Showing 120001 words to 123000 words out of 152206 words

Chapter 41 - HALYSAAH by Khlst Hydrr

13 May 2026

60

Malam?" Mama Zubaida tace "Ko tafiya kauyen ne ya taso?" Shi
dai bai tanka su ba ya dinga goge takalminsa da yayi ƙura, Umma ce karshen fitowa ita ma ta tsaya tana
kallonsa ta kasa cewa komai don tasan manufarsa, ko baccin kirki bata yi ba daren jiya tsabar yanda
hankalinta ya tashi, Nenne ce ta shigo gidan yafe da zaninta tana ganin Malam Ali tace "Yauwa ko sallah
kar ka jira kayi idan kaje tashar kayi a can Ali, ga er soyayyiyar nama da gurasa na kullo maka ka ci a
hanya" Mama Shatu tace "Tafiya zai yi ne Nenne?" Nenne tace "Babu ruwan ku, ku dai ku yi masa fatan
Allah ya kiyaye hanya" Malam Ali ya amshi kullin nama da gurasan da Nenne ke mika masa, yana kallon
matan nasa yace "Toh sai Allah yayi min dawowa" Mama Shatu tace "To ai shikenan, Allah Ubangiji ya
tsare Malam" Mama Zubaida ma tace "Allah ya tsare duk da muna da hakkin ka sanar mana inda zaka je da
asuban fari Malam" Nenne tace "Bazai sanar ba Zubaida, uban me sanin inda za shi zai kara maki?" Mama
Zubaida ta juya ta koma daki, Mama Shatu ma ta tabe baki ta koma dakinta, Nenne ta kalli Umma tace
"Wato ke ce isasshiyar da bazata yi masa Allah ya kiyaye ba ko Zahra'u" Shi dai Malam Ali tuni har ya fice
daga gidan, Nenne na nuna Umma tace "Mugun abun ku zai kare maku da ke da er ki wallahi, babu wanda
ya isa ya salwantar min da ɗa na lokacinsa bai yi ba" Daga haka ta bi bayan Malam Ali da sauri zata rakasa
bakin titi ya samu adaidaita sahun da zai kai sa tasha. That same day bayan an idar da sallahn asuba Jay ya
shigo parlorn Mai martaba da sleepy face ta dalilin kiran da yayi masa, ganin irin zaman da Abba yayi
kamar yana fadarsa ya gane serious issue Abban zai yi discussing da su kenan, ya kalli Ajay dake parlon
zaune shi ma alamar kiran sa Abban yayi, Aunty ma na zaune parlon, Jay ya sauke kansa ya karasa kusa da
Ajay ya zauna kasan lallausan carpet din parlon, dabi'ar Abba ne sai ya iya minti biyar zuwa goma kamar
me nazari kafin ya fara magana in ya tara ku, Jay ya sunkuyar da kansa ya lumshe ido, Ajay ya ɗan kallesa
sanin sai ya iya bacci a haka, ai ko yaga baccin yake, Ajay ya ɗan tunkudesa da elbow dinsa, Jay ya bude
ido da sauri yana gyara zama, shi dai Abba kallonsu kawai yake, At last Abba yayi gyaran murya cikin
nutsuwa yace "First of.... Ina son sanin zaman me ku ke har yanxu a garin nan baku karasa gida ba?" Duk
suka yi shiru babu wanda yace komai kansu a kasa, Calmy Abba yace "Ohk take ur time, amma kuyi kokari
ku je gida kafin hutun ku ya kare, Secondly.... maganar da nayi da ku a Maryland naji babu wanda yace min
komai a kai har yanxu, ga lokacin da na baku ya cika, nayi maku uxurin mantuwa shi yasa nake tunatar da
ku yanxu..." Nan ma duk suka yi shiru babu wanda yace komai, shi ma Abban yayi shiru yana kallonsu
yana jiran amsa a duk sanda suka shirya, sun san shirun da Mai martaba yayi amsarsu yake kira ko da zai
dau 10min ko fin haka ma kafin su basa amsan he won't mind zai jira su patiently, sanin halin Abban nasa
yasa Ajay ya daga kai, Softly yace "Ayi hakuri ranka shi dade ba mantawa muka yi ba, in sha Allah we are
working on that very soon" Mai martaba yace "Is that so?" Ajay ya sauke kansa don kalman Abba na nufin
