Showing 102001 words to 105000 words out of 168506 words
fargaba ta fara
ratsata sanda suke nufar sassan sultane din. Tsinkewa kawai takeji zuciyarta tanayi
zuwa pieces a cikin qirjinta.
Ta fahimci hakan mammina.......saita damqe hannunta da suke cikin nata
tana magana qasa qasa.
"Karkiji tsoro......ina tare dake" Maganar data sake saukar da wani dan guntun
sassauci kenan cikin ranta.
To amma daga sanda mammina tayi sallama cikin parlor din sultane din,ta
kuma hangi morsa safiyyah zaune a gefansa tana sake tsiyaya masa ruwan
markadaddiyar apple sai taji tana neman rasa duk wani qwarin gwiwar tata saboda
abubuwa biyu.
Abu na farko yanayin fuskar sultane din. Wani baqon yanayi ne da sai me
zuzzurfan kusanci dashi......me zuzzurfan hangen nesa da tsinkaye kuma shine zai
iya karantar kwantaccen bacin ran dake kai kawo saman fuskar tasa. Duk da cewa ga
me gajeran nazari wanda ba wata zuzzurfar alaqa Taakaninsa da sultane din zai dauka
yanayi ne kawai irin na yau da gobe.
Morsa safiyyah. ....wanzuwarta a gurin gabanin zuwansu ya sake rusa
mata duk wani kyakkyawan zaton da ta shigo dashi.
Ko sau daya......koda lokaci qwaya daya bata taba saqa alkhairi akan
matar ba. Da yawan dagulewar al'amuranta tana alaqantashi da morsa safiyya
din,alkhairi bai taba gifta mata ba muddin tana a gurin.
Idanunta ta dauke a hankali tana lumshesu,tana kuma takawa zuwa ga
sultane din bisa qwarin gwiwar mammina da kalaman da take gaya mata qasa qasa.
Kalaman da ba lallai kai dake kallonsu kai tsaye ka dauka wani magana takeyi da
ita.
Cikin qasa da second uku wata irin shimfidaddiyar fara'a ta wanzu a
fuskar mammina,idanunta tsakanin sultane da morsa safiyya.
"Sannu da hidima" Tace da morsa safiyya dake qoqarin rufe tambulan din lemon data
gama zubawa sultane.
"Kece da sannu zaituna....." Ta amsa mata da salon daya sanya mammina jin wani iri.
Kasancewarta mace me wata irin halitta da tasha banban data mata da yawa,irin matan
nan da sukan iya shanye komai su kuma jure jin komai daga bakin wanda sukaso,saita
maida mata da martanin murmushin,ta kuma qarasa a nutse daura da sultane tana yiwa
akhnan mazauni daura dashi din,daidai sanda take cewa.
"Muna neman sassauci da afuwa ranka ya dade........na shigo ba tare da ka nema haka
daga gurina ba......zuciyar d'iyata cike take da fargaba da kuma zullumi,bata da
qwarin gwiwar tunkarar mahaifinta sam a wannan ranar" Takai qarshen zancan tana
zame yatsunta daga cikin na akhnan,ta kuma ja baya kadan alamun dake nuna tafiya
zatayi.
"Ina zuwa?" Sultane din ya tambaya kanshi tsaye yana ajiye tambulan din hannunsa.
Duk da yadda morsa taqi jinin yadda dukkan wata kebantacciyar alaqa ko
dangantaka data shafesu mammina ke ciki tsulum tsulum,amma ita kanta a yau din tafi
buqatar zaman mammina akan fitarta.
"Komai na d'iyarkin yanzu dake za'aci gaga da yinsa......domin shaida ta zama a
wuyanki" Ya qarasa maganar yana gyara zamansa,irin zaman cikakken basarake,yana
mata kuma nuni da kujerar dake kusa da morsa safiyya.
A hankali ta dawo a nutse,taqi bari wannan murmushin nata yabar kan
fuskarta,ta zauna a nutse tana fadin.
(08187255862 lu'u lu'u paying)
"Lamarin d'a da uba koda mu iyaye ba kasafai aka fiya son saka kai a ciki
ba......shi yasa ban tsaurara ba wajen son sanin laifin da ayau tayi ba". Ta
qarasa maganar tana sadda kanta qasa a girmame.
