Showing 45001 words to 48000 words out of 152206 words
kuwa zan san yanda za ki yi, ke wa ya aike ki yi masa rashin
kunya? Da sai ki yi shiru da bakinki har in fitar da shi daga gidan, Laptop dinsa na dauko daga can gida
yana bacci ban san akwai aikinsa da zai yi put foward ta email ba, yana ta kiran wayana kuma ina bacci na
sa wayar silent, that was what brought him here" Zaunawa tayi kan kujera tace "That doesn't still warrant
him ya shigo gidan mutane kai tsaye, ko magana bai min ba ina bude kofa ya kusa bangajeni fa ya shigo
parlon, am i a joke to him?" Dariya Jay yayi yana gyada kai yace "This energy u used in attacking him
Allah ya baki irin energy din kiyi using ma Boyfriend din ki" Wani kallo Khaleesat tayi masa, shi dai
murmushi kawai yake still not looking at her yace "Naga kamar kin damu da abinda kika masa, ko in kirasa
ki basa hakuri ta waya komai ya wuce?" mikewa tayi a takaice tace "Allah ya kiyaye" Daga haka tayi
wucewarta kitchen, shi dai murmushi kawai yake looking at a different direction, yasan yau da kyar Ajay
yayi bacci akan abinda tayi masa. Bayan Khaleesat ta gama girkin da take ta fito parlor tana kallon Jay
ganin fita zai yi don har ya shirya yana saka agogon wrist dinsa without looking at her yace "I think sai
gobe zan dawo in sha Allah" Ta marairaice amma bata ce masa komai ba, har cikin ranta ta fara jin tsoron
kasancewarta ita kadai a gidan, ya ɗan kalleta yace "Any problem?" Ta hade rai tace "Toh ka bani
makullinka idan ka zo goben sai kayi knocking in bude maka kofar" Da mamaki yace "Why?" Tace "So
that baza kaje ka ajiye key din recklessly ba wannan mutumin ya gani ya dauka" Yayi dariya yace "To ya
dauka yayi me da shi?" Ta nufesa tace "Bani" ba musu ya bata makullin ta amsa sannan a hankali tace "To
abincin fa?" Yace "Abinci? Wani iri?" Bata tanka sa ba ta juya ta koma kitchen din, after some minutes sai
ga ta ta dawo da plate din rice and stew, ya ɗan bude ido yace "Wa zai cinye duk wannan?" Tace "Kai
mana" Ya zauna sannan ta mika masa abincin, yana girgiza kai yace "It's very plenty" tace "Should i get
you water?" Yace "I will appreciate that" kitchen din ta koma ta dauko masa ruwan gora da drink din
gwangwani, yace "Thank you Halysaah" dakinta ta wuce, after a while taji yayi knocking kofar dakinta,
bayan ta bude yace "Zo ki bude min kofar zan tafi" Makulli ta dauko ta tafi ta bude masa kofar yace "Thank
you, see yah tomorrow" ita dai bata ce komai ba ya fita daga parlon ya nufi garage, a hankali ta kulle kofar
da makulli sannan ta tafi window ta ɗan bude labulen tana kallonsa har ya bar garage din after some
minutes, Sake curtain din tayi, walking slowly ta tafi kitchen, bude abincin da ya rufe tayi taga kadan ya ci
a ciki, Allah yasa yayi spoon hudu, naman ma kawai daya ya ci, kulle abincin tayi ta dawo parlor ta zauna,
dai dai nan taji anyi knocking kofar parlon mikewa tayi da sauri tana kallon kofar a tsorace, da kyar tace
"Waye??" Muryar Safiyyah taji, lkci daya ta sauke ajiyar zuciya sannan ta tafi ta bude kofar, Safiyyah tace
"Har kin gama laundry din?" Khaleesat tace "Na gama" Safiyyah tace "Housemate din naki ya fita kenan?'
