Showing 159001 words to 162000 words out of 168506 words
qasaitaccen table aka zuba duk wani kayan buqata na hadawa da kuma shan
coffee.
Sai daya sha cup daya sannan ya shimfida abun sallah. Wuturi daya rage
masa yayi,ya zauna yayi tarin addu'o'insa sannan ya zame yana barin gurin.
Sai daya daidaita tsakiyar gadon bayan ya ajiye abokin hirarsa wato
coffee a gefe,ya rage hasken wutar dakin duka,ba hasken da kake gani saina system
din dake gabansa.
Cikin mintuna talatin ya kammala rubuta duk wani experience nashi na
ranar,ya soke yatsunsa cikin na juna ya tallabi kumatunsa dasu ya zubawa rubutun
idanu yana sake bibiyarsa.
"Akwai wani baqon kallo da emotions a tattare da ita,akwai wani reflection dake
nuna connection tsakaninta da wanda ka kira da TAMIM. Connection na tsananin jituwa
ko kuma na akasin hakan.....yaya akayi wannan bawan dake tsaye bakin window sunansu
yazo daya da wanda ya shigo parlor din sultane?......indai har ba amintaccen
sultane ko wani daga cikin mutum ukun dake ciki ba......mammina......ita akhnan din
da tamim na biyu daya shigo ba.....bata yadda za'ayi da tarin masu tsaron dukka
qofofin ya samu isa wannan gurin dake da matuqar tsaro.
Idan har kuma amintaccen ne na gaske,me ya hanashi qarasawa cikin
kanshi tsaye?,me ya tsaya ji?,me ya tsaidashi cikin yanayin dake nuna zallar rashin
gaskiya tattare dashi?.
Gumin fuskarsa a sanda yaji motsinsa......kallon dake cikin idanuwan
mammina sanda ta ganshi,me yasa bata qaunar baqo da zafi irin haka?,bayan masarauta
ce.....cike take da tsari da yanayi na amsar baqi a kowanne lokaci,cikin kuma
kowanne yanayi?,me yasa yanayinta yake nuna zallar kishi?,kishin kada kowa ya
kusanci sultane?,kishin kada kowa ya fita kusanci dashi?. Yaga haka a idanunta
sanda akhnan ke yunqurin yin magana da mahaifinta......kallon data masa yasha
banban da wanda ta yiwa tamim ME YASA?. Me yasa take matsa hannuwan akhnan a sanda
take yunqurin roqar mahaifinta?.....me yasa ta hanata magana?,me yasa bazata barta
ba?. Siririn tsaki yaja,yana tuhumar zuciya da kwanyarsa. Wannan din ba abinda ya
shafeshi bane,abinda ya shafeshi kadai shine yayi binciken dukkan wani dake da
alaqa da sultane dama masarautar......ya kula da motsi da takun kuwa,ya kuma zaqulo
wanda suke nema muddin yana a cikin masarautar yana kuma rayuwa. Amma baya ga
haka,dukkan wani abu da zai faru.....dukkan wata alaqa ba huruminsa bane shigarta.
"Tabbas akwai Oromian.......akwai Ethiopian cikin masarautar" Ya fadiwa kansa kai
tsaye yana tuna lafazin mutumin daya fara gani a balcony.
Yaren oromo ne fes saman harshensa......da accent din da sai haifaffen
yaren kawai zai iya lanqwasa harshensa izuwa wannan yanayin.
Idanunsa ya sake qanqancewa yana dawo da sautin muryoyinsu dukka
cikin kansa. Akwai sautin mutum daya da harshen sa ya karye sosai.......ya kuma
banbanta dana sauran mutum ukun dake wajen,lanqwasuwar harshen tasha banbam data
saura.
"Nasrumminallah" Ya furta yana motsa labbansa masu glowing dinnan a hankali.
Idanunsa ya maida ya lumshe,yayi relaxing bayansa jikin kujera,dakin
yayi shuru kamar yadda ilahirin gidan ya dauki shuru,yayi relax sosai kaman me
sauraren wani abu,saidai kuma baya iya jin komai daga shurun da gidan ya dauka,sai
qananun qwari dake bada mabanbancin sauti,da kuma qananun sautukan na'urori na Ac
da sauransu da basuyi qarfin da zasu takura kowa ba.
