Showing 132001 words to 135000 words out of 168506 words

Chapter 45 - luu luu Book1 by Huguma

Qin aminta da hakan yaji zuciyarsa tayi,indai wannan mahaifiyar
ce.......wannan dai mahaifiyar data yi aike cikin girmamawa da karramawa.......tayi
aike cikin bashi dukkan cikakkiyar dama......cikin neman alfarma da qasqantar da
kai daga dukkan girman da sarauta ya bata take neman ya zamewa yaranta
malami.........indai itace zuciyarsa da ruhinsa basu gamsu ta dauki kowanne dabi'a
nata ba!.

"Dole akwai daga inda damuwan yake!" Ya fadi a hankali yana bude idanunsa gami da
motsa labbansa.

"Matan sultane nawa?" Tambayar data tsaye masa a ka kenan,yake jin ya kamata ya
sani. Tasiri aikinsa yayi masa sosai cikin rayuwarsa da yakan saurin harbo wasu
abubuwan a sanda yake ganin tafiyarsu ba daidai ba. Ya qarasa wankansa a nutse,ya
kuma nade jikinsa da babban towel,ya nade sumarsa da wani,sai fuskarshi tayi
kyau,kaman wanda yayi hakanne da manufar ado. Kusan komai ya sanya kyau yake
masa,duk da shigarsa me sauqi ce amma kuma sutura ce da kowacce zaman kanta takeyi.
Tsadarta kadai idan kaji xaka sake kallanta ka qara. Dukka jallabiyarsa daga asalin
factory din da mafi yawa suke saqa jubah,cloak robe da jallabiyyar gidan sarautar
saudiyya ne.

Wata mitsisiyar waya da duka duka batafi tafin hannun qaramin yaro ba
ya jawo,ya danna wasu lambobi dake haddace a kansa ya soma kira.

Bugu uku aka dauka,muryar maher ta bayyana cikin girmamawa.

"Matan aure nawa ne cikin gidan sarautar agadez?".

"Biyu ne obbo" Ya amsa masa,saidai kafin ya qara cewa wani abu maher yace.

"Morsa safiyya.....da mammina zaituna......morsa itace ta saka oustaz Ousmane ya
kawoka a madadinsa,mammina zaituna itace uwargidansa,kuma ita ke riqon shalelensa
akhnan,wannan ya sanya matsayinta yake na daban cikin gidan".

"Is okay" Ya fadi yana katse maher,don ba wai dogon bayani yake buqata ba. Koda
yana da buqatar yana ji zai bincika ne da kansa.........yana sake jin buqatar zama
da wanzuwa cikin gidan tun daga sanda zuciyarsa ta ayyana masa wanda yayi yaren
oromo yana da alaqa da cikin gidan.
Wayar ya janye gefe yana daukan hand drayer don tsane kansa da ita.
Basai ya tsawaita tunaninsa ba.......zaiyi wahala daukan dabi'u da ra'ayiyyikanta
ta samosu ne daga UWAR RIQONTA?.

"zai iya kasancewa" Ya bawa kanshi amsa yana qoqarin cillar da tunanin. Ya gaji da
tuna komai da ya shafi gidan sarautar,yana buqatar tuntubar nasa ahalin,yana
buqatar jin muryar nanay dinsa,wadda ita daya ke debe masa duk wani gajiya da xaiji
daga can cikin kwanyarsa akan aikinsa.


β˜…

πŸ’Ž *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*πŸ’Ž


*H U G U M A*


PAGE 66
__________________________
Bononza bononza https://wa.link/l1gcz8
Assalamu alaikum yan uwa mata masu albarka
Zuzeam ventures zatayi promo karshen wannan watan har zuwa cikin watan nan me
kamawa insha allah
-Da 6k kachal zaa baki kaza da ciccibi da gari da tsumi da gumba pills shaki matse
masu kyau da ingancin dazai sakaki dawowa ki qara harma ki kawo wani,
-Da 11k zaa baki kaza full da ciccibi da gari da tsumi da gumba, da maganin sanyi
wannan promo ne akan murnar cika shekara 10 cif da fara sanaa a online Dan haka duk
wadda take bukatar shiga cikin wannan promo Dan samun wannan garabasa to tayi sauri
kafin ta kare
Kuma ku sani tsakani da Allah zaayi wannan promo komi me inganci ne
Kyau sosai zaa baku tsakani da Allah Idan kinada 4k ma zaa baki ciccibi kawai sai
gari da tsumi masu kyau da ingancin suma,
Dan haka duk wadda take da bukata kofa a bude take
Idan kinada Yan uwa da abokan arziki zaki iya tallata masu idan kin kawo mutun goma
suka shiga na 10k kinada package din 5k
Idan kin kawo mutun goma suka
Karku manta promo kwana 3 ne an kare insha Allah
__________________________