"Bana tunanin tsakanin wannan awannin abinda tayin zai buya daga idanu da kunnen
sauran masarautu........" Yayi maganar cikin bagararwa,yana karbar toothpick daga
hannun morsa wadda ta miqa masa,dukka tana yunqurin shanye abinda ke taso
masa.......tana ta qoqarin shanye bacin ranta ne kawai da controlling din kanta.
Wacce irin gurbatacciyar soyayya ce wannan?,wacce irin mayaudariyar
qauna ce ta banza da wofi?.......wanne irin lullubin biri ne wannan?,wanne irin
nau'in kisan mummuqe ne wannan?. Dukka lokaci daya morsa safiyya ta yiwa kanta
wadannan tambayoyin daidai sanda take zube kallonta kai tsaye akan mammina din
tamkar a fili tayi mata dukka wadannan tambayoyin.
Tambayoyine da zataso ace ba cikin ranta ta furtasu ba,tambayoyine da
take buqatar bayyanasu da sautinsa don sultane yaji........to amma kuma fitar tasu
tayi imanin ba wani sauyi ko gagarumar rawar da zai taka da zata kawo irin canjin
da takeso.
A jikinta mammina din taji?,ko kuma tana shirye da karban kallo
makamancin wannan daga gurin morsa din?,sai kawai ta daga nata idanun,suka kuma
fada cikin na morsa safiyya.
A cikin su biyun,ba wanda bai tantancewa kansa kalar kallon da dan
uwansa yakeyi masa ba.......ba wanda bai qissima abubuwa da dama ba,amma kuma sai
mammina din ta maye gurbin kallon da jifan morsa Safiyya da wani irin murmushi da
ba komai cikinsa sai zallar nuna sanyi da rashin daukan abubuwa da zafi,sannna ta
cire idanuwanta daga cikin nata,tana maida dubanta ga sultane din da ayau yake
zaune cikinsu da fuskar da yake zama a fadarsa cikin talakawansa.
"Ya kukayi da abood ramadan?" Ya jefa tambayar ga akhnan,wadda banbamcinta da
tambayar awanni nawa ya rage ta mutu kadanne.
Dame zata amsawa sultane?,bayan tayi imanin yasan komai.....ya kuma ji
komai.......yanayinsa kadai ya gaya mata hakan. Shuru parlor din ya dauka,tamkar
babu wani sauran ne rai daya rage a gurin.
"Ya kukayi da abood nace!" Sultane ya sake tambayarta da wata irin tsawa data kada
'ya'yan hanjin dukka su uku dake gurin,saboda wata dabi'a ce dake baquwa ga dukka
halayyar sultane din.
"Bap......bapp.......iii"
"Baiyi miki ba" Ya fadi bawai da sigar tambayarta ba......a'ah da sigar bada amsa
ta kai tsaye.
Sake yin qasa tayi da kanta tana jin kamar zata narke,tana jin dama
qasa zata tsage mata tabbas da zata shiga ciki ta buya daga tuhume tuhumen sultane
din.
"Wannan shine ya baki qwarin gwiwar daga hannu ki mari baligin namiji?!!!!" Ya daka
mata wata sabuwar tsawar,abinda ya sanyata curewa guri daya tana kuma cukuikuye
mammina duk da dan nisan tazarar dake tsakaninsu.