Nauyi idanunsa sukayi,kaman bacci yana son daukarsa,take duhuwar dake
cikin idanunsa ta ingizo masa hotonta fes cikin gizanniya.
"Subhanallahil azeem" Ya furta da sauri da wani qaramin amo da iyakarsa qasan
maqoshinsa kadai. Zama yayi sosai saman sofa din,ya sanya yatsansa babba da dan
manuni yana matse idanunsa,tamkar wanda hakan zai taimaka masa wajen fidda hotonta
daya gilma masa a idanunsa.
Ya dauki tsahon wasu mintunan a haka,sannna ya bude idanun nasa da
suka kada suka sauya launi yanajin qirjinsa yana masa nauyi.
Yana da wani yanayi da dabi'a dake saurin shiga kansa. A duk sanda yaga
gilmawar wani abu daya shafi mace yakan zauna masa wani lokaci cikin kansa,wannan
ya sanya yake cire kansa gami da nesanta kan nasa daga dukkan wani lamari daya
shafesu. To amma a wannan karon besan me yasa abun keson dadewa cikin kansa ba tare
daya barshi ba.
"Hasbunallahu wa ni'imal wakeel" Ya fadi da cikakken nutsuwa yana qarasa kashe
system din tasa,sai kawai ya dauki wayoyinsa ya zura bedroom slippers dinsa yana
zarcewa dakin bacci.
β
*AKHNAN*
Kayan jikinta kawai ta cire ta sauyasu da kayan bacci. Pyjamas masu
rigar data tsaya iya cinya me dogon hannu,silk ne me dogon wando daya zauna mata,ya
fidda shape din jikinta tamkar bawai kayan bacci bane a jikinta.
Lamo kawai tayi saman gadonta,cikin jibgegen duvet dinta da tsabar
laushinsa take sake nutsewa a dukka motsin da zatayi. Wani irin zafi zuciyarta keyi
mata,a yau sultane yayi mata abinda bai taba yi mata ba,wanda ya soma jefa shakku a
cikin ranta game dashi. Anya kuwa akwai wannan soyayyar?,akwai wannan qaunar?. Anya
kuwa morsa safiyya bata shiga tsakiyar wannan alaqar ba?.
Furuci da kuma tsaiwar da sultane yayi akan hukuncinsa ba tare da nuna alamun
samun sassauci daga gareshi ba,wani abune daya bata matuqar mamaki. Wani abu ne
kuma daya zo mata a bazata,don bata taba kawowa da tsammatar hakan daga gareshi ba.
Saidai a jikinta take jin koma yaya ne ba zata taba yarda ta zama mallakin wani
hakeem ba,koda kuwa hakan zai sababba fushin sultane ko kuma daukan mataki daga
gareshi,wannan ya sanya take jin abun kamar baikai nisan da hankalinta zai tashi
sosai ba,duk da hankalin nata ya gaza kwanciya yadda ya dace ace ya kwanta din,duk
da alwashi da maganan da sukayi da mammina bayan fitowarsu na qarshe.
"Kada ki damu ko kuma ki daga hankalinki,ni bazan gaji ba wajen nema maki da kuma
sama miki farinciki da dukkan qarfina,da kuma dukkan iyawata muddin ina raye. Gobe
ma zan koma,zan kebe da sultane,zan kuma tabbatar da cewa ban baro gurinsa ba saida
labari me dadi".
Wannan issue din ya kamata ace yafi damunta fiye da komai,amma saita
tsinci zuciyarta tafi jin zafi da qunci kan abinda sultane yayi mata a gaban
BAQUWAR FUSKAR da har yanzu take ji a jikinta bawai baquwa bace......tana ji a
jikinta tasan fuskar......tasan kuma idanun.
Maganganun da sultane ya fadi a kanta a gabansa ya dawo mata,qirjinta
ya wani quntata guri daya,har a yanzu tana jin yadda ta wani muzanta,kaman a yanzu
sultane keyi wadannan maganganun.
"Idan ya kasance shine ne na hippodrome fa?" Zuciyarta ta jefa mata tambayar data
tilasta mata ture bargon da take ciki,ta kuma miqe zumbur ta zauna saman tattausan
gadon nata,kafin kuma ta janyo jikinta a hankali tana sauka daga saman gadon,tare
da bin makunnin fitilar dakin ta sake kunnata.
