Showing 81001 words to 84000 words out of 168506 words

Chapter 28 - luu luu Book1 by Huguma

data
zama wani abu mafi girman daraja da tsada da sultane yake dashi a duniya" Idanu
haisam ya lumshe sannan kuma ya budesu,yana jin maganganun Maher din a wani muhalli
da sam bai gane masa ba.
(08187255862 lu'u lu'u paying)

"Idan kace ita daya ya mallaka bakayi laifi ba.....duk da a zahiri diyoyinshi guda
biyu ne.......sangartacciyar 'yar gatar da ake tattalinta da dukka abinda
takeso.......da kuma dukka abinda taga dama takeso ya wanzu a yadda take muradi.
Tana hukunci tana alfarma,tana kuma zartarwa dukka a qarqashin nata ikon,saidai
wani abun mamakin kuma.......ba wani wanda zai iya baka cikakken siffa da
kamanninta,don ganinta ido da ido a gurin jama'ar yankin nan bai zama abu me sauqi
ba".

Wani abu haisam ya hadiye a hankali yana qoqarin faffasa kalaman
Maher,yanason kawo daidaito tsakanin maganganunsa dana Ousmane.

"Akwai maganganu da yawa a kanta ga wadanda ke rayuwa kusa dasu.......tana da wata
irin izza girman kai da alfaharin daya zarta na mahaifinta.......tana da tsare
tsare da dokokin da muddin zaka rayu tare da ita dole ka kiyayesu.......har ila
yau......ita daya ce tilon macen da take iqirarin har a yanxu ba'a haifi nau'in
namijin da zai dace da rayuwarta ba.......har yanzu babu namiji irin nau'in
ajinta....." Idanu abdii ya waro yana duban haisam da gabansa kawai yake
kalla,hankulansu suna rarrabuwa kashi kashi. Yanayin unguwar da suke tafiya a cikin
ta,yanayin mutanen dake kai kawo jifa jifa,sai wani dan qaramin kaso na hankalin
nasa daya miqa akan maganganun Maher. Dukkan alamu sun tabbatarwa abdii hankalin
haisam baya kai dari bisa dari,sai ya janye idonsa daga kan haisam din ya mayar kan
Maher yana mamakin me ya hana wannan baqon labarin da yasha banban da labaran da
suka saba ji da gani su dauki hankalinsa?.

"Amma ita din wacce irin halitta ce ita?......yaya take?......wani irin launi
gareta da dukka mazan duniya basu tsaya a mataki da cancantar samun aurenta ba?".

Sosai shima Maher yake da nutsuwa,irin nutsuwar da zai wahala ka
fuskanci shi din daya daga cikin ma'aikatan NISS Ethiopia ne.

"Mutum ce kamar kowa......amma nasha jin hirarta a bakunan mutane a guri daban
daban da lokuta daban daban.....mutum ce amma tasha banban da tarin
Mata........tana da wani kyau kwarjini da kebantattun abubuwa da naji suns cewa ta
cancanci zaben duk kalar mijin da takeso.....ko waye ko wanne iri ne......"

"Meye alaqar koya karatuna da yaran sarki da ita?" Yayi tambayar ta kai tsaye ba
tare daya kalli Maher ba,don yanason banbamce wasu abubuwa da baiso su zama cikin
qurataccen lokaci. Uwa uba ya gaji da jin soki burutsun bayanai a kanta......abu
guda yakeson tantancewa shine.......ta kasance bata cikin mutanen da zasu fado
hanya ko gonarshi.

Girman kai......izza da raina mutane,wasu dabi'u ne da yanzu yanzu
suke raba tsakaninsa da kai. Wasu dabi'u ne da ya tsana yayi matuqar yin hannun
riga dasu.

"Tana Niamey tana gudanar da kasuwancinta.......itace CEO na SAHEL COUTURE" A
nutse haisam ya maimaita sunan kamfanin can qasan ransa.

Kalman CEO babbar muqami ne ko matsayi a kamfani. CEO yana tsaiwa akan
komai da komai daya shafi cikin kamfanin dama wajensa......to amma ta yaya tana da
wannan matsayin fuskarta ta zama wata boyayyar aba?.

"Zanso naga wannan......." Abdii ya soma fadi,saidai baikai ga qarasawa ba haisam
din ya tari numfashinsa

"Abdii" Ya kirashi still idanunsa yana kan hanya.
"Obbo" Ya furta yana maida hankalinsa jikinsa.

