Showing 135001 words to 138000 words out of 168506 words
mutane da shiga masarauta,sunansa ya sauya daga
almaz......sunansa ya koma FARRE ABBA JALAAL sunansa dana mahaifi". Jinjina kai
tamim yayi da wani irin nauyin dake gwada ya karbi dukkanin umarninta,ta miqe a
hankali tana takawa.
"Zan aiko da yalwa da wasu CFA din da dukkan adadin nauyin da kuke buqata....."
"Godiya nake uwar gijiyata" Ya fadi yana tattara dukka qarfin halinsa ya
miqe,daidai sanda almaz ya karkace ya koma saman lalallausar sofa din yayi
kwanciyarsa yana ji a ransa duk duniya bai taba jin abu me laushi kaman gadonsa na
can dakin ba da kuma wannan kujerar.
*AKHNAN*
Da qyar takai kanta daya daga cikin bedrooms dinta,ta kuma samu ta
zube saman gadon da yake shimfide da wata shimfidar alfarma tana tura kanta cikin
comforter din dake saman gadon tana jiran a buqaci amfani da ita.
Batasan yaya ba......bata kuma san daga ina ba,dukkan wani qwarin
gwiwarta ya soma kwaranyewa. Dukkan wata jarumta tata ta soma sulalewa tana barinta
da iya zallar halinta,abinda ya sanya wani irin kuka tsinke mata,a karo na farko
tun bayan data mallaki hankalin kanta da kuka me nauyi irin wannna me cike da
kadaici ya tsinke mata. Wani irin kadaici kawai takeji yana ratsata,tana maimaita
kiran sunan mammina. Ina mammina ta tafi ta barta a irin wannan yanayin?,a irin
wannan lokacin da tafi buqatarta sama da ko yaushe?,a irin wannan lokacin da komai
yake shirin jagule mata?.
Ko da imagination ba zata ita hakaito hakeem a mazaunin mijinta
ba......koda zata rasa soyayyar sultane ba zata iya aminta da hakeem a mazaunin
mijinta ba.
Hakeem fa?,mutumin da yafi dukkan mazan da suka taba zuwa don ganawa
da ita qansqanci?,mutumin da shine mafi qaranci matsayi......daukaka.....wayewa da
sanin ilimin zamani dame duniya take ciki?. Ba hakeem ba......koda wanda ya fishi
komai.....koda wanda zai iya cika sharudda ya kuma hada qualities din da takeso
bata jin zai samu amsa cikakken sunan miji a gareta,ballantana hakeem din da ko
cikin 'yan uwanta na jini ba zata lamunce masa ya samu ba.
Malamin addini fa?,me qarancin wayewa?,banda bai iya boko ba
sam.....wanda baisan komai ba sai karantarwa......baisan komai ba sai wa'azi?,bazai
taba iya tsaiwa a guraren data tsaya ba a duniya,cikin dubban yaruka.....cikin
dubban masu jajayen kunne......cikin qwarrarrun doctors masana masu tsananin
wayewa. Tana running company irin sahel couture taje ina da malamin addini?,tana
zuwa taruka na duniya da qasashen da suka isa,ta tsaya gabansu tayi magana da salon
harshen da yake burge kowa ya kuma girgiza kowa,ya daga darajarta......ina zataje
da malamin addinin da baisan kowacce kalar wayewa ba?.
Me yasa sultane bazai fahimta ba?,me yasa bazai gane babu kima ko guda
daya game da wannan tunanin nasa ba?.
Hankali kwance take takowa cikin gidan,a nutse kuma tana karantar akwai
wani abu daya canza tattare da gidan. Motsi da karsashin da kowa keyi yadan ja baya
kadan,abinda ya alamta mata akwai abinda ya faru tabbas da gaske kuma.
Sanda qafafunta suka taka sassanta yalwa ta hange tsaye tana jiran
isowarta,wanda ganin shigowarta ya sanya yalwa matsowa cikin girmamawa.
"Allah shi baki yawan rai......ina tunanin akwai matsala yau cikin gidan nan,akwai
damuwa" Yalwa tayi maganan da sautin da zai sanya ka tsammaci batasan komai ba,bata
da masaniyar komai daya faru.
"Me ya faru?" Mammina ta fadi tana zame takalmanta,daya daga cikin hadimanta ta
tsugunna tana kwashesu gami da ajiye mata wasu masu sauqi ta soma zura qafafunta a
ciki.
"Gimbiya akhnan ce.....ta shigo dazu a birkice tana nemanki,kiran sunanki kawai
takeyi". Sosai fuska da yanayin mammina ya sauya yana juyawa zuwa yanayi na razana.
