tun jiya take wishing ace Sophie na kusa da ita ko ba komai zata
dinga Consoling dinta tana karfafa mata gwiwa da bata assurance, lkci daya hawaye ya cika idonta cikin
rawan murya tace "Sophie" Safiyyah ta sauke ajiyar zuciya tace "Khaleesat, i am so happy you are safe and
sound, dama fatana kenan, plss kina ina haka yanxu in taho don Allah" Khaleesat ta girgiza mata kai cikin
sanyin murya tace "Bana kano Sophie" Da mamaki Safiyya tace "To kina ina?" Khaleesat ta daga kai ta
kalli Housemate dinta dake kallonta, sauke idonta tayi da kyar tace "Ina Lagos" Safiyyah tace "Lagos wajen
wa? Ko wajen Aunty Farida?" Khaleesat tace "Um" Safiyyah tace "Amma Umma bata san kina nan ba" a
hankali Khaleesat tace "Bata sani ba" Safiyya ta sauke wani ajiyar zuciyar tace "Pls kar ki tada hankalinki
kinji kawata, i know ur Housemate won't allow u do that, kuma in sha Allah babu zaman aure tsakaninki da
Abdul don bai yi deserving din ki ba, i can't imagine what he will turn you into, in Allah ya yarda bazai ci
nasara akan ki ba, Allah zai raba auren cikin gaggawa, shi kadai yasan mugun Intention din dake ransa akan
ki shi yasa yayi haka, amma Allah ya fi sa" Khaleesat dai gyada mata kai kawai take hawaye na sauka
idonta ta kasa cewa komai, Housemate dinta ya mike ya nufeta ya amshi wayar a hannunta ya koma ya
zauna yace "Safiyyah" A sanyaye Safiyyah tace "Na'am Ya Jawwad, Please kawata bata da wanda zai tsaya
mata akan issue din nan, ba da intention me kyau ya saka aka daura auren ba wallahi, mugu ne azzalumi,
har abusing dinta yana yi" Jay dake sauraronta yace "In sha Allah we will try our very best ki taya mu da
addu'a" Safiyyah tace "In sha Allah, but how can i be reaching her?" Yace "Don't you have her aunt's
number" Safiyyah tace "Sure ina da shi, i will be calling her ta wayar Aunty Farida" Jay yace "Keep this
confidential pls Safiyyah" Safiyyah tace "Trust me Ya Jawwad, i now have rest of mind knowing my frnd is
safe" Da haka suka yi sallama ya ajiye wayar, Khaleesat ta ajiye plate din abincin hannunta don ta kasa ci,
iya spoon uku kawai ta iya yi, tuni Aunty Farida har ta ajiye ma Jay abincin da ta zubo ta nemi waje ta
zauna, sai da ta jira suka gama waya da Safiyyah sannan ta kallesa tace "Ina Junaid din ga abincin na zuba
maku" Jay yace "Aunty bamu dade da cin abinci ba da gaske" Aunty Farida tace "Ai ko in baku ci ba bazan
ji dadi ba, haka jiya ku ka bar min abincin ku ka ki ci, yanxu fa karfe biyu da rabi ake nema kuma breakfast
kace kawai ku ka yi" Jay dai murmushi kawai yake, can yace "Toh zan ci Aunty" Tace "To ko kai fa, ina
Junaid din kayi masa magana ya shigo ku ci" Jay na shafa kansa yace "Ai shi ya ci snacks a mota bazai ci
abincin ba na sani, bai fiye cin abinci da rana ba" Aunty Farida tace "Ikon Allah to saboda me?" Jay yace
"Haka yake, iya breakfast da Dinner kawai yake yi" Aunty Farida tace "Iko sai Allah" Jay na kallon abincin
da Khaleesat ta rage ya mike ya dauko yace "Zan ci wannan kar mu bata abincin Aunty" Aunty Farida tace
"Don Allah ka ajiye ka debi abinci ga plate nan Jawwad" Yace "Aunty wannan fa ya isheni ba iya cinyewa
zan yi ba ma" Spoon din ya dauka ya fara cin abincin, Khaleesat dai kallonsa kawai take, Aunty Farida tace
"Ai shikenan" Karfe uku da yan mintuna Ajay da Jay suka bar gidan, Jay ne ke driving din idonsa akan titi
yace "To ya ku ka yi da Lauyan?" Ajay yace "He said we should meet in kano" Jay ya ɗan kallesa yace
"Zuwa gobe kenan?" Ajay yace "Sure, tomorrow in the morning za mu tafi kano" Jay bai sake cewa komai
ba har suka isa gida, yau dai traffic din da ɗan sauki, bayan Jay yayi parking ya juya yana kallon Ajay yace
