Showing 141001 words to 144000 words out of 168506 words
Da wannan kwarjinin cikar haiba da kamala yake takawa zuwa inda ya
bada umarnin a saukeshi. Tsam ya miqe wani irin kwarjinin haisam din yana cikashi
tun kafin ya qaraso. Wani gefen na zuciyarsa kuma mamaki ne yake kamashi,a qalla ba
aksar ba,ya haifi haisam din,bai taba zaton ganinsa yaro qarami irin haka da wannan
babban muqamin ba. A shekarunsa ba'a taka matsayin dashi yake dashi cikin national
security intelligence agency.
Kai tsaye haisam ya bashi hannu shima ya miqa masa suka gaisa.
"Bismillah" Haisam ya fadi yana masa nuni da mazauni cikin nuna alamun girmamawa.
Abun ya burge minister sosai,akwai alamun tarbiyya da kuma ilimi me zurfi a tare
dashi. Sai da minister ya zauna sannan shima ya zauna suka sake gaisawa kafin su
fara tattaunawa akan dalilin zaman.
Kusan duka tattaunawar tasu da harshen French ne......abinda yayi
matuqar bawa minister houdu mainassara mamaki. Yadda yake sarrafa yaren saman
harshensa zaka rantse haihuwar qasar French ne,harma yana so ya fishi qwarewa wajen
furta yaren kaman shine da kuma haifaffe ga yaren.
"Mun lamunce da zamanku......kuma zamu baku dukkan wata gudunmawa wajen kama wanda
kuke nema,muma din zai bamu cikakken tsaro ai da kwanciyar hankali cikin qasarmu".
Kai haisam yake gyadawa cike da nutsuwa.
"Ma sha Allah.....a madadin gwamnatin qasar Ethiopia da shugabannin NISS muna miqa
godiya a gareku da gwamnatin qasarsu,kuma in sha Allah zanyi qoqari a yau dinnan
zanyi magana da His Excellency mr President,zan shaida masa goyon bayan da muka
samu daga gareku" Murmushi houdu mainassara ya saki,haisam din yana sake burgeshi
ya miqa masa hannu suka sake musabaha. Confidence dinsa da irin qwarewarsa,fasahar
zance da yadda yake kowacce magana cike da nutsuwa suna sake kama hankalin
mainassara.
"Ina fatan zumunci bawai zai tsaya bane iya batun daya shafi aiki kawai" Minister
ya fadi sanda haisam ya masa tattakin rakiya zuwa bakin motarsa guda daya da yazo
da ita saboda kauda hankalin jama'a daga kansa.
Murmushi haisam din ya saki,bai fahimci me mainassara yake fadi kai
tsaye ba,amma with time yasan zai fahimta.
"In sha Allah.....saidai kada ka sanyani alqawarin yin ziyara a tsakaninmu saboda
yanayin aiki" Dariya kadan mainassara ya saki yana jinjina kai
"Bazan sanyaka ba,har sai sanda ka gamsu da kanka,ko ni aka bani dama nazo" Kai
haisam ya jinjina,ya kuma ja da baya da kansa yana rufewa mainassara qofar motar.
Tare suka taka da omari suna komawa ciki yana gayawa omari din wasu
daga cikin abubuwan da omari xai iya sani.
"Mun kama hanya,inaji a jikina" Omari ya fadi,sai haisam ya gyada kanshi.
"In sha Allah,komai zai tafi daidai".
Lokaci ya duba sanda yake komawa daki,akwai sauran mintuna kafin ya
fita agadez palace,don haka ya zauna ya soma lalubar number president na Ethiopia
don bashi bayanan da suka dace,kafin nan kuma ya kira bobbo muhammad daud shima.
President Amaan Mikel andom wanda haisam yayi saving number dinsa da Mr
amaan. Daya daga cikin tsayayyun shugannin qasa a tarihin Ethiopia da qasar ta
samu,jajirtattu da sukayi tsaiwar daka a kanta.
Kasancewar masarautar jimma daya daga cikin masarautun dake da girma da
qarfin iko.....kyakkyawan tsari na aiwatar da mulki da samarwa mutanenta ci gaba ya
haifar ya kuma samar da kyakkyawan alaqa tsakanin gwamnatin qasar Ethiopia da
masarautar. Uwa uba tsirowa da kuma samuwar jajirtaccen dan kishin qasa,qwararren
ma'aikacin national intelligence and security service prinsii muhammad haisam cikin
masarautar jimma,wannan ya qara zurfafa alaqa a tsakaninsu.