A lissafin rayuwarta gaba daya,sau daya tak zata iya tuna an taba
mata tsawa. Tsawa......fada ballantana uwa uba dukka dukkansu wani abune sabo kuma
baqo cikin dictionary din rayuwarta.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki
kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer π³πͺ*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITAπ*
βπ½
*HUGUMANKU CE*
π *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*π
*H U G U M A*
PAGE 50
___________________________
Bononza bononza https://wa.link/l1gcz8
Assalamu alaikum yan uwa mata masu albarka
Zuzeam ventures zatayi promo karshen wannan watan har zuwa cikin watan nan me
kamawa insha allah
-Da 6k kachal zaa baki kaza da ciccibi da gari da tsumi da gumba pills shaki matse
masu kyau da ingancin dazai sakaki dawowa ki qara harma ki kawo wani,
-Da 11k zaa baki kaza full da ciccibi da gari da tsumi da gumba, da maganin sanyi
wannan promo ne akan murnar cika shekara 10 cif da fara sanaa a online Dan haka duk
wadda take bukatar shiga cikin wannan promo Dan samun wannan garabasa to tayi sauri
kafin ta kare
Kuma ku sani tsakani da Allah zaayi wannan promo komi me inganci ne
Kyau sosai zaa baku tsakani da Allah Idan kinada 4k ma zaa baki ciccibi kawai sai
gari da tsumi masu kyau da ingancin suma,
Dan haka duk wadda take da bukata kofa a bude take
Idan kinada Yan uwa da abokan arziki zaki iya tallata masu idan kin kawo mutun goma
suka shiga na 10k kinada package din 5k
Idan kin kawo mutun goma suka
Karku manta promo kwana 3 ne an kare insha Allah
____________________________
"Bappi........" Ta kira sunansa da wani sauti da ya daki zuciyarsa a take
kuma ya karyata,saidai duk da hakan bai bata koda space qwaya daya da zata fahimci
hakan ba.
"Karki sake kiran sunana........"
"Afuwa ranka ya dade.......afuwa,a huce haka" Mammina ta furta cikin kwantar da
murya,tana kuma tarairayo akhnan sosai cikin jikinta tana qoqarin daga Fuskarta.
Hawayen dake malala saman Fuskarta ya sake karyasu,saidai tsakanin
sultane da morsa safiyya ba wanda ya bata daman karantar hakan,yayin da morsa
safiyya ke bin mammina da kallo,wadda ke qoqarin tsaida hawayen akhnan,nata idanun
suna cika da hawayen da suka soma neman fitowa.
Sosai mammina din ta rungume akhnan din,hawaye suna kubce mata.
"Saketa ta gama amsa tamanyoyina!" Sultane ya fada cikin dakewar zuciya da
kakkauran sauti,sai mammina din ta zame akhnan din daga jikinta,saidai kuma ta gaza
sakin hannuwanta kamar wadda aka ce za'a rabasu.
Idanu morsa safiyya ta janye,tana jan lahula wala quwwata illa billa a
ranta. Komai tana ganinsa ne kamar almara,dabi'u da acting din mammina yana sake
kashe mata duk wani karsashi nata.
Daga sanda baqon yazo ya tafi,bata bawa armelle ko kowa na kusa da ita
kowacce dama ba bare taji abinda ya faru. Fargaba ce taf ranta data hanata
sakewa,sai kawai tayi amfani da wannan damar,ta shiga kitchen da kanta,ta soma
hadawa sultane abinci kaman yadda takanyi lokaci bayan lokaci.
Gurinsa takeson zuwa,amma bataso ta tunkareshi haka kai tsaye,don
batasan ya zata taras dashi ba,wanne yanayi zata samu da zai bata hasken dukkan
abinda ke faruwa?.
Yadda ta samu fuskarsa duk da yadda yake qoqarin tarbarta da girmamawa
amma gwiwarta ta sanyaya.......yanzun ta fahimci komai daya faru.....mammina kuma
na sake kasheta da wannan salon nata......salon nan dai na shekara da
shekaru.......wannan salon da take tunanin ya sanyata ta cimma gaci,gacin da a
wajen morsa faduwa ce wanwar.......lokaci! Shine keda kowanne hisabi......shine
gwanin bayyana komai.
Dukkaninsu sun dauka sultane ya gama duk wata magana da zaiyin,amma
kuma yadda bai basu izini ko umarnin tafiya ba ya tabbatar musu akwai sauran magana
a ranshi.
"Kin bijirewa abood?".
"Tabata yaso yayi ranka ya dade.......taba akhnan babban zunubi ne kaima ka sani"
Mammina ta furta tana sake yin qasa da kanta,saidai yanayin maganarta kadai ya nuna
akwai zafi cikin maganar data fada din.
Wannan karon kasa daurewa morsa tayi,ta daga kanta tana duban akhnan
dake qudundune tana sharar hawaye,abinda ta mance rabon data gani a idanun akhnan.
