Showing 135001 words to 138000 words out of 152206 words
in sha Allah, zan mata duk abinda ya kamata a matsayin ta na 'ya ta" Abdul ya kasa cewa
komai yana kallon Momynsa, Momy tace "Mu je ka ci abinci" Bata jira cewarsa ba ta fita daga dakin, bin
bayanta yayi ya fita amma duk tsaurin idonsa sai yaji nauyin ce ma uwar tasa komai, haka nan Momy ta
dauko masa abincinsa da ta hada masa da kanta ta jera masa su a dinning sannan ta koma kitchen zata hada
abincin Khaleesat, Abdul ya zauna kujeran dining amma ya kasa cin abincin, shi fa bai yi niyyar ma kwana
gidan da Khaleesat ba don irin burin da ya ci a kanta yau ai sai Allah, nan da nan yaji ransa ya baci, ya
mike ya shiga kitchen ya samu Momy ta sa mai aikinta ta jera ma Khaleesat abinci a tray, don irin abin da
ta hada mata har ya fi na Abdul, Momy na kallon mai aikin tace "Tafi ki kai mata bangarena ki jirani ina
zuwa" Mai aikin ta fita daga kitchen din da tray din, Abdul na kallon Momy a fusace yace "Toh wai
menene yasa Meemah zata ce min Daddy ba shi da lafiya critically bayan ma ashe baya kasar?" Momy tace
"To ai ganin likita yaje a Amurka, ko bai gaya maka bane? Karfe hudu na yamma jirginsu ya tashi, shi yasa
kaji nake cewa baka taho da wuri ba don duk zatona zaka tarar da shi" Abdul yayi shiru yana kallon Momy,
Momy tace "Ni dai bari in je wajen diyata, kar ka wani huce kan Meemah don ba ita ta hanaka matarka ba"
Daga haka Momy ta bar sa tsaye a kitchen din, tsaye ta tarar da Mai aikinta a bangarenta tana jiranta don
kofar a kulle yake, Momy ta bude mata suka shiga ciki, Mai aikin ta ajiye abincin gaban Khaleesat, Momy
na kallon mai aikin wanda ranan ne ranan farkon da ta shigo mata daki tace "Toh fita ki ban waje...." Mai
aikin ta fita da sauri ta kullo kofar, Momy tayi murmushi tana kallon Khaleesat tace "Ga abinci nan
Mamata" Momy ta tafi ta dauko handbag dinta ciro wani kulli ta dawo kusa da Khaleesat ta bude kullin ta
barbada mata abinda ke ciki a farfesun kayan cikin dake cike a bowl tace "Maza ki shanye har romon kin
ji" Kai kawai Khaleesat ta gyada mata, Momy ta tafi ta zauna kan kujera tana murmushi ta dau remote ta
kunna TV din dakin, a hankali Khaleesat ke shan farfesun tunani iri iri na yawo a kanta, to yanxu kenan
hakuri kawai zata yi da auren Abdul, since gaba daya family dinta sun nuna sun yi accepting auren, sannan
ga Mum dinsa ma ta ga tana sonta, kilan zaman aure da Abdul a kaddarar rayuwarta yake, she should just
accept it with good faith, most important of all gashi mahaifiyarsa na sonta, his sister won't be an issue
tunda mamansa na sonta, kawai ta saka ma ranta salama ta amshi auren tunda haka Allah ya kaddara mata,
Housemate dinta ne ya fado mata, lkci daya taji hawaye ya cika idonta, da sauri ta sunkuyar da kai kar
Momy ta gani cikin dubura ta dinga goge hawayen tana jin wasu masu zafi na sakkowa, sai da Momy ta
tabbatar ta ci abincin sosai, sannan ta umarceta da taje tayi wanka ta tabbatar ta sake tsarki da duk
abubuwan da ta nuna mata a bandaki, kafin Khaleesat ta fito Momy ta dauko mata kayan bacci da inner
wears, Khaleesat ta shirya tayi sallan isha'i, Momy bata tashi barin dakin ba sai kusan karfe tara da rabi,
bayan ta sa Khaleesat ta kwanta kan gadonta sannan ta kashe mata wutan dakin ta bata remote din Ac a