Samun irin haisam cikin hukumar abune me wahala,matashi me ji da gata
fikira kyau uwa uba ga sarauta a gefe,amma hakan bai hanashi jin sha'awar taimakaw
qasarsa da dukkan fikirar da Allah ya bashi ba.
Muhammad haisam din yayi ayyuka masu tarin yawa.....ayyuka masu zafi
wadanda ba'a taba yin irin su a tarihin hukumar ba,wannan ya sanya sosai mr
President Aamani yake ji dashi.
Tun ba'a wani jima ba yaso hadashi da d'iyarsa,shalelensa wadda ita daya
ce 'ya mace daya haifa wato HAANA amma a hankali da kanshi ya fahimci hankalinsa
baya ta gurin. Duk da hakan bai sanya ya janye qudurinsa ba,yaci gaba da qarfafa
alaqar zumunci a tsakaninsa da haisam,a tsakaninsa da masarautar jimma ta dukkan
hanyoyin da suka dace,yana sanya ran watarana alaqa me qarfi ta qullu tsakanin
haisam din da haana.
*MOMMA*
Daga waccan ranar har kawo yanxun da take tsaye gaban closet dinta bayan
ta ciro wata alkyabba da aka samar da ita daga wani silk material me tsadar gaske
tana sakata a jikinta......hankalinta da tunaninta gaba daya bai sauka daga kan
akhnan ba.
A kowanne rana tana sanyawa cikin sirri ana laluba mata halin da take
ciki. Koda kebe kanta da tayi na wadannan kwanakin tana kwanciya ne ta kuma tashi
da tunaninta ya take ciki?,me takeyi yanzu?,me yake gudana a kewayenta?.
Koda sau nawa akhnan zata aikata laifi.....koda meye zatayi batajin
zuciyarta zatayi nesa da ita,zuciyarta zatayi nesa daga soyayyar da take mata,wanda
wani bangarene kawai na soyayyar safeena da tayi fiffike ta sauka a kanta.
A nutse ta waiwaya tana duban falaak data shigo dakin da sallama gami
da amsa mata sallamar,rungume take da litattafanta,wani kwantaccen murmushi yana
fita saman fuskarta. Idanunta ta lumshe ta kuma budesu duka lokaci guda,a kwanakin
nan wani nutsuwa da tarin walwala momma take hanga shimfide saman fuskar falaak
din. Ga wata irin nutsuwa data sake fahimtar tana shigar falaak din,duk da dama ita
din bame hayaniya bace ko zafi surutu ko rawan kai,saidai tana da kuzari sosai da
hira ga duk wanda ta aminta ta kuma saki jiki dashi.
Sake duban falaak din tayi,dukka yanayin dressing dinta yana sake
canzawa,duk da dama can ita ba ma'abociyar shigar bayyana tsiraici bace,wannan din
tarbiyyar hairaan ce......hairaan kuma rainonta ce,duk kuwa da cewa suna rayuwa
cikin masu jajayen kunne,to amma wannan yanayin dake tattare da falaak na dabanne.
Har a cikin ranta,har kuma zuciyarta tana jin cewa inama ace biftu ce
ta samu dukkan wannan kamalar?,inama ace biftu ce ta samu wannan nutsuwar?,inama
ace biftu ce ta samu wannan walwalar?.
"Momma" Falaak ta furta a shagwabe,tana waving hannunta saitin fuskar morsa
safiyya.
"Momma wannan kallon kamar bakisanni ba?" Ta sake fada a narke. Murmushi morsa
safiyya tayi,tana qoqarin maida hankalinta jikinta gami da soma gyara rigar
jikinta.
"Meye ne haka yake sauyamin ke falaak?,ko dukka karatunne?" Wani qawataccen
murmushi daya qara bayyana kyan falaak din ya qwace mata,wata 'yar qaramar kunya da
batasan me ya haddasata ba ta taso ta rufeta,saita matsa tana taya morsa safiyya
gyara rigar jikin nata.
"Ko dadin karatun sheikh muhammad dinne?" Morsa ta sake fadi tana fatan samun wani
haske da zuciyarta ta jima tana haska mata shi.