bai gamsu da abinda yace ba kenan, Shi dai Jay yaki dago kai, a hankali Ajay yace "A gafarce mu a ɗan
kara mana lokaci Abba..." Aunty da har ta fahimci maganar da ake ta ɗan yi gyaran murya ta nemi
permission din magana gun Mai martaba, ya gyada mata kai alamar ta fadi abinda zata fada, cikin nutsuwa
tace "In na fahimci maganar da ake ranka shi dade, magana ce akan su fito da matan aure duba da yanda
shekarunsu ke gaba ba baya ba, wannan magana kuma ba sabuwar magana bace don an fi shekara 3 ana yin
ta amma babu wani progress, a takaice basa daukar maganar da muhimmanci, to amma dai ina ga ka ɗan
sha'afa ne ur Highness, don shi Jawwad ai akwai maganar sa da Hadeeyah a kasa duk da ba wai maganar
tayi karfi bane kuma wannan hadi, hadi ne me kyau da zai kara karfafa zumunci don mahaifiyar Hadeeyah
jininka ce kuma ita ta kawo wannan shawara duk da Fulani wato mahaifiyar Jawwad uwar dakinta ce tun
asali, shi kuma Junaid a yanda na lura da shi zai fi maraba da zabin ka garesa duba da nature dinsa da
rashin choice dinsa, don haka shi Jawwad a tsaida maganar sa da Hadeeyah kawai ina ga hakan zai fi, shi
kuma Yarima i think we should get him a princess from neighbouring states, ko ni zan iya jagorantar hakan
don arranged marriage zai fi suiting dinsa duba da nature dinsa, kuma ina son a bar komai a hannuna ranka
shi dade..." Ajay ya daga kai ya kalleta zai yi magana mai martaba ya dakatar da shi, Ajay ya sauke kansa,
Speaking Calmly Mai martaba dake kallon Ajay da Jay yace "Za ku iya tafiya, Allah yayi maku albarka"
Sai a sannan Jawwad ya dago kai ya kalli Aunty dake ɗan murmushi ganin Mai martaba yayi na'am da
shawaranta, tuni Ajay har yayi disappearing daga parlorn fuska a murtuke, Jay ya mike shi ma ya bi bayan
Ajay yana tafiya a hankali, bai taɓa sanin baya son Hadeeyah da aure ba sai yau da Aunty ke bada shawaran
a tsaida ranan aurensu da ita, yasan kuma duk abinda Aunty tace kamar Abba ya aikata hakan ya gama ne,
kawai yaji hankalinsa yayi mugun tashi yaji wani zufa na keto masa, dakinsa ya shige ya kulle da makulli
ya jingina da kofar ya lumshe ido zuciyarsa na bugawa, Ajay na shiga dakinsa shi ma ya kulle da makulli
ya zauna gefen gado ya dafe kansa da hannu biyu, this is not the first time da Aunty ke kasalanda akan duk
abinda ya shafesa gashi Abbansa baya basa listening ears ko me Aunty tace masa kawai haka za ayi abun
nan komin munin abun, at this point he felt he is of no importance to his father, he felt dejected, and it's
been like this for so many years, he have no one to stand for him, a hankali ya juya yana kallon wayarsa
dake vibrate, Number Aunty Farida ya gani a gaban screen din wayar, ya kalli agogo yaga karfe shidda da
minti biyar na safe, request din Khaleesat na jiya da ta kirasa ya tuna, hakan yasa har kiran ya katse bai
daga ba knowing she might be the one calling, kiran ya sake shigowa ya kalli screen din nan ma bai daga
ba har ya katse, sau hudu kiran na shigowa continuously, hakan yasa ya maida attention dinsa kan wayar ya
ɗan yi jim with different thought running his mind, ganin kiran ya katse an sake kira making it the 5th time
of calling yasa ya dau wayar ya daga ya kai kunne yayi shiru waiting to hear who is on the line, a hankali