Kadan kadan murmushi ke fita saman fuskarta ba tare da tasan hakan tana
kasancewa ba. Cikin sukuni da saituwar al'murabta take jin kanta,tana hango wasu
kwanaki kadan masu zuwa yadda komai zai zo mata da irin tsari da burin da take
muradi. Ta sani ta jima tana shan wahala ta zuciya da gangar jiki,tana jin wannan
kadai ya isa ubangiji yayi mata alfarmar bude mata kowacce qofa don isa ga sauran
muradanta na duniya da suka rage mata.

A nutse motar dake lullube da baqaqen glass tinted ta sauka daga
hannunta,ta kuma fara kutsawa cikin wani qaramar gona da yafi girman lambu ba tare
da damuwa da adadin shukokin da take takewa ba,don dama bawai anyi shukokin bane
don su amfani kansu kosu amfani wasu ba,ba kuma an dasa su sun kuma girma bane don
suci gaba da rayuwa irin rayuwar da kowacce shuka keyi don isa ga wani mataki ko
kuma muradi.
Tafiyar mintuna goma kacal motar ta fita daga cikin shukokin,wani
dan madadaicin fili ya bayyana a gabanta,wanda wani plate house ne daga tsakiyar
filin,qawatacce da wata irin qofa me kyan gaske.

Matuqin baiyi koda horna ba gate din ya bude qaramar farfajiyar gidan ta
bayyana,motar kuma ta kutsa kai zuwa cikin gidan,ta tsaya daga tsakiya,sannan mutum
daya cikin mutane ukun dake tsaye a gurin suka qaraso da sassarfa da kuma tsananin
girmamawa suka bude hannun da mammina ke zaune.

A qasaice ta sauko,wanda kafin qafafunta su qarasa direwa a qasa ta
saki tamabayar.

"Ina tamim yake?".

"Bai qaraso ba" Suka amsa mata cikin matsanancin girmamawa suna sauke kawunansu a
qasa.

"Muje na ganshi" Ta basu umarni na kai tsaye,wanda tana sauke maganar sukayi gaba
da hanzari suna mata jagora.

Qawataccen parlor ne da aka zuba wadansu irin kayan alatu da sam bana
qasar bane ba,wasu irin kayan alatu masu daukan hankali da nuna asalin tsadarsu da
nauyin kudin da aka kashe domin siyansu.

Gaba daya daga cikinsu yayi zuwa daya daga cikin rufaffun qofofun da suke
kulle,mammmina ta bishi a baya,har zuwa sanda ya murda dakin ya tura ya budewa
mammina yana tsayawa daga gefe alamun bata daman shiga.

"Bacci yakeyi?" Ta jefa tambaya ga mutumin da yake tsaye din kansa a qasa. Tambayar
tata da alama baiso ta fada a kansa ba,ko kuma baiso ta ruskeshi ba,don hannunsa ya
aza saman kansa yana shafawa a nutse.

"A'ah......yadan sha......"
"Sake bashi kukayi?!" Ta furta a tsawace cikin wata irin fusatacciyar murya data
haifar da shuru cikin falon. Ba wanda ya iya motsawa ko ya amsa a cikin su,sai
sadda kawunansu da sukayi a qasa.

"Sau nawa zan gaya muku?.......sau nawa zan maimaita muku?" Ta sake musu tambayar
da duk cikinsu ba wanda keda amsarta. Itama ta fahimci babu me iya bata amsa,don
haka ta taka da hanzari tana cusa kai cikin dakin.

Yalwataccen daki ne da aka zuba masa set ma kayan gado masu tsananin
tsada da daukan hankali,gami da dauke hankalinka daga ainihin duniyar da kake zuwa
wani ni'imtaccen guri na daban.