Daga yanayin haisam Maher ya fuskanci baya buqatar hirar......hirar
kuma bata dace da mode dinsa ba,don haka bai sake cewa komai akai ba,har zuwa sanda
sukayi doguwar tafiya sosai.

"Ina buqatar qarin sani akan komai daya shafi cikin gidan......sauran zan bincika
da kaina" Ya fadi yana tattara hankalinsa guri daya.


โ˜…โ˜…โ˜…Cikin girmamawa kowacce qofa ta gidan da masu tsaronta mataki mataki take
motsawa tare da budewa don samun damar shigar motocin dake dauke da akhnan din
cikin ainihin ginin gidan.

Basu tsaya ba har sai da sukakai gurin ajiyar motoci na musamman na
cikin gidan,wanda ke dauke da tarin motocin sultane dana mammina da ragowar na
akhnan din,harma dana morsa safiyya wanda ba kasafai ta fiya hawansu ba.

Tun kafin motocin su kammala tsaiwa take iya hangen mammina din. Tsaye
cikin adon nan nata da kowanne lokaci yake qara nuna ita din matar sarki
ce.....matar babban mutum me alfarma ta daya sultane muhammad hammud. Iya suturar
dake jikinta kawai wani babban jarinne a gurin dubbunnan mutane,daga bayanta kuma
hadimanta ne su biyar,ciki harda yalwa ta hannun damanta.


zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki
kamar haka da naira (700) kacal*


*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer ๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261


*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA๐Ÿ‘‘*

โœ๐Ÿฝ
*HUGUMANKU CE*


๐Ÿ’Ž *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*๐Ÿ’Ž


*H U G U M A*


PAGE 40
___________________________
*_M&A EGYPTIAN ABAYAS_*

*Assalamualaikum*

*_Ina dandazon tawagar gayyar MATA 'YAN QWALISA?_*

*_WADANDA SUKAYI AMANNA DA ADO SUNE MUTUNCIN D'IYA MACE?_*๐Ÿ‘˜๐Ÿฅป

*Ina masu son sari ko siyan daya na Egyptian abaya masu quality su iso garesu cikin
Aminci???*

*M&A EGYPTIAN ABAYA itace zabinku NA FARKO*

*kuse ABAYAS takanas kuma kai tsaye DAGA EGYPT su iso gareku cikin kasa da kwana
โœŒ๐Ÿฝ
goma KACAL! *

*_Ina masu son siyan abaya Amma Kuma basuda halin siya lokaci daya?_*

*_zaki iya ringa biya ahankali har ki kammala abaki abayarki cikin aminci_*๐Ÿ™Œ๐Ÿฝ
*Sannan gamasu San siyan airfreshener a farashi mai sauki muna dasu*

*muna turo da mayukan kitso original AMLA da VATIKA*

*Idan kana da wani personal shopping dakakesan ayi ma duk munayi CIKIN QASAR EGYPT
da yardar Allah*

+20 114 341 0873 ko kuma
0810 959 7791

https://chat.whatsapp.com/Hm9HBCXeyfjFDwi3OPSFqP?mode=wwt
____________________________



Dauke idonta tayi tana sauke ajiyar zuciya,jikinta duka a mace yake
kuma a sanyaye,saboda har yanzu bata da tabbaci ko tartibin abinda zai faru da ita.

Alamun bude mata murfin motar ne ya dawo da hankalinta jikinta,ta
fidda numfashi me nauyi tana jin yadda zagin gidan yaketa wasata

"Gaba salamun baya salamun......barka da isowa zuciyar sultane.....tauraruwar qasar
agadez......me alfarma 'yar masu alfarma,wallahi ganinki kadai ya ishi bawa
alkhairi,zamanki tare da mutum alfarma ce,qarin daraja a wajensa,sukari me farin
alkhairi,bango majinginar bayi........me kyauta da hannun damanta hagunta bata sani
ba,me darajar da babu ta biyunta.....ga khadijatul kubra". Sau tari yadda zagin ya
iya tsara da jero kalamai a kanta abun yana matuqar burgeta,uwa uba kuma ba wanda
yakewa sai ita daya,koda sultane kuwa baya yiwa,ita kadai ya tsayawa yake yiwa,shi
yasa sosai take sakar masa kudi.

Mutum ce ita me amana,meson kuma mutum me amana. Wannan ya sanya zai
wahala kayi magana da ita ma ka jita a gurin koda su aisa ne,amanarta da zallar
miskilanci da izzarta ma ba zasu bari ba. Amma a yau din sai takejin kirarin nata
yana damunta har cikin kanta. Ta daga ido tana duban wanda ya bude mata
motar,mammina ce da kanta,ta miqa mata hannu kuma tana sakin mata murmushi,take
taji zuciyarta ta karye,wani qaunar matar yana sake ratsata,qauna tsantsa mara
algus a ciki.