"Please since gobe za mu tafi kano ka bar maganar hotel da kace zaka koma" Ajay yace "Ai matar ne ta fiye
takura da sa ido" Jay yayi dariya bai dai ce masa komai ba suka sauka zuwa cikin gidan, Ummi na zaune
parlon Hadeeyah na kwance kusa da ita da daura kanta a saman cinyar Ummin, ba tare da Ajay ya kalleta
ba ya gaisheta a takaice zai wuce sama Hadeeyah ta gaishesa ya amsa yana haura stairs, Jay ya zauna
parlon ya gaida Ummi ta amsa tace "Sai yanxu? Ko dai ba Bar beach din ku ka je ba?" Jay ya ɗan buda ido
yace "Mun fasa" Yana magana ne yana kallon Hadeeyah da ta hade rai tana danna wayarta kamar bata
gansa ba, Ummi ta kalleta tace "Ke baki ga yayanki bane" Hadeeyah na ci gaba da danna wayarta tace "Oh,
ok, Good evening" Jay yace "Ya hanya?" Tace "Lafiya lau" Ummi na kallonsa tace "Mami tana sama" Jay
ya mike yace "Ohk" Sama ya wuce, Hadeeyah ta bi sa da kallon gefen ido har ya fara hawa stairs, bayan ya
tafi Ummi na kallon Hadeeyah tace "Fadan ku ka sake yi kenan?" Hadeeyah ta ɗan yatsine fuska taki cewa
komai tana danna wayarta, Ummi ta kyabe baki tace "Kun fi kusa dai" Jay na bude kofar dakin da yasan
Maminsa na ciki ya sameta zaune tana waya, ya karasa ya zauna kusa da ita yana kallonta yayi mata side
hug ya jinginar da kansa a shoulder dinta a hankali yace "Mami" Mami tayi ma warce suke wayar sallama
ta ajiye wayar hannunta tana kallonsa tace "Ina ka je tun safe Son? I was thinking zaka zo airport kayi
picking din mu" Jay ya ɗan kalleta yace "Karfe nawa ku ka iso Mami?" Tace "Karfe sha daya da rabi na
safe" Jay yace "Mun fita ne da Ajay, Ummi bata gaya maki ba" Mami tace "Kaga da ubansa ne zai sauka
Lagos duk abinda yake yi barin sa zai yi ya tafi ya taro sa, amma kai uwarka ta sauka Lagos ya ja ka kun
tafi gantali" Jay bai ce mata komai ba, Mami na kallonsa tace "Duk karatun ne yasa ka fada haka? Are you
okay?" Jay yace "Stress din tafiyar da nayi zuwa Nigeria ne" Mami tace "Nasan shi zai zugaka ku dawo
Nigeria kar ka biyo min ta UK" Jay ya ɗan hade rai yace "Ya fa riga ni dawowa Nigeria Mami, ni ba jiya na
dawo ba, shi kuma ai tun last week yake Nigeria" Mami ta tabe baki bata ce komai ba, Jay ya mike ya nufi
kofa yace "Zan je inyi wanka" Mami tace "Dama gobe ka shirya mu tafi Bauchi ban san gantalin da yake
jan ka ku ke yi a Lagos ba, kai da ko ance ka sauka Lagos baka taba yarda sai gashi saboda Junaid na lagos
kai ma ka zauna a lagos, to gobe za mu tafi Bauchi kuma Hadeeyah ma a can zata yi hutu" Jay ya juya ya
kalleta yace "Mami ni ban gama abinda nake yi ba, kawai ku yi tafiyar ku" Bai jira me zata ce ba ya fice
daga dakin. Wajen karfe biyar da rabi Jay da Ajay suka sauko downstairs, dakin dake kasa suka nufa don
Mami na ciki tare da wata bakuwarta warce suka hadu da dadewa a Saudia suna zumunci sun zama kaman
en uwa, jin Mami ta shigo Lagos sai matar ta taho gidan gaida Mami tunda ita ma a Lagos din take, Ajay ya
zauna kan 1 sitter dake dakin ya gaida Mami sannan ya gaida frnd dinta, Jay ma ya zauna ya gaida kawar
Maminsa, matar me suna Hajiya Batula ta amsa da fara'a tana kallonsu sai kuma ta kalli Mami tace "Wanne
ne son din naki a ciki Hajiya?" Mami tayi pointing Jay tace "That is my son" Matar na kallon Jay tace "Maa
sha Allah, ai kuwa ga kama na gani" Shi dai Ajay danna wayarsa kawai yake bai dago kansa ba, Jay ya
mike yace "Mami za mu je Gym ne" Mami ta kallesa tace "Da yamman nan ga uban traffic din Lagos ne
zaka je Gym?" Jay yace "Ai ba nisa Gym din" Hajiya Batula tace "Nan Area din ma ai da Gym ba sai sun je
da nisa ba" Jay ya kalli Ajay yace "Mu je" Mikewa Ajay yayi ya nufi kofa Jay ya bi bayansa suka fice daga