(08187255862 lu'u lu'u paying)
Irin murmushin dazu ta kuma saki tana fara sawa morsa safiyya
maballan rigar.
"Nima ban sani ba momma.....kawai dai ya iya karatu gaskiya,yana da wani irin
fasahar koyar da karatu,bani ba hatta badeea tace bata taba jin dadin karatu irin
nasa ba.....momma ilimin dake kanshi da fasahar dake harshensa yafi qarfin koya
karatu a gida......jami'a ya kamata ya tafi cikin dubannan dalibai.....momma har
yanzu mamaki nake,jikina yaqi gamsuwa da cewa shi din gama garin malami ne kamar
kowa". Shuru morsa safiyya tayi,tana jin yadda falaak din ta tsinke da surutu har
fiye da bayaninma da momma din ta tambayeta.
Murmushi ta saka me dan sauti,a hankali ta soma takawa.
"Nagartacce ne kenan?" Momma din ta fadi ba tare data waiwaya ta dubi falaak ba,don
batason ta bata haske akan wani abu take zargi. Tasan falaak sarai,tana da wani
irin alkunya,tsaf zata tsinke zaren zancan ba tare kuma da ita takai ga gaci ba.
Idanu falaak ta fidda waje tana qaramar dariya.
"Momma......idan nace miki har yau sau daya tak ya taba kallona zaki yarda?" Har
cikin ranta momma din taji mamakin abun,amma sai tace
"Kaman yaya?,shi baya kallon mutane ne?".
" Momma.....bama kallo kawai ba,ko magana sau daya zuwa biyu take hadamu har a gama
karatun,idan kinga yana sake fuska to da aaera ne,don ko da Aafreen ba sosai
ba.....na fuskanci yana da tausasawa da tausayawa ga yara,yadda yakewa aeera karatu
daban da yadda yakewa Aafreen,nima yadda yakemin daban da yadda yakewa Aafreen,wani
irin qasaitaccen murmushi yakeyi momma,saika lura sosai kake iya
banbancewa.......me kyau dashi momma".
"Halan ke tsira masa idanu kikeyi ko?,bayan shi kame ganinsa yake?" Maganan momma
din kenan data dawo da ita hayyacinta.
Bakinta ta rufe tana dariya gami da girgiza kai,sai a sannan taga kaman
maganganun data saka sunyi yawa.
"Aah fa momma.....idan zanyi tambaya ne ko shi ya tambaya wani abun,ko idan yana
yiwa su Aaera karatu......"
"Sai kita qare masa kallo kafin azo kanki kenan ko?". Wata qaramar tsawar kunya ce
ta buga cikin kan falaak,kaman zata nutse a wajen. Ya akayi momma ta gano ainihin
gaskiyar qarshen zancan?.....da gaske ne,tana yawan satar kallonsa idan suna karatu
dasu Aafreen kafin ya sallamesu yazo kansu,amma daga nan bata iya sake
kallonsa,saboda wani mugun mahaukacin kwarjini yakeyi mata,idan yazo musu karatu
duk sai taji ya cika gurin da kwarjininsa,wannan qamshin da bata taba jin
makamancinsa ba,hannunta har rawa yakanyi wasu lokutan,tana samun lalubo nutsuwar
ta ne da zarar ta gama biya karatun jiya baice komai akai ba,alamun ta iya ba gyara
ba kuskure.
"Saura awa daya ku shiga aji,kinsan dokarsa ai ko?" Momma ta fada tana takawa don
ficewa daga dakin,ganin falaak ta daskare a wajen ta kasa cewa komai.
Saida tayi nisa sosai da gurin sannan murmushi ya kubcewa momma din.