ya mike jin abinda Aunty Farida ke ce masa ta wayar, bai san sanda ya zame wayar daga kunnensa ba rate
din heartbeat dinsa na karuwa, da sauri ya nufi kofarsa ya bude ya fice daga dakin ya murda kofar dakin Jay
yaji a kulle, knocking ya dinga yi non stop kafin Jay ya bude kofar da mamaki yana kallonsa yace "What is
it?" Ajay ya shiga dakin yana shafa gashin kansa da wani expression yace "He tracked her to Lagos" Still
Jay yayi a inda yake tsaye ko kwakkwaran motsi baya yi yana kallon Ajay, Ajay ya ja numfashi sannan ya
zauna kan kujeran dakin ya lumshe idanuwansa ya jinginar da kansa jikin kujeran trying to calm himself,
Jay was speechless and shock at the same time, da kyar ya ja kafa ya zauna gefen gadonsa ya dafe kansa da
yaji yayi masa nauyi, kamar an tsikare Ajay ya mike yace "Book us ticket to Lagos" Daga haka ya fice daga
dakin.
[6/12, 8:02 PM] khaleesat Haiydar ✍️: Aunty Farida ta share hawayen da yaki tsaya mata tana kallonsu
Ajay da kyar tace "Wallahi ban san ko har su nawa bane a motar, ban ma san ya motar take ba tunda ina
cikin gida sanda abun ya faru, yaran makota dake diban ruwa a bakin rijiyar tare da ita ne suke cewa kawai
suna diban ruwa sai ga motar ta shigo street din, wasu mutane suka sauka a motar suka ja ta zuwa cikin
motar suka tafi da ita, a sannan an idar da sallahn subahi kenan kun ga gari bai waye ba ai" Ajay was
speechless, bai taɓa zama confuse haka a rayuwar sa ba don ya ma rasa abun cewa, likewise Jay dake
jingine jikin mota tun da suka iso unguwan dama shi bai ce komai ba, Ajay ya daga kai after some seconds
ya kalli Aunty Farida a hankali yace "Amma yana da number ki ne Aunty?" Aunty Farida tace "Ba shi da
wannan number tawa gaskiya sai tsohon layi na, kwanaki Maman Khaleesat tayi rashin lafiya sai na tafi
kano dubata to a hanya na yar da wayata, da na zo kano sai na siya sabon layi kafin inyi welcome back din
tsohon layin, to har yanxu ban yi welcome back din ba" Ajay yayi shiru yana nazari, Aunty Farida na
hawaye tace "Tsautsayi yasa ta fita deban ruwan yau, amma tunda ta xo wallahi ni ke diban ruwana bana
barin ta dibar min tunda har yanxu gata nan ne dai bata dawo dai dai ba, wani lkcn ma da daddare idan na
dawo kasuwa nake yi tunda ana wahalar ruwa a season din nan don yawanci rijiyoyi kafewa suke yi sai ana
bari ruwan na taruwa sannan a diba, gashi ba a samun wuta balle a samu ruwan pampo, a jiyan nayi girki
me yawa ne na wani biki duk sai na gaji ban deba ruwan da daddare ba, da na tashi kuma sai nake jin
zazzabi, kun ji dalilin fitarta ta debo mana ruwa kenan" Ajay ya jingina da motarsa ya lumshe ido ya bude,
gaba daya ƙansa ya gama kullewa, bai yi zaton Abdul ya wuce yanda yayi zatonsa ba, the guy is really
something else ko wani salon tactics na mugunta ya san sa gashi har yau yaki kunna wayarsa balle a san
inda yake, ko by mistake baya kunna layin, shi dai Jay dama bai taɓa underrating Abdul ba dai dai da rana
daya duba da irin actions din da ya dinga portraying, kawai dai tracing din Halysaah har zuwa Lagos is the
least thing da yayi zaton Abdul zai yi, tunda bashi da access da Aunt dinta, but like seriously how did he
even find his way, bayan bashi da active line din Aunty Farida sannan bai san unguwan da take ba, ya sauke
wani boyayyen ajiyar zuciya yana tunanin ta inda za su fara billo ma wannan lamari, tunda dai babu ta