Rungumeta tayi a jikinta tana fadin.

"Sannu da zuwa......sultane ya sakamin ke a gaba gashi ya jawo miki tafiyar
mota,Allah ya rabaki da ciwon jiki". Ido kawai ta lumshe,tana jin dadin yadda
mammina ke kula da ita,tana jin dadin yadda mammina ta damu da damuwarta,suna raba
farinciki da kuma baqinciki tare da mammina din......suna raba samu da asara a
tare,suna raba ciwo da lalura dukka idan suka sameta,wasu abubuwa kenan da bata
taba hangensu ba ga matar da ake faman kira UWA a gareta.

To wai ta yaya ma zata iya raba wannan qaunar?,wannan soyayyar?,da
wannan kulawar?. Batasan ta inda zata fara azasu akan mizani guda daya ba sam sam
sam.

A hankali ta daga kanta daga jikin mammina din tana dubanta.

"Kinsan dalilin kiran sultane a gareni?" Ta fada da muryarta me laushinnan wadda ta
qara sirancewa. Murmushi mammina ta saki tana kai hannunta fuskar akhnan din.

"Na fiki son insan dalilin da yasa ya kirakin tun kafin ki iso" Ta furta wanda har
a qasan zuciyarta hakan take nufi,saidai kuma ta lullube da wani bayanin.

"Don bana qaunar abinda zai taba farincikin wannan halitta komai
qanqantarsa.......koma meye ni nasan bazai taba yin abinda zai cutar dake ba,koda
ace fushi yayi........amma koda irin hakan zata iya faruwa,ni ina bayanki,ina kuma
tare dake a duk wani hukunci da sultane zaice zai yanke". Wannan tsadadden
murmushin nata ta saki,ta dora hannunta saman hannun mammina dake fuskarta,labbanta
dake da pink color ya motsa a nutse tana furta kalmar.

"Na gode" . Inda akwai wani matsayi a duniya da yafi matsayin mahaifiya,tabbas da
zata bawa mammina shi,don ta cancanci hakan.

"Ku kai mata su sassanta,zamu wuce ciki da ita" Mammina ta juya cikin isa tana bawa
su buhaina umarni,wadanda suke dauke da handbag din akhnan wayoyinta da wata 'yar
qaramar jakarta guda daya data saka suka zuba mata abubuwanta masu muhimmanci da
zata iya buqatarsu,saita riqe hannun akhnan sosai cikin nata suna wucewa zuwa
sassanta tana qoqarin sako mata labaran da zasu dauke hankalinta.

Sosai akhnan ta cika da mamakin tarbar da mammina ta shirya mata,tamkar
wadda tayi wata tafiya ta shekara da shekaru bata nan. Kalolin abinci da abubuwan
sha iri daban daban,gyara na musamman tasa aka yiwa dakinta dake sassan mammina
din,wanda a baya cikinsa take rayuwar quruciya harta zama budurwa sanda aka wareta
daga sassansu. Ta ajiye mata abubuwa masu yawa da tasan tana sonsu,sai akhnan din
ta tsaya kawai tana kallon komai kamar almara,kafin ta mayar da dubanta kan mammina
din.
Girarta dukka guda biyun ta dage mata alamun yes,sai kawai akhnan din
ta fada jikinta tana sakin shagwababben kukanta.

"Ya isa mana babyn sultane" Ta fadi da wani salo can baya da ake kiranta dashi.
Janyeta tayi saman wata tattausar qaramat Royal chair dake dakin tana qoqarin
kwantar mata da hankali,bata bar dakin ba sai data tabbatar ta samu nutsuwa.

"Akwai sauran lokaci,ki wanka ki huta kadan,don sultane ya fita,amma a gida yace
zaiyi sallar isha'i,kafin sannan saiki shirya ki shiga ki gaida mommanki". Duban
mammina tayi,tana jin ranta yana baci yanzun nan.

" Momma na?" Rai mammina ta hade tana kuma daga mata kai alamun eh. Yadda yanayin
mammina din ya canza ya hanata sake cewa komai,sai ta miqe kawai ta soma zare kayan
jikinta. Ta kammala tsaf ta barsu a zube a gurin ta daura towel tana wucewa
bathroom din dake da sassa biyu,toilet da bathroom din kansa.