Ta yaya zata bari wani mutum qwaya daya ya gagareta a rayuwa?,abinda
kaf cikin tarihin rayuwarta bata taba samun hakan ba?....ta yaya wani dan adam zai
shigo qasar da mahaifinta ke mulki da ita ya dasa mata abubuwan da zasu tattare
dukka nutsuwarta suyi gaba da ita?......ta yaya zata bari hakan ta kasance?,wanda
kamar 'yar manuniya ce ta cewa ya raina girman izza da matsayin da take
dashi,daidai da daga mata yatsa saitin idanunta.
After dress dinta dake fidda sassanyan qamshinta daya kama duk wata
sutura tata ta sanya,ta yane kanta da siririn mayafinta,ta murda qofar ta fito zuwa
parlor din farko.
Kai tsaye ta isa ga landline,ta kumayi kira zuwa dakin birra. Cike da
mamaki birra ta daga kiran ta saka a kunnenta,bata kuma barta tace komai ba ta aza
mata umarnin dalilin kiran.
Ki dubomin tamim duk inda yake......ki kuma shaida masa ina buqatar
ganinsa yanzu yanzu".
"An gama" Ta fada a ladabce amma cike da tarin mamaki.
Wayar ta mayar ta ajiye,saita sake takowa zuwa parlor na biyu. Duk
girman gurin ba digon tsoro a tare da ita,kasancewar ta sani kewaye take da tsaron
daba wani dan adam indai ba aljani ba daya isa ya iske inda take. Cikken motsi
kawai mai qarfi ya isa ya kawo masu tsaron qofofinta zuwa inda take.
Da wani irin yanayi take kaiwa tana kawowa cikin kebantaccen gurin data
saba ganawa da tamim din. Cikin lokacin ba abinda take ji take kuma gani sai mugun
dadewa da yalwa tayi,wadda ta aika ta kira mata tamim a duk inda yake.
Duk da cewa a zahiri bawai dadewa yalwa tayi ba,to amma qaguwa da
ganinsa a gabanta ya sanya take gani kamar jiran yayi tsaho da yawa.
Wani irin zafi takeji a jikinta da zuciyarta gaba daya idan ta tuna cewa
MATSALA zata iya kunno kai. Tana jin kamar akwai abinda yake ba daidai ba,akwai
abinda yake buqatar ta sanshi ko ta gyara zamansa ya zamana a daidai.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Sallamar tamim ta sanyata Waiwayawa da sauri,bata kuma tsaya amsa
sallamarsa ba tace.
"Shigo.....qaraso ciki". Cikin sakanni ya bayyana,idanunsa cikin na mammina. Kanta
ta jinjina a hankali tana hango wani abu cikin idanun tamim din. Ba haka ta saba
ganin fuskarsa dama yanayinsa ba gaba daya,sai take hango kamar akwai wani abu daya
taba ranshi.
"Waye shi?" Ta jefawa tamim tambayar kai tsaye,kaman tana da tabbaci da masaniyar
cikakken sanin tamim gareshi.
Kai tamim ya jinjina,ya kuma matsa gefe yana neman gurin zama. Tun daga
sanda ya baro gurin sultane bai samu zama ba ya shiga laluben wayeshi?. Ya sani
tabbas zata buqaci sanin hakan,daga ganin irin kallon dake fitowa daga idanunta a
kansa yasan hakan zata kasance. Haka kawai shima yaji wanzuwar matashin a gurin ya
sauya yanayin gurin dana jikinsa ma gaba daya. Babban abinda ya fara fusgar
hankalinsa shine.......kwarjinin da yaji ya masa,ya kuma cike gurin gaba daya duk
da cewa a qalla zai bawa matashin shekaru kusan ashirin,amma sai yakejin wani irin
girma nasa cikin idanunsa. Uwa uba......abu mafi girma shine wanzuwarsa cikin
masarautar ba tare da shi ya sani ba.
Babu wata halitta da zata wanzu cikin masarautar,ta yaro ko
babba.....mace ko namiji saida saninsa,saida cikakken sani daga gareshi,sanin kuwa
daya hada da inda ka fito,me zaka shigo yi?,adadin ikon da zaka iya samu cikin
gidan,wa'adin zamanka dama fitarka dukka suna tafin hannunsa qarqashin tsananin
qwarewarsa wajen aiwatar da dukkan wannan abun cikin hikimar da ba damqa masa
alhakin hakan akayi ba,shi ya baiwa kansa wannan girman,shi ya baiwa kansa wannan
matsayin.