dakin, Hajiya Batula tace "Amma ɗan uwansa ne wannan din ai ko, naga suna yanayi sosai" Mami tace "Eh
Cousin dinsa ne" Hajiya Batula tayi kasa da murya tace "Ko dai shi ne ɗan sarkin dai?" Mami ta tabe baki
tace "Shi ne" Hajiya Batula tace "Ya sunansa?" Mami tace "Sunansu daya Ahmad amma Junaid ake
kiransa" Hajiya Batula tace "Ikon Allah, shi kam Jawwad babu ruwansa..." Cike da takaici Mami tace "Ni
babban bakin cikina yanda har yanxu Jawwad bai san ciwon kansa ba, hakan na ci min tuwo a kwarya
wallahi, controlling dinsa kawai yake yana bin sa, ko a America din ma Junaid din ne ke juyasa" Hajiya
Batula tace "A'a gaskiya bai san ciwon kansa ba naga alama, shi ko kishi baya yi, kuma gaskiya Mai
martaba ya nuna son kansa a fili karara nada ɗan sa da yayi Yarima me jiran gado a maimakon Jawwad, ina
ce Jawwad din ya girmi ɗan sa?" Mami tace "Ya basa watanni har uku" Hajiya Batula ta rike haɓa tace
"Amma in tambayeki mana Fulani, bayan rasuwan mahaifin Jawwad wato me martaba Sarki Ahmadu
Yusuf shi brother din nasa wanda shi ne sarkin yanxu bai nemi rikon Jawwad a gabansa ba?" Mami tayi
shiru, can tace "Cikin Jawwad na da wata bakwai mahaifinsa me martaba ya rasu aka nada kaninsa wato
mahaifin Junaid, dama su uku ne gun babansu Sarki Yusuf Ibrahim, daga Mahaifin Jawwad wanda shi ne
babba sai Mahaifin Junaid sannan Maimuna warce nake gidanta yanxu suna kiranta da Ummi...." Hajiya
Batula tace "Ikon Allah, to amma...." Shigowar Ummi dakin ne yasa Hajiya Batula tayi saurin canza topic
din tace "Yanxu goben za ki koma Bauchi kenan Hajiya?" Mami tace "In sha Allah" Ummi ta ajiye plate
din hannunta tace "Sannun ku, gashi nan kaza na tsaya gasa maku" Hajiya Batula na murmushi tace "Allah
sarki, sannu da aiki" Ummi tace "Bari in kawo maku drinks din, a can parlor mai aikin ta ajiye" Daga haka
ta fita daga dakin, Mami tace "Da ma kin ci gaba da maganar ki, ita ma ai bata so Junaid din da aka nada
Yarima me jiran gado ba" Hajiya Batula tace "To ke sai kika zuba ido aka yi hakan Fulani? In uban Jawwad
din bai mutu ba a ina kanin nasa zai samu har yayi sarauta? Kuma shine bazai yi kara ya nada ɗan yayansa
da ya mutu ya bar masa sarautan Yarima me jiran gado ba sai ya nada ɗan cikin sa?" Mami tayi wani
murmushi tace "Ni fa ko a jikina hakan da aka yi, Jawwad is doing fine beside shi mulki ma baya gabansa,
as far as my son is okay, i think da a nada sa Yarima da kar a nadasa duk daya..." Hajiya Batula tace "To
halan Junaid din kadai sarkin ya haifa?" Mami tace "Wani Junaid? Amaryarsa da suke kira da Aunty na da
ɗa me shekara 29, ita in son samu ne ma a nada ɗan ta Yariman ai" Hajiya Batula ta rike haɓa tana kallon
Mami. Ajay yayi parking kenan bayan sun dawo gida wajen karfe bakwai na dare ya kalli Jay zai yi
magana wayarsa ya fara ring, ya dauka yana duba me kiransa ganin number wani abokinsu ne da kamar
bazai yi picking ba kawai sai kuma ya daga ya kai kunne, after few seconds of listening to what the frnd
was saying ya zaro ido yace "What???" Kallonsa Jay yayi da sauri don intonation din da yayi using ya nuna
ba lafiya ba, Da kyar Ajay ya cire wayar a kunnensa yana kallon Jay dake kallonsa shi ma babu ko kiftawa,
Nan da nan Jay yaji hankalinsa ya tashi don babu inda mind dinsa yaje immediately sai gun Khaleesat, Ya
fixge wayar hannun Ajay yace "What's happening plss?" Ajay ya kasa cewa komai tsabar yanda ya girgiza,
Jay ya shiga call logs din wayar da sauri yaga Adams abokinsu ne ya kira nan yaji hankalinsa ya ɗan
kwanta don yasan ba abu bane da ya shafi Khaleesat, dialing number yayi amma har ya gama ring ba a
daga ba, a hankali Ajay yace "Salim aka harba" Jay bai san sanda ya ajiye wayar hannunsa ba yace "What?