kusa da ita, tayi mata sai da safe ta fita daga dakin, har ta kulle kofar ta sake budewa ta shiga tana kallon
Khaleesat tace "Ko tashi kika yi zaki kama ruwa cikin dare kiyi tsarki da abubuwan nan fa Mamana kar ki
manta" Khaleesat tace "Toh Momy" Momy ta kara mata sai da safe sannan ta fita ta kulle kofar da makulli
ta sauka downstairs, Abdul kadai ne zaune parlor yana kallon kwallo amma kana ganinsa kasan ransa a
bace yake, Momy tana kallonsa tace "Sai da safe Babana" Ciki ciki ya amsa mata, ta juya ta koma sama
zuwa dakin da su Meemah suke, duk suka dinga kallon Momy bayan ta shigo, Aunty Karima tace "Ya dai
Momy duk ta yi?" Momy tayi wani murmushi tace "Tun yaushe kuma" Meemah tace "Alhamdulillahi, shi
Abdul din fa?" Momy tace "Shi ai dama a miyar shinkafa aka ce na zuba masa maganin, sai ruwan lipton,
na kori mai aikin taje bakin pampo tayi wanke wanke shine na samu duk na zuba masa nasa" Meemah tayi
murmushin mugunta tana gyara zama sanin Momy bata bin malaman banza, kai in malami yace zai amshi
kasa da 1M a wajenta ma bata yarda da ingancin aikinsa ba, inda ake aikin da gaske take zuwa, ko da kuwa
miliyan biyar zata kashe bata kyashi don tasan aiki na gaske ake mata.
[6/19, 8:55 PM] khaleesat Haiydar ✍️: Washegari da safe bayan Khaleesat ta shirya cikin tsadadden Abayan
da Momy ta bata, Momy ta gama hada mata shayin da take yi cikin cup tace "To zo kiyi breakfast din kar
ya huce Mamana" Khaleesat bata ce komai ba ta karasa ta zauna kan darduman da aka jera mata breakfast
din, Momy tayi murmushi tace "Idan farfesun bai isheki ba sai ki bude warmer ki ƙara, dankalin ma akwai
saura a warmer in bai ishe ki ba" Ita dai Khaleesat kai kawai ta gyada mata, tana juya shayin gabanta a
hankali da spoon din ciki, Momy ta koma kan kujera ta zauna tana kallonta tace "Duk da ma ina lura jiya
baki wani ci abincin da aka kawo maki da yawa ba, ko maganin cin abinci zan sa a samo maki mamana"
Khaleesat tayi murmushin karfin hali bata dai ce komai ba ta dau shayin tana kallon ciki, sai tayi tunanin
lipton din ne kilan ya fashe a cikin ruwan shayin, sipping din shayin tayi kadan ta ajiye sannan ta fara cin
irish din, Momy dai kallonta kawai take kasa kasa, Bude kofar dakin aka yi Momy ta juya, ganin Abdul
tace "Sai yanxu ka tashi Babana" Bai ce mata komai ba ya karasa ya zauna saman kujera, Khaleesat ta ɗan
kallesa taga kallonta yake, sauke idonta tayi a hankali tace "Ina kwana" Ya kauda kai yace "Lafiya" Momy
tace "Ka tashi kaje kayi breakfast din ka" Yace "Momy za mu je shopping ne, bata zo da kaya ko daya ba"
Momy na kallonsa tace "To wanda ka gani a jikinta yanxu kai ka siyo mata?" Shiru Abdul yayi yana kallon
Momy, Momy tace "To har na tura ma Meemah kudi su je su yi mata siyayya ita da Karima tunda kai baka
da ƙara" Mikewa Abdul yayi ya nufi kofa ya fice daga dakin, Momy ta bi sa da kallon gefen ido, sai da
Momy taga Khaleesat ta gama cin abinda zata ci na breakfast din sannan ta mike ta fita ta kira mai aikinta
ta fitar da sauran abubuwan da Khaleesat ta rage, bayan mai aikin ta fita Momy ta bude bayan labulenta ta
dauko wani karamin jarka ta kawo ma Khaleesat tace "Wannan tsumi ne Mamana, daga yanxu har zuwa
dare nake son ki shanyesa gaba daya" Ita dai Khaleesat kallon jarkan take, Momy tace "Kin ji ai ko?"