Daga can saman yalwataccen gadon da aka qawatashi da wani tsadajjen
bedsheets da comforter gami da pillows da aqalla sun kusa shida. Mutum ne
kwance,wata irin birkitacciya kuma hargitstsiyar kwanciya da kana mata duba daya
zakasan ba cikin nutsuwa akayita ba. Domin komai na gadon a yamutse yake,kaman
yadda qafafunsa suke zube a qasa wadanda ke sanye da snickers din da ko samun daman
ciresu ba'ayi ba.

Idanu ta zuba masa ranta tana jin yana wani irin baci. A duniya idan
akwai wani abu qwaya daya daya kasance rashin sa'arta na duniya zata iya cewa almaz
ne......yana daya daga cikin miyagun qaddarorinta.......yana daya daga cikin
qaddarorin data gaza sarrafasu har sai da sukaso yin wasan kura da rayuwarta.

"Tasheshi" Ta fadi rai bace tana duban murdeden qaton da shine ya buda mata qofar
dakin,bayan tayi dukkan qoqarinta don tayar da almaz din amma bai wani motsa ba.
Hannunsa yasa ya juya almaz yana kuma wancakalar dashi gefe,har sai da
mammina taji abun har zuciyarta.

"Kada ka sake kwata irin wannan......kada ganinsa a haka ya sanya ka dauka wani
wulaqantaccen kaya ne maras daraja......shi din daraja ce gareshi me yawan gaske".
Qas yayi da kansa sannan ya furta.

" A gafarceni" Kana yadan ja baya daidai sanda almaz ke buda idanunsa da qyar
wadanda sukayi masa nauyi.

A karo na biyu ya sake ganin inuwarta cikin idanunsa. A karo na biyu
bayan hankalinsa ya fara kutsawa sassan jikinsa yana sake maimaita masa
karatunta.....fuskarta......sunanta......alaqarsu......dangantarsu.......da kuma
tarin wasu tsarika daya soma shiryawa kansa.

Tsarikan da ya jima yana gayawa kansa ba masu cika bane......tulin
mafarkaine kawai masu qaryata zahiri.....kwatsam sai wani dan mitsitsin qyalli ya
wulqa da sauri ya fara haska masa wata qofa.

"Ana" Ya fada da wani sauti me nauyi,wanda shi zai gaya maka zahirin nauyin dake
cikin jikinsa dama hankalinsa. Idanunta ta dauke daga saman kyakkyawar
fuskarsa......wannan fuskar dake tuna mata da tarin abubuwa masu yawan gaske da
suka shude mata......wannan fuskar da kullum ta kalleta take tone wani birnannen
abu da takejin ya kamata yayi nisan da ba zata iya koda tunawa dashi
ba.......wannan fuskar dai da a haka take da wata irin kamala da nutsuwar da tasha
banban da abinda ke shimfide a ruhin mamallakin fuskar.

"Ku sashi ya dawo daidai nan da minti sha biyar kacal ku fito ku sameni a
parlor.......babu lokaci,kafin cikar wa'adin a nemomin tamim ya iskeni a nan yanzu"
Ta furta gaba daya tana juya gami da ficewa a dakin.

Idanunsa ya maida ya lumshe kaman zai sake komawa baccin,saidai kuma
wannan basamuden bai qyaleshi ba,ya kamashi yana tayar dashi. Bai musa ba ya
miqe,don shima ya gaji da kwanciyar,yana buqatar wanda zai taimakeshi yace
kwanciyar ta isa haka.

Zaune kawai tayi a falon,idanunta kafe guri daya,yayin da zuciyarta ke
shirya mata yadda lamarin almaz zai iya zama barazana a gareta muddin komai bai hau
kan saiti ba.

Mission da qudurinta akan almaz me girma ne.......wani abune da batasan
yawan adadin shekaru darare da sa'o'in data laqume tana lissafin zuwansa ba.

Wani irin murmushi me bayyana tsananin qololuwar nishadin da zuciya ke
ciki ne ya subuce mata,saita dauke hannuwanta tana goyesu a qirjinta tana kuma ci
gaba da takawa d'ai d'ai.

Iya tuna yadda al'amarin zai kasance kadai walwala yake bata......wani
irin sukuni yake saukar mata,tare da mantar da ita daya bangaren muhimmin aikin
nata,duk kuwa da cewa wancan aikin zai iya zama mafi muhimmanci fiye da
wannan.......saidai kuma ita din tana bawa MAIDA MARTANI da BADA SAKAMAKON ABINDA
KA SHUKA da matuqar muhimmanci fiye da maida hankali ga abinda zai iya jawo mata
asarar dukiya.

