Showing 66001 words to 69000 words out of 168506 words
gwada dukkan wasu dabaru ja tsaida doki a irin wannan yanayin.
Dabararta ko daya batayi ba,firgici ya sake shigarta,tasan irin wannan
yanayin idan doki ya shiga iya controlling dinsa sai Allah. Zuwa sannan hankulan
mutane sun fara yowa kanta,musamman hadimanta da masu tsaronta wadanda suke da
alhakin kula da lafiyarta.
Sosai hankula sukayo kanta,al'ummarmu da son daukan abubuwa idan suka
faru,da son ace sune suka fara dauka ko suka fara haskawa tuni suka fara nadar
yadda abun yake kasancewa.
Da wasu dawakan aka soma bin nata dokin da zummar shan
gabansa,saidai hakan ya sake zama kamar wani qaimi suka bashi,don tunaninsa yana
sake bashi anci gaba da wasanne......ana kuma son cimmasu,yanason cika umarnin uwar
dakinsa ne kawai na tserewa duk wata halitta da zata wucesu,bama halittar doki dan
uwansa kawai ba.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki
kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer π³πͺ*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITAπ*
βπ½
*HUGUMANKU CE*
π *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*π
*H U G U M A*
PAGE 33
____________________________
*_M&A EGYPTIAN ABAYAS_*
*Assalamualaikum*
*_Ina dandazon tawagar gayyar MATA 'YAN QWALISA?_*
*_WADANDA SUKAYI AMANNA DA ADO SUNE MUTUNCIN D'IYA MACE?_*ππ₯»
*Ina masu son sari ko siyan daya na Egyptian abaya masu quality su iso garesu cikin
Aminci???*
*M&A EGYPTIAN ABAYA itace zabinku NA FARKO*
*kuse ABAYAS takanas kuma kai tsaye DAGA EGYPT su iso gareku cikin kasa da kwana
βπ½
goma KACAL! *
*_Ina masu son siyan abaya Amma Kuma basuda halin siya lokaci daya?_*
*_zaki iya ringa biya ahankali har ki kammala abaki abayarki cikin aminci_*ππ½
*Sannan gamasu San siyan airfreshener a farashi mai sauki muna dasu*
*muna turo da mayukan kitso original AMLA da VATIKA*
*Idan kana da wani personal shopping dakakesan ayi ma duk munayi CIKIN QASAR EGYPT
da yardar Allah*
+20 114 341 0873 ko kuma
0810 959 7791
https://chat.whatsapp.com/Hm9HBCXeyfjFDwi3OPSFqP?mode=wwt
____________________________
Cak yayi a gurin yana kallon yadda suke bata kashi a tsakaninsu. Idanunsa
ya dauke daga gurin,bacin ransa yana sake ninkuwa.
Tseren doki da mace?,macen ma irin wannan da ba gama sanin yadda tsarin
halittar dawakai da yadda ake hora doki da bashi umarni tayi ba?.
"Kaje kace musu su tsaida dukkanin mutanen da suke binta" Haisam ya motsa labbansa
yana furtawa omari dake tsaye kusa da dokinsa cikin bacin rai.
Karon farko tun bayan wani lokaci da omari yaga shimfidadden bacin rai
akan fuskar haisam din,sai ya juya a hankali cikin sanyin jiki yana nufar gurin
masu bada sanarwa a wajen.
"Kowa ya dakata!.....a dakata.....mahayan dawakai duka su fita a filin" Sanarwa
data isa kunnuwansu kenan. Da yawansu abun bai musu dadi ba.....suna cike kuma da
kokwanton yadda zasu bari dokin yaci gaba da galabaitar da ita. Wasu a cikinsu kuwa
tuni sun fara hasashen irin tarin kadara da dukiyar da zasu mallaka sanadin tsaida
wannan dokin.
Tabbas sunsan cewa muddin ka zama silar tsiranta.......Allah ne kadai
yasan daukakar da zaka samu a wajen sultane of agadez,don haka ba tare da abun ya
musu dadi ba kowa ya janye abun hawansa daga filin,filin ya zamana ba kowa,daga
dokin nata dake sake rikicewa,sai haisam da yayi tsaye saman nasa dokin yana
dubanta.
