Showing 39001 words to 42000 words out of 152206 words

Chapter 14 - HALYSAAH by Khlst Hydrr

13 May 2026

81

surutu, pls get out Ajay, gerrout
pls" Khaleesat dake sauraron conversation dinsu ta wani taɓe baki ta juya ta koma parlor ta zauna wani
mugun haushin mutumin da taji ana kira da Ajay take ji a ranta, taga Abdul ma balle shi, Salem ya mika ma
Jay hannu zae taimaka masa ya tashi, Jay yace "Pls kace mata ta kawo min bottle water, or you check the
kitchen ka dauko min" Salem ya juya ya fita, Ajay dake taɓe baki ya juya ya fice daga dakin shi ma, direct
ya nufi kofar fita daga apartment din yayi ficewarsa ya koma can waje ya tsaya jikin motarsa, Salem dai ya
bi sa da kallo ya sauke ajiyar zuciya ganin fita yayi, sannan ya kalli Khaleesat ya gaya mata ta dauko ma
Jay ruwa, ta mike ta tafi kitchen ta dauko ruwan ta basa, ba a dau lokaci ba sai ga shi sun fito tare da Jay,
mikewa tsaye tayi tana kallonsa, Jay ya zame hannunsa a na Salem ya zauna saman kujera ya jinginar da
kansa da kujeran ya lumshe ido, a hankali Khaleesat tace "Amma hospital zaku je ko?" Da kyar yace "No,
gida za mu je ya min treatment" Khaleesat tace "To Allah ya sauwake, Allah ya baka lafiya" Ya gyada mata
kai sannan ya mika ma Salem hannu ya mike tsaye, Khaleesat na son tambayarsa abu amma ta kasa, ganin
za su fita daga parlon ta dake tace "Can i get ur digit so i can be checking up on you?" Salem dai ya juya ya
kalleta da ɗan mamaki jin tambayar da tayi, does this mean basu san juna ba kenan tunda har bata da
lambarsa, Housemate din nata ya juya ya kalleta yace "Ai zaki gane gidan da muka je ranan da na mance
makulli da daddare bayan kin dawo Nigeria, that's our home, zaki iya zuwa at anytime...." Khaleesat dai ta
dinga kallonsa, sai kuma yace "Salem give her my digit, ko kuma ka bata nata kar ta kira bata sameni ba"
Salem yace "Ohk bari in bata nawa" Khaleesat ta dauko wayarta sannan ta amshi number Salem, bayan ya
gama bata suka fita daga parlon tare da housemate din nata, tana tafiya a sanyaye ta karasa gun window ta
bude labule tana kallonsu, sae da suka fito Ajay ya shiga motarsa, bayan sun shiga yayi zoom off. Khaleesat
ta sauke idonta sannan ta juya a hankali ta koma cikin parlon. Bayan kwana uku Khaleesat sun fito daga aji
tare da Safiyyah dake waya, ita dai Khaleesat na tafiya ne amma gaba daya hankalinta na wani gun daban,
Safiyyah tace "Wai ya jikin Housemate din naki yanzu? Ko ya dawo ne baki gaya min ba?" Khaleesat ta
kalleta tace "Har yanzu ai bamu yi magana da shi ba" Safiyyah tace "To wanda ya baki number sa fa ko har
yanzu bai daga kiran naki ba?" Khaleesat tace "Aa ya daga jiya, amma sai yace min he is much better, da na
tambayesa ko yana kusa sae yace min a'a yana bacci, kawai ni dai i hope da gasken jikin nasa da sauki..."