Khaleesat tace "Eh" Safiyyah tace "Jiya da daddare da kika gaya min ya zo gidan ta chat wallahi nayi farin
ciki, don mutumin na da kirki sosai" Khaleesat bata tanka ta ba, ta koma cikin parlon ta zauna tace "Ban
gan ki da laptop dinki ba" Safiyyah tace "Abeg i will use urs, bani da strength din dauko laptop, kin yi girki
kuwa? Don yunwa nake ji, wancen er iskar matar faten wake tayi saboda tasan ba na ci, hegiya dama
bayerabiya ce ta wajen uwarta ai" Dariya kawai Khaleesat tayi ta mike ta tafi kitchen, abincin ta zubo ma
Safiyyah, ita kuma ta dau wanda Housemate dinta ya rage, ta dauko masu ruwan gora da lemon kwali
daya....
✍🏻
07087865788
[5/13, 6:21 PM] khaleesat Haiydar ✍️: ✨✨HALYSAAH✨✨
✍🏻
By _Khaleesat Haiydar_
16.....
Ko da wasa Khaleesat bata ba Safiyyah labarin abinda ya faru tsakaninta da Ajay ba, amma fa bata da rest
of mind gani take kamar zai iya dawowa gidan at anytime, upon all her restlessness bata ji tayi da ta sanin
abinda tayi masa ba, dama haushi yake bata, Safiyyah na kallonta tace "Ke kwana biyu shiru banji kince ga
abinda Abdul yayi maki ba ko dai ya fara canzawa ne? This is so unusual, ko baki gaya min ba in dai ya
maki wani abu you are always moody in school, ta haka nake ganewa" Khaleesat na powering laptop dinta
ta tabe baki tace "Ni ina naga wannan time din yanzu ga exams a gabana" Safiyyah tace "Atoh dai, wallahi
naji dadin da kika fara daukar shawarata kina fita sabgarsa, sauranki abu daya yanzu" Khaleesat ta daga kai
ta kalleta, Safiyyah ta gyara zama tace "Saura ki fara mayar masa da magana, in ya gaya maki daya ki gaya
masa biyar" Ita dai Khaleesat bata sake ce mata komai ba tana neman softcopy na course din da za su yi
studying tare da Safiyyah. Bayan tafiyar Safiyyah... Khaleesat ta wanke utensils da suka yi amfani da
sannan ta wuce dakinta, wayarta ta dauka ta shiga WhatsApp don ganin ko Ummanta tayi mata reply din
message da ta ajiye mata daxu, wajen karfe goma da rabi tana shirin kwanciya wayarta ya fara ring, dauka
tayi taga Abdul ne ke kiranta, ta dinga kallon wayar, tun sanda Ummanta tace mata tana ganin kamar lkci
aka tsayar take wani jin tsanarsa a zuciyarta, gashi yaki gaya mata ko da gasken an tsaida lkcn ko ba a
tsayar ba don Ummanta ba wai ta tabbatar bane ita ma a gari ta ji, dama tana Nigeria din ne ta san gun
warce zata je taji ko hakan ne ko ba haka ba, ɗaga kiran tayi kafin ya katse ta kai kunne, muryarta kamar
me bacci ta gaishesa, ya amsa, a hankali tace "Ya aiki?" Yace "Lafiya lau" Shiru tayi bata sake cewa komai
ba, yayi ƙasa da murya yace "I don't know, kawai ina missing din ki ne yau, i want to be with you Baby" Ta
kauda kai kamar irin yana kusa da ita din nan tace "Um" Yace "Yaushe za ku fara jarabawan?" Tace "Nan
da wata daya" A hankali yace "Ohk, sai da safe, naga kamar kin fara bacci" Tace "Um, ina son tashi inyi
karatu ne anjima shi sa na kwanta da wuri" Yace "To ci gaba da baccinki, sai mun yi magana" Daga haka ya
katse wayar, ta jefar gefenta ta ci gaba da chatting da take da Ummanta. Washegari lahadi Khaleesat na
zaune dakinta tana morning Supplications dinta taji ana kwankwasa kofar parlor, wayarta ta jawo tana duba
agogo taga bakwai ya wuce, ta daure ta mike tana tafiya a hankali ta fito parlor, bayan ta karasa bakin kofar
with calmness tace "Waye?" Taji muryar Housemate dinta yace "Good morning" bude kofar tayi ta koma