Idanuwa hankula da wayoyin dake tsakiyar filin suna nadar abinda ke
faruwa Allah yayi yawa dasu. Da yawansu kuma sai suka maida daukar LIVE kai tsaye
kenan daga hippodrome Niamey,wannan saqon ya bada notification a wayar tarin
miliyoyi kuma dubbannin al'umma,kai tsaye kuma ya fada wayar falaak dake kwance
cikin sofa tana qoqarin duba tafsirin wata aya a YouTube dinta,notification daga
channel din SAUTI HIKIMA ya bayyana daga saman wayartata,sai kawai ta samu kanta da
dannawa ta shiga ganin live video ne.
Da fari bata fahimci komai ba,illa dai gudun da dokin yakeyi da
matashiyar a samanta itama sai da taji ya tsinka mata Zuciya. Tana shirin sauka
sunan yaja hankalinta. Princess khadeeja muhammad hammud(akhnan),sai kuma idanunta
suka sauka akan comment da mutanen dake kan live din.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Falaak ta fadi tana fidda dukka idanunta cikin
tsananin tsoro,sannan ta sauka daga saman sofa din da wani irin gaggawa tana
qwalawa momma kira a gaggauce.
Kusan kowa ya sare a wajen......yana ganin shima bazai iya tsaidashi
ba,ganin yana tsaye kyam akan nashi dokin,ko saukowa baiyi ba.
Wucewar farko ya bawa dokin wani sauti da ita kadai ta jishi,sautin da
yafi kama da fito saidai ba fito bane.......ya sake wucewa a karo na
biyu.......daya hangi yana shirin zagayawa karo na uku,sai ya saki linzamin nasa
dokin ya diro daga samansa ya tsaya saman qafafunsa,ya riqe linzamin yana takawa
dashi a hankali zuwa wannan iyakar yayi tsaye yana kallon yadda dokin yake tayar da
qura yana nufoshi da gudun da ya rage da maganar daya masa dazu daga kaso dari
cikin dari zuwa kaso saba'in cikin dari.
Baya kadan yaja,sannan ya zube a qasa ya kafu akan gwiwoyinsa yana daga
hannuwansa sama da wani irin yare da yasan ana tsaida dokunan hadaddiyar daular
larabawa wato dubai.
Duk da itace a saman dokin......duk da irin birkicewar data gama yi
amma hakan bai hanata hasashen yadda nan da 'yan mintuna ko sakanni dokin nata zai
murqesheshi yabi ta kansa ba. Tuna iya adadin yadda zai murjeshi ya canza masa
kamanni kawai ya sanya tsigar jikinta zubawa. Wanne irin rawar kai ko tsautsayi
koma dai tace qarar kwana ce zata sakashi tsaiwa haka gaban thunder a irin wannan
yanayin?.
Daidai imda tunaninta ya katse daidai sanda thunder din yaja wani irin
birki daya kusa sakata fadowa ta gaba,bata kuma gama daidaituwa ba ya saki wata
haniniya yana daga qafafuwansa na gaba sama,abinda ya sakata yin baya gaba daya ta
tafi suuuu zata daki qasa.
"Innalillahi wa 'inna ilaihi raji'un" Momma safiyya ta furta tana miqewa da wata
irin razana......dukkan gabanta suka dauki rawa,zuciyarta na wani irin rawa itama
kamar zata tsinke,yayin da falaak ta ruqunqume momma din da kyau wani irin tsoro
yana cikata.
Yayi imanin idan har ta fado a irin wannan yanayin ba abinda zai hana
qashin qugunta tabuwa koma ta rasa lakarta gaba daya........yana matuqar qyamatar
taba koda yatsar daba halal bace......amma kuma indai ya bari ta hadu da matsala
daya cikin biyunnan ya tabbatar yana da nashi laifin a gurin Allah,wannan ya masa
qaimi,cikin wata irin azama kar cirar walqiya ya isa gurin yana tokare kansa da
qafarsa dake cikin boot,ya kuma miqa hannunsa guda daya ta fado akai,ta mirgina
gaba daya ta fado jikinsa da wani irin matsanancin bugun zuciya daya bayyana a
dukka gabanta da suke rawa.
Iya qwayar idanunta kawai ya iya gani data fito ta tsakiyar helmet din
kanta,ya zareta daga jikinsa da sauri yana tsaidata saman qafafunta gami da furta.