Safiyyah tace "Shegen mutumi in ba kinibibi ba me yasa zai wani ƙi baki lambar Housemate din naki sai na
shi, me za kiyi da lambarsa when u have no business with him, in ni ce ke cewa zanyi a'a ba nasa zai ban ba
gaskiya, amma fa har yanzu abun na ban mamaki ace duk mutuncin Housemate din nan naki bai taɓa
requesting phone number din ki ba ko sau daya, ji ma sanda kika je Nigeria, to ko me yasa oho" Ita dai
Khaleesat kallonta kawai take bata ce komai ba, Safiyyah tace "To wai ma ba kince har cewa yayi ki je
gidan nasu ba, tun jiya nake ce maki mu shirya mu je kin ki, in baki je kin dubasa ba ta yaya zai san kema
kin damu da halin da yake ciki, ai ance gaida me gaisheka, beside da bakinsa ya maki kwatancen gidan
nasu ai, to me yasa baza ki je ba, da Nigeria muke sai mu ce ai bai kamata ba saboda yan sa ido da yan
fassara lamari but this is USA Khaleesat, kuma abu ai kamawa yake for 3 days baki san halin da mutumin
nan yake ciki ba gashi ke kanki kina testifying kyawawan halayyarsa, wallahi ki shirya in rakaki mu je ki
dubasa da jiki, kuma kafin nan mu fara biyawa ta shopping mall kiyi masa shopping da zaki kai masa, shi
ma sae yaji dadi wallahi" Khaleesat tace "Kawai sai in kama tafiya har gidan nasu duba shi? Ai bai ma dace
ba sai kace wasu marasa kamun kai Safiyyah, be it in USA still bai dace ba, mu mata ne fa" Safiyyah ta
mata wani kallo, can tace "Ai da naki matsalar ya taso haka ya cire kudadensa sama da miliyan goma sha
biyar ko fin haka if i am not mistaken yayi solving maki matsalar ki, shi kuma bai da lafiya rai kwakwai
mutu kwakwai kince zuwa dubasa rashin kamun kai ne, to rashin dacewa ya wuce zaman da ku ke yi gida
daya? Shi wannan me za ki ce masa? Wani lokacin baki ma nazarin maganar dake fitowa bakin ki
Khaleesat, in zuwa dubasa bai dace ba to zamanku gida daya ma ai bai dace ba be it in USA" Khaleesat dai
sai kallonta take ta kasa cewa komai, can dai tace "Ban gane ba, Miliyan goma sha biyar for what??"
Safiyyah ta mata wani kallo tace "Ohh for what ko? da yake business class ticket din da ya siya maki an
gaya maki na wasan yara ne ai, to bari ki ji Business class ticket kusan 5000 dollars ne base on Airline, ki
lissafa 5000 ko 4000 dollars kudin Nigeria kiga nawa zai baki" Khaleesat was speechless after realizing
Safiyyah is saying the truth, banda dala dubu dayan da ya bata da zata tafi, sannan ga kuma domestic flight
ticket from lagos to kano, and from kano to Abuja, bata mance irin hotel din da ta zauna na few hours a
garin Lagos ba, sauke idonta kasa tayi bata sake cewa komai ba, Safiyyah ta ja tsaki tace "Wallahi ki ajiye
wnn kauyancin naki ki zama wayayyiya ki dinga yin abun da ya dace, komai a rayuwar nan kamawa yake
Khaleesat, to wai ku ka zauna apartment daya ba ace rashin kamun kai ba sai don zaki je dubasa bai da
lafiya? ni abinda ke daure min kai kenan" Khaleesat dai taki cewa komai with many thoughts running her
mind, a haka dai suka rabu kowa ya tafi gida... The next day sai da Safiyyah tasan duk yanda tayi
convincing din Khaleesat da dadin baki da masifa da bacin rai, daga karshe Khaleesat ta yarda su je can
inda Housemate dinta yace gidansu ne su dubosa amma fa don babu yanda ta iya da Safiyyah ne don har
cikin ranta tsoron zuwa anguwan take don unguwa ce na masu kudi a kasar, to in ma sun je su ce me ya kai
su? What if iyayensa ko wasu yan uwansa mata na gidan sai su yi yaya kenan? Kasa hakura tayi har sai da
tayi ma Safiyyah wannan tambayar, Safiyyah tace "Dai dai kenan in ma iyayensa na gidan, ai ba Nigeria