Kalmar ta yiwa kunnuwan morsa nauyi da girma,ta sake duban idanun mammina dake
kallon qasa. Idan ita din uwace ga akhnan,kuma ya tabbata abood ya taba
jikinta......shin zata bari duniya taji?,zata kuma gayawa wani maganar koda
mahaifin da yayi silar zuwanta duniya ne?.
Ga yarinya irin akhnan,fitar wannan lafazin mummunan batanci ne da kuma
tabo da zai iya yaduwa yanzu yanzu kamar wutar daji.
Ko daya maganarta bata zaunawa morsa safiyya ba.....duk duniya,koda
mammina dake tutiyar ta raineta ta kuma girmar da ita bata tunaninta ta fita
karantarta. Akwai wasu dabi'u na SAFEENA akwai wasu dabi'u na DIORY FAMILY da suke
cikin jininta,wadanda suka cakuda da dabi'u da halayen SARAUTA cikin jininta.
Bata tunanin akwai wani d'a namiji da akhnan zatayi doguwar tsaiwa
dashi,doguwar tsaiwar kuma da zata bashi daman taba wani sashe na jikinta. Wannan
halin nata shi kadai ne yake bata nutsuwa da kwanciyar hankali a zamanta a
Niamey,banda wannan tabbas koda dawowarta agadez ta zauna kusa dasu yana nufin
mutuwar aurenta da sultane......koda hakan zai zama silar daukar wuqa ga akhnan ta
yanka wuyanta,to tabbas zatayi silar dawowarta agadez.
Ta sani,tana da wani irin jin kai,tana da wata irin ajiyayyar izza da
bata tunanin akwai wani namiji ma daya taba ganin koda singalalin hannunta bare
jikinta,ballantana hakan ya zama sanadin da zaikai hannunsa jikinta. Akwai dai wani
abu daban daya faru......amma banda zancan taba jiki.
"Kin tsallake abood.....ina me miki albishir din kin rasashi kenan.......zabinmu na
gobe zaizo gurinki.......daga sanda yazo kuma ki kalleshi da idanun da mace ke
kallon mijinta.........wannan shine maganata ta qarshe dake". Sultane ya fadi.
Wani irin nauyi taji kanta yayi mata,qamqam ta riqe mammina tana jin
wani bala'i yana kewaya kanta.
"Sultane bazai haqura ba?,ba zai haqura ba mammina......na rantse har yanzu babu
irin mijin da........." Ya isa akhnan,ki godiya ki wuce muje" Ta fadi tana qoqarin
dagata,yayin da sultane din yayi kaman baisan da wanzuwarsu a gurin ba,ya gyara
kashingidarsa yana maida idanunsa ga tv din dake haska labarai daga France 24.
Da wani irin kallo morsa ta daga idanunta tana duban mammina sanda
suka fara takawa.
"Zaituna" Ta kirata da yanayin da ya fusgi hankalin mammina din qwarai. Ta jima
bataji wannan sunan saman harshen morsa safiyya ba,tun a wasu shekaru masu dan yawa
can baya da suka shude.
"Maganar taba jiki akan kowacce diya mace zubewar kima da martabarta
ne.........inason wannan maganar ya shafe daka bakinki shafewa na har abada" Tayi
maganar da harshe dake nuna gargadi.
Wani irin zazzafan kallo ta zubewa morsa din tana kafeta da idanu. Sai
kuma ta saki murmushi gami da sanyaya kallonta akan morsa din.
"Kinfi gaban haka ai,kina iya bada umarni nabi,akhnan nan kuma diyarki halak
malak,diyar da kinfini iko da kusaci da ita,ayimin afuwa" Ta fadi tana dan rusunawa
kafin ta kama akhnan da zummar su wuce.
Zamewa kadan akhnan tayi daga riqon mammina.
"Me kikeyi na ba daidai bane?,ko yaushe baki iya ba?,ko yaushe kome zaki mata ba
daidai bane?" Akhnan ta fadi a zafafe.
Fes ya fahimci wannan fushin,wannan taurin kanne ya motsa,saita riqeta
sosai
"Indai na isa dake muje kawai" Ta fada tana duban tsakiyar idanunta.
Wani sauka taji ta soma yi,ba musu ta juya a hankali tana takawa
mammina na take mata baya.