"Me ya faru da ita?,me ya sameta?,me yasa ba wanda ya sanarmin?,wanne irin sakaci
ne wannan da rashin sanin martaba da muhimmancinta?,hakan yana nuna kenan ko bayan
babu raina babu wanda zai iya kula da ita?,ba wanda zai iya kula da damuwarta?,ina
morsa safiyya?,me yasa batayi komai akai ba?" Tayi maganganun cikin fadan daya
sanya kowa ya sake rissinar da kansa,suna jin tabbas su masu laifi ne,jikinsu kuma
yana sake yin sanyi. Dukkaninsu sunsan cewa akhnan din wata halitta ce me matuqar
muhimmanci a garesu......ita din wata halitta ce da damuwarta taba ta ko shiga
rayuwarta kayi mata wani abu na ba daidai ba babban kuskure ne a tare da kai.
"Muje na ganta" Mammina ta fadi tana sauya akalar tafiyarta zuwa kebantacciyar
hanyar da zata sadata da sassan akhnan.
Daga yanda taga dukka hadimanta a cure a guri daya ta tabbatar lallai
abun babbane,hankalinta ya tashi hankalin kowa ma a gidan ta tabbatar sai ya tashi.
Da alama ta shiga wannan yanayin nata na tsananin fushi da fusata,tasan kowa dole
yaji a jikinsa,komai nata kuma zai canza. Tako ina gaisuwa suke saukewa mammina
din,suna kuma sake rusunawa zuwa qasa.
"Me kukeyi a nan?,meye amfaninku da kuka barta ita daya a ciki kuka dawo nan?!" Ta
jefa musu tambayar a tsawace tana dubansu.
"Allah ya huci zuciyar giwa.......ita ta buqaci hakan,dole ne cika umarnin gimbiya
akhnan,mun nisanceta ne bawai don haka yake muradinmu ba" Birra ta fadi cikin
tsantsar ladabi. Shuru tayi dake nuna alamun tana calming fushinta,sannan ta juya a
hankali tana wucewa qofar farko da zata fara sadaka da sitting room da falukan
alfarma kafin kakai ga isa ainihin shiyyar bedrooms dinta.
Dan qaramin murmushi ta sauke,duka falukan ba gilmawar kowa sai na'urori
daketa aiki abinsu suna bada qara mara sauti sosai wadda bata da damuwa sam. Ta
dora hannunta kan qofar dakin data gani a bankade ko.maidata ta rufe bata samu
daman yi ba,ta tura da sallama,sannna ta lalubi makunnin hasken dakin ta kunna,take
haske ya gauraye dakin,daidai kuma sanda ta miqe daga saman gadon sukayi ido hudu
da mammina din.
Da sauri ta ture comforter din kuka yana sake narke mata,ta sauko da
sassarfa ta nufo mammina tana jin duk duniya damuwarta ta yaye da ganin mammina
kadai da tayi.
"Meye haka biftu?......me ya sameki?,waye ya sakaki kuka?" Dukka mammina ta hada
tambayoyin ta jefa mata su tana ware hannayenta akhnan din ta shige ciki tana sakin
wani kukan.
"Sultane ne mammina......sultane ne" Ta qarasa maganan da yanyin da zai gaya maka
zallar sakalci da gata data samu a dukkanin rayuwarta.
"Subhanallah......sultane dai kuma?,me kikayi masa?" Ta tambaya tana dan bubbuga
bayanta alamun lallashi.
(08187255862 lu'u lu'u paying)
"Don na sallami hakeem......bana sonshi mammina baiyimin ba,malamin addini ne fa
mara wayewa sam sam.....yanxu kina ganin irin wannan mijin ya dace da d'iyarki?" Ta
fada tana jin cewa matsalarta tazo qarshe. Ko kowa bai fahimceta ba mammina tana
fahimtarta,ko kowa bai kawo mata mafita cikin matsalolinta ba mammina tana kawo
mata,ko kowa bai goyi bayanta ba mammina tana goya,tsanani.....wahala ko dadi basa
sanyawa mammina ta janye mata ko ta daina goyuwa da bayanta.
Wannan karon ga mamakinta sai taji mammina na zameta daga
jikinta,abinda ya tilasta mata daga kanta a hankali tana duban mammina din cikin
zallar mamaki.
Mamakin ya sake ninkuwa yadda taga mammina na dubanta da wani irin
kallo,wannan tausayin.....wannan tausasawar.....wannan laushin dukka babu su. A
hankali mammina ta soma girgiza mata kai.