Ta soma tariyo maganganun falaak da kuma yanayinta. Tun daga sanda taga irin yabon
da sultane yayi masa,da kuma daukansa a mazaunin mashawarcinsa na musamman taji
dari bisa dari ta yarda dashi. Ballantan Aeera da kowanne lokaci cikin hirarsa
take?.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki
kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
✍🏽
*HUGUMANKU CE*
💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
Page 71
_____________________________
*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa
wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group
namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
____________________________
Ajiyar zuciya ta sauke me nauyi,fatanta da mafarkinta a kullum
shine,Falaak da akhnan suyi auren isa da qasaita.......idan tace hakan bawai tana
nufin qasaitaccen namiji me kudi ba.....aah qasaitaccen namiji tsayayye isashe
ma'abocin sanin haqqoqin matarsa akansa. Wanda zai tausayawa ainihin rauninsu na
diya mace......zai riqesu bisa gaskiya da tsantsar amana.....koda rayuwa tazo da
juyin da duk wani abu me daraja a tare dasu zai tafi ya barsu,kyau ne mulki nasaba
ko dukiya?. Wanda bazai wulaqantasu ba bayan sun rasa dukkan wadannan
abubuwan,wanda zai zame musu mijin HUCE HAUSHI......namijin kerewa sa'a da nunawa
duniya gurin samun kulawa kariya da kuma riritawa.
GARKUWA take nema musu a sanda duniya zata iya harar
rayuwarsu.......DIRKA take nema musu a sanda duniya ke neman ruftowa saman
kawunansu.......MAFAKA a sanda rayuwa zata iya kadasu kota hargitsa su.
Indai ya zamana wani al'amari ya darsu a zuciyar falaak game da sheikh
muhammad haisam.......lallai zatayu bacci cikin nutsuwa cikin rayuwarta,zatayi
bacci harda minshari bisa samun tabbaci da yaqinin kyakkyawan zabin da falaak ta
yiwa rayuwarta,saidai fatan ta samu kwatankwacin abinda take tare dashi daga
gareshi.
Amma can qasan zuciyarta zataso ace dukkan hakan ta kasance da
akhnan. Hakeem kusan yana da wasu daga cikin qualities din daya sanya taji ta
aminta da hadinta dame martaba......amma akwai abu daya da har yanzu yake tantama a
kansa. Hakeem bashi da ZAFI bashi da ZARRA baida TSAIWAR DAKAN da take tunanin ita
kadai ce zata bashi daman juya akhnan......ita daya ce zata bashi daman tafi da ita
a sunan matar aurensa. Har a qasan ranta takejin kamar shi din BA JAJIRTACCE
BANE.....irin jajircewar da take buqata take fatan ta kasance cikin jini halayya da
dabi'un dukka mijin da zai zama mallakin akhnan din,domin sune abokan tafiyar iya
zama da wannan TAURIN KAN nata,sune abokan tafiyar wannan KAFIYAR TATA.
A wannan yammacin tana jin dukka dauriyarta ta qare,tana buqatar riskar
akhnan din a inda take,ta zauna da ita,tayi maganan fahimta da ita,irin maganan da
UWA zatayi da DIYARTA.
Ta kusa da parlor din qarshe ta samu buhaina tana faman goge
gogen falon da sassanyan turaren daya kama sassan,wanda anihinsa an samar dashi ne
daga companyn INCENSE BY KABO DAUGHTER +234 803 211 9803. Wani turare ne na
dindindin daya kama komai na parlor din. Tana tsananin son qamshin,amma ita kanta
batasan daga inda ake samo turaren ba.
"Ta fito dazun,ta zagaya ta wancan shiyyar qarshen sassanta" Buhaina ta fadi kanta
a duqe da girmamawa. Kai morsa safiyya ta jinjina.
"Buhaina" Ta kirata a sanyaye
"Allah ya baki yawan rai".
"Kuyi qoqarin riqe amana da kyau......ku kula da akhnan kaman yadda masarautar
agadez ta yarda daku ta dauki amanar abu mafi soyuwa a ranta ta baku".
"In sha Allahu......in sha Allah da dukkanin iyawarmu,sai inda qarfinmu ya qare" Ta
fada cikin girmamawa tare da jin qarin qaunar matar da ganin darajarta me tarin
yawa a idanunta.
Awa daya saura lokacin karatu ya shiga ya qaraso cikin masarautar,ya
kuma samu jagorancin me wada cikin girmamawa zuwa ga sashen guda da me martaba ya
mallaka masa a duk sanda yake da buqatar zama.
"Allah ya qara kusanci.....dukkanin gurin nan mallakinka ne halak malak muddin
rayuwarka......ga osama nan......" Ya fada yanayin nuni da wani nutsatsen saurayi.