(08187255862 lu'u lu'u paying)
Qasa da kanta morsa safiyya tayi,don taji dukkan abinda akhnan din ke
fadi. Wani irin d'aci ke zarcewa maqogoronta tun daga saman harshenta,kalar d'acin
da jinsa ya zame mata jiki,amma har yanxu ta kasa daina jinsa.
"Safiyya" Sultane ya kirata a tausashe yana tsareta da ido.
"Allah ya taimakeka" Ta furta a nutse tana motsa labbanta da tun dazun taji sunyi
mata nauyi. Sarqafewa idanuwansu sukayi guri daya ita dashi,kafin ya janye nata
idanun zuwa wani sashe na daban.
Ya sani,shurun safiyya yana nufin abubuwa da dama,duk da cewa ba komai
take iya yiwa shurun ba,ba kuma komai take iya ajiyarsa a ranta ba......amma muddin
akace tayi shuru,to tayi shurunne,ba kuma zata qara magantuwa akan komai ba.
Ta sani baiji duk abinda akhnan ke fadi ba,don sautinta bame qarfi
bane duk iyakar inda takai ga yin magana cikin bacin rai,a daidai lokacin kuma
hankalinsa ya tafi sosai akan wayarsa da batasan me ya janye masa hankali akan
wayar haka karon farko ba.
"In sha Allah......zan tabbatar da zamana mahaifi kaman kowanne uba.......in sha
Allah" Ya fada yanason karanto wani abu ko yaya dake ranta. Sake daga kanta tayi
tana sakin murmushi a hankali kafin tace.
"Allah ya baka iko.....ya qarfafeka a dukka lamuranka" Idonsa ya lunshe shima yana
gyada kai.
"Ameen..........yaghana ta dawo.......yanzun nan suna filin jirgi". Wani murmushi
ne ya subuce mata,wanda sam bata ma shirya fitarsa ba.
"Alhamdulillah" Ta fada a fili walwalarta tana qaruwa. Watanni bakwai da sati shida
kenan da barin yaghana masarautar agadez,watanni bakwai din da suka dinga zuwarma
morsa safiyya da wani irin tsanani,bata taba zaton yaghana tana da wani muhimmanci
me girma haka a rayuwarta ba sai sanda tayi nesa dasu. Duk da kusan cikin kowanne
motsi da kai kawo a masarautar tana tare dasu,amma wannan nisan dai bai canza daga
yadda yake ba.
Yaji dadin yadda karon farko albishir dinsa ya saukar mata da fara'a d
walwala,ya gusar da wannan yanayin daga fuskarta,sai yadan tsokaneta kadan.
"Yanzu zami fara cike takardu kafin samun damar ganinki kenan,tunda yaghana ta
dawo?" Murmushi tayi tana girgiza kai.
"Duk muhimmanci da yaghana ke dashi,bana tunanin ta kama qafar naka". Shuru ya
danyi yana jinjina kai,duk da yana kokwanto a maganarta.
" Yanzu sai ina kenan?" Ya tambayi safiyya dake gyara babbar rigar da take
ta'ammali da ita a duk sanda zata baro sassanta don sake suturce jikinta.
"Ba wanda ya gayawa isowarta yau,ina tunanin harkai......dole akwai buqatar shirin
gaggawa" Ta kammala fada tana rufe jikinta ruf zagayayyar fuskarta dake yawan tuna
masa da safeena ta bayyana. Sai yaja numfashar cikin hunhunsa sannan yace.
" A sauka lafiya"
"Godiya nake" Ta furta cikin rusunawa ta juya tana takawa da wannan nutsuwar tata
da ba abinda ya banbantata data safeena.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki
kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer π³πͺ*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITAπ*
βπ½
*HUGUMANKU CE*
π *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*π
*H U G U M A*
PAGE 51
___________________________
*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa
wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group
namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
___________________________
*AKHNAN*
"Tayi nasara.......tayi nasara mammina......tayi nasarar shiga tsakanina da
mahaifina,ki gayamin mammina.......wai da gaske ne?,da gaske ne wannan alaqar da
kike cewa akwai a tsakaninmu?,da gaske ita din uwace a gurina?". Akhnan da