Khaleesat ta gyada mata kai tace "Toh Momy" Momy ta dauka ta mayar bayan labule sannan tace "In zaki
yi kallo sai ki kunna TV abun ki, bari in je zanyi bakuwa ban san ko ta iso ba" Khaleesat tace "Toh" Momy
ta fita daga dakin ta kulle da makulli tana rike da makullin ta sauka downstairs don aminiyarta godiya ta
kirata ta sanar mata tana hanya, tana shigowa parlor taga Abdul zaune dinning area da breakfast din da
Khaleesat ta rage a gabansa, da karfi Momy ta kwala masa kira, ya juya yana kallonta, ta karasa wajen da
mugun sauri tace "Banda abun ka ba ga naka a kitchen ba Abdul me zaka yi da wanda aka rage? Ko har
kaci wannan din ne?" Abdul dake kallonta yace "Ban ci ba, amma menene idan na ci?" Momy ta kwalo ma
mai aikinta kira, Mai aikin ta taho da sauri Momy ta kunduma mata wani ashar tace "Nan nace ki ajiye
sauran abincin er iska kawai er neman jidali? Me yasa ke dakikiya ce? Wallahi zan kore ki fa a gidana na
gaji da maganar da kike sa ni kamar kanwar uwarki, yau ga shegiyar mata kawai" Abdul ya kalli Momy
yace "Ni fa nace ta kawo min nan, beside what is wrong with the food da bazan ci ba?" Momy ta mata
tsawa tace "Dauka ki wuce ki ban waje guntuwar banza kawai" Mai aikin na ba Momy hakuri ta dauke jiki
na rawa ta tafi kitchen da breakfast din, Momy ta kalli Abdul dake kallonta, yace "I want to understand
meye da abincin da bazan ci ba Momy?" A takaice Momy tace "Kayan gyaran mata mana? Ko kai na mace
ne?" Bata jira cewarsa ba ta bar wajen ta shige kitchen ya bi ta da kallo, Tuttular da shayin tayi a sink
sannan ta juye sauran irish din da kwai da farfesun duk ta cakudesu waje daya tace "Gasu nan ki kai ma
karnuka, in kuma kwadayin ki ya ja ki kika ci ke kika jiyo" Mai aikin ta risina ta amsa tace "Toh Hajiya"
Sai da Momy ta jirata har ta dawo bayan ta kai ma karnukan can cage dinsu sannan Momy ta dau breakfast
din Abdul ta kai masa kan dining din tace "Ga naka nan" Daga haka ta juya ta bar wajen, dai dai shigowar
Godiya gidan, da fara'a Momy ke mata sannu da zuwa Abdul ya dauke kai kamar bai ganta ba don ya tsani
matar with passion, tun asali dama baya gaida ta, Haka Momy ta ja ta zuwa sama tana cewa "Mu je ki ga
surkar tawa ku gaisa" Da ido Abdul ya bi su har suka haura sama, Momy na isa kofar dakinta ta bude da
makulli suka shiga, Khaleesat dake gyara gadon Momy ta mike tsaye tana kallonsu, Momy na murmushi ta
kalli godiya tace "Kin ganta" Da fara'a sosai Godiya tace "Maa sha Allah, ai ko ga ta kamar balarabiya Maa
sha Allah, sannu amarya, ya sunanki?" Momy na murmushi tace "Sunan Baabata gareta, Hauwa sunanta"
Khaleesat ta zame kasa ta sauke idonta ta gaida Godiya, Godiya ta karasa kusa da ita ta dafata tare da
ɗagota ta zaunar da ita gefen gadon Momy tace "Lafiya lau diyata, ya bakunta?" Khaleesat bata ce komai
ba kuma bata dago kanta ba, Momy na kallon Khaleesat tace "Kin sha tsumin da nace ki sha kuwa?"