Daidai lokacin suke fitowa daga dakin. Almaz yana gaba yana biye da
almaz din. A karo na biyu ya sake dubanta,yana tuna shekarun daya dauka bai sake
sanyata a idanunsa ba,idan ba mantawa yayi ba shekaru shida kenan cif cif. Tana nan
a yadda ya santa a baya,ba wani abu daya canzata,tsufa ko wani yanayi da zai nuna
shekarun mutum suna tafiya sam babu ko daya a tare da ita. Idan har yana lissafi a
daidai......ganinta yana samuwa a gareshi ne bayan kowacce shekara shida,a tsahon
shekarun daya dauka a rayuwarsa,shekara ashirin da tara kaman yadda yaji ana
fadi,sau uku tak! Ya taba ganinta,wannan shine cikon na hudun.

Gani ukunnan wani gani ne da yasha banban da dukkan wani gani da
zaiwa kowanne dan adam,alaqa da kusanci da ake gaya masa wanda ke tsakaninsu har
yanzu yana jinsu a wasu abubuwa da basu gama shiga damuwarsa ba......saidai a duk
sanda zatazo ta tafi tana tsayewa a ransa da idanunsa da kuma tunaninsa,har xuwa
sanda zata cike shekaru shidan ta sake dawowa. Dubanta yake sakeyi,yana mamakin
abinda ya hanashi ganinta a shekaru shidan daya kwashe gidan prison yana
zaune?......to amma kuma sai ya taqaita mamakinsa sanda ya tuna WAYE SANADIN
FITARSA A YANZU DA YAKE TSAYE A NAN DIN?.

(08187255862 lu'u lu'u)

A nutse ta zauna tana dubansa gami da masa nuni da inda zai zauna din
shima. Bai musa ba ya zauna da yanayin jikinsa da babu wani qarfi sam sam. Wani
irin rashin qarfi da qwaya da kuma miyagun kayan shaye shaye suka dade da yin gaba
da duk wani kuzari na jikinsa.

Idanu ta sake zuba masa,kaman yadda shima ita yake kalla,saidai kafin
takai ga cewa komai tamim ya shigo bakinsa da sallamar neman izini.

Daga masarauta yake,kuma a wannan yammacin ya gama biyan salary din
masu kula da dawakan sultane,wanda kusan duka ire iren wadannan abubuwan masu
muhimmanci da suka shafi sultane a hannunsa suke. Da kayan ma'aikatan cikin gidan
ya kamata ace sune a jikinsa,amma a yanzun sanye yake da wasu kaya. Wani irin yadi
ne me kyau da tsada da aka yiwa dinkin 'yar shara,sai ya saka wata farar riga a
ciki,sai dogon wandonta mahadin kayan,yayin da kansa ya kasance sanye da wata hula
ire iren hulunan da akasan fulani na ta'ammali dasu.

Shigar shigen ta fulani ce,saidai sam shi din baya zubi ko kama dasu.
Abune me wahalan gaske ka iya gare yare ko qabilan tamim,don yayi kamanni da wasu
yaruka na qasar niger din,kaman yadda yayi zubi sosai da su.

Iya kallon mammina a gareshi kawai yana iya gaya masa matakin
farinciki baqinciki ko tuhumarta a kanka. Don haka a yanzun yana shigowa ya ratsa a
hankali ya yiwa kansa mazauni a inda yake ganin yafi dacewa dashi,wanda yana
kammala zaman duk wani mahaluki dake numfashi a parlor din ya juya ya fice,mutum na
qarshe kuma yaja musu qofar yana rufeta,sa'annan sukayi tsaye a nisan tazarar da
aka lamunce musu suna kuma gadin koda tsuntsu daka iya nufar qofar da zummar
shigewa.

"Anya zaka iya?.....anya ka shirya aikin nan almaz?" Mammina ta fadi fuskarta a
hade tana dage dukka girarta guda biyun idanunta cikin na almaz din.

Duban seconds yayi mata,sannan ya janye idanunsa daga kanta yana
sakin wani irin murmushi,hankalinsa kwance ya soma magana.

"Ana ko?.....Duk da iqirarin dangantakar da kike a tsakaninmu.....amma har yanxu
bakisan waye almaz ba......bana tunkarar komai saina shirya masa.....bana kuma
tunkarar komai saina tabbatar zan iya".