bane nan USA ne, kuma tsaf za su amshe mu hannu bibbiyu su yi farin ciki da zuwan mu don duba ɗan su
muka je yi bai da lafiya" Khaleesat ta sauke wani boyayyen ajiyar zuciya, Safiyya tace "Amma ni har raina
ina son sanin dalilinsa na dawowa apartment dinki ya zauna bayan ga nasu gidan can, nace da wani abu a
kasa kince min ba haka ba, wallahi kilan ya san ki from somewhere Khaleesat" Khaleesat tace "Sai kuma
kiyi ai, nace maki bamu taɓa sanin juna da shi ba" Safiyyah tace "Ma ji ma gani dai" Sai da Safiyyah ta fara
jan Khaleesat zuwa inda za su siya kayan ciye ciye sannan suka yi ordering Uber da zai kai su unguwan,
tun da suka shigo Safiyyah ke kallon manyan Gidaje with fascination, Khaleesat kuwa gabanta sai faduwa
yake sai addu'a take a ranta, ita banda Safiyyah tayi insisting da babu abinda zai kawota wai duba
Housemate dinta, dai dai kusa da gidan Uber din ya tsaya duk suka sauka, Safiyyah dake zaro ido tana kare
ma Glass house din kallo tace "Ke kin tabbata nan ne kar mu shiga gidan mutane a kira mana 911 mu shiga
uku Khaleesat" Khaleesat bata san sanda tayi dariya ba amma bata tanka ma Safiyyah ba, Khaleesat ta ciro
wayarta tayi dialing number Salem ita kanta zuciyarta bugawa yake gaba daya she is afraid, sai da kiran ya
kusa yankewa ya daga, sai gashi a mota zai fito daga cikin gidan, sauka yayi daga motar ganinsu, yana
kallon Khaleesat da mamaki yace "Ohh you are here, sannu da zuwa...." Gaishesa tayi ta sauke idonta kasa
kamar munafuka, ya amsa da fara'a, Safiyyah ma ta gaishesa sannan tace "Dama ta zo duba jikin
Housemate dinta ne shi ne na rakota" Yana gyada kai yace "Ohh that's so thoughtful of her, mu je ciki to...."
Suna biye da shi suka shiga cikin katon gidan, Safiyyah dai sai gwale ido take tana bin gidan da kallo ta
gefen ido, ita dai Khaleesat gabanta sai faduwa yake sosai ko daga kai ta kasa, after walking briefly sai
gasu sun iso entrance din shiga parlon gidan, kofar shiga parlon ma kadai sai ka kalla ka sake kalla,
Safiyyah ta saci kallon motoci uku dake compound din kuma masu tsada, suna shiga parlon gidan
Khaleesat ta hada ido da Ajay dake zaune kan kujera ga different fruits daga gefensa yana kallon abu a
wayarsa at the same time yana cin apple dake hannunsa, 3 quarter ne baƙi a jikinsa with gray polo, tuni ta
dauke idonta tsabar yanda ta rikice bata ma san sanda ta bude baki ta gaishesa ba tana makale bakin kofa,
hade rai yayi ya dauke kai ya ci gaba da kallon abinda yake a wayarsa.



✍🏻
07087865788
[5/11, 5:06 PM] khaleesat Haiydar ✍️: ✨✨HALYSAAH✨✨




✍🏻
By _Khaleesat Haiydar_




14....

Safiyyah ma dake kallonsa kamar munafuka tana in-ina tace "Good... good evening sir" Without looking at
Safiyyah ya amsa yana cin apple dinsa, Salem na kallonsa speaking calmly yace "Ajay sun zo duba jikin
Jay ne" Ajay ya ajiye apple din hannunsa, sai kuma ya kai wayarsa kunne alamar bashi da lkcn basa amsa,
ganin haka Salem ya juya ya kalli su Khaleesat yace "Bari in masa magana a sama, za ku iya zama ku jira
ni, have a sit pls" Daga haka ya nufi stairs, ko haurawa saman bai yi ba Khaleesat ta zaro ido tace
"Innalillahi" da sauri ta koma bayan Safiyyah ganin wani jibgegen kare ya nufo su yana haushi, Safiyyah ta
dinga buga ma karen jakar hannunta tana koransa ita ma a tsorace, Salem ya dawo parlon da sauri ganin
haushin da karen ke yi zai yi attacking dinsu, Ajay ya mike ya nufi karen yana kiransa yace "C'mon
Legend" Karen ya juyo da gudu ya dawo gun Ajay da yayi patting din kansa, Salem ya dawo kusa da su