"Me martaba yace abaka shi don yi maka dukkan wata hidima ta cikin gidan nan,kome
kake da buqata kuma kana iya sanar dani,in sha Allah za'a samar maka dashi da
gaggawa". Me wada ya fadi bayan ya gabatarwa da haisam kansa a mazaunin babban
bawan dake da alhakin kula da hadiman dake da alhakin kula da sassannin iyalai name
martaba,wanda a yanzun haisam ya shiga qarqashinsu. Koshi me wada yayi mamakin kawo
haisam din kusa da villas din iyalin me martaba haka har kusa kusa,amma bayan
kallon farko da ya yiwa haisam din,kwarjininsa ya cikashi ya kuma ga dacewa da
cancantar hakan.
Cikin nutsuwa ya gyada kai
"Ina godiya,zan sanar idan akwai buqatar wani abu"
"Na barka lafiya" Me wada ya furta yana juyawa gami da barin wajen.
A nutse abdii wanda a yau ya samu nasara haisam ya taho dashi yake
qarewa sashen kallo. Babban bangare ne da aka wadatashi da dukkan nau'in kayan
alatu......saidai bai ko kama koda kwata kwata kwatar gidansu na nan cikin agadez
ba.....ballantana har ya taka ya tsallaka ya kuma kai kimar sassan da prinsii
haisam din yake mallakinsa cikin masarautar jimma. Kallon abun abdii yakeyi yana
dariya qasa qasa,wannan shine daidai da karin maganar da yakan ji lokaci lokaci,ana
cewa wai a rashin sani kaza ta kwana kan dami. Baisan adadin gidaje irin wadannan
dama wadanda suka bigeshi a girma kyau da daraja ba da muhammad haisam ya badasu
kyauta ga mutanen da basu da muhallin rayuwa ba,yana kuma kan bayarwa,don ko a
tahowar nan tasu ana gab da kammala ginin estate guda me dauke da gidaje dubu da
zai rarrabawa mutanen da basu da matsugunni,da kuma 'yan gudun hijirar da gwamnati
ta yarda da zamansu. A yanzun aka saka masa bindiga baisan adadin gidajen da obbo
din nasa ya gina ya bayar ba,gidaje kuma complete gida da furniture da komai,bawai
kangon gida ba.
"Gaskiya ne.....nan fa babban karramawa aka yi maka ko?......da gaske ne da akace
qaramin sani qunqumi" Abdii ya qarasa fadi yana sakin dariya sosai,har yana fadawa
saman daya daga cikin sofas din parlor din.
"Abdii' ya kira sunanshi da wani irin tone da yaja hankalin abdii din,sai ya miqe
ya zauna daga dariyar da yake qyaqyatawa.
"Ka manta da rules dina?" Ya sake tambayarsa calmly yana shawagi cikin parlor din.
Gaban wani window ya isa,yasa hannu ya yaye labulen ya kuma buda window din,take
sassanyar iska ta fara shigowa ciki.
"Afwan obbo.....bazan sake ba". Abdii ya fada cikin d'ari d'ari. Burinsa su zauna a
nan din tare da haisam din,to ya tabbatar indai baiyi wasa ba kadan daga aikin
haisam ya maidashi gida. Wannan ne kuma sam bazai iya haqura ko lamuncewa
ba,qafarsa qafar haisam din,don bazai bar komai da zai cutar dashi ya rabeshi
ba,zai zame masa kaman garkuwa ne koda obbo din baya son haka,zai riqe wannan
amanar ta motii da nanay.
Idanunsa ya sauke ta gurin,wani irin guri ne me kyau yake fuskantar
gurin,wanda da ya duba da kyau sai ya fuskanci ginin benensa na sama akwai balcony
na musamman da aka fiddata tana fuskantar gurin. Wani sirrintaccen murmushin
qasaita ha kubce masa,kawai ya hango gurin da zai zauna ne yayi karatunsa cikin
nutsuwa,sai ya maida window din ya rufe yana dawowa da baya.
"Kana iya tafiya sai na nemeka" Yace da abdii kai tsaye.
Idanu abdii ya fiddo waje yana duban haisam din.
"Amma obbo......"
"Shshshsh" Ya fadi yana dora yatsansa akan lips dinsa gami da zubewa abdii din
idanunsa.
Janye kallonsa yayi daga kan haisam din,ya karyar da wuya kalar