Khaleesat ta gyada mata kai tace "Na sha" Momy tace "To maa sha Allah, Allah ya maki albarka Mamana,
zuwa anjima sai ki kara sha kin ji" Khaleesat tace "To" Bayan few minutes Momy da Godiya suka fita
dakin, Momy ta sake kulle kofar da makulli sannan ta cire makullin suka tafi wani daki dake sama, bayan
sun shiga Momy ta kulle kofar tana kallon Godiya tayi murmushi tace "Duk tayi amfani da abubuwan babu
gardama godiya, iya na jarkan nan ne kawai ya rage yanzu" Godiya ta zauna gefen gado tace "To madallah,
shi ma Abdul din duk kinyi yanda aka ce kiyi da na sa?" Momy tace "Kwarai kuwa" Godiya tayi wani
murmushi ta bude handbag dinta ta ciro wani babban laya bakikirin da shi ga er karamar kwado a jiki ta
mika ma Momy tace "To aikin karshe kenan wannan Hajiya, Malam ya ce ki samu inda kika san baza a
taɓa tono sa ba ki binne a cikin gidan nan" Momy ta zauna gefenta tana murmushi ta amshi layan tace "To
laya nawa na binne gidan nan ba a tono ba godiya, ai wannan karamin aiki ne a wajena don ba sabon abu
bane" Godiya tace "Yauwa, bayan kin binne Malam yace ki basa yarinyar kawai, wallahi yace min in har ta
wuce sati biyu Abdul bai rabu da ita ba to bazata wuce sati biyar ba a gidansa" Fara'ar fuskar Momy ya
bace tace "Har sati biyar Godiya? Ni da yace min sati daya kacal a waya" Godiya tace "Halan bai gaya
maki irin abubuwan dake ƙan dan ki bane? Da yaya ma aka samo kansa har asirin nan yayi tasiri? Ai
abubuwan ƙan Abdul sun fi karfin wani asirin wallahi kiji in gaya maki" Momy ta sauke ajiyar zuciya tace
"An taɓa gaya min haka da dadewa wallahi, don ni akwai malamin da yace min ma yanda asiri ke cin
ubansa shi sai an wahala asiri zai ci sa" Godiya tace "To wallahi Malam sai da ya tura masa aljanu don ma
ki ji Hajiya, aikin nan sai da Malam ya hada da wasu malaman don aiki ne me wahalan gaske yace min
wallahi" Momy tace "To ni fargabana kada fa in mika masa yarinya ace asirin nan bai ci ba abinda muke
gudu ya afku mu shiga uku Godiya" Godiya tace "Sai kace yau Malam ya fara maki aiki? Ai da aikin bai yi
ba kinsan bazai boye mana ba, sai dai ya kara mana lokaci yayi wani sabon aikin fa, dama yace in na
yarinyar ya ci shine zai sa na Abdul din ma yayi tasiri sosai" Momy tace "Haka ya ce kam" Godiya tace
"Don haka zuwa gobe ki basa ita kawai su tafi an gama aiki sai jiran result, kuma ina me tabbatar maki zaki
sha mamaki" Momy na murmushi tace "Toh shikenan godiya, nagode sosai, zan tura masa cikon dubu dari
biyar dinsa anjima" Da yammacin ranan bayan Momy taga Abdul ya fita gidan tayi maza ta aiki mai aikinta
kasuwa saboda tayi amfani da daman ta haƙa rami a garden din gidan ta binne layan da Godiya ta kawo
mata, bayan mai aikin ta tafi Momy ta zaga zuwa garden din gidan ta samu spot me kyau ta fara haƙa rami
da wuka, bayan ta haka yayi zurfi yanda take so sannan ta jefa layan ta mayar da ƙasan wajen ta dau wani
dutse ta dora dai dai wajen don kada a ga alamar an tono kasa, tap ta bude don wanke hannunta da wuƙan
da tayi using, Khaleesat ta karasa bakin window din dakin Momy jin ƙaran bude ruwan pampo, in ta gaji da
zaman dakin dama jikin window take zuwa ta tsaya tana kallon waje, ta tsaya jikin window din tana ta
kallon Momy dake ta wanke hannunta bayan ta wanke wuƙan, bayan ta gama ta kara komawa kusa da
dutsen tana seta sa da kyau ta yanda ko da wasa baza a ga tonannen ƙasa ba, sai kuma ta mike ta fara tsinko
doddoya dake Garden din, sannan tayi using wuƙan hannunta ta yanki pumpkin leaves isasshe bayan ta