"Astagfirullah wa'atubu ilaih" Da sautin daya tsaya iya saman labbansa,yanajin
istigfarin yana zarcewa har cikin zuciyarsa.
Tuni hadimanta suka fara bullowa da sauran ma'aikatan da hukumar wasan
suna cika filin. A nutse yayi taku biyu baya sannan ya juya da zafin nama yana
gyara zaman helmet dinsa yana takawa a zafafe da dukka kuzarinsa yana barin gurin.
Duk takunsa daya idanunta yana kanshi.......duk da yawan jama'ar dake
gabanta,wanda dukkaninsu sun iso ne su sake tabbatar da saukarta lafiya qalau.
Kowanne taku nasa daya sai ya tada qura saboda karsashi da energy din da yake
dashi,sannu a hankali har ya saje cikin dubbannin mutane ya bacewa ganinta.
*MORSA*
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un,innalillahi wa inna ilaihi raji'un"
Shine abinda momma kawai taci gaba da maimaitawa ta kasa barin bakinta. Har yanzu
hannunta yana dafe a qirjinta,har yanzu kuma tsananin bugun da zuciyarta keyi bai
sassauta ba ko ya dakata,tashin hankalin da takeji kadan ya sauka,daga kashi dari
zuwa casa'in.
Me yakai akhnan jikin wani?.....me ma yakai akhnan filin tseren
dawakai?,me ya sanyata a jerin 'yan wasa?,yaushe ta shiga?,yaushe ta fara?,bayan
abubuwan da tasan tana yi a Niamey yaushe wannan din ya shiga cikin dabi'unta?.
Har yanzu falaak na lafe a jikinta cikin matuqar tsoro,itama qirjinta
bugawar kawai yakeyi har yanzu,gefe daya wasu siraran hawaye masu dumi suna sauka a
hankali a kuncinta.
Da gaske tana son 'yar uwarta......da gaske tana son biftu fiye da
komai,tana da matsuguni me girma a zuciyarta,bata kuma sake gasgata hakan ba sai
yanzu da wani mummunan abu ke daf da samunta. Batasan tana da girma da matsayi har
haka a zuciyarta ba sai yanzu,shin menene a baya ya lullube girman wannan qaunar da
take mata?,me yasa abaya bata fuskanci haka ba?.
Rashin tashi da rayuwa qarqashin mahaifiya daya?,ko rashin rayuwa ne
qarqashin kulawa iri daya?,ko nisan zango da tazarar dake tsakaninsu ya haifar da
haka?.
A mugun kasalance ta janye jikinta daga na momma din,sannan ta daga
idanunta tana duban cikin idon momma. Maida kallonta itama momma din tayi a kanta,a
nan falaak ta tsinci taruwar hawaye kwance cikin qwayar idanun momma din,wadda tayi
murmushi wa falaak da zummar batar dasu,saidai maimakon su koma sai suka yiwa kansu
hanya suka zubo.
Sosai falaak taji wani irin tashin hankali ya yanko mata. Momma
kuka?,yau momma ce da kuka?. Matar dake da wani irin dakakkiyar zuciya?,matar dake
da wani irin juriya da jajircewa akan dukkan wahala ko tsanani?.
"Momma....." Falaak ta fadi tana kai hannunta fuskar momma din. Riqe tsintsiyar
hannun falaak tayi tana qin bari murmushin ya bace daga fuskarta.
"Na kasa falaak......na kasa komai akan rayuwar akhnan......ina gani ina kallo a
gabana rayuwarta take tabarbarewa a hankali a hankali da wani irin mataccen salo da
zai qarasa maida rayuwarta abar qyama......na kasa falaak" Ta fada da wani irin
mugun karaya.
"Baki kasa ba momma......baki taba kasawa ba......a kullum ke din me nasara ce,a
kullum cikin cin nasara kike kuma zakici gaba da cin nasara har abada......koda
yaushe kina gayamin......akwai wani abu tattare da yaa biftu......akwai wani abu a
rayuwarta......akwai abinda yake faruwa......su waye?.....meye a tattare da ita?"
Falaak ta fada da mugun son jin komai a bayyana,kamar yadda ya zame mata dabi'a duk
shekarun da suka shude.....tun daga shekarar da hankali ya fara zuwar mata zuwa
yanzu,amsar da har yanzu batakai ga fahimtarta ba.