Harbi kuma? Is he dead?" Ajay ya dau wayarsa shi ma ya kara dialing number Adams amma har ya katse
bai daga ba, available flight to kano ya fara dubawa immediately.....
[6/3, 9:01 PM] khaleesat Haiydar ✍️: Washegari sai da rana Ajay da Jay suka samu ganin Salem a hospital
din da aka yi admitting dinsa, iya kafadarsa ne kadai aka nannada ma bandage alamar a nan aka harbesa
amma duk kamanninsa ya canza alamar ya ci duka ba na wasa ba, Jay ya zauna kujeran dake kusa da gadon
yana kallon Salem that was in pain yace "Hasbunallah, How did this happen Salem?" Shi dai Ajay na tsaye
ya rungume hannu shi ma yana kallon Salem ganin yanda aka canza masa kama, ya ma kasa cewa komai,
Salem dake kishingide jikin pillow da kyar don ko iya motsa kafadarsa daya baya yi ga duk jikinsa yayi
tsami yayi karfin halin cewa "Ban san su ba suka yi attacking dina" Jay yace "Har gida suka same ka?"
Salem ya girgiza kai yace "I stayed out late yesterday in wudil naje gurin wani abokina, he insisted i stay
till the next day amma saboda ina da abun da zanyi washegari da safe a kano sai naki kwana a garin muka
yi sallama da shi, bayan na kusa unguwan da nake da zama sai na lura da wata mota na biye dani a baya
amma ban yi tunanin komai ba na zata ya shigo layin ne bai san hanya ba shine yake bi na ko nima fita
zanyi daga unguwan mun fita tare, bayan na shigo layin mu babu kowa saboda dare yayi tun kan ma in
sauko daga motata in shiga gida in bude gate sai nake ma motar alama da hannu ya tafi gaba zai samu
hanya, sai kawai matukin motar ya fito ya nufo ni, duk da haka ban wani damu ba na zata direction zai
tambayeni, na tsaya har ya iso dai dai gabana ban ankara ba kawai sai jin saukan naushi nayi ta ko ina a
fuskata ina kokarin defending kai na sai sauran mutane ukun dake cikin motar suka fito su ma suka hau
dukana ta ko ina at the same time they were asking me about a girl i know nothing about, wai inyi
providing dinta ko su kashe ni" Da wani expression Jay ke kallonsa, sai kuma ya mike da sauri ya dafa
gadon da Salem yake kai yace "A girl?" Salem ya gyada kai da kyar yace "Wai Khaleesat, ni ban ma taba
jin sunan ba wallahi, suka yi ta dukana wai sai na fadi inda take ko su harbeni" A tare Ajay da Jay suka kalli
juna, Salem yace "Kashe ni suka yi niyyar yi banda Allah ya rufa min asiri kururuwan da nake yi wani soja
dake kusa da gidanmu ya fito da bindiga, da wani makocina da ya fito da adda, kafin makota na su fito ne
suka min harbi har biyu daya ya sameni a kafada daya kuma bai sameni ba ya sami gate, sojan da makoci
na suna fitowa suka shige motarsu suka tsere, ni wallahi ban taba jin sunan yarinyar da suka ambata ba ma"
Aunties din Salem biyu ne suka shigo ward din da sallama, Ajay ya gaida su sannan ya fita daga ward din
ya tafi haraban asibitin ya zauna, after almost 10 mins Jay ma ya fito, inda Ajay ke zaune ya nufa ya zauna
bai dai ce masa komai ba, Ajay yayi breaking silence din yace "He is tracking me, ni yake nema ba Salem
ba, but tana da number Salem a wayarta ne?" Jay ya sauke wani ajiyar zuciya yace "Yawanci shi take kira
ya bani waya if there is anything she wants to tell me, ko number ka ma ai Salem ne ya tura mata, instead
cewa zaka yi he is tracking the both of us

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login