"Wannan karon.....idan har kin bijirewa maganan sultane,idan har kin kasa biyayya
wa umarnin sultane,to tabbas bana tare dake......". Mamaki ya tsayar da kukan
akhnan gami da wani dan siririn firgici daya ratsata.
"Mammina......ke kikamin alqawari fa". Kai ta daga a hankali tana takawa da baya.
"Nice akhnan......saidai akwai abubuwa da dama da suka tilastamin tunanin janye
wannan alqawarin........morsa safiyya,nice mutum ta farko da zata kalla wadda ta
zigaki ta kuma doraki akan turbar bijirewa maganan sultane....."
"Morsa safiyya!......morsa safiyya!......har yau har yanzun dai ita!......ita kadai
ce matsalata a dukka wani cikar muradina?,itace damuwata a dukka
burikana?!......qanwar uwata ce amma BA UWATA BACE!......ba itace ta haifeni ba,kin
yarda mammina WATA MACE CAN ta shiga tsakaninki da tausayin dake zuciyarki game da
'yarki?" Ta fadi da wani irin zafi bacin rai da kuma tarin gungun tsanar morsa
safiyya sabo daya bude shafinsa cikin kwanyarta.
Wani abu ne me girma ya motsa can qasan zuciyar mammina. Ta samu
nasarar dasa DASHE na farko,wani sabon babin sabon aikin da zai zame mata sharar
fage a dukkan komai da zai biyo baya.
"Akhnan......ko kinaso ko bakiso morsa safiyya wani bangarene me girma na
rayuwarki.......tana da matuqar muhimmanci a rayuwarki......ita din jininki
ce........wata sashe ce ta rayuwarki,jini iri daya ne yake yawo a jikinku......ko
baya ga wannan SULTANE zai iya shiga sahun mutanen dake zargin akwai sanya hannuna
kan dukkan wani abu da kikeyi,akwai sa hannuna akan duk wani abu da kike
aiwatarwa.......musamman idan hasashe na ya tabbata yi masa tunani akeyi.......ba
shine yake tunanin ba,bazanso bata wannan alaqar ba......bazanso rasa wannan yardar
da amincin da yayimin akanki ba,akan zan iya kula dake.....akan zan baki kalar
rayuwar da MAHAIFIYA zata bawa 'YARTA,wannan karon dole ki biyayyawa umarnin
sultane" Tana kaiwa fuskarta na nuna wani irin narkakken qauna da tausayin akhnan
saman fuskarta. Sai ta juya tana ficewa a dakin.
Sulalewa tayi kawai ta zauna gefan sofa,tana jin komai tana kuma ganin
komai kamar wata almara,kamar komai ba gaske bane. Yau ita mammina ta kwarewa
baya?. To amma still idanuwanta suna iya hangen raunin mammina cikin dukka
maganganunta,idanunta suna iya hangen wani abu me kama da qauna da kuma tausayinta
cikin ranta......wannan kawai ya isa ya tabbatar mata da gaske mammina zata
tilastata ne kawai tabi sultane saboda tsoron hukuncinsa......zata tilastata ne
tabi sultane saboda gudun xamowarsu masu laifuka dukkaninsu a gurinsa.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki
kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
✍🏽
*HUGUMANKU CE*
💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
PAGE 68
___________________________
Bononza bononza https://wa.link/l1gcz8
Assalamu alaikum yan uwa mata masu albarka
Zuzeam ventures zatayi promo karshen wannan watan har zuwa cikin watan nan me
kamawa insha allah
-Da 6k kachal zaa baki kaza da ciccibi da gari da tsumi da gumba pills shaki matse
masu kyau da ingancin dazai sakaki dawowa ki qara harma ki kawo wani,
-Da 11k zaa baki kaza full da ciccibi da gari da tsumi da gumba, da maganin sanyi
wannan promo ne akan murnar cika shekara 10 cif da fara sanaa a online Dan haka duk
wadda take bukatar shiga cikin wannan promo Dan samun wannan garabasa to tayi sauri
kafin ta kare
Kuma ku sani tsakani da Allah zaayi wannan promo komi me inganci ne
Kyau sosai zaa baku tsakani da Allah Idan kinada 4k ma zaa baki ciccibi kawai sai
gari da tsumi masu kyau da ingancin suma,
Dan haka duk wadda take da bukata kofa a bude take
Idan kinada Yan uwa da abokan arziki zaki iya tallata masu idan kin kawo mutun goma
suka shiga na 10k kinada package din 5k
Idan kin kawo mutun goma suka
Karku manta promo kwana 3 ne an kare insha Allah
___________________________
"Bazan iya ba wallahi......bazan iya auren hakeem ba......ban shirya
rayuwa qarqashin ikon kowa ba,gashin kaina zanci gaba daci.....halastaccen 'yanci
da babu takurawa ko kuma qunci a ciki" Ta fada tana girgiza kanta..