gefe ya shigo, sau daya ya kalleta yace "How was ur night" Ta kulle kofar tace "Alhmdlh" Materials din
hannunsa ya ajiye saman 1 seater sannan ya kwanta kan doguwar kujera, ita dai bin sa tayi da kallo taga har
ya kulle idonsa yana gyara kwanciyarsa alamar bacci zae yi, tana tafiya a hankali ta koma dakinta, ta karasa
azkar dinta sannan ta kwanta. Har wajen karfe daya na rana Khaleesat bata fito dakinta ba, ta ɗan juya daga
kwancen da take tana kallon kofar dakinta jin ana knocking, kiranta taji Housemate dinta ke yi, mikewa
zaune tayi still tana kallon kofar amma bata sauka daga kan gadon ba, Calmly tace "I can hear you" Yace
"Are you alright? Naga kamar baki yi breakfast ba ko?" Shiru tayi bata ce komai ba, bude kofar taga yayi,
ta gyara blanket din jikinta tana kallonsa, ya tsaya daga bakin kofar dakin yace "Hope nothing?" Ta
langwabar da kai tace "Nothing" Yace "To me yasa baki fito kinyi breakfast ba or are you fasting? Beside
today is sunday" Ta kauda idonta tace "Kawai dai..." Sai kuma tayi shiru, ya karasa cikin dakin yace
"Kawai dai me?" Kamar baza tace komai ba sai kuma dai tace "Ina jin ciwo a kafana ne" Yace "Ciwo a kafa
kuma? Yana maki haka ne?" A hankali tace "Once a while" Shiru yayi jin abinda tace, can yace "Then what
is the cause?" Ta ɗan kallesa, sai kuma ta bude hannu alamar bata sani ba, yace "Kun taɓa zuwa hospital a
kan hakan?" Ta dai yi shiru without looking at him, sai kuma tace "It's fine, i will get better before evening
in sha Allah" Ya juya as if trying to diagnose without examination the cause of her leg pain at her age, sau
daya ya kalli gaban dressing mirror dinta sai kuma ya juyo yana kallonta yace "Ok i get, Allah ya
sauwake..." Ta ɗan kallesa, yace "Try getting a hot shower, you will feel better" Juyawa yayi ya fita daga
dakin, a hankali Khaleesat ta koma ta jingina da pillow, ko tashi tsaye bata jin zata iya a yanzu dai, kilan
zuwa can anjima ta ɗan ji relieve before she can stand up and do anything, kiran Abdul ne ya shigo wayarta
ta kife wayar taki dagawa don ko magana bata so, after some minutes ta kalli kofarta jin knocking at the
same time ya bude kofar dakin ya shigo ciki rike da cup din hot chocolate, sauke idonta tayi daga kallonsa
ya karasa har side din da take ya duka yana mika mata Mug din hot chocolate din yace "Try drinking this,
will get u pain reliever now" Ta amshi Mug din without looking at him a hankali tace "Thank you" Yace
"You are welcome" Daga haka ya fita daga dakin ta bi sa da kallo babu ko kiftawa, yana fita kiran Abdul ya
sake shigowa wayarta still taki dagawa daga karshe ma tayi silencing wayar, khaleesat na gama shan hot
chocolate din ta ajiye cup din a bedside drawer sannan ta koma ta kwanta tayi lamo kan pillow, kamar zata
kira Safiyyah daxu wajen karfe sha biyu sai kuma ta fasa hoping the ache will subside, har ta fara bacci
Housemate dinta yayi knocking wajen karfe biyu almost 20 mins bayan fitarsa daxu, sai da ta amsa sannan
ya bude kofar, ita dai bata juyo ba, ya zaga ta inda take calmly yace "Are you sleeping Halysaah?" Ta bude
ido tana girgiza kai, ya ajiye ledan abincin hannunsa da pain reliever da ya siyo mata yace "Baki yi hot
shower da nace kiyi ba?" Tace "Zan yi" Yace "Ohk ga maganin sai ki ci abinci ki sha" Ta mike zaune
without looking at him, a hankali tace "Thank you" Yace "Zan fita but i will come back around 6pm in sha