โ˜…A nutse sanye kuma da budaddiyar abayar data rufe ilahirin jikinta ta
kuma sake qawata shigar tata da dan qaramin Malaysian hijab take qarasowa inda
morsa safiyya take.

Kebantaccen guri ne da ta ajjiyeshi kawai saboda ibada,ko da tsakiyar
dare,ko bayan sallar magariba ko bayan sallar asuba.

Daga kai tayi tana duban falaak din sanda take zama a gabanta,takai
qarshen addu'ar dake bakinta sannan tace.

"Ya akayi?". Kadan tadan yamutsa fuskarta.

"Tun dazun akace tazo.....amma banga ta shigo gaidaki ba momma" Sosai morsa safiyya
ta zubawa falaak idanu,tsoro yana neman yin tasiri a ranta. Tsoron wani abu
takeyi,tana tsoron faruwar wani abu.....wannan abun kuma da idan ya farun zai sake
jaddadawa zaitun nasararta.

Wannan jarumar zuciyar tata ce ta motsa,ta kuma mamaye duk wata
fargaba tata. Murmushi ta saki tana ajiye dan qaramin littafin azkar din dake
hannunta.

"Annabin rahama S A W yana cewa:- duk wanda yayi imani da Allah da ranar lahira,ya
girmama baqonsa.....biftu a yau da kuma kwanakin da zatayi tabar gidan nan duka
baquwarmu ce.....ke me kikayi don girmamata a matsayinta na wadda take gaba dake?"
Morsa safiyya takai qarshen maganar tana duban idanun falaak. Idanu falaak din ta
zubawa momman tata,so take ta bambance kariya momma take bawa akhnan ko kuma dai
tana fadin abinda da gaske haka ya kamata ya kasance?.

Ta karanci hakan a tattare da ita.......ta kuma gane me takeson
karantowa,don haka ta sake lullubeta.

"Kin manta?,kinmin alqawarin kusantar da kanki da ita?,kinmin alqawarin zaki tayani
ta koma kamar yadda nakeso?,ina wannan alqawarin falaak?". A hankali sai fuskar
falaak din ta washe daga wani kaso zuwa qasa da hakan.

"Na sani,nice nayi alqawarin,kuma zan cikashi momma" Dubanta morsa safiyya keyi
tana jinjina kai. Koda falaak bata daukota a komai ba,amma ta dauko dabi'arta ta
cika alqawari......ta dauko halayyarta ta cika magana muddin ta fadi zatayi,don
haka ta bita da murmushi.

"Naji dadin hakan,Allah yayi miki albarka,ya kuma baki damar cikawa kaman yadda
kika dauka".
"Ina zuwa" Falaak din ta fadi tana miqewa a nutse da zummar ficewa a dakin,sai
hakan ya tunawa da morsa maganan da sukayi da ustaz Ousmane dazu.

"Gobe bayan sallar la'asar sabon malaminku zaizo,zaku dinga zama karatu juma'a da
asabar,qarfe hudu da rabi na yamma zuwa shida,awa daya da rabi zai dinga yi ba
kaman ustaz Ousmane ba da yake awa biyu ba harda rabi......yana da
qa'idojinsa,bayaso kuma a karya masa su". Fadin qa'idojin ya sanya falaak
dakatawa,ta kuma waiwayo sosai tana duban momma fuskarta na yamutsewa.

Fata take kada dokokinsa su zamana masu tsauri kuma masu takura......don
muddin hakan ya kasance bata jin tafiyarsu zatayi tsaho. Ta sani,ba wani hukunci da
zai musu momma ta qalubalanceshi,duk dama bata tunanin koda kallon banza akwai
malamin da zai iyayi musu ballantana kuma takai ga hukuntawa.

"Dole ku dinga rigashi isa gurin karatun kafin ya qaraso.....idan ya rigaku isa har
sati uku a jere akwai hukunci" Momma ta fadi murmushi yana subuce mata. Haka kawai
takejin abun da malamin yana burgeta. Ba abu bane me sauqi don zaka koyar da yaran
masarauta......masarautarma diyoyin cikin sultanr ka rattaba musu dokoki hankalinka
kwance,bin dokokin kuma shine damarsu ta daukan karatu a wajenka.

"Momma......baisan......"

"Ya sani,kada ma ki tambayeni,amma hakan shine daidai,kuma a raina naji cewa sai
yanxu kuka samu malami irin malamin da nakeso,duk da ban sanshi ido da ido
ba.......girmama karatu akan dalibi dashi.....kasan girma da martabar abinda ake
koya maka,kin manta ne?". Kai falaak ta jinjina,duk da haka tana jin kamar ya cika
jaye jaye da yawa.