Tsam momma ta miqe......har a ranta tana sake jin wata sabuwar qwarin
gwiwa da iya kalaman falaak kawai.....kalaman da kullum suke shige dana
hairaan,kalaman da sune kadai qwarin gwiwarta,sune kuma suke riqe da duk wani
motsinta har kawo yanzu,har izuwa yau.
"Akwai wani lokaci yana zuwa......akwai wani zamani tafe da za'ayi kyakkyawar farar
walqiya.......a lokacin fuskokinsu da ayyukansu zasu bayyana.....inajin hakan a
jikina falaak......amma me zai hana ne?,me kuma ya hana sultane tsaiwa a
tsagina?.....ya tsaya a gefe na?"
"Ni zan tayaki momma......ni zan tsaya a tsaginki" Falaak data dora hannunta a
bayan mahaifiyarta ta fada,tana jin yaqinin da dukka zuciyarta kan abinda ta fada
din.
"Zan kusanci ya biftu kaman yadda kikeso.....zan samu kusanci da yaa akhnan kamar
yadda kika tsara......zan zama a kusa da rayuwarta momma,na miki wannan alqawarin".
A hankali a nutse kuma momma ta waiwayo tana duban falaak da dukka idanunta. Irin
wannan nutsuwar......irin wannna kamalar....irin wannan dabi'un taso su zama rigar
akhnan,irinsu taso ta siffantu dasu,koda falaak din ce zata kasance kamar akhnan a
yanzu.....indai akhnan ta kasance kamar yadda falaak take a yanzun bata damu ba.
(08187255862 lu'u lu'u paying)
Jawo falaak tayi cikin jikinta tayi mata kyakkyawar runguma tana fadin
"Allah yayi miki albarka......Allah ya hadamin kawunanku.......Allah ya baku dukkan
kariya da tsari irin tasa".
*AKHNAN*
Runtse idanunta tayi tana me lafewa sosai cikin kujerun motar. Tun
daga nan gurin.....tun kuma a sannan ta fara jin faduwa da muzanta sosai tana
zagaye duk ilahirin jikinta. Daga sanda tayoyin motocinta suka fara dagawa suna
barin gurin......mic din dake zagaye da gurin ya karade da sautin neman wanda yayi
nasarar......kwatankwacin abinda ya faru a wancan satin da ita.
First winner da suke kira a yanxu.....wanda da alama basu da cikakken
sunansa,a wancan satin war haka sunanta ake kira......sunanta ne ya karade ilahirin
amsa kuwwar ana nemanta a matsayin wadda tazo ta farko da gagarumar nasarar zubda
maza sha daya,shin a yanzun meye ya canza wannan labarin?,meye ya canza wannan
nasarar tata?.....WAYE SHI?.
Wannan tambayar ita ta zame mata tambaya mafi muni kuma mafi
barazana.......FADUWA RASHIN NASARA kalmomin da tafi tsana.....kalmomin da tayi
nisan nesa dasu tsahon wasu shekaru yau gasu a kanta.
Ta sani.....babu abinda zai canza wannan tarihin......babu abinda zai
gogeshi.......babu abinda xai sauya sai idan har ta sake gwabza wani wasan ne tayi
masa ninkin kayin da yayi mata.
Ya cinye wasan......ya kuma zama shine wanda ya ceceta daga hannun
thunder?,wanne irin asara ce wannan har haka a gareta?.
Namiji ya kubutar da ita?,duk da tarin matan dake wajen?,bayan ya jawo
mata asarar bacin suna?,anya kuwa har abada tana da maqiyi sama da wannan?