yana murmushi yace "Mu je saman kawai tunda tsoron kare ku ke, ai ba abinda zai maku kawai yaga baƙin
fuskoki ne shi yasa" Khaleesat da jikinta ke rawa ta bi bayan Salem da sauri Safiyyah na biye da ita, a haka
Salem yayi leading dinsu har sama zuwa Bedroom din Jay, knocking yayi yana tsaye bakin kofar, Khaleesat
sai waige waige take tana ganin kamar karen zai sake biyo su saman, sai da Jay ya amsa ma Salem
knocking din da yayi sannan ya kallesu yace "Bari in sanar masa yana da baƙi" Daga haka ya bude kofar
dakin ya shiga ciki ya kullo, Safiyyah ta rike haɓa ta kalli Khaleesat murya can kasa tace "Ke wani tantirin
ɗan iska ne wannan muka gaida a kasa ya mana walakanci haka?" Khaleesat bata tanka ta ba, har sannan
kuma bata daina waige waigen da take ba don gani take fa karen nan zai iya biyo su har sama, sai ga Salem
ya fito daga dakin yana kallonsu yace "Za ku iya shiga, ni zan ɗan fita sai na dawo" a hankali Khaleesat
tace "Ohk mun gode" Bude kofar dakin tayi still gabanta na faduwa ta shiga cikin massive room din da
sallama Safiyyah dake gwale ido na biye da ita a baya, wani ɗaddadan kamshi hade da sanyin Ac ne yayi
welcoming dinsu a cikin babban dakin, Housemate din nata na zaune saman makeken gadonsa alamar
Salem just woke him up, his room was just something else wajen tsaruwa da haduwa, Khaleesat taki yarda
ta hada ido da shi zuciyarta na bugawa ta zauna nan ƙasan lallausan carpet din dakin, a hankali yace
"C'mon Halysaah, ga gefen gado ku zauna, ko ku zauna kan kujera" Khaleesat bata dago kanta ba tace "I
am comfortable here" Ya lura kamar she is frightened, ya kalli Safiyyah dake kallonsa bayan ita ma ta
zauna, dan murmushi yayi mata yace "Hello...." Kana jin muryarsa kasan he is still recovering, Safiyyah ta
gaishesa da fara'a tana tambayarsa jikinsa, yace "Alhamdulillah, ya karatu?" Tace "Alhamdulillah" Ya kalli
Khaleesat yace "Ya kwana biyu Housemate? Hope you are doing good?" Sai a sannan ta daga kai ta kallesa
tace "Ya jiki?" Yana murmushi yace "Da sauki, Alhamdulillah" A hankali tace "To Allah Ubangiji ya
sauwake ya kara lafiya" Yace "Ameen ya Allah" Safiyyah ta ajiye ledan hannunta kusa da gadon dakin tace
"She got you this" Khaleesat ta kalleta, godiya yayi masu gaba daya, sai kuma ya fara kokarin sauka daga
saman gadon yace "Bari in kawo maku ruwa" Edge din gadon ya zauna kamar bazai iya tashi ba, Khaleesat
tace "Aa mun gode, we are okay" Ya kalleta a hankali yace "To ai ba ke kadai nayi offering ba Housemate"
After some seconds ya tashi ya bude portable Fridge din dake dakin ya dauko masu ruwa da tsadaddun
lemuka duk ya ajiye masu sannan ya fita daga dakin walking slowly, exactly irin kayan jikin Ajay ne a
jikinsa shi ma, Safiyyah ta rike haba tana kallon Khaleesat bayan ya fita, sai kuma tayi kasa da murya tace
"Khaleesat kin dai ga arziki ko? Gidansu kenan fa a Amurka ina ga Nigeria kuma?" Khaleesat ta hade rai
tace "Pls stop this Safiyyah" Safiyyah ta rufe baki da sauri, sai kuma tayi kasa sosai da murya tace "Kuma
haka fa, kar ace da Cctv a dakin mu ji kunya" Khaleesat ta wani kalleta tace "Ki ji kunya dai, tun da mun
gaishesa ki tashi mu tafi kawai" a hankali Safiyyah tace "Gaskiya Housemate din nan naki is more than
nice and calm, ni har naji yana burgeni wallahi, look how he welcomed us warmly duk da bashi da lafiya"
Khaleesat ta daga ido ta kalleta sai dai bata ce komai ba, ita dai Safiyyah sai bin katon dakin take da kallo
with fascination, tayi kasa da murya tace "In na samu irin wannan dakin ai mance me ya kawo ni kasar ma