"Allah ya kaimu" Ta fadi kawai tana juyawa tana fita a dakin,a qasan ranta kuma
tana juya wanne irin malami ne wannan?.

Duk da takan shiga kitchen lokaci bayan lokaci,don girki yana daya
daga cikin abubuwan da sukan bata nishadi,amma sosai a yau ma'aikatan dakin girkin
sukayi mamakin shigowarta da kanta. Sun sani,tana da sauqin kai irin wanda sam ba
zaka hadashi da na 'yar uwarta ba.....tana da sassauqar mu'amala da kowa ma zata
iya mu'amalanta.

"A hadamin duk wani abu me muhimmanci da akasan yaa biftu tana son ci yanzun
nan......nimra ki zubasu a kwando zamu wuce sassan mammina".

Sak kowa yayi cikin kitchen din,har ita da kanta ta karanci haka,saita
dakata da zabar inibin da aka shigo dashi yanzu cikin kwando me yawa ta kalli
fuskokinsu.

"Lafiya dai?" Ta tambaya tana son jin amsa.

"Ai ranki ya dade.......ba wanda yasan abincin da tafiso taci kaf gidan
nan......inajin illa mutum uku,giwa mammina......buhaina sai birra" Girarta tadan
yamutsa abun yana daure mata kai. Wasu abubuwan idan aka fadesu a kanta sai taji
tamkar ita ke mulkin bawai sultane ba. Tayi shuru tana nazari kafin ta sake cewa

"Koda dan wani abu qanqani da tafiso ba wanda yasan satar amsarsa?" Shuru kitchen
din ya sake dauka,kaman ba za'a samu me magana ba kafin nimra tace

"Abu daya zuwa biyu na gani......ana yawan kai madara sashenta,sannan ana yawan
shiga da kayan itatuwa,duk da ba kowanne nau'i naga ana shiga dashi ba" Kai falaak
ke jinjinawa.
"A shirya iya wadannan ababen.......a hada da kilishi da zuma,in kin kammala nimra
ki sameni a bakin mararraba".

"An gama Allah ya taimakeki" Ta amsa cikin girmamawa hadi da rusunawa sannan ta
juya tana komawa can cikin kitchen din,ita kuma falaak din ta fice.

Da mutum uku suke nufar sassan mammina din. Duk da dare ne amma kowacce
qofa kowanne taku cike yake da dakarun dake tsaron sassan. Duk inda tazo giftawa
gaisuwa suke kaiwa sannan su bude mata hanya ita dasu nimra su wuce zuwa ciki.

Daidai lokacin da akhnan din ke zaune cikin dakin nata,tana saman
wata armchair. Ta dora habarta kai hannunta riqe da wayarta tana scrolling a
hankali. Wani statistics na company neesha ta aiko mata take dubawa. A zahiri tana
kallo ne kawai,amma a badini ba abinda take fahimta,tana dakon jiran kira ne kawai
daga sultane,daga ina kiran zaizo?,me kuma zai biyo bayan kiran?.

Da sallama a bakin falaak ta tura qofar dakin tana shiga. Bata dago ba
akhnan din bata kuma juyo ta dubi me shigowar ba. Kawai tana son gane waye ya keta
mata doka ya shigo mata daki haka Kai tsaye a sanda ta buqaci kowa yayi nisa da
ita?.

"Yaa biftu" Sunan da aka kira din ya kawo mata zaton falaak din ce,saita miqe ta
zauna sosai tana kuma waiwayowa ga falaak din.

Idanunsu ne suka gauraya dana juna,dukkaninsu kowa abu na daban na sauka
qasan ransa.

Ta dauka zata rufe falaak da fada ne kaman yadda ta qudirta a ranta
sanda ta miqe ta zauna,amma sai taji wannan qudurin yana zagwanyewa sanda falaak
din ke qarasowa cikin dakin bayan ta ajiye kwando na biyu data amso daga hannunsu
buhaina da iyakacinsu wancan parlor din na farkon farko.

Har yanzu da wannan murmushin akan fuskarta,saita tako kanta tsaye ta
qaraso gabanta ta zauna tana tura mata kwandon.

"Naji kinzo......tun daxun banga motsinki ba,nace bari na shigo mu gaisa na karbi
tsarabata kuma" Tayi maganar da irin yanayin daya sanya take akhnan din taji girma
ya motsa mata. Irin girman da yaya takeji akan qannenta,irin girman da yake tuna
maka akwai wasu 'yan uwa qasa da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login