To amma dukka awannin daya shafe yana bincike a kansa abu guda ya samu.
Malami ne da gaske,kuma dan cirani,maras wani gata ko galihu da yawan neman ilimi
ya fado dashi hannun oustaz Ousmane,sukayi musanye a sanda oustaz din ya samu daman
fita qaro karatu. Bashi da cikakken muhallin zama,don babu wanda yasan taqamaimen
inda yake zaune,wannan ya sanya sultane bashi gidan da yake maqotaka dana gimbiya
akhnan. Wadannan sune bayanan da tamim ya yiwa mammina.
Ido ta zuba masa tana jin tantama akan bayanansa. Duk kuwa da cewa ta
sani,batun qwarewarsa gurin iya bincike da kuma bin diddiqi akan komai bayyananne
ne,yana daya daga cikin dabi'unsa da halayensa da take matuqar so take kuma
alfahari a tattare dashi,to amma wannan binciken haka kawai takejin bai kwanta mata
ba. Kanta ta dauke,tayi kuma taku uku zuwa gaba tana girgiza kanta a nutse
"Bazan qaryata abinda ka binciko ba.....saidai wannan binciken ba shine ainihin
abinda yake boye ba,inaji a jikina koda ba wani boyayyen al'amari a tattare
dashi,to ba shakka akwai wani abu da zai iya faruwa a nan gaba,don haka inaso ka
sanya ido a kanshi da dukka wani motsinsa,banaso ka bawa kowa wannan aikin,kai
nakeso ka gudanar dashi da kanka,har zuwa lokacin da zan gamsu da cewa ba komai a
tare dashi din........." Tayi maganan tana takawa zuwa ga hanyar da zata sadata da
ciki,sai kuma ta tsaya cak.
"Akwai alamun wani motsi daga K'ASATA?" Kai ya jijjiga.
"Babu,ba wani motsi,komai ya tsaya cak,komai kuma ya lafa,al'amura suna ci gaba da
gudana,a hankali sunansa da faruwar al'amarin yana bin awanni da shekaru yana
salwancewa". Tsayawa tayi kaman me nazarin wani abu,murmushi kuma yana qwacewa daga
kan fuskarta.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki
kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer π³πͺ*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITAπ*
βπ½
*HUGUMANKU CE*
π *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*π
*H U G U M A*
PAGE 80
___________________________
*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa
wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group
namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
____________________________
"Inajin kamar lokutan sa'ata suna dab da haduwa guri daya......anya ba zamu
gwada wani abu ba?,.....idan muka dace sai ya zame mana hanya mafi sauqin da bamu
taba zata ba,hanya mafi sauqin da muka jima muna jiranta shekara da shekaru"
Zamewa kadan tamim yayi daga saman qafafunsa,yana jin zuwa yanzun ya kamata shima
ya soma motsa nasa qudurin,quduri guda daya da yakejin dukkan wahala da bautar nan
ta shekara da shekaru shine kadai zai wanke masa.
"Ba laifi bane.....kuma a shirye nake na tsara hakan,a shirye kuma nake na tsara
yadda komai kasance.......amma ina da wani shakku da kokwanto kadan" Ya fada
fuskarsa da muryarsa suna suna muhimmancin abinda zai fada din.
"Kamar?" Mammina ta tambayeshi tana riqe da labule.
"Bazai zama matsala ko cikas ba?,bayan cikar ko kusa da cikar muradanmu idan na
buqaci tukuicin farko daga gareki?". Ido ta zuba masa tana jin kamar ya raina
girman izza da isarta,kamar ya raina dimbin arziqin da ta mallaka ita daya ranta.
"Tamim........kana manta wace GIWA?,kana manta wace izzatu?,sunan GIWA kana
taqaitashi ne kan ma'ana guda daya tal?". Murmushi yadan saki yana kada kai.
"Wane mutum wane aikinsa.......ba daya da nake musantawa a ciki......girman
tukuicin da zan buqata ne nake ganin kamar........"
".....kamar me?" Ta fadi cikin fara jin haushin maganganunsa. Qasa yayi da kansa
cikin qasqantar da murya.