zan yi gaba daya, anya ma kuwa student ne Housemate din nan naki" Khaleesat ta hade rai tace "Tashi mu
tafi tunda mun dubasa Safiyyah" Safiyyah tace "Amma ai kya jira ya shigo mu yi masa sallama ko, dadina
dake a ko ina sai kin nuna halin ki, kamar ana koranmu daga shigowa gida kice mu tashi mu tafi" Budewar
kofar dakin ya sa duk suka yi shiru, Housemate dinta ya shigo da sallama ya zauna kan kujeran dakin ya
jinginar da kansa da kujeran, sai ga wani chef din gidan ya shigo da wasu tsadaddun cookies ya ajiye masu
kusa da su, sannan ya juya ya fita, Jay na kallon Khaleesat yace "Naga kina son cookies sosai Housemate,
here are some for you and ur frnd" Bata yarda ta kallesa ba tana wasa da gyalenta tace "I am okay, tafiya
ma za mu yi" a hankali yace "So soon? Amma sai kun ci cookies tukun" Khaleesat ta ɗan kallesa suka hada
ido a karo na farko tun shigowarsu dakin, sosai taji gabanta ya fadi tayi saurin sauke idonta, ya kalli
Safiyyah yace "In bazata ci ba ke ki ci abunki... Amma ban san sunanki ba kawar Housemate" Safiyya tayi
murmushi tana bude cookies din ta dau guda daya tace "Sunana Safiyyah Adam" Yace "Maa sha Allah, it's
nice meeting you Safiyyah, i am Jawwad Ahmad, or you call me Jay" Safiyyah tace "Nice meeting you too
Jay" ita dai Khaleesat wasa da gefen veil dinta kawai take kanta a kasa, Safiyyah ta bude handbag dinta
saboda kiran wayarta da ake yi, tana dubawa taga Cousin brother dinta ne, ta mike tace "Let me pick a call
pls" Jay yace "Alright Safiyyah" Kofa ta nufa ta bude ta fita sannan ta kullo masu kofar, ledan da suka
shigo dakin dashi ya ɗan bude yace "You got me all this Halysaah" Khaleesat ta ɗan kallesa tace "Um"
Yace "Ohk thank you so much i really appreciate" Tana kallonsa a hankali tace "Ya jikin?" Yace "I am
getting better gradually, daxu sai naji ina sha'awar wannan tuwon da kika yi some days back" Tana kallonsa
tace "Na vegetable soup?" Yace "No, wannan da na kasa ci, the dark soup, I can't remember the name" Bata
san sanda tayi murmushi ba tace "Ok miyan kuka?" Yace "Shi... kawai naji shi nake son ci sincerely" a
hankali tace "Ohk zaka je can gida anytime soon ne?" A hankali yace "Idan na samu lafiya in sha Allah" Ita
dai Khaleesat kallonsa kawai take, shi kam idonsa na gun different direction, Ajay ne ya bude kofar dakin,
kai tsaye ya shigo ya nufi Jay yana mika masa wayar hannunsa yana kallonsa, ita dai Khaleesat ta sunkuyar
da kanta bata kalli inda yake ba, Jay ya amshi wayar yana duba screen din, sauke ƙafafuwansa yayi daga
kan kujeran da yake zaune ganin wanda ke kan layi, ya kai wayar kunne da ladabi yayi sallama hade da
gaisuwa, sai kuma yace "Alhamdulillah Abba da sauki, wayar a silent yake ne shi yasa" Sai kuma ya daga
kai ya kalli Ajay jin abinda Abban ke ce masa, a hankali yace "A'a ba haka bane Abba, i do eat... but not
much, ba gaskiya ya fada ba" Daga haka yayi shiru bai sake cewa komai ba, after a minute yace "To in sha
Allah Abba, Allah ya kara girma" Sai da ya jira Abba ya katse wayar sannan yayi wurgi da wayar saman
gadonsa yana kallon Ajay, wani kallo Ajay yayi masa ta gefen ido ya juya ya tafi ya dau wayarsa a kan
gadon sannan ya fice daga dakin, Khaleesat ta gama tura ma Safiyyah text din da take na cewa tayi masu
ordering Lyft su tafi gida, sai kuma ta daga kai ta kalli Jay, ganin mood dinsa ya canza, a hankali tace
"Baka cin abincin ne ko?" Yace "Ki kyalesa mana, i took cereal daxu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login