Tafin hannunta takai kan dantsenta,har yanzu tana jin shati da alamun
yatsunsa a gurin,har yanzu tana jin yatsunsa da irin tsautsarar riqon da yayi mata
sanda take fadowa. Wani malolo yazo ya tokare mata a wuya,daga haihuwarta zuwa
yanzu,babu wani d'a namiji da ya taba riqe koda farcenta ma bare yatsa ballantana
kuma akai ga dantsenta. Sultane kadai.....sultane kawai a mazaunin mahaifinta shine
ya taba samun wannan damar a dukka fadin rayuwarta.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki
kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer π³πͺ*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITAπ*
βπ½
*HUGUMANKU CE*
π *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*π
*H U G U M A*
PAGE 34
____________________________
*_M&A EGYPTIAN ABAYAS_*
*Assalamualaikum*
*_Ina dandazon tawagar gayyar MATA 'YAN QWALISA?_*
*_WADANDA SUKAYI AMANNA DA ADO SUNE MUTUNCIN D'IYA MACE?_*ππ₯»
*Ina masu son sari ko siyan daya na Egyptian abaya masu quality su iso garesu cikin
Aminci???*
*M&A EGYPTIAN ABAYA itace zabinku NA FARKO*
*kuse ABAYAS takanas kuma kai tsaye DAGA EGYPT su iso gareku cikin kasa da kwana
βπ½
goma KACAL! *
*_Ina masu son siyan abaya Amma Kuma basuda halin siya lokaci daya?_*
*_zaki iya ringa biya ahankali har ki kammala abaki abayarki cikin aminci_*ππ½
*Sannan gamasu San siyan airfreshener a farashi mai sauki muna dasu*
*muna turo da mayukan kitso original AMLA da VATIKA*
*Idan kana da wani personal shopping dakakesan ayi ma duk munayi CIKIN QASAR EGYPT
da yardar Allah*
+20 114 341 0873 ko kuma
0810 959 7791
https://chat.whatsapp.com/Hm9HBCXeyfjFDwi3OPSFqP?mode=wwt
___________________________
An haifeta abar riritawa......abar yiwa tattali.....abar gatantawa
da shagabawa,abu mafi girman daraja da tsada da agadez ke qunshe dashi.......wannan
ya sanya ta zama abar kaffa kaffa da bawa kulawa. Ganinta koda a cikin gidan ma
wani abune da ya zamana babbar sa'a ga duk wanda ya samu hakan.......bayan ta girma
kuma,wannan jinin na sarauta ya fara motsawa a jikinta,wannan izzar isar taqamar da
qasaitar da sarauta ke saukarwa ta sake mamaye jininta da kyau. A hankali ta
fahimci irin tsadarta......ta gane darajarta,ta kuma karanci tattalin da ake
mata,saita sake sawa ranta da gaske ita din ta musamman ce.....da gaske tasha
bamban da dukka mata.....harta 'yar uwarta dake da daraja kwatankwacin tata wato
FALAAK. Tana ji a ranta ita da falaak ba daya suke ba......akwai wasu tarin
banbamce babance da darajoji data dara falaak din dashi nesa ba kusa ba.
Tana jin a yau kamar ya barar da dukka wani wadannan darajoji da kima
tata da wadannan laifukan guda biyu da yayi mata. Ta yaya zata barshi yaci
bulus?,ya kamata ta bincika tasan koshi waye.......ya kamata ta fara hukuntashi ta
kunyatashi ta hanyar bashi kayi kaman yadda yayi mata a gaban idanun
mutane......kafin kuma tasa a masa mafi munin hukunci a bayan idanun kowa......a
nesantashi da qasar da take rayuwa a cikinta.
Abinda ke ranta yaqi wuce mata bare ta samu ta huta,har zuwa sanda ta
zare kayan jikinta tsaf da takeji ta tsanesu ta bada umarnin a fita dasu,kada a
sake dawo mata dasu cikin gidan,koda gilmawarsu bata qaunar ta sake gani,ta wuce
zuwa bathroom dinta da yafi kama da wani parlor din alfarmar,ta wuce cikin jacuzzi
ta sakarwa kanta ruwa me bala'in dumin da kadan ya rage yayi zafi sosai.
Batasan adadin awannin data dauka cikin ruwan ba yana saukar mata
tsakiyar kanta ba. Idanunta kan ruwan dake gudu ta rariyar,tana jin inama wannan
ranar ta wuce da dukka wani memory na dukka al'ummar da suke wajen abun ya
faru?,inama ace zata iya shafe komai ta mantar da kowa komai ya wuce tamkar bai
faru a ranar ba?.
Dukka hannuwanta ta saka tana maida jiqaqqiyar sumarta baya,wadda ta
lafe saman farar fatarta tsahonta yana kaiwa dab da mazaunanta. Iska ta furzar daga
bakinta ta cikin ruwan,tana