★★★Kwanaki biyun da suka biyo baya sun zamo wasu irin kwanaki ne da suka sauya
launi da kalar rayuwar wasu cikin gidan. A kwanakin komai na gidan yana nuna akwai
wani kwantaccen abu dake faruwa cikin gidan,kwanaki ne dake sake bawa ko tabbacin
da gaske akhnan itace zuciya kuma hasken gidan. Sai komai ya zama wani iri,kowa
cikin takatsantsan da walwalarsa yakeyi kada taci karo da yanayin da ake ciki a
wannan lokacin.
Kwana biyunnan cur ba wanda ta bari ya ganta,kaman yadda bata bari
taga kowa ba,koda aisa shehnaz ma.
Koda sultane baiyi wani yunqurin nemanta ko neman sake ji daga gareta
ba,ya riga ya gama yanke hukuncinsa a wannan karon,ya kuma tsayarwa da ransa ba
abinda zai sanyashi janyewa. Baya son ya bata kowacce irin dama da zata sakata jin
cewa akwai yuwuwar ya janye nufinsa ko ra'ayinsa,don haka hatta da mammina ko morsa
safiyya baima zauna yayi zancan da kowa ba,shirinsa kawai ya farayi na yadda komai
zai kasance.
Nannie kawai ya saurara har suka tattauna ta nemi ganinsa akan
batun,ranta a matuqar bace,hankalinta kuma dukka a dagule,cikin tsananin bacin rai
tana fadin.
"A wannan karon ka barni,sai naci mutuncin biftu......wai shinma dame aka halicceta
ne?,da qarfen lu'u lu'u ko na gold da zata dinga wulaqanta mutane masu daraja?,masu
darajanma irin hakeem......malamai magada annabawa?,masanin ilimin da zai kaika
tudun muntsira?.....fatan kuma kowanne musulmin kirki kenan?" Ta qarasa maganan a
sanyaye. Murmushi kadan sultane ya saki,irin murmushin dake cike da nutsuwa da
sanin ciwon kai.
"Duk maganan nan da kikeyi fatima bata baki ne.......karki cewa khadeejatu
komai,kulawa ma ai yabawa ce,tayi duk abinda zatayi,ban gani ba,bansan kuma abinda
zai saukeni daga wannan hukuncin dana yanke ba". Kai Nannie ta jinjina,hakan daya
fada da kuma tsaiwarsa akan hukuncinsa wannan karon ya mata dadi,amma can qasan
ranta tana jin wani dan rashin dadi kadan,kaman hakan zai zama takura da auren dole
ga akhnan din kenan?,bayan Shehnaz da aisa kowaccensu an bata dama ta fidda wanda
takeso?.
"Amma yaaya.......tun jiya aisa tacemin tana sassanta,taqi yarda ta fito taqi kuma
yarda taga kowa".
"Shirme kenan,tayita zama,idan ta gama zata gaji ya fito" Ya fada cikin rashin bawa
maganar wani cikakken muhimmanci.
"Yaaya" Nannie ta sake fada. A nutse sultane ya aza dubanshi a kanta,da alama
dukkan wannan qwarin ran da fadan da takeyi akan akhnan raunin nan irin na diya
mace yana tattare da ita.
"Ina saurarenki" Sultane ya fada yana tattarawa Nannie hankalinsa.
"Nace anya ba jinnu ba sihiri a al'amarin biftu?" Tayi maganar qwayar idanunta suna
nuna da dukka gaskiyarta take maganan. Shuru ya ratsa a tsakani na wasu
sakanni,kafin daga bisani sultane ya saki wani murmushi.
"To......gida dai irin namu ba za'a ce bamu da mutanen boye na gado ba,mutanen boye
na ainihin kan gidan ba,amma ba masu cutarwa ba,ba wandada zasu dinge bige mana
d'iyoyi suna faduwa ba suna sakasu fagamniya ba......sihiri kuwa ba wani a waje
daya isa ya jefi daya daga cikin zuri'armu ya kamashi.......saina cikin gidan,a
cikinmu kuwa bana zaton akwai wanda zaiwa biftu wani mummunan aiki.....ko akwai?"
Sultane ya qarashe tambayar yana duban nannie.