yanda za su ce yayi kidnapping Halysaah da ke a matsayin matarsa ta sunna. Khaleesat na zaune at the far
end of the large room ta hade kanta da gwiwa, zuwa sannan ta hakura da kukan da take don ba ma ta da
strength din kukan amma tana jin zuciyarta na mata zafi ga wani azababben ciwon kan da take ji da kishin
ruwa da ya dameta, tafi awa sha biyu zaune a dakin ba ci ba sha, don tunda aka shigo da ita har zuwa
sannan babu wanda ya sake zuwa dakin, infact bata ji motsin kowa a gidan ba alamar ita kadai ce a ciki,
bandakin dake cikin dakin take shiga tayi alwala ta fito tayi sallah duk da ba sanin lokaci tayi ba kawai tana
amfani da instinct dinta ne, at this point in time tasan bata da wani sauran gata sai wajen Allah, domin kuwa
tasan Abdallah ne kawai zai sa a zo ayi mata irin wannan daukan, wasu hawaye masu zafi suka zubo idonta
tana tausayin rayuwarta, all she could remember vividly was that tana bakin rijiyan dake kusa da gidansu
Aunty Farida tana diban ruwa wasu mutane biyu suka zo a mota, lokaci daya kuma suka yi leading dinta
zuwa motar tasu, at first turje masu tayi ta fara kokarin raising alarm tana ihu, yaran dake bakin rijiyan duk
suka gudu suka shige gidajensu, tana kururuwa daya mutumin ya rufe fuskarta da wani Handkerchief da
sauri, taji ta shaƙi wani abu kamar dust, lkci daya kuma ya cire handkerchief din a fuskarta, daga nan kuma
ko kokarin ihun bata sake yi ba cause she became weak, ita dai tasan all through the ride she was conscious
but not fully, gashi ta kasa tabuka komai don duk jikinta ya mutu, kanta yayi mata nauyi idonta suka dinga
juya mata.... Da sauri Khaleesat ta dago kanta ta mike tsaye jin ana ƙoƙarin bude kofar dakin ta waje da
makulli, gabanta ya dinga bugawa da karfi idonta na kan kofar har ya bude ya shigo, she wasn't expecting
anyone but him dama, ta sauke kanta bayan sun hada ido, wasu sabbin hawayen suka fara zuba idonta,
muryarsa taji ya daki kunnenta cike da isa da gadara yace "Har yanxu Body guards din naki basu biyo
bayanki bane? Ai yaci ace sun iso zuwa yanxu don naga It's almost 12 hours now, how comes basu zo
cecen ki ba duk capacity din su" Sai a sannan Khaleesat ta daga kai ta kallesa cikin rawar murya tace "Ka ji
tsoron Allah...." Kasa ci gaba tayi ta fashe da matsanancin kukan takaici, shi dai yana tsaye yana kallonta
da wani murmushin mugunta kwance fuskarsa, ta dago kai da sauri jin yana takowa har zuwa inda take
tsaye, mannewa tayi da bango tana jin kamar bangon ya tsage kawai ta shige gabanta na bugawa da karfi,
sai da ya zo dab da ita cikin kwantar da murya yace "Me kika ce?" Ta girgiza masa kai da kyar gabanta na
ci gaba da faduwa muryarta na rawa tace "Kaji tsoron Allah Ya Abdul, kaji tsoron...." Bata rufe baki ba taji
saukan lafiyayyen mari a fuskarta wanda sai da taga taurari, ta dafe kuncinta tana kallonsa babu ko kiftawa,
cikin husky voice dinsa yace "You still have the guts to repeat what u just said saboda baki da kunya ko? Ni
zaki gaya ma in ji tsoron Allah? To tsoronki zan ji ko tsoron uban ki dake Mariri idan ban ji tsoron Allah
ba?" Da kyar Khaleesat ta dake tace "Ka zageni amma kar ka sake zagar min uba" Still bata rufe baki ba ya
sake sauke mata wani wawan marin a other side of her face, this time around sai da dakin ya juya mata don