gama ta bar garden din tana rike da ganyayyakin hannunta, babu abinda Khaleesat ta kawo a kai don
tunaninta ganye Momy taje diba a garden din, Momy na kai ganyayyakin kitchen sai ga su Meemah sun
dawo daga shopping din da ta aikesu su yi ma Khaleesat, dariya Momy ta dinga yi a parlor ganin wasu
shegun abayoyi masu saukin kudi da suka kwaso ma Khaleesat irin wanda ake dinkawa a kano, ga wasu
shegun dogayen riguna su ma masu arha, hatta inner wears da suka siyo duk very low quality ones ne, babu
wani abu na arziki da suka siyo ma Khaleesat, Momy na ci gaba da dariya tace "Duk maida su cikin ledojin
kawai na yafe ganin wannan tarkace haka karima, amma baku da kirki yaran nan" Aunty Karima na dariya
ta maida kayan cikin leda ta kulle tace "Su ne dai dai er talakawa ai Momy, da so kika yi ki ga abayan dubu
hamsin zuwa sama? Ai ita Meemah ma en gwanjo ta so mu je muyi selecting mata kawai" Dariya kawai
Momy take, ita kuwa Meemah danna wayarta kawai take don duk wani abu da ya shafi Khaleesat ko kadan
baya bata dariya, she just can't wait taga irin rabuwan da Abdul zai yi da Khaleesat don shine babban
abinda ke gabanta yanxu. Wajen karfe takwas da rabi Momy na zaune parlor da Abdul tana ta yi masa hira,
shi dai wayarsa kawai yake dannawa baya responding kamar ma bai san me take cewa ba, Momy ta kwalo
ma mai aikinta kira, Mai aikin ta taho da gudu tace "Na'am Hajiya?" Momy tace "Zaki ga Kankana da na
yanka a kitchen ki dauko ki kai ma Mamata a sama" Mai aikin tace "To Hajiya" Juyawa tayi ta koma
kitchen sai ga ta ta dawo rike da bowl din kankanan tana kallon Momy cikin ladabi tace "Amma Hajiya
dakin a kulle yake" Momy tace "A'a a bude yake tun daxu, ki je ki kai mata" Bayan mai aikin ta tafi ta kai
water melon din ta dawo ta tafi kitchen ta ci gaba da aikin da take, Momy ta dau wayarta tace "Bari in inyi
waya da Alhaji, daxu na ga kiransa ina kitchen wallahi" Shi dai Abdul bai ce mata komai ba har ta shiga
dakin dake downstairs ya bi ta da kallo... Bayan minti biyu ya mike ya nufi stairs direct ya tafi bangaren
Momy, yana bude kofar dakin Khaleesat dake zaune saman darduma bayan ta idar da sallah ta gama duk
addu'o'in da zata yi ta juya ta kalli kofar, sosai gabanta ya fadi bayan sun hada ido da Abdul, ya karasa cikin
dakin babu yabo babu fallasa yace "Ta shi mu je shopping...." Khaleesat da gabanta ke faduwa ta nuna
masa ledan da Momy ta kawo mata daxu duk da bata duba kayan ciki ba cikin sanyin murya tace "Ai
Momy ta sa an min shopping din, ka gan su can ma" Ya hade rai yace "Kee... Get up nace, i am not asking
for ur opinion" Ta sauke idonta ta mike tsaye da kyar ta dauke darduman tana linkewa, sosai taji hankalinta
ya tashi, a ranta ta dinga addu'an Allah ya kawo Momy dakin immediately, fixge darduman hannunta yayi
ganin it's taking her a whole eternity to fold, ya ajiyesa saman kujera sannan ya kama hannunta suka nufi
kofa fuskarsa a daure suka fita daga dakin, Khaleesat dai bin sa kawai take a tsorace, downstairs suka sauka
har sannan yana rike da hannunta, babu kowa a parlorn sai mai aiki dake goge goge a dining area, ya dau
makullin motarsa da ya bari kan center table, Khaleesat ta marairaice masa cikin rawan murya tace "Ya
Abdul Momy fa bata sani ba, kar ta shiga dakinta taga bana nan, kaga babu dadi haka" Wani kallon da yayi
mata yasa tayi shiru zuciyarta na bugawa, bata sake gigin ce masa komai ba har suka fita parlorn gidan
zuwa parking space, Khaleesat taji hawaye ya