Kai ta girgiza a hankali,dukka maganganunsa tasan haka suke,ko ita
kanta shaida ne,ta taba rayuwa da kishiyar da tace nata aikin asiri da jifa
ne,qarshe ya koma mata da wani irin zazzafan haukan data dinga yinsa har ya zame
mata ajali. Tabbas ga dan waje cinsu da asiri bame yuwuwa bane,cikin gida kuwa
tsakanin ahalin sultane,takun saqa da sabani irin na harshe da haqori dole
akwaishi......amma bata tunanin asiri a ciki.
To shin ma idan akace da asirin waye zaiwa biftu?. Morsa safiyya duk
duniya bayan sultane tafi kowa kusanci na jini da akhnan.....ba yadda za'ayi uwa ta
jefi diyarta da asiri. Mammina kuwa......wani abu ne da sam hankali bazai dauka
ba......sam tunani da sharrin me sharri ma bazai biyo ta gurin ba. Matar data zame
mata uwa tun tana da shekaru hudu a duniya?......ta zame mata wata irin garkuwa
abar misali. Tabata zaifi zuwanma mutum da sauqi akan taba akhnan. Dukka tunaninta
da damuwarta kan yadda akhnan zata rayu cikin 'yanci da walwala ne,to waye zai
aikata wani mugun abu a kanta cikin mutum biyun???. Qatuwar tambayar data sanya ta
bawa kanta amsar yin tambayar ma ba abu bane me ma'ana.
"Ki rabu da ita kawai,zatayi dukka ta gama,munyi aure da safiyya kuma mun zauna
shigen wannan zaman,amma yanxun bai zama tarihi ba?" Ya fadi yana duban nannie.
Murmushi ya subucewa nannie din harma sultane din yana tayata. Ta sani shima ya
sani,kowannensu ya tuna wani abu ne daya shude da zamewarsa tarihi ya zame musu
wani abun tunawa da sanya dariya.
*KWANA NA UKU*
Yammaci ne dake dauke da wani irin lullumi da ya bada wani sassanyan
hadari daya wanzar da canzawar launin sarararin samiya zuwa ruwan toka toka. A
dukka sasannin qasashe da suka samu irin wannan yanayin daya kasance tamkar wani
sassauci ko rahama daga ubangiji na zafin daya dinga koda mutane a kwana biyun da
suka shude,irin zafin damina dake tayar da hankali ga duk mutumin da bayason zafi.
Daidai lokacin da mammina ke zaune farfajiyarta ta musamman,tana kuma ganawa da
baqin data zabi iya wadanda take buqatar ganawar dasu.
Su uku ne a yanzun a gurin,Shehnaz aisa mammina din sai kuma yalwa data
kasancd mutum ta hudun.
Dukkaninsu saman qawatattun kujerun gurin suke,hakanan akwai yawaitar
kayan marmari dana maqulashe aka zube a gurin da duk me buqata ya dauka yayi amfani
dasu.
"Ina jinku 'yammatan sultane" Mammina data ajiye wayar data gama amsawa ta fada
cikin mayalwacin murmushi gami da nuna tsantsar kulawa a kansu.
Aisa ce ta ajiye wayarta a gefe,sannan ta jawo wani file ta tura
gaban mammina.
"Mammina.......game da sabbin muqamai da ma'aikatan da aka dora ne a sahel
couture......munso muyi maganan da biftu amma har yanzu hankalinta bai jikinta,ba
wanda yake samun damar ganinta ma". Ido ta zubawa file din kafin ta dubi aisa cikin
mamaki.
"Wani abunne yake faruwa a sahel din?". Tayi tambayar da yanayin dake nuna zallar
kulawa.
(08187255862 lu'u lu'u paying)
"A zahiri ba wani damuwa bace ta fili" Shehnaz ta fadi kai tsaye.
"To me ya kawo qorafin 'yammata?" Mammina ta fadi tana sanya yalwa bude mata file
din tana bibiyar rubutun ciki.
Dukkaninsu duban mamminan suke suna jiran ta kammala,cikin qasa da
mintuna ta gama,yalwa ta maida ta rufe.
"Ban gano wani damuwa ba a ciki 'yammata" Ta sake fadi da wannan shimfidadden
murmushin kan fuskarta.
"Akwai abubuwa da yawa muke buqatar qarin haske mammina.....nidai bazanyi qarya
ba,ta bangaren office dina kusan komai a makance yake tafiya,ba komai na fiya
fahimta ba,akwai muqaman da aka bayar kuma da suna buqatar dogon nazari kafin a
bawa wadanda aka bawa din,ko kuma a jira dawowar