"Allah ya huci zuciyarki ya baki yawan rai......tukuicin DAN MUTUM nakeso......shi
zan buqata giwa,ban sani ba,a sanda na buqaci hakan zaki iya daukoshi daga hannu
daga kuma mallakin ko waye ki maidashi mallakina?". Murmushi ya sake subuce
mata,tana jin babu wani abu me sauqi sama da haka. Sanda yake gaya mata sai lokaci
yayi.......sai lokaci yayi zai gaya mata tukuicin da yake buqata,wani lokaci takan
jima zaune tana hasashe da tunanin me dame tamim zai iya cewa yanaso a matsayin
sakamakon bauta na shekara da shekaru?.....amma a yanzun ta samu wani irin tarin
sassauci data jima bata jishi ba.
"Qarqashin mallakata akwai tarin jama'a......akwai tarin bayi nau'i nau'i,ka zabi
dukka adadin dakaga dama,adadin da yayi maka.......zaka zama mutum mafi rabauta a
duniya daga randa BURIKA BIYU na zaituna suka gama cika cif cif qarqashin
jagorancinka,na maka alqawari zan baka duk abinda kake buqata".
β
***Da kallo birra ke binsa sanda taga fitowarsa daga shiyyar mammina. Tadan sake
kallon sararin sama tana qiyasce nisan dare a wannan lokacin. Ko ba'a gaya mata ba
tasan cewa dare ya soma shiga sosai,kuma doka ce a dukka fadin gidan na haramtawa
kowanne jinsi shiga sashen da bana jinsinsa ba,daga sanda akayi kiran sallar
magariba. Abu mafi ban mamaki ya fito ne daga sassan da sukafi kowanne tsaro,sukafi
kowanne dokoki tsaurara,kuma a cikin dare irin wannan?.
"Gimbiya akhnan ce take kiranka" Ta fada tana rusunar da kanta ganin irin kallon da
yake binta dashi,fuskar nan mai cike da qasumba a dinke tsaf.
Sosai yaji batun yazo masa banbarakwai,saboda wannan shine karo na
farko da ya soma jin hakan,sai kawai ya gyara damarar jikinsa da baya rabo da ita
kulli yaumin yace.
"Muje" Tayi gaba yana biye da ita a baya.
Sanda suka isa a farfajiya ta barshi,ya soma bin gurin da kallo,don
kuwa wannan shine karon farko da qafafunsa suka fara taka sassanta. Sassanta yafi
kowanne sashe tsananin doka tsaro da kuma qa'idojin da SULTANE kadai aka yarjewa
aga qafarsa a cikin gurin. Da idanunsa yake bin ginin da kallo da mamakin yadda aka
tsarashi cike da tsaro da kuma ado da qawa.
Zubewa tayi qasa tana shaida mata isowar tamim din,sai ta miqe tana
gyara lullubin after dress dinta data rufe ko ina a jikinta tana fadin.
"Muje".
Da hanzari ya sauke kanshi daga nazarin da yakeyi yana maidawa inda ya
jiyo takunsu,da sauri cikin tsananin girmamawa ya sauke kanshi,sannan ya karya
gwiwarsa guda daya ya kaita qasa yayin daya cake tafin qafarsa a qasa da dayar
qafar yana yin qasa da kanshi.
Wani girma takeji yana ratsata a duk sanda yayi hakan a gareta. Yana
cikin mutane da suke lissafinta na gaba gaba da sukafi kowa iyawa da sanin yadda
zasu girmamata.
"Tashi ka zauna" Tace masa bayan ta zauna,saiya tashi din amma ya tsugunna ne saman
qafafuwansa.
"Muhimmin aiki nake tafe dashi......kuma nakeso idan ka fara shi ba dawowa saida
cikakken amsa da bayanai masu gamsarwa".
"Umarninki kawai nake jira" Ya fadi kai tsaye,yana jin qarin samun wani matsayi
daban yana tunkaroshi,yana jin cewa shi din me nasara ne da har gimbiya akhnan zata
nnemeshi cikin dare irin wannan da buqatunta.
"Basai na tsaya tambaya ko tantama ba......tabbas kana da labarin tseren dokina na
qarshe a hippodrome da wani baqon mutum dan wata qasa?". Kansa ya gyada a hankali
yana sadda kanshi qasa,sanin halaye da dabi'unta,da kuma