ba marin wasa yayi mata ba, ya fixgota yana mata wani irin kallon da ya gigitata don tuni idonsa yayi jajur
yana huci yace "Ina magana kina mayar min how dare you poor wretched girl?" Ta fashe da matsanancin
kuka tana jin dama Allah ya dau ranta kawai ta huta a wannan lokacin, zata durkusa kasa ya hadeta da
bango yace "Yau ina body Guards din naki dake goya maki baya kina min iskanci? Tell me where they are
today? Da aurena a kanki kike hulda da wasu banzayen gardawa saboda ke jahila ce warce bata san me take
ba" Tana kuka sosai bata san sanda tace "To wai ana aure dole ne dama Abdul? Nace bana son auren, bana
son ka, gwara kawai ka kasheni duk mu huta" Da karfi ya bugata da bango har sai da taji numfashinta ya
dauke na few seconds, yana mata wani mugun kallo yana huci yace "Dama ke baki san aurena wajibi ne a
gare ki ba ko kina so ko ba kya so? Dama shi ubanki bai gaya maki hakan ba ko mantawa kika yi saboda
kin fara bin maza? Wallahil Azeem kin ji rantsuwar musulmi ko? Duk ranan da kika sake yunkurin guduwa
ko kuma yin wani silly act to rayukan twin siblings din ki za su zama fansar aurena idan kika kuskura kika
min jakanci, ko kina so ko baki so lallai dole ki zauna da ni ko kuma in salwantar da ran kanninki i am
promising you this Billahil Azeem, kuma babu abinda zai faru don tamkar na kashe banza ne daga ke har
iyayenki babu abinda za ku yi, su kansu Body guards din naki ba kyalesu nayi ba don sai na dau revenge
din intruding da suka yi a sabgata, i will teach them a lesson kina ji kuma kina gani" Khaleesat ta kasa cewa
komai don sama sama kawai take jin numfashinta kalmansa na cewa zai salwantar mata da siblings dinta ya
sa jikinta ya fara rawa, ya juya cike da isa ya tafi ya bude closet din dakin wanda duk kananun shegun kaya
ne yace "All this are your wears, in kin yi sallah kin shirya ki zo ki sameni a dakina which is 3 rooms away
from this, ina jiranki at exactly 7pm and this is just 6:30pm" Yana kai wa nan ya fice daga dakin yana rike
da key din dakin, a hankali Khaleesat ta sulale kasa tana sauke numfashi tana jin wani abu ya tsaya mata
cak a zuciya, gashi ba ta ma da strength din da zata yi kuka sosai ko zata ji relieve don tun jiya rabonta da
abinci, she was just weak and helpless, ga idonta da taji ya fara ciwo saboda marin da yayi mata don dama
ba warkewa idon yayi gaba daya ba lkci lkci tana jin yana damunta, tsoro da fargaban kada ya sake dawowa
dakin yayi mata fiye da abinda yayi mata yasa Khaleesat tayi karfin halin mikewa da ɗan sauran strength
din ta da ya rage tana tafiya da kyar ta shiga bandakin dake cikin dakin ta tara ruwan pampo tana sha ko
zata ji saukin abinda take ji a zuciyarta, bayan ta sha ruwan ta dinga kallon fuskarta da yayi ja ta madubi, a
hankali ta zame kasan bandakin ta jingina da tile din bangon hawaye masu zafi na zarya a fuskarta, tafi
minti goma a haka lokaci daya ta yunkura ta mike bayan ta tuna time din da ya bata kar ya sake dawowa,
she wish akwai makulli a jikin kofar bandakin don da kulle bathroom din kawai zata yi in ma mutuwa ne
tayi a haka don yafi mata kasancewa da Abdul, cikin rashin kuzari ta cire hijab dinta da kayan baccin dake
jikinta ta fara wanka da shower gel din dake bandakin,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login