Allah" Tana kallonsa tace "Toh makullin gidan fa?" Ɗan murmushi yayi yace "Ai a jikin kofar kika bar sa
daxu da kika bude min da safe" Tace "Amma baza ka tafi da shi ba ai" Yace "To taso ki kulle kofar" Ta
wani kallesa, er dariya yayi yace "Shi fa Ajay nasan yanxu kuma ya mance abinda ya faru tsakanin ku, may
be sai ranan da ya kara ganinki zai tuna, but for now i am assuring you ya mance wallahi he is even busy
with his upcoming defense, beside you misperceived him, Ajay is more than nice and calm, ba shi da
matsala, kawai dai shaidan ne ya saka rashin jituwa tsakaninku tun a ranan da ku ka hadu" Khaleesat dai ta
kyabe baki don ko duk jikinta kunnuwa ne bazata taɓa yarda da abinda yake fadi ba, Jay yace "Baki yarda
ba ko?" Ta buda ido sosai tace "To dama saboda me zan yarda?" Dariya kawai yayi yace "Take care of ur
self Halysaah, in kin ci abincin ki sha magani, let me get you bottled water" Daga haka ya nufi kofa ita dai
ta bi sa da kallo har ya fita, sai gashi ya dawo mata da ruwan gora mara sanyi ya ajiye a inda ya ajiye mata
ledan abinci da magani wato bedside drawer, yace "See yah later" a hankali tace "Thank you, and pls do not
mishandle the key" Murmushi kawai yayi ya gyada mata kai ya fita daga dakin ya kullo mata kofar, ta
sauke idonta kasa, after some minutes ta dau ledan abincin da ya ajiye mata a hankali tana budewa don
ganin abinda ya siyo mata. Karfe shidda saura Khaleesat na zaune kasan dakinta ta kwantar da kanta jikin
gado tana voice note da Ummanta, zuwa sannan she is feeling very much better don har ta gyara dakinta ta
wanke bandaki tayi wanka, parlor ne dai taji bazata iya gyarawa ba, wajen karfe hudu suka yi chatting da
Safiyyah tace mata zata zo karfe bakwai, Khaleesat ta dan yi jim bayan taji kamar an bude kofar gidan,
gabanta ne ya fadi bayan Ajay ya fado mata, ta ajiye wayar hannunta a hankali tana kallon kofar dakinta,
after few minutes taji an yi knocking kofar dakin, she felt a bit relieved, with calmness tace "I can hear
you" Taji muryar Housemate dinta yace "Can i open the door?" Tace "Okay" bude kofar dakin yayi yana
daga bakin kofar a tsaye yace "Good evening Housemate, how are you feeling?" Tace "Da sauki" Yace "Are
you sure?" Sai a sannan ta daga kai ta kallesa, ta dan kwantar da kanta gefen gado tace "It's better than
before" Yace "To Allah ya sauwake, where you able to go to the kitchen?" Ta gyada masa kai, yace "Ohk"
Har zai kulle mata kofar sai kuma ya tsaya yace "Ko mu dan yi strolling as exercise, around the
neighborhood, it will help you feel much better too" Khaleesat ta daga ido ta kallesa, yace "I will be
waiting for you at the parlor, make sure to put on ur jacket cause it's freaking cold outside" Yana fadin haka
ya fita daga dakin, Khaleesat dai na ta zaune kamar me nazari, it took her almost 5 mins of deciding kafin
ta mike a hankali, veil dinta kawai ta dauka ta yafa ta dau wayarta tana tafiya a hankali ta fito daga cikin
dakin, tsaye ta gansa ya jingina jikin pillar dake kusa da study area yana danna wayarsa daya hannunsa rike
da jacket dinsa, yana ganinta yace "Are you ready? Where is ur jacket?" Karasawa yayi inda take tsaye
yace "It's cold outside" Yana fadin haka ya ajiye mata Jacket dinsa kan kujeran dake kusa da ita yace "Use
this, bari in dauko wani" Dakinsa ya koma ita dai ta bi sa da kallo, ba a dau lokaci ba sai gashi ya dawo