"Banga alama ba......" Ta fada tana katse hanzarinsa. Idanu ya zuba mata alamun
neman qarin jawabi da idanunsa da suke a shanye koda yaushe saboda yawan buguwa.

"Kasan a yau ya kamata nazo na sameka a shirye kana karbar horo tsarikan dana
baka?!" Tayi maganan a dan tsawace rai a bace tana dubansa. Still dai baice komai
ba,don a rayuwarsa ya tsani tsawa ko ka gaya masa magana kai tsaye haka kome zaka
bashi. Fahimtar hakan wataqila ya sanya mammina sassauta muryarta tana dubansa.

"Almaz......na baka dukkan wata masaniya,na kuma baka dukkan wani kundi......na
baka shafukan rayuwarta kaf gaba daya.......tun daga quruciyarta har kawo
yau.......me takeso?,me ta tsana?,me yafi burgeta?......shin me ya rage maka
almaz?.....me ya rage banda nazo na sameka ka fara qoqarin zama irin wannan
mutumin?.......ko kasan daga yau ya kamata komai ya fara motsawa?,daga yau ya
kamata ace komai ya fara tafiya?". Shanyayyun idanunsa ya janye daga kanta,tsaki
yakeso yaja saboda hayaniyar da take masa amma ya taushi kansa.

"Wannan yarinyar.......tsaurinta da tsarinta yayi yawa,banga kuma ta inda zan
farauto soyayyarta harta aure ni ba".

"Dama kana tunanin kyanka iya kalamanka ko wani quality dana tabbatar baka dako
daya ne zaisa ta soka ta aureka?.......a matsayinka na qasqantacce maras
daraja?!.....ni zaituna ni zan sanya akhnan ta aureka ba tare data shirya hakan
ba......ni zan tsara yadda zata mallaka maka zuciyarta bawai qoqarinka nakeso kayi
wajen faruwar hakan ba......kawai kayi qoqarin daidaita kamalarka da
hankalinka......kayi qoqarin zama BASARAKE kayi wanka da ruwan da 'ya'yan sarakuna
keyi......ka siffantu da IZZA wadda ita daya ce makamin daka iya janye hankalin
biftu akan d'a namiji. Izza gadonta ce......izza wani abu ne a jininta,so dole taso
namiji ME IZZA ba tare da tasan da wannan abun cikin ranta ba" Takai qarshen tana
nuna qirjinta.

IZZA da mammina ke maimaitawa ta sanya yaji ya kwadaitu dason ganinta.
Shima a jininsa ne......mace me izza tana burgeshi.....ba mace ba koda namiji ne me
izza hakan yana qawatar dashi,to amma dole ne kaman yadda ta buqata ya saisaita
nutsuwarsa. Zata iya hangen finsa samun alfanun komai......to amma kuma shi yana
hangen alfanun da zai samu saiya ninka nata.

"Dole kayi nisa da dukkan wani nau'in kayan maye......dole ka haqura dasu na wasu
watanni......kana iya ci gaba bayan komai ya saitu ya kammala......amma yanzu
kyanka da hankalinka mukafi buqata" Ta fadi da sautin dake nuna da gaske kowacce
kalma ke fita a bakinta.



zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki
kamar haka da naira (700) kacal*


*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer πŸ‡³πŸ‡ͺ*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261


*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITAπŸ‘‘*

✍🏽
*HUGUMANKU CE*


πŸ’Ž *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*πŸ’Ž


*H U G U M A*


PAGE 67
____________________________
*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa
wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group
namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
___________________________


Idanunta ta juyar zuwa ga tamim tana maida kallonta a kansa. Bai zaci zata
maida dubanta a kansa haka da wuri ba,sai yayi saurin sake sadda kansa qasa saboda
nuna tsantsar biyayya.....saidai kuma,can qasan ransa da zuciyarsa wata iri nau'in
wuta ce me zafi take tartsatsi.

"Nutsuwarsa tana hannunka........a duk lokacin daya sake fita daga saitinsa laifin
baya wuyan kowa saikai.......zansan yadda za'a rage maka ayyuka da nauye nauye a
masarauta......don ka samu cikakken lokacin tarbiyyantar dashi da al'adu da yanayin
sarauta ta yadda zatabi jininsa........abu na qarshe daga yau.......daga kuma sanda
zai fara fita don sajewa da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login