parlon with another Jacket, ya saka a kan rigar jikinsa yace "Mu je" Ta sauke idonta ta dau Jacket din nasa,
Kofar parlon ya nufa ta bi bayansa har suka fita daga parlon, ya kulle kofar ya kalleta yace "Na lura kina
son so much perfume ke dai" Ta girgiza kai tace "A'a ni ban sa ba yanzu" Yace "Ohk" A tare suke tafiya
with nobody saying anything, tun ba su kai ko ina ba taji tana jin sanyi sosai, hakan yasa ta ɗan saci
kallonsa sannan ta saka jacket din hannunta yace "Ai na zata baza ki sa ba kina forming big gal" Kawai dai
tayi murmushi bata ce komai ba, tana jin kamshin turarensa da ya cikata na jikin Jacket din, dai dai yake
tafiya da ita to keep same pace with her, slowly suke tafiyar with absolute silence har suka yi nisa away
from home, Jay yayi breaking silence din yace "Soon za a fara snow" Tace "In sha Allah kafin nan mun
gama Exams dinmu" Zai yi magana wayarsa ya fara vibrate ya ciro a aljihunsa yana duba me kiransa, ta
gefen ido ta kalli wayar tasa taga Ajay, yayi silencing wayar ya mayar aljihunsa, ta tabe baki tace "Shi dole
sai ya dinga damunka da kira ne as if you are with his kidney?" Jay yayi dariya yace "Kidney ai me sauki
ne, cewa za ki yi kamar life dinsa na wajena dai, a rana sai ya kirani sau ashirin in banyi hankali ba"
Khaleesat ta kyabe baki sai ga shi ya sake kiran wayar, Jay ya kara ciro wayar yayi picking ya sa Hands-
free yana tafiya yace "What again?" Daga daya bangaren Ajay yace"I need ur laptop, zan duba references
dinka, na mance zan shiga schl gobe, i am outside with my frnd now" Jay yace "Da laptop din na fita ai,
kuma i am not coming back home anytime soon" Ajay yace "Gidan wannan mara kunyan ka koma kenan?
Wai are you even okay Bruh? Me kake yi da wannan yarinyar da ya sa kake zama gidanta? Ko iskanci ka
fara ne? In ma iskancin zaka yi why with that little local brat pls?" Jay that was trying not to laugh yace
"Kai kar ka bata min rai fa" Ajay yace "On a serious note idan baka daina zuwa gidan nan ba i promise you
am gonna report you back home kasan karamin aikina ne hakan ko?" Jay yace "In ka fasa, kai duk takurani
da kake da yan iskan abokanka a can gida ban kai report ba sai ni da na bar maka gidan for peace to reign
shi ne zaka kai karata? To references din ma baza a nuna ba, go and sort ur self out" Yana kai wa nan ya
katse wayar ya mayar cikin aljihu, ita dai Khaleesat bata kallesa ba kuma bata ce komai ba amma har cikin
ranta take jin Ajay bai mata ba, she doesn't like him or anything concerning him, ta tsani mutum that is too
pompous and proud of himself, Jay yace "Baya karatu fa, in ma wani aiki ne sai dai kai kayi ya gani sannan
yayi nasa, har ma nasan yafi naka at the end" Khaleesat tace "To me yasa har yanzu ba a koresa ba daga
makarantar?" Dariya sosai Jay yayi yana kallonta yace "Baya karatu doesn't mean he is dull Halysaah,
kinsan Genius? That is who Ajay is, he is naturally gifted, he graduated as one of the best medical student
during our degree program in this state and masters, kuma kar kice wani karatu yake, mu ne dai sai mun yi
karatun za mu wuce" Yana murmushi ya kare maganar, Khaleesat ta wani kyabe baki kamar bazata ce
komai ba, sai kuma tace "To ai gwara kai karatun kayi ka wuce, shi kuma banza kawai yake ci" Jay na
dariya yace "Ai shi sa na bar masa gidan cause idan na ci gaba da biyesa da abokansa wucewa zai